Showing 234001 words to 236327 words out of 236327 words
igiyar akayi a wuya, tare da ɗaura ta kan wani dogon abu, hankalin kowa da kowa ne ya dawo filin ya ɗau tsit babu abinda kakeji sai ihu da shewar Hafeezah, bata ankare ba kuwa aka ja igiyar dake rataye da wuyar ta sama kafin a tunkuɗe abinda ƙafafun ta ke kai, take filin ya ɗauki sautin *ALLAHU AKBAR* babu ƙaƙƙautawa, shure-shure Hafeezah tayi tayi tana ciccila ƙafafu a haka har ta gama ƙafafun suka saki haka ma jikin ta da alamu dai rai yayi halin sa.
Wata iriyar nannauyar ajiyar zuciya sarki ya saki yana sadda kai ƙasa, wasu 6oyayyun hawaye ne suka zubo masa jikin sa yayi bala'in sanƴi, da kyar ya iya miƙewa ya tashi ya bar wurin a sanƴaƴe fadawan sa na mara masa baya.
B'angaren YAZEED kuwa jin ƙuwa da tashin sautin *Allahu Akbar* ya tabbatar masa da cewa an yankewa mahaifiyar sa hukunci.
Zamewa yayi ya zauna daga tsayen da yake wasu irin hawaye masu zafi na tsiyayo masa, riƙe kansa dake barazanar 6allewa yayi da hannu bibbiyu yana tsoron irin makomar da mahaifiyar sa zata tarar, a haka ya wuni cikin ɗakin ba tare da ya fita koh da jana'izarta bane ba.
*BAYAN SATI ƊAYA*
________Har izuwa wannan lokaci basu gama fita daga cikin shock ba dukda kuwa Hafeezah mai laifi ce a wurin su amma hakan bai hana jikin su gabaɗaya yin sanƴi ba da rashin ganin ta cikin su ba.
Sosai YAZEED ke ƙoƙarin yakice abinda ya faru da ita daga cikin zuciyar sa, koh kaɗan baya son tunano ta sai dai kuma a kullum baya gajiya da yi mata addu'a da kuma nema mata sassauci wurin Ubangiji.
ZEEYAD ma hakan take a wurin sa, gabaɗaya ya rasa meke yi masa daɗi, zuciyar sa cike take da jimamin mutuwar Hafeezah ga kuma tausayin ɗan uwansa da ya cika masa zuciya, though a kullum DEENAH na iya ƙoƙarin ta na ganin ta kwantar masa da hankali, sai dai hankalin nasa yaƙi kwanciya dan kuwa tun bayan yankewa Hafeezah hukunci bai sake sanƴa YAZEED ɗin a idanu ba, he just do hope yana cikin ƙoshin lafiya ga kuma dama bai gama warkewa har chan ba.
A haka rayuwa ta cigaba da tafiya, cikin watanni biyu kowa ya mance da wata Hafeezah inda suka tsiro da sabuwar rayuwa mai cike da so da ƙaunar juna abin gwanin ban sha'awa.
Rahinah yafiyar JALILAH da kowa ta nema cikin fadar akan gur6atattun halayen ta a garesu, nan kuwa duk kowa ya kar6e ta tare da nuna mata babu komai.
Ayaan kuwa sake yanke hannun sa likitoci sukayi inda akayi masa aiki aka sanƴa masa ta roba, shima yayi nadamar halayen sa sannan ya nemi yafiyar kowa da kowa musamman ma DEENAH da ZEEYAD.
Cikin wannan shekarar duk suka jesu aikin Umarah dan sake roƙon zaman lafiya mai ɗorewa da farin ciki a wannan ahalin nasu.
Sosai suke gudanar da zaman lafiya mai cike da ƙauna a wannan family ɗin.
DEENAH da ZEEYAD kuwa Nigeria suka zo tare da kawowa su Umma ziyara, sosai da sosai Umma, Jafar, Mami, Anty Khadija wacce itama auren ta ya kusa dama kuma Amirah da mahaifin su sukaji daɗin wannan ziyara ganin yadda DEENAH ta zama wata fresh da ita gwanin ban sha'awa ga kuma little ZEEYAD mai kama da mahaifin sa wanda a halin yanzu yake da shekara ɗaya da ƴan watanni.
Sati biyu sukayi wa su Umma suka koma Egypt, inda kuma anan ne suka cigaba da gudanar da rayuwar farin ciki.
Cikin wata shekarar da ta zagayo mai Martaba ya sauƙa ya baiwa ZEEYAD mulki dan kuwa a cewar sa ya gaji da mulkin haka shima yana buƙatar hutu, ai kuwa an samu adalin sarki mai kwazo wanda kuma yafi mahaifin sa iya aiki da tafiyar da mulki, sosai jama'a ke jin daɗin mulkin sa, cikin shekaru biyu ya dawo da wannan ƙasa abar kwatance a ƙasashen duniya baki ɗaya.
Su DEENAH kuwa an sake murjewa an zama manƴan mata kuma Sarauniya, farin ciki gun wannan ahali ba'a cewa komai.
A yanzu su YAZEED ma na da ɗansu mai shekara ɗaya, Grandma kuwa ta sake tsufa amma har yanzu da sauran ƙarfin ta, sosai takejin farin cikin kasancewa cikin ahalin ta.
*5 YEARS LATER*
_____Abubuwa da dama sun faru cikin wannan shekaru, ciki kuwa harda mutuwar Grandma da mai Martaba, sosai sukayi baƙin ciki da mutuwar wadannan mutane biyu mafi soyuwa a garesu daga ƙarshe dai sun wallafa Allah komai inda suka cigaba da yi musu adduar samun rahamar Ubangiji a kullum.
Yau ma kamar kowacce ƙarshen wata su kan haɗa family re-union dan ganawa da dangi dama kuma abokan arziki.
Wurin hutu ne ƙato cikin MASARAUTA wanda daga gani kai kasan special ne wurin ba kowa ne ake bari yake ma ra6ar arear wurin ba, sosai tsari dama kuma gine-ginen cikin MASARAUTAR suka canza da alama dai ba ƙaramin cigaba ake samu kullum ba, ga kuma yadda Bodyguards ke zagaye da wurin kowanne hannun sa riƙe da bindiga.
Kyau da tsaruwar wurin hutun ba zai faɗu a baki ba, daga nesa daga ciki kuwa na hango su zazzaune kan manƴa-manƴan darduma masu kyau na alfarma, duba na na maida gun wasu dattijai dake zaune suma nasu wurin daban, kallo na ƙare musu tsaf Abdulhakeem, Abhi, mahaifiyar Sadeeq, mahaifiyar Jalilah dama kuma Sarauniya Nazeerah ne zaune gaban su kuwa abubuwan more rayuwa ne kala-kala suna ci suna ɗan ta6a hira cike da nishaɗi.
Maida duba na nayi kan dardumar dake tsakiya wanda ya kasance wasu irin kyawawan yara ne akai wanda aƙalla zasu kai su goma koh ɗan ƙasa da haka gwanin ban sha'awa kamar dai ka sace su ka arce, kundai san yaran larabawa da shegen shiga rai😝, sannan manƴan cikin su ba zasu wuci 13yrs ba, suma wasan su suke duk fuskokin su ɗauke da walwala except yaro ɗaya wanda duk ciki shine kyakkyawan cikin su fuskar nan tasa a matuƙar ɗinke yaja gefe ɗaya ya zauna yana gungunai tare da aikawa da sauran yaran kallo cike da haushin su.
Daga ɗayan gefen kuwa su ZEEYAD, DEENAH, YAZEED, JALILAH, Sadeeq wanda Rahinah ce matar sa yanzu, Ayaan, Sooraj da wata budurwa a gefen sa wacce da alama dai matar sa ce, sai kuma ƴaƴan Nazeerah mata Layla, Raudat dama kuma mazajen su, sune duk zazzaune da ka gansu kasan kwanciyar hankali da jindaɗi ta zauna musu kowannen su fuskar su ɗauke da fara'a suna hira suna cin abubuwan dake jibge kaca-kaca a gaban su.
Ɗaya daga cikin yaran wanda ba zai wuci shekaru huɗu bane yayi masa gwalo hannun sa riƙe da wata kyakkyawar yarinƴa da ba zata wuci watanni bakwai da rabi ba sai lagwaigwaya ta yake wai shi a hakan riƙon ta yayi da kyau.
A fusace yaron farkon wanda ba zai wuci 7yrs ba ya iyo kansa kafin ya shiga jan yarinƴar a hannun sa, ihu ɗayan ya fara yana faɗin ya sake masa ƙanwar sa ai batason sa ne yasa bataje wurin sa ba.
Shi kuwa ɗayan in banda huci babu abinda yakeyi daga ƙarshe dai yayi nasarar kwace yarinƴar daga hannun sa yana rungume ta a jikin shi, Kuka ɗayan ya fashe dashi ganin yafi ƙarfin sa ya kwace masa ƙanwar sa.
Hankalin mutanen wurin ne ya dawo gun su, DEENAH da suma tasu wurin zaman daban miƙewa tayi a fusace tare da faɗin "Abyad."
Juyowa yaron yayi yana kallon ta bar yanzu yana nan rungume da yarinƴar sai huci yake da alama dai zuciya ne dashi.
Ƙarasawa wurin mai kukan tayi tana tayar dashi tsaye kafin ta shiga share masa hawaye tana bashi haƙuri.
"Ummie ai shine ya kwace Ummu-kulsum a wuri na" cewar yaron yana nuna inda Abyad ke tsaye.
"Shushh, kayi shiru haka kaji?, zanyi maganin sa itama yanzu zan kwace ta sai hankalin ka ya kwanta koh?."
Kai ya jinjina mata yanajin daɗi a zuciyar sa.
Ƙarasawa tayi gun Abyad kafin ta sanƴa hannu tana amsar Kulsum a hannun shi, da yatsa ta nuna sa kafin tace "I warned you several times akan yawan zuciyar ka amma baka ji, daga yau ba zaka sake ta6a kulsum ba, kana sonta amma kuma kullum kana cikin faɗa da yayan ta tayaya itama zata ji daɗi ta soka idan taga kullum kana cikin faɗa da yayan ta, eh?."
Shiru yayi yana kallon ta kafin ya buɗi baki kamar wanda bayason maganar yace "But he is hurting her bai iya riƙe ta ba."
"Just do as i asked you to."
"Ba zan ƙara faɗa dashi ba indai Kulsum zata soni akan hakan."
Murmushi tayi tana basa peck a kumatun sa tace "Good Boy maza kaje ka rungumi Zaid ku shirya yanzun nan."
Kamar yadda ta umarce sa ya ƙarasa gaban Zaid yace "Am so sorry Zaid, ka yafemin kaji?."
Kai Zaid ya jinjina masa kafin kuma su rungumi juna cike da farin ciki.
Murmushi duk mutanen wurin sukayi, juyawa tayi tana komawa wurin zaman ta, Kulsum hango Ummien ta ya sanƴa ta fara yayyarfa mata hannu alamun ta ɗauke ta, murmushi JALILAH tayi tana amsar ta daga wurin DEENAH.
Cikin raɗa ZEEYAD yace da DEENAH "I wonder why your Son yake da zuciya haka."
Murguɗa masa baki tayi tace "Kaji ka da wani magana, halin ka ya ɗauko, which means a gunka ya ɗauko komai ma."
Murmushi yayi yace "Do you think the Boy is in love?."
Wani irin kallo tayi masa kafin tace "Mai kake faɗa ne haka?, mai ma ya sani he is just fond of Kulsum shine kawai."
Ɗinke bakin sa yayi tare da yin shiru dan kuwa ba ƙaramin halin ta bane yanzu ta balbale sa da masifa tunda ta samu sabon ciki abu kaɗan ke bata haushi.
Kukan wani yaron suka sake jiyowa nan duk suka juya suna kallon sa Abyad ne da wani daga cikin yaran da zai wuci sa'an sa ba kowanne riƙe da kafaɗar juna kamar wasu raguna zasuyi karo suna faɗa, dafe goshi DEENAH tayi, ZEEYAD ne ya daka masa tsawa take ya saki yaron ya tsaya kamar wani Boss yana aika masa da mugun kallo.
"Mai ya haɗa ku ku kuma?" cewar Nazeerah tana kallon su.
Ɗaya daga cikin yaran wacce ba zata wuci 9yrs bane tace "Wai dan Latif yace idan mun girma shi zai auri Kulsum shine kawai Abyad yaji haushi ya wanke sa da mari, shine fah suka hau yin faɗa, suka takawa Imran ƙafar sa" ta ƙarashe da yin kwafa tana sunkuyawa gun yaron dake kuka ya riƙe ƙafar tasa.
Duk baki suka saki suna kallon yaran cike da mamaki, yafito Abyad DEENAH tayi da hannu, nan ya tako zuwa inda take, kallon sa tayi tace "On your kneels."
Ba tare da yayi musu ba yayi kneeling ɗin yana ɗaga hannayen sa sama fuskar nan tasa a matuƙar tsuke.
Kunnen sa ta kama taja tace "Maiyasa bakajin magana?."
Runtse idanu yayi kafin yace "Shine yace wai Kulsum..."
Cikin faɗa ta katse shi da faɗin "Shikenan kuma kada kowa ya ra6i Kulsum sai kai, let this be the last warning da zanyi maka, muddin ka sake yin faɗa da wani then babu abinda zai hana ni maida ka gun Grandma a Nigeria sannan ba zaka sake dawowa ba, ba zaka sake gani na koh Abhi ba bale kuma Kulsum, kaji?" ta faɗa tana murɗa kunnen nasa.
Kai ya jinjina mata kawai yana runtse idanu cike da zafi.
"Zauna anan, ba zaka koma cikin su ba har sai an tashi."
Zama yayi inda take nuna masa ɗin yana naɗe ƙafa tare da sadda kai ƙasa.
Kallon DEENAH ZEEYAD yayi tare da sakar mata da murmushi, ɗan makar ƙeyar sa tayi tace "Stop staring."
Dariya ƴan wurin sukayi baki ɗaya kowa ya cigaba da harkar gaban sa.
Rarrafowa Kulsum tayi gun Abyad tana hawa jikin sa, ta gefen ido ya saci kallon iyayen nasa kafin ya ɗan riƙo ta yana bowing kansa dai-dai kunnen ta ya raɗa mata "I love you Kulsum, and oneday... you will be my future wife" ya ƙarashe a hankali.
Dariyar da ya bayyanar da cute dimples ɗin ta ta saki kamar wacce taji abinda ya faɗa nan shima ya saki murmushin yana kallon ta.
Ɗagowa yayi nan yaga duk kallon sa suke sadda kansa yayi ƙasa yana murmushi.
ZEEYAD ne ya ɗago glass ɗin champaigne ɗin hannun sa yace "Cheers y'all."
Duk ɗaga nasu sukayi tare da faɗin "Cheers" kafin kowa ya kafa nasa a baki.
ALHAMDULILLAH, LAIFIN DAƊI ƘAREWA.
Yake 6oyayyiyar makaranciyar ZEEYAD, koh da ba zakiyi min comment a last page ɗinnan ba toh ina mai roƙon ki da girman Allah kiyi min addu'ar dacewa duniya da lahira koh da kuwa cikin zuciyar ki, sannan kuma ki faɗamin darasi ɗaya da kika ɗauka cikin wannan littafi musamman ku masu yimin comment da nuna min ƙauna a kullum *WANE DARASI KIKA ƊAUKA CIKIN LITTAFIN ZEEYAD??*
*Alhamdulillahillazi bini'imatih tatimmus salihat, ina miƙa dumbin godiya ta ga Allah(SWT), da ya bani aron lokaci har izuwa yau da nake kammala littafin ZEEYAD, ina mai roƙon Allah da ya bani ikon nishaɗantar daku tare da wa'azantar daku ya kuma bani wani aron lokacin na gabatar muku da wasu litattafaina na nangaba, ina roƙon Allah da ya yafemin a duk inda nayi kuskure cikin wannan littafi ya kuma bani ladar saƙon da na isar muku cikin sa🤲🏽🥰*
*GODIYA TA MUSAMMAN*
Godiya ta musamman gareku *ZEEYAD FANS CLUB*, haƙiƙa kaunar ku daban take cikin zuciya ta, inayi muku so fisabilillah, alkhairin Allah ya isar muku aduk inda kuke a faɗin duniya.
*JINJINA TA BAN GIRMA*
Gareku my best Commenters, haƙiƙa comments naku is something else wollah, ina matuƙar jindaɗi da nishaɗi aduk sadda nake karanta comments naku
Lateefat
Fatima Bet
Ice
Mrs Nuruddeen
Sadysglam
Queen Hafsy
Mom Misrah
Mom Fauxullah
Mrs Kabeer
Ummu Muhseenah
Beebarh
Halimatu Umar
Mmn suhailat
Nucieey
Maesart
Ummu Khaleel
Maman shurem
Maryearma
Aysha s.b.a
Maman Ameer
Nana Ruqayyah
Ammy
Zainab Jaja
Ummu Mahbub
Haseenerh
Maman Arpha
Asiya Abdulkadir
Umma Ammar
Maryam Abdulmajalil
Kai gaskiya kuna da yawa dama dai wadanda ban lissafo ba kuyi haƙuri, duk kuna raina kuma ina ƙaunar ku sosai da sosai, Allah Ubangiji ya bar Kauna tsakanin mu🤲🏽🥰
*JINJINA GAREKU ƳAN UWANA MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION, ina ƙaunar ku fisabillah, Allah Ubangiji ya bar mu tare yaqara mana basirar rubuta litattafai masu tsabta.*
Yanzu kuma sai wani Lokacin idan Allah ya kaimu inda zanzo muku da sabon littafi na mai ɗauke da sabon salo watau *ABHI* ku daga jin sunan shi ba sai nace daku komai ba, kudai kawai ku shirya alƙalamin comment naku nikuma zan shirya alƙalamin yi muku typing, zai zo muku very soonn insha Allah..............
*MHIZZ JIDDHERR🖊️*