Showing 1 words to 3000 words out of 175193 words

Chapter 1 - KUTSE COMPLETE HAUSA NOVEL

07 Feb 2026

519

??ࡱ?>?? % ????????????? ?
?
? ?
?
????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????Z

 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?Root Entry???????? ?F!WordDocument?????#0Table?????????Data
???????????????????? P???KSKS??#W????????pp----??? ?
|
-??????????$??*p--??----?????????- ?>`??>Normal$a$KHOJPJaJW???8?Zh?4?????Z?"?Itdv?,?T?4?|??G?f4~??l?n????+?@TP|kf??
?t?????r???#?=?J?_?m?~? ??????&?0?^`N&?/2=?H?`^v?x?F??????? p:6J?Wba$q??4?4?????0????X%>B?W}?p? ???
?F1?Kh
???Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/FOOVbfIM8yREJrSo1YU2oD


KUTSE

PAGE 1
??
? ? NA

MOM HANEEF

ADABI WRITERS ASSOCIATION

Shinfid'a.

Rayuwa ta aure bata da tabbas, yau lumana gobe rikici da rigima, washe gari shiru mai nauyi kamar dutse.

Haka nan duk duniya basufi karfin zargi ba, acikin gidan komai yana tafiya dai-dai a ido, amma akwai wata rana dazata cenza komai batare da sun san ranar tanatan zuwa ba.

Ta mallaki zuciyar mijinta mallakar da kyawawan halayanta da kuma karuwar haihuwar yara biyu duk mata wanda suka taimaka wajen siye zuciyar sa.

Haka nan bata taba zata akwai wani wanda yake da hak'k'in shiga cikin tsarin data ginaba, a tsarinta babu aure na biyu, babu Abokiyar zama haka?
Babu wata mai so da gaskiya.

Sai a rana d'aya kwatsam mijinta mai so da k'aunarta ya kutso da wata halitta wacce bata kasafta da ita ba a cikin tsarin rayuwar ta, ya shigo da kishiyar ta mace mai nutsuwa wacce zuciyar ta tacika da shiru addu'a da tsoron Allah.

Duk da cewar aure halal ne bisa izinin Allah, amma sam ba haka bane a idanun Rashida, tana kallon hakan a matsayin kuskurene kuma wan nan shine kutse mai cike da tashin hankali a wajenta wanda bazata taba iya yarda dashi ba.

Da farko Rashida ta dauki komai da salama da murmushi, amma komai ya canza da zarar k'ofa ta rufe, sai kuma kalmar zagi, gori, tsinuwa da kuma tozarci suka fara d'aukar sararin gidan kamar kid'an garaya mai cike da kad'awar tantanin kunnuwa.

A wajen maryam kuwa ita bata yarda da rikici da tashin hankali ba, ta yarda tayi shiru tayi addu'ar da zata zame mata tsani da kuma sauyin alkairi.

Amma wan nan shiru na maryam zai zama shaidar alkairi ko akasinta?

Shin auren Nasir da maryam zai zama aure ne ko fad'uwar rayuwa awajen Rashida?

Kuma wacece da laifi? wacce akace ta kutso ko kuwa wacce ta hana shigowa da adalci?

Duk wan nan k'arin bayani da amsoshin mu zamu samesu ne a cikin k'ayataccen labarin mu mai suna kutse, wanda ke tattare da tsantsar rashin adalci da kuma san kai mai tattare da muradin mutum d'aya.

Kudai kubiyoni da bani goyon baya domin samun cikar muradin ku da yardar Allah.

*****

Bissimillahirrah manirrahim

Da sunan Allah mai rahama da jin kai tsira da amincin Allah su tattara su k'ara ta babbata ga annabin da baya zalunci ko san rai a cikin al-amarin sa, sai gaskiya da bada Kai ga fad'adar ubangijin sa.

*****

Nasir

Kallon kansa kawai yakeyi a jikin mudubin ban d'akin dake mak'ale a jikin bango, akai akai zuciyar sa take tsinkewa tare da neman mafitar dabai hango ta yadda zai tsara kasantuwar taba.

Sumar kansa ya k'ara shafawa tun daga goshinsa har zuwa k'eyarsa yana tunanin Abinda ya dace yayi a wan nan takin, koda yagama wankan samun kan masai yayi ya zauna yana kuma k'arewa kansa kallo a jikin badubi yana mamakin wai shine yau aka d'aurawa aure?

Aure fa? Kamar shi? Gashi wani b'ari na zuciyar sa na fad'a masa cewar bai cancantaba, bai cancanci k'arin aure ba a yanayin zaman dad'in da suke ciki da matarsa Rashida, Rashida mai so da k'aunar sa, ta yadda dashi haka ta aminta da dukkan lamarunsa, amma yau gashi shine dayi mata kishiya Abinda tafi tsana a cikin rayuwar ta ta gidan duniya, bazai manta ba takance.

"Babu abinda na tsana arayuwata sai kishiya, banason ka saka wata ta kutso cikin mu domin samun madogara, tabbas bazan dubaba bazan had'a kowacce halittar mace dakai ba, inasonka mijina haka ina gudun wacce zata rab'eka.

D'an gemun fusakarsa yashafa wanda bai wuce kamu biyu ba yace "innalillahi wa'inna ilaihirraji'una, wace iriyar rayuwa na jefa kaina da kuma Maryam?

Yana wan nan tunanin yaji ana masa bugun k'ofa kamar za'a b'alle d'akin, da azama ya fito daga band'akin yayi saurin bud'e k'ofar d'akin yana kallon Rashida wacce tayi ciki ciki da idanuwa duk kuwa da girman su tace

"Yau kaine da kulle k'ofa baban Halima? Meyake faruwa? Naga tunda kadawo garin nan d'azu na kasa gane kanka? Kana shigowa fa gaisawa kawai mukayi ka tashi ka shigo d'aki, kuma kashigo ka kulle kanka a ciki, wai lafiya? Me yasa kafara Abinda ban saba dashi ba?

Kasa magana Nasir yayi sai raba idanuwa waje-waje da juya kai yana yake yadda bazata ganeba.

Ganin yakasa magana yasa tayi murmushin da ita kad'ai ta san ma'anar sa tace.

"Baban Halima ka nutsu kafito haka, yana dakyau kazo kaci abinci kuma kayi min bayanin waccen yarinyar daka tawo da ita daga daura, dan gatacen tana barci a cikin falo.

Zuciyar sa yaji ta buga da k'arfi amma duk da haka sai ya aro jarumta yace "karki damu maman Halima gani nan fitowa nad'an watsa ruwa ne.

Rashida

Gyad'a kai tayi tare da juyawa tana mamakin irin sauyin mijin nata wanda bata tab'a gani a wajensa ba, tana isa falo ta tsaya akan maryam wacce ke barci hankalinta a kwance domin ta d'ebo uwar gajiya ga uwar yunwa tanata kwakwalar cikinta, rashin sanin abinyin yasa ta kwanta kan kujerar tana barci.

Gyad'a kai Rashida tayi tare da wucewa kichen dan ta had'owa nasir abincin kafin ya fito, wani Abin mamaki kuma tana wucewa maryam na mik'ewa tangararan kamar bamai barci ba, kallon nasir take cikin burgewa da soyayyar sa data shiga ruhinta tafarad'd'aya tana masa murmushi, shima murmushin ya maida mata kuma hakan yayi dai-dai da fitowar Rashida daga kichen d'in da kayan abincin a hannunta.

Nasir na ganinta yayi saurin kauda kai daga kallon Maryam yana cewa "Maryam kin tashi? Gyada kai tayi Alamar Eh tana mutststsike idanunta.

Fuska babu yabo babu fallasa Rashida ta k'araso wajen tana kallon Nasir wanda duka alamun sa ya nuna a tsarge yake tace

"Kafito baban Halima? A kakkauce ya d'aga mata kai yana yak'e yace "nashir ya zama naci daddad'an abincin matata.

Murmushin dabai kai zuciya ba Rashida tayi tana jin zuciyar ta na k'ara nauyi saboda ganin yadda mijinta yake wasu abubuwan da takasa gane kansa tun sanda ya diro gidan.

Sai data gama shirya dining d'in san nan ta tako ta rik'e hannun nasir tana cewa "yau Abu na musamman na girka maka, nasan zakayi farin cikin ganin sa san nan bakinka zai zak'u dayaji d'and'anansa, murmushi Nasir yayi tare da saurin zama yana bud'e warmers d'in yana cewa.

"Tuwon acca kikayi min nama canka, ya k'arasa yana zaro ido yace "woohoo, sai dake matar Nasir, ai shiyasa nake k'ara k'aunar ki, keta musamman ce a wajena.

Murmushi Rashida tayi tare da gutsuro tuwon ta samishi miya ta kawo bakin sa, karb'a yayi cikin jin dad'i yanajin nauyin zuciyar sa na sauka k'asa a hankali.

Har sud'e hannun nata yayi a sanda tagama ciyar dashi tuwon kamar zai had'a da yatsun nata ya taune yanata sid'ar baki.

Sun manta da maryam dake zaune dan haka suke idan suna tare basa tunanin kowa daman sai kansu, sai da Rashida ta mike zata k'ara zubawa Nasir lemo ta kula da Maryam wacce ta sunkuyar dakanta tana d'an murmushi tare da wasa da yatsun hannunta, goshi Rashida ta dafe tace "ouch" ashe fa muna da bak'uwa wallahi na manta baki d'aya ma, bara na zubo miki abincin kici kafin ya samu nutsuwa ya gabatar min dake da kuma Abinda ya kawo ki cikin iyalai masu d'umbin farin ciki da k'aunar juna.

Nasir

Gabansa ne yafad'i dajin wan nan furucin na Rashida, da sauri ya mike yana shafa gemunsa wanda bai wuce kamu biyu ba ya sharshe gumin da yafara tsattsafo masa yana cewa "karki damu ai Maryam mutuniyar kirki ce taci abincin sai muyi maganar, koda maryam tagama cin abincin sai Nasir ya kira sunan ta yace ta dawo k'asa ta zauna, jiki a sanyaye ta sauko daga kujera ta zauna k'asa cen gefe ta sunkuyar dakanta kamar munafuka tanajan numfashi a hankali dan kar tayi da k'arfi ace tayi laifi.

Sai da Nasir yayi namijin k'ok'ari ya tattaro duka jarumtar sa yace.

"Maman Halima, D'aga kanta tayi ta kalli Nasir tace "baban Halima, sai ya sakar mata murmushi ya cigaba da cewa.

"Wan nan yarinyar sunanta Maryam, kuma amanace na d'auko daga cen garin daura dan haka ki....

"D'aga masa hannu Rashida tayi tace "ban gane amana ba? Karka soma cemin ka d'auko wan nan yarinyar nan ne ka kutsota cikin iyalaina saboda ta zauna, gaskiya kafad'a mata gaskiya ta koma gida saboda bata da muhalli a cikin gidan nan.

Zuciyar Nasir ce taketa dokawa da k'arfi da k'arfi saboda daman yasan halin Rashida, batasan bak'o batasan duk wani Abu dazai saka su takura ita da yaranta da mijinta, shi abin ma yabashi mamaki da har ta yarda Maryam ta zauna na wan nan a wannin batare data tayar da hankalin taba.

Ganin Nasir yakasa magana yasa Rashida tatashi tsaye tace "bara na d'auko mata kud'in mota ka kaita tasha dan gaskiya bata da wajen kwana a cikin gidan nan, batabi ta kansa ba tayi wucewar ta d'aki tanajin haushin Maryam a zuciyar ta.

Toya kuke ganin zata kasance? Maryam zata koma inda tafito ne kamar yadda Rashida take fata? Ko kuwa Nasir zai ci galaba akan Rashida Maryam tacigaba da zama a cikin gidan Rashida wacce bata yarda da kowane irin kutse ba?

PLEASE COMMENTS AND SHARE
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/FOOVbfIM8yREJrSo1YU2oD


KUTSE

page 2

? ? ?? Na

Mom Haneef

ADABI WRITERS ASSOCIATION

Nasir

da sauri nasir ya tashi yabi rashida d'akin yana kiran sunanta, bata amsa ba domin ranta a matuk'ar b'ace yake da Abinda yayi mata? Gaban gadon d'akin ta matsa ta zauna tana tunanin wane irin salo nasir d'in ta zai b'ullo mata dashi ne? Taya zai d'auko wata bare ya kawo mata cikin iyali? Jin yana kwala mata kira yasa tayi saurin mik'ewa daga kangadon ta nufi wardrobe ta bud'e, badan zata d'auki wani abin aciki ba sai kawai dan ta rikice tama rasa mai zatayi, kuma tabbas bata son sakashi cikin damuwa domin a take yake mayar da damuwarta ta zama tashi harma wani sa'in yafita damuwar, shiyasa tayi saurin k'irk'irarwa kanta Abinda zai kau da hankalin sa daga damuwarta.

Shi kuwa Nasir da sauri ya k'araso inda take tsaye tare kama hannunta baki daya yace "dan Allah maman Halima ki tsaya ki saurareni, inason kibani hankalinki wajena kuma kiyi min kyakkyawar fahimta, bafa Abinda kike tunani bane, karki fassara hakan da rashin girmama Abinda kikeso a wajena.

Dafari tak'i koda kallonsa, amma dataji wan nan maganar tasa da kuma yadda yake furtata da sanyi yasa ta d'ago ta kalleshi, had'a idanu sukayi sai ya sakar mata murmushi, ido ta sauke k'asa tare da cewar "ina sauraren ka.

Zaunar da ita yayi a saman gadon yana wasa da yatsun hannunta yace.

"maryam amanace na d'auko rashida, bawai amana data shafi wani abinba, Maryam k'anwace a wajena kuma kinsan mahaifiyar ta, sanin kanki ne bazan kawo Abinda zai shafi zaman mu ko tarwatsewar rayuwar muba, nifa inasonki keda yarana san nan ina gudun Abinda zai shafeku marar kyau, dan haka dan Allah da annabin sa kiyi hak'uri kibar maryam ta zauna damu shine rok'o na kawai a wajenki, bance lallai sai kin yarda ba, amma ki sani wan nan itace Alfarma guda d'aya kacal dana nema a hannunki tunda na aureki.

Shirune yad'an ratsa d'akin san nan cen Rashida tace "naji zan amsheta amma sai ka gayamin tartibin Abinda yasa kabarota da gidan su ka kawota nan.

Gaban Nasir ne yafad'i har gumi yafara tsattsafo masa, da sauri ya dake yace "yarinyar nan fa marainiya ce, 'yar gidan gwaggwo mariya ce k'anwar mahaifina, babarta ta rasu dad'ewa, kuma Abinda yasa na kawota nan saboda tanason tazo gidana, koda yaushe muddin zanje garin takance "dan Allah nazo da ita ta zauna daku saboda tana sonku, ai tuk'uicin k'auna soyayya, shiyasa ni kuma naga gwara tazo d'in ta zauna tunda tana so, kuma banda ma abinki Rashida, ai ke k'anwa na kawo miki, itace zata dunga gudanar da ragamar aikin gidan nan, tunda tun cen nace miki ki d'auko mai aiki amma kink'i saboda sona da kishina da kikeyi, dan haka kinga fad'uwa tazo dai-dai da zama, daman ai Yukan? gidan sun miki yawa, dan haka ina k'ara sanar dake cewar

"Maryam mutuniyar kirki ce, zakiji dad'in zama da ita, san nan ina da yak'inin zatayi miki biyayya, haka bazata tab'a tsallake umarnin kiba kinji?

Rashida

Badan zuciyar ta tamata dad'i ko kuma taji ta yadda da zaman maryam ba, amma dolene ta nunawa mijinta amintar ta dan su zauna lafiya, dan ita batason taga ranshi ya b'aci ko kad'an, san nan batafiya son ja'inja ba shiyasa ta sakar masa ta amsa da to, har zata tashi nasir ya rik'o hannunta yace "ba haka kika saba bani kulawa ba matata.

Tasan sarai me yake nufi, kuma zuciyar ta babu dad'i, amma a haka ta daure ta zauna kusa dashi tana sakar masa murmushi da kallon? dake tafiya da duka imanin sa.

Bayan awa biyu

Maryam

Duk da tagaji dazaman wajen da take amma haka taita zama tana wasik'ar jaki, ji takeyi zuciyar ta ta k'untata da sanyin da jikinta yayi, tunanin halin dazata shiga take muddin Nasir yamaida ta gida amatsayin yafasa zama da ita, to wai ita Abinda bata ganeba ma shine

"Rashida tace zata koma gida, to zata koma gida amatsayin me? Zata koma gidane amatsayin sakakkiya ko zata koma gidane amatsayin jingina, ita kam ba bak'uwar zafi bace ko d'akin da tagani a soron gidan za'a bata ta zauna to tabbas zata zauna muddin Rashida zata sahale mata zaman gidanta.

Tana wan nan tunanin taji Alamar ana shigowa da sallama k'asa k'asa, D'aga kanta tayi a hankali taga yara biyu sun shigo da murna a yanayin su, kallon yaran tayi tsaf taga duk ba wasu manyan azo a gani bane, da fari dai ita babbar kamar shekarunta bazasu wuce sha uku ba, ita kuma k'aramar bazata wuce shekara tara ba, uniform ne a jikinsu da kuma jakar makaranta rataye a bayansu, sai lunches d'insu wanda yake sak'ale a hannayen su, murmushi tayi tana kallon su da burgewa ganin uniform d'in nasu irin na 'yan gayu mai kyan gaske, komai nasu d'ad'as d'ad'as Abin sha'awa.

Hannun yarinyar ta rik'e tana jawota jikinta tace "sannu da zuwa, yaya sunanki? Kai sadiya ta langwab'ar kamar zatayi kuka tace "Ban saniba.

Da sauri Halima ta rufe mata baki tace "ke sadiya" ba Abba ya hanamu yiwa Babba rashin kunya ba?

Daga fad'ar haka sai sadiya ta wullar da lunch box d'in nata tafara dire dire tana kuka tana kiran mama.

Baki sake Maryam ke kallon iKon Allah tace "to fa, me akayi miki? to Kiyi hak'uri kinji.

"Murgud'a mata baki sadiya tayi tace "Bazan yi hak'urin ba, ai kece kika kulani, ni banson ganin kowa, ta wullar da jakar tata tayi d'akin su tare da fad'awa kan gadon tana kukan futsara.

Rashida

Da sauri ta fito daga band'akin bayan ruwan data watsa, kallon Nasir tayi tace "kamar fa sadiya ke kuka? Ko bakaji ba? Kai Nasir ya d'aga yana jifanta da murmushi yace "naji mana, ai nasan tab'arar tace tatashi.

Girgiza kai Rashida tayi tace "babu zancen fa shagwab'a, idan basuyi son ransu a gidansu ba aina zasuyi? Ta k'arasa tana d'aga masa gira.

Da sauri nasir yayi kanta yana dariya zai cafkota, itama da saurin ta zame ta fice da gudu daga d'akin tana dariyar farin cikin daya sakata a lokaci k'ank'ani.

Akan kujera ta tarar da Halima zaune tana bawa maryam labarin makarantar su, cikin jin haushi Rashida tace "ke Halima, kin santa ne? A d'an furgice Halima ta jijjiga kai tana kallon maryam wacce tayi k'asa da kanta, cikin fad'a Rashida take cewa "amma baki santaba kika zauna kina hira da ita? Ko ban hanaku shisshigewa mutumin da baku saniba? Banason irin haka fa, maza tashi kije ki cire kayan nan, ina sadiya?

Da hannu Halima ta nuna mata d'akin su batare da tayi magana ba tashige d'akin jikinta a sanyaye.

Wani kallon banason shisshigi Rashida tayiwa maryam san nan tashige d'akin su haliman tana kiran sunan sadiya.

Maryam

Kanta ya kulle gaba d'aya da lamarin zaman gidan nan, itafa so take Nasir ya sanar da ita hukuncin da matarsa ta yanke akan zaman su, gashi basuce mata komai ba daga shi har ita, k'arin Abin haushin kuma sun shiga d'ayan falon sun barta zaune a wan nan babban falon ita kad'ai yawa mayya, gashi tana Jiyo hirarsu da dariyar su, wan nan wane irin abune,a gogon bangon falon tak'ara kallo taga har tara da rabi na dare, ajiyar zuciya ta sauke tana lumshe ido dan barci ne fal a cikinsu, ganin sun manta da ita yasa ta cire hijabin jikinta ta shimfad'a a nan k'asan kafet ta kwanta tare da takurewa waje d'aya.

Nasir

Bai samu kansa ya fitoba sai da suka shafe sama da k'arfe shad'aya na dare suna hira, Allah yasani kuma Allah yagani Maryam tana ransa, duk hirar ma da Rashidan ke masa wallahi hankalin sa ba awajenta yake ba, sai da taga yafara amsa ta da "Eh, A'a, san nan ne ta dubeshi sosai tace "baban Halima ko barci kake jine? Da sauri ya d'aga mata kai yace "tabbas kuwa dan har yanzu akwai gajiya a cikin jikin nan nawa.

D'an murmushi tayi tace " uhnmm, to bara nakai yaran d'akin su sai Muzo mu kwanta.

Da sauri ya Mike ya zari sadiya yace "karki damu had'e littafin home work d'in nasu bara nakai su, da to ta amsa san nan tafara had'e littafan nasu shi kuma yafice.

Yana fitowa yafara waige waigen inda zaiga Maryam, acen daga k'urya ya hangota kwance nannd'e cikin hijab tana barci, numfashi ya sauke wani Abu me nauyi a k'asan ransa wanda bai masa dad'i ba yana zungurar zuciyar sa wucewa yayi ya kai sadiya san nan yadawo ya d'auki Halima itama, koda ya dawo ya zauna kan kujera sai ya kalli Rashida yace

"Maman Halima kin manta munada bak'uwa ne? D'an girgiza kai tayi tace "ban manta ba baban Halima, kawai dai ina nazarin inda zan d'an samu na sakayata ne dan kasan banida wajen aje bak'i ai.

D'an yak'e yayi yace "uwar gidana kenan, amma ai yakamata abawa Maryam wajen kwana saboda tanacen tana barci a falo.

Bai san Abinda maganar sa zata haifar ba dabai soma furtata ba koda tazo bakinsa.

Rashida

Cikin ba'kin cikin ce mata uwar gida da yayi tace "ban gane uwar gida ba? Me kake nufi da wan nan furucin? Daman kayi min wata amaryar ban saniba? Banason haka Nasir, karka k'ara furta min kalmar uwar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login