Showing 171001 words to 174000 words out of 180809 words
ki tatali arzikinsa ki tatali lokacinsa, ki yi hakuri na tabata zaki kai ga ci, an sha yin auren da ba soyaya sai ki ga kuma hakuri ya sayi soyayar, an sha yin auren da soyaya ce jigon komai aman sai ki ga rashin biyaya da hakuri ya kashe soyayar nan an dawo ana gannin bakin junna, Nana ki rike tsafta, ta muhalinki da jikin ki, ki rike masa tsaftarsa, ki kula da abincinsa sannan ki kula da komai nasa, a haka zaki ci ribar zama da shi sosai kin ji?"
Aisha ta ringa sauke ajiyar zuciya tana jin wani irin nutsuwa na shigarta, nasihar da ya dace uwa ta zauna ta yi mata ne kakanta ya yi mata kuma ta shigeta sannan ta dauka ta kuma yarda zata ci gaba da aiwatarwa dan samun nutsuwa a tare da mijin aurenta!
A office din HISHAM
Kallon mahaifiyar Aisha kawai yake kafin ya maida dubansa kan mahaifin Aisha
Magana ta ci gaba da fada kamar haka" Kar ka yi, kar ka yi kiran kowa, ka barshi zai huce, idan ba abin tsoho ba aikin nan da shi fa muka dogara mu dukanmu, ba sanadiyar aikin bane har ya samu aka masa aikin nan sannan har jikar tasa ta samu mijin wani? "
Mahaifin Aisha ya yi gyaran murya yana kallonta ya ce" Ashe baki da hankali? Tsalakowa zaki yi kan ubana ko me? Ke kin san bana hada maganar Papa da ta kowa a duniya!, da kike cewa a kyale shi mahaukaci ne shi? Ta yayama zaki ringa fadar magana marar tsari wai da aiki na dogara? Da Allah dai aiki menene banda matakin takawa mai hanya biyu wuta ko aljannah?, uban nawa kike cewa haka? Kin ga dai ina girmama naki iyayen har suka bar duniya, ki kiyayi maganar bakinki, tabas ina da son kudi da son mulki aman kuma ban yi bacewar da har zai yi umarni na take ba!"
[7/24, 10:20 AM] BAK'A CE: 🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾
*DUK NISAN JIFA*
_(K'asa zai dawo)_
🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾
_RUBUTAWA_
*SAJIDA*
*SADAUKARWA*
*GA*
*MASOYA NA*
💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝
☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️
https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/
_Bismillahir rahamanir rahim_
63
Da mamaki take kallonsa, muryarta ta rage sosai tana nuna shi da dan yatsanta ta ce" Yanzu Aisha baba (Baban aisha da zabarmanci ), sai ka zubar da aikin karatun da ka dauki shekaru kana yi , da irin wahalar da ka sha kafin ka kawo wannan wajen dan kawai ran tsoho ya bace?"
Hisham ya maida dubansa kanta a karro na uku sannan ya sada kansa yana sauraronsu a zaune dangalgal a saman kujerarsa ta duba mararsa lafia
Mahaifin Aisha ya ce" Abu mai sauki ma kuwa, dan ke kin fi kowa sannin ubana ya isa da ni!"
Kamar ya caka mata mashi a tsakiyar ranta ta ce" Yau harda gori kake min? Ai nima uban nawa ya isa da ni kuma da na bijire na aureka ai kai ka hure min kunne !, ba komai aman ka sani idan har ka bar aikin nan ni kuma ba ni ba kai Kalamu!"
Murmushi ya yi yana girgiza kansa har ta kusa fita ya ce" Tabas idan hakan ta kasance maganar tsoho ta tabata, matar dake sonka zata zauna da kai a halin akoy ko babu, idan har kika barni dan aikina dama ba ni kike so din ba, ki je ba zan maki baki ba aman nima a yau ban ga anfanin aikin da harta iyalinka sunna zaune da kai ne dominsa!"
Ficewa ta yi a dakin har kamar zata kifa dan sauri ta fita kwata kwata ta tsayar da dan sahu ta masa kwatancen gidan su Hisham ( Duniya kennan )
Bayan fitarta mahaifin Aisha ya sauke dubansa a kan Hisham, shi walahi tunda suke kwaba lamarinsu suna sha bai taba jin kunyar yaron ba irin na yau, yau dinma ya tabata da Papy bai matse masa lamba har ya kora masa bayani a kan irin yadda suke kwana rayuwa tunda suka shigo garin Damagaram da a haka zasu ci gaba da tafia? Rayuwar yarsa kwalin kwal ce ya yi ball da ita haka? Shin me matarsa take nufi da duniya ne?
A hankali ya ja kujera ya zauna yana kallonsa, muryarsa ya sanyaya sosai ya ce" Ka yi hakuri Hisham "
Hisham ya dago da sauri ya ce" Ba komai fa"
Mahaifin Aisha ya girgiza kansa ya ce" Akoy komai, walahi akoy komai, sai dai ina so in fada maka tarbiyar Aisha ba irin tamu bace, a hannun kakanta ta girma ya bata tarbiyar da mu kanmu mukan yi mamakin nutsuwarta da halayanta, kar abinda muka aikata maka ya saka ka tunanin ka auri matar da bata dace da zama uwar y'ayanka ba, kar sanadiyar shiga tsakaninka da farin cikinka ya saka ka raba a kan baiwar Allahn cen, Aishama biyaya ta mana, kuma na tabata zata zauna da ku da zuciya daya, ka yafe mana ka ji? "
Hisham ya saki murmushi a sanyaye ya ce" Ka daina neman yafiyata Aba, ba komai kun isa da ni tunda har kuka girme ni kuma kuka haifa min abokiyar rayuwa mai sanyin hali".............. ya fadi maganar nan ne tsakaninsa da Allah, ya fadeta ne tun daga kasan zuciyarsa, tabas ya fadeta ne dan haka yake tunani, Aisha bata masa laifin komai ba, idanma tana sonsa itama ce mata aka yi an mata miji ko ta dauka ko a samu matsala kamar yadda aka gingindaya masa abubuwa a tsakaninsa da Billynsa, Aisha din nan yarinya ce mai ladabi da biyaya, tana da sanyin hali balema a lokacin da ta budi baki ta nuna masa ita tana son abinda yake so kuma zata zauna da ita da zuciya daya, sai kuma yanzun abinda kakanta ya aiwatar ya bashi nutsuwa a zuciyarsa, ko ba komai auren dolen da aka yi masa an hada shi da ta gari, fatansa ta dore a haka
Ba su su fito a asibiti ba sai da papy ya masu nasiha sosai, har ya dora da fadin a kawo masa dayar jikar tasa ta zo mai yiwuwa ita ta ce ta fasa da likita sai shi
....nan dai suka fito zuciyoyinsu fesss sannan Kader ya tuka su har gida
Sunna zuwa a falo ta ga ya ajiye ledar da bata ga lokacin da ya daukota ba
Hannunta ya kama ya zaunar da ita saman kujera yana kallonta
Murmushi ya sakar mata wanda ya saka ta sada kanta cike da jin kunyarsa, da nauyinsa a sanyaye ta ce" Ka yi hakuri na tsayar da kai yau , ka tashi ka je kanwata fa"
Murmushi ya kuma sakar mata ya ce" Zan je yanzu, aman ina so idan na fita ki yi wanka, ki cenza kayanki ki yi sallah , ga abincinki nan ki ci, sai ki kwonta ki yi chatting sannan ki yi barci, sam sam bana son wani abu a cikin abinda ke zuwa ya dame ki ya zo ya dame ki kin ji?"
Ajiyar zuciya ta sauke tana kallonsa cike da kaunarsa a zuciyarta, a ranta take fadin' Dama ka furtan kana so na, dama ka ce da ni kana so na'
A bayane kuwa sai ta kai hannunta wajen fuskarsa, wajen sajensa a hankali ta ringa shafawa kafin ta ce" Allah ya tsare, Allah ya kare, ya kiyaye hanya "
Murmushi ya mata kafin ya mike tsaye, itama mikewar ta yi hakan ya sa ya dan rage tsayinsa ya mana mata kisss a goshinta sannan ya juya ya tafi
Direct gidan sarki suka dauki hanya, sai dai sunna zuwa wajen shiga na sallon aka ce da su su zagaya babar kofa sunna bangaren Mai baban daki
Su dai sun zagaya din kuma ya shaidawa Tati cewar sun zo
A cen ciki kuwa Tati ce ke bin Bilkisu da kallo cike sa kauna, da birgewa, Bilkisu na tsugune a gaban mutun hudu, mahaifiyar Najeeba, mahaifiyar Mai damagaram, Tati, sai Najeeba dake dan gefe tana shayar da yaronta tana kallon yadda Bilkisun ke hawaye
Nasiha suke yi mata, dabaru suke fada mata, kowa na tofa albarkacin bakinsa kafin Mahaifiyar Najeeba ta rufe da fadin" A karshe zan jadada maki Mai Gado, ba kyau, isa, nasaba zata saka miji ya so ki ya mutunta ki ba, Biyaya, hakuri, yi na yi, bari na bari, su zasu kara dankon soyayarku, idan yanada ku zauna idan bashidama ku zauna domin ba abinda yake dorewa a duniya farin ciki ko bakin ciki, arziki ko talauci, kar wai dan namiji na sonki kamar ya mutu ya aure ki ki rike hakan a matsayin wani makami na yin yadda kika ga dama, du soyayar da ba kyautatawa haskenta disashewa yake, idan mai yi maki laifi ne ki kasance mai yawan yafe masa, kar ki bari gaba ta ringa shiga tsakaninki da shi, yawanci lokuta ki ringa yin kamar baki san an bata maki ba, kamar baki san ciwon kanki ba, aman kuma idan abin ki nuna masa bacin ranki ne kar ki dane ta yadda zai zama baya shayin bata maki, ba da hargagi da masifa zaki fada masa ba, ki samu dabarar da zaki ringa hora shi ta ruwan sanyi ta yadda zai gasu dan kansa ya nemi sulhu, aman yafiyarki ta fi neman fushinki yawa"
Tati kanta dake zaune shanyewa take tas, hakan ya sa sai dane kiran Hisham take ta ki dagawa har sai da suka gama suka tashi
A nan yan matan gidan suka dauko kayayakin Bilkisu , su turaran wuta ne, su kayan gyara ne, da su kujera harta da itacen tsugunin da su miski kai abin ba kadan bane masu daraja sosai suka bi bayansu har wajen motar da su Hisham suke jingine
Kasancewar a yanzuma cikin zumbulelen hijab din take gashi ta ja ta kare fuskarta Hisham bai lura da yannayin da take ciki ba, sai sansanyan kanshin da take fitarwa wanda yakan lumshe idannuwansa ya shaka ya kuma shaka
Waya yake da mamansa har suka shiga gidan nasu suka parker
Mama ta ce" Na shiga uku Hisham a yanzu kake nufin zaka zo dan kawai yau baka ganni ba?, ka ga ka bari gobe idan Allah ya kaimu sai ka zo"
Bilkisu ta lumshe idannuwanta tana kallo ana kai mata kayayakinta kafin Tati hankali kwonce ta kamata suka yi ciki kamar yau ne aka rakota dakinta sai tarairayarta ake
Tati ce ta zauna kusa da ita saman kujera ta kama hannunta tana kallonta ta ce" Babyna, Alhamdulilah, ba zan ce komai a kan auren yayanki na farko ba sai dai na bar haka a matsayin kadarar rayuwarmu ne baki dayanmu, a gaskiya da ace yarinyar ta dauko halayan iyayenta ni da kaina zan tsayar da tafiar, sai dai Nana...." ta fada tana riko hannun Bilkisu dake dauke da jan kunshi sai daukan ido yake ta ce" Bata da laifi, sannan mai biyaya ce, Billy am da ace mai izgili ce ni da kaina zan katse, a yanzu haka kafin na yarda cewa zata zauna sai da aunty ta fada min cewa kar na shiga hakinta, kar na kara daukan wani hakin dan kawai san raina, ahine kadai dalilin da ya sa na hakura na ture komai gefe"
Kuma sauke ajiyar zuciya ta yi ta ce" Ban san ta yada zan yi ki yafe min ba, abinda na sani ni mamanki ce, kuma Allah yana gani ina kaunarki, ban farga cewar na ginawa kaina rami ba sai na ga hawayenki, ban san irin rokon da zan maki ba, ban sani ba Bilkisu....."
Da sauri Bilkisu ta dora kanta a kan kirjin Tati tana dan shashekar kuka, muryarta a sanyaye ta ce" Inata, kadarar ce, kuma ni tawa da sauki Alhamdulilah domin ga dukan alamu zamu zauna lafia da ita, a irin yadda ta shigo rayuwarmu harma ta shige gidan Hamma am, na zubar da makaman yakina na yarda cewa baka isa ka tsarawa kanka rayuwa ba sai yadda Allah ya hukunta maka, shigowarki ciki kuwa dalili ne, Inata daina neman yafiyata haka Allah ya hukunta mana, kuma mun amsa da hannu bibiyu"
Soyaya, tausayi, girman yar yarinyar suka kara shiga zuciyar Zainab, kuma ita kanta yan lafuzan yarinyar sun kara nutsar da zuciyarta harma ta ji cewar a gabanan idan abu ya tunkarota zata dauke shi kan haka Allah ya hukunta mata
A sanyaye ta ce" Ki kula da kanki, ki kula da mijinki da dukan karfinki, ki yi masa biyaya, kar na ji kar na ga soyayar da yake maki ta disashe, ina so a gabanan ta yi ta hauhawa, kin ji? Allah ya maku albarka bara na tafi dare na yi"
Da sauri Bilkisu ta kara makalkale hannunta tana dan girgiza kai ta ce" Aya Innata kar ki barni ni kadai a nan dan Allah ki yi zamanki mana da ni"
Zainab ta yi daria tana shafa kanta ta ce" Ai na tabata ba za'a rasa mai bugamu a jarida ba, kin ga idan kika ga abinda bai maki ba ko karfe dayan dare ne bugo min waya zan zo in kwashe abina ko in daki bakin dan Asma'u ehe!"
Bilkisu ta saki murmushin da bata shirya ba a haka dai Zainab ta ci gaba da rarashinta kafin ta mata dabara ta fice ta barta zaune ira daya
"TO ka je ka ce tati fito ki tafi gida dare ya yi ni zan kula da matata, tunda kai tunda ka yi aure ka rikice baka da ta ido!" KADER ya fada yana kallon Hisham
Hisham ya tabe baki ya ce" Dama bani da ita, kai yanzu ka duba ka ga tunda safe fa Tati ta zo, ni dai dan Allah ka fada mata ba'a yiwa amare haka, barinsu ake su gane a sama suke ko a kasa kafin a ringa zuwar masu, kuma ta fitar da mu ko mema aka masu wa ya sani, ka ga kuma dai ta zaunawarta a ciki shi yasa fa na ki binsu dan kar a je ta zaune, aman kuma ka ga shiru kar dai ta kauro nan in shiga uku!"
Kader zai bashi amsa suka hango Tati ta fito ta nufo motar hakan ua saka Hisham yin murmushi ya bude motar ya tsaya kasa kasa ya ce" Na rantse maka yau idan kuka yi fadanku da wancen yar uku dala din ka zo min da asuba sai na karya maka hannu"
Kader ya gyada kansa ya ce" To kuma da yaushe zan fada maka? Ka ga fa har yanzu ba wai mun shirya bane ba fa, ta kulani ma na kasa samu sai ta gama saurarena mudul mudul ta yi cikin gida gajarta uwa inuwar dogo da yama!"
Hisham ya yi murmushi ya ce" Idan ka shafa min lafia da matata zan san abin yi a daura maku aure na huta, idan ba haka ba Allah ni zan je in ce mata kar ta kuma kulaka baka da lafia"
Kader ya saki baki yana kallonsa daidai tati ta iso
Sosai Tati ta ringa yi masa nasiha, jadada masa take ya rike amana, ta kuma fada masa cewar ya kasance mai adalci dan gobensa kafin su tafi
Da dan sasarfa ya nufi falon
Yana budewa ya ganta zaune wajen da Tati ta barta sai dai a yanzun ta dora fuskarta a rafin hannunta dake ajiye saman cinyoyinta yana dan shashekar kuka kasa kasa (Ki kula hajia, kukan nan yana da mahinmanci, koda bakya so koda baki ga dalilin da zaki yi kuka ba ki kwatanta, ki yi na kirsa, ba kawai dan soyewar ido da zumudi ki wani kerare idonki idonsa, gobe kukan me zaki yi ya dubeki bayan baki yi na rabaki da iyayenki da ya yi ba?😃 )
Da sauri ya nufeta yana mai ajiye ledar dake hannunsa
Gabansa ne ya ji ya fadi a lokacin da ya ga da gaske ba kunnayensa bane le jiyo masa , kuka ne take
A dan rikice ya saka hannayensa ya dagota ya budi bakinsa zai yi magana sai kuma ya shagala da kallon fuskar tata
Ya salam, wani irin bugu zuciyarsa ta kara a lokacin da ya ga fuskar tata, ba wani kwaliya a jiki sai dai an saka mata gashin idon nan naturel masu matukar kama da na ido masu laushin gaske, sai kwalin da aka rangada mata sosai ya kama idon masha Allah, sai dan jan baki kalar pink mai haske sosai wanda aka shafa dan kadan sosai aka murje shi ya hadu da lalausan lebunnanta
Hawayen da suka zubo mata suka kuma jika gashin ido sai dan yannayin da take yiwa bakinta na tabara tana kukan sakalcin ya saka shi janyota da sauri ya rungumeta a jikinsa ta yadda sai da ta ji zata rasa numfashinta da dan karfi ta ce" Hamma numfashina "
Kafin ya sasauta mata rikon ya cirota a jikinsa yana kuma kallon fuskar tata
Ajiyar zuciya yake ta saukewa sannan yana yi mata kallon da kamar zai dauketa da idannuwan nasa
A sanyaye ya iya janyo ledar, kasancewar tak away ne cikin yar robarsu suke harda su cokula da aka nade a paper ya ajiye a saman table ya janyo shi kusa da su sosai sannan ya bude ya kuma juyowa yana kallonta wace itama shi take bi da kallo duk wani motsinsa na kara bugun zuciyarta cike da kaunarsa da begensa da jin kamar ta ringa ihun sunnansa tana fada masa irin son da take masa
A hankali ya janyota jikinsa sosai bayan ya bude ya kuma saka cokalin ya dibo ya dubi fuskarta cikin idannuwanta a sanyaye ya ce" Ha "
Kallon nasa idannuwan take da suka shanye sosai suka yi wani lulu da su lokaci daya kuma tana lalubar wajen da zata iya samu a cikinta dan kuwa a yau irin abinda suka titika mata ya zarce abinda ta saba