Showing 30001 words to 33000 words out of 180809 words

Chapter 11 - DUK NISAN JIFA COMPLETE HAUSA NOVEL

sajida   

02 Feb 2025

12959

ba, ana tafiar nan za'a wayi gari mai gida zai karro aure, mai gidan nan naki da ya nuna maki baya son kyale kyali zai kyalo wata kyalareriyar yar cika watau yar a ci da cokali ya wanke ya wanko ya wanka maku a cikin gida, Madame zata ringa tafiar yan gayu a baban falo tana juya mazaunai koda kuwa bata da su, ke gaki da wata zumbuleliyar riga irin ta mu shige mu ukun nan tamkar kakarki ta wanke ta baki, kin daura dan kwalin tsohuwar shadarki wuyanki dauke da carbi kina janye da yara watau ke taki ta kare ko na ce ke a tunaninki biyaya kike yiwa miji kuma zaki ci ribar hakan, a hankali mai gidan zai kwatanta hanna amarya cika kwaliya.....amarya yar zamani ta nuna masa aa, kwaliyar nan fa da ita ya ganta ya kyasa a tunaninta shi mai taya ta ne, zata dauko bangaren adini ta ce da shi haba darling kwaliya ai tana cikin tsafta, wanda bashi da tsafta aljannah ta haramta a gare shi...sai kawai ta fashe da kukan kisa ta dora tana fadin Haba honey watau zuma, me ake da mace ba kwaliya ba kanshi ba yanga? Ai du mace ba wannan ta mayar da kanta tinkiya .......,

a hankali zai saki murmushi ya ji kalamai ga kisa ta mata zai rungumi abinsa a ci gaba da gashi, ke dai bara na takaita maki sannu sannu kayan Allah wata rana kin zo wucewa da shigar nan taki ta katon hijab da shiri irin na ustazai dan kar ki taka dokar mai gidanki zaki wuce ta gefensa kamar daga sama zaki ji wata tsawa , kafin ki warware za'a dora da fadin ke wai rainon ina ce? Shikenan wannan shiga ba dare ba rana tamkar *TINKIYA?* ke bakya jin kunyar a ganki a waje haka ko a shigo cikin gidana a ganki a haka? (Watau du shekarun da kika yi a hakan sai yanzu ya fahimci ba daidai bane ), Haba ki cenza hali wannan sai ace ni ke tauye ki bayan Allah na ganni daidai gwargwado ina yin bakin kokarina"

Bilkisu ta dakatar tana kallonta a hankali ta ci gaba da fadin" Ke baki ji dadin yannayin jikinki da irin shigarki ba, ko a musulunci baki yi yanda zaki ringa kwadaita masa zama da ke ba dan a ganninki kauna ta saka shi nuna maki daina kwaliya, ke baki saka a cikin mata kika juya kika motsa zuciyoyin mataye ba, ke dai gaki nan kina tafe kamar mai jira ya ambaci sunnanki tamkar Tinkiyar kin dakako a guje, har ta kai ya fada cewar ke din nan Tinkiya ce! Sai kuma a dauki kafa a fita ana yamadidin cewa yau wane ne ya dube ni ya ce da ni Tinkiya, suma iyayenki dan son kai ba zasu dubi yannayin naki ba za'a kebe baki a ce' Uhum, namijin? Ba aure ya yi ba? Ki yi jiran komai daga gare shi' wata harma zata ce ' kadan daga asirin kishiya ko makircin kishiya to walahi ki tashi tsaye dan sone ake a shafe ki a idannuwan mijinki!' Ke baki ga irin ilar da kika yiwa kanki ba, ke baki ga shafe kanki da kanki da kika yi a idannuwansa ba dan bakar jaraba daga an dan zauna an samu y'aya uku hudu shikenan ke ga kushewa a tsufa , ga guzuma kin saki jiki kin tara teba kina shirme da datin zani a cikin gida! Laila idan ke baki san darajar kanki da kanki ba D'anki ne shi da zai sani?"

Laila kam a yau sai ita kanta ta ringa kallon Bilkisun kamar ta ga bakuwar halita, ta sani sarai Bilkisu na tare da abubuwan mamaki, aman bata taba kawowa ranta cewar wai Bilkisu har ta san ta kan rayuwa haka, ko ta gane wani abu a cikin rayuwar kanta har haka ba, duba da irin shagwabarta, shegantakarta da shiriritarta

Bilkisu ta saki hannunta tana kara gyara zamanta ta ce" To idanma na auri namijin da zai hanna min kwaliya, juyi a gabansa, sangarta, fayacewa soyaya harafofinta ai na cuci kaina! Kai ina dole na cazawa mijina kwakwaluwarsa da tunanin yau a yaya zan tarda ita? Dole na ringa shigar da zata saka mijina yiwa harta mata iyaka da bangarenmu walahi"

Da mamaki Laila ta talabe kumatunta ta ce" Ashe kema yar duniya ce? To aman kin san da abubuwan nan me yasa kike nuna masa ke baki taba son sa ba? Me ya sa ba zaki tunkareshi ki ce da shi kina son sa ba? Sai ki yi ta yi masa biyaya ?
Bilkisu a rayuwarki ta duniya a shirye kike ki aikata aiyukan yayanki koda tsakiyar dare ne, girki na gidan duniya kina koya ne dominsa me hakan ke nufi? Ko ka san abu ne ba zaka anfanuwan kanka ba? "

BILKISU ta sauke kafa daya kan dayan da ta dora ta dora hannayenta saman table din da suke zaune tana kallonta ta ce" Aman ban taba sannin cewa ke baki da dogon tunani ba sai yau, a zamanin Annabi Muhammad sallalahu alaihi wa salam aka yi furtawa Namiji kalmar so ya amince har ya auri mace a je a shinfida rayuwa mai kyau a zauna lafia ba zamaninmu ba,a yanzu idan kika yi haka bara ki ji sunnan ki a duniya *Marar kunya, marar kamun kai, ko kai son maza* danma kar na fadin dayar mumunar kalmar
A wajen wanda kika furta hakan kuwa in mai adini ne mai kuma bin dokokin adinin, aka taki sa'a shima yana mutuwar son ki....zaku je kadaran kadahan, aman na rantse maki sai an wayi gari namijin ya ce da ke yau yau ga masifa yana zamansa kika nuna kina son sa, kika nace masa sai da ya aure ki yazu ga fitina ta ishe shi, shi fa baya son takura a barshi ya huta!
Wanin kuwa zaku zauna kulun yana cikin alfahari da tuna maki cewar ke fa kika ce kina son sa tsabar kyansa(lolz) ke kawata matasalar duka a inda ta fi tsanani idan da rabon a yi aure za'a yi, za'a je gidan auren ki sha wahalar rayuwa, domin ko wani abu ya hado ku sai dai ke ki yi hakuri ki hadiye , ba daga kafa, ba kawar da kai domin ke kike sonsa ba shi yake son ki ba, ke zaki ci bakar wahalar zama da shi ba wai shi zai zauna ya hadiyi abubuwa ba saboda ke, idan kuwa dama dan iska ne zai yarda da soyayar nan, ya yi anfani da damar nan, koda kuwa ke din mai kilace kanki ce, mai kiyayewa ce sai an wayi gari ya rinjaye ki ya tafka maki muguntar da zaki kasa gane hanyar gidanku, ya kwace maki abinda Allah ne ya baki, sannan ya ci gaba da wulakanta ki, ki tashi a banzar bazara, *ke ba ga Mahalicinki ba, ba ga iyayenki ba, ba ga yan garin ba, ba ga shi din ba"*

Shiru ta yi na dan lokaci tana hanga ajinsu, gannin ba'a fito ba ta dan cije lebenta na kasa domin yau sai ta kirtawa malamin da ya kore su iskanci, haka kawai dan ya tsane su ya kasa barinsu su zauna a aji ko sunna so sai ya wani ringa korar su bayan biya suka yi, dan kawai ta ce EPS ba abin koyarwa bane a aji? Ta ci gaba da fadin" *Biyaya* , ya zama wajibi na yiwa Ubana Biyaya! A yanzun Yayana shine UBANA domin kuwa a wannan matsayi muke da shi, yaya kike so na kasa amsa kiran abana da gudu? Yaya kike tunanin zan yi sanya da bangona majinginata da ta mahaifiyata? Ke yayana Ubana ne zan yi masa biyaya ne har karshen numfashina, da wahala ki gane abinda yake zuciyata Laila har sai na bayana maki idan lokacin hakan ya yi..............."

Da sauri ta mika hannu ta dauki jakar Lailar ta ce" Bani compa "

Laila ta sauke ajiyar zuciya ta ce" Me zaki yi da compa kuma? "

Bilkisu da ta riga ta ciro trus din Laila ta buda ta ciro compa din mai tsini biyu ta cire hijab dinta da sauri ta ajiyewa Laila ta juya ta yi hanyar wajen ajiyar abubuwan hawa na malamai

A hankali ta ringa bi tana kallo har ta kawo daidai motar malamin su na EPS, wata yar karamar mota baka mai kyau

Dukawa ta yi wajen tayoyin ta maida hankali ta yi aikin da ya kawota da sauri sannan ta mike ta koma wajen Laila da ta hada kayansu ta yi tsaye tana jiranta ita da fareeda

Murmushi ta yi ta mika mata compa din suka tsaya sunna kallo ana ta firfitowa

Maimakun su tafi sai kawai Bilkisu ta ki tafia har sai da makarantar ta kusan watsewa baki daya sunna dariar iya shegen da ta yiwa tayoyin motar Malaminsu

Sai da ya nufi wajen motar sannan du suka nufi wajen baburansu dan tafia gida

A lokacin da ta zo daidai shi ya tsaya ya rike kugu cike da mamakin gannin tayoyin motarsa na baya sun zube ba iska ba komai bayan lafia lafia ya barsu. Tsayawa ta yi ta dan dage casque din dake kanta

Murmushi ta masa a bayane ta ce" Sai Malan, Allah ya sa da yan cenjin hawa adaidaita sahu ko yauma bashin yan kofar IPES din zak'a ci?"

"BILKISU Jauro na fi ki danyen kai, zaki gani dan wannan maganar sai na maimaitawa Professor ita " ya fada a zafafe yana hararanta

Bakinta ta tabe kasa kasa ta ce" da tsofo ne da yan makarantar nan zasu kashe min shi, komai kankantar laifi a wani kwasa a fada masa, du sai na goge numbobinku a wayarsa kitika kitikan karti kuna kai karan yara kannanu kawai! "

Shata ya yi da baki yana kallonta har ta kunna babur dinta ta matsa shi da kyau ya yi kuka sosai sannan ta caka giya ta daga abinta

Abinda ta yi niyar kuwa sai da ta yi, watau siyan karamar waya samsung fara kar ta saka a cikin jakarta ta baya ta rufe da hijab dinta ta dauki hanyar gidansu cike da tunanin yanda zata bilo anfani da waya yayanta bai sani ba


Tana zuwa ta tarar da motocin gidan kaf sunna nan harda bakin motoci hakan ya nuna mata cewar yana gidan

Murmushi ta yi ta sauka a babur dinta ta kai dubanta bangarensa

Baya kofa aman da takalma a kofar irin sahu cikin nan har kamar biyar take hange

Wani murmushin ta yi ta juya ta nufi bangarensu da salama a bakinta

Ido hudu suka yi da budurwar, bata san dalili ba sai ji ta yi gabanta ya kwonci kwonci ya fadi, Kyakyawar Budurwa ce mai sasaukan yannayi, a irin zaunen da take zaka fahimci ba dai duwawu ba domin kuwa gasu nan sun bayana kansu sun baje kamar ba na ita kadai ba
Kanta ba dan kwali, kanta dauke da kitso manya na gashin kanta hakan na nunin irin cikar gashinta domin kitson ya yi mata kyau, fuskarta ba kwaliya sam sai hannunta dauke da watsetsiyar wayar android dinta tana dan murmushi zaune dangalgal a saman kujera

Murmushin da ta kuma sakarwa Bilkisu ya sakata dan kifta idannuwanta aman bata mayar mata da martani ba

"BABYNA, oyoyo " ta tsinkayi muryar Tatinta na mata oyoyo harma tana bude mata hannu irin ta zo din nan

Sai kuma ta ji sansanyar muryar sanyin zuciyarta na fadin" ya haka kin coge a bakin hanya kina bin mutane da kallo Bilkisu kamar wata marar wayau? Zo ki gaishe da baki mana " ta karashe a dan hasale kadan dan ta farkar da ita da kallon da ta ja ta tsaya tana yiwa matan biyu da bata sani ba

Matar ce cike da yannayi na yar dagwas gwas ta dago hannunta na dama ta ce" Wauh, masha Allah, wannan yan matan fa ko dai kanwar docter ce hajia? Kai aman wannan a bani ita na koma da su na hada da AISHA wayo yau na yi y'a nima "

Cikin ikon Allah a tsayen nan sai ta kasa motsawa , kamar wata wace aka sakawa stop ko ake son ganar da ita mutane ne ba aljannu ba a gabanta haka ta tsaya tana mai bin su da kallo

Mama ta dan tabe bakinta da takaicin tsayuwar Bilkisu a wajen nan, ita bata shigo ba ita bata nufi dakinta ba ga baki ta wani ja ta tsaya tana bin mutane da kallo, hakan ya sa ta dan daga muryarta ta ce" Ke lafia ? "

Firgigit ta yi daga tunani da kuma mutuwar jikin da ta ji sun sameta a shigowarta ta kikifta ido kamar sau biyu sannan ta daga kafa a hankali ta nufi wajen su Tati da bakuwar nan domin sun fi kusa a irin zamansu fiye da mama dake dan nesa kadan tana gyaran salak din da ta tabata na yayanta ne

A hankali ta dora lalausan hannunta a cikin na matar nan dake ta yi mata murmushi , muryarta sanyaye ta shiga gaishe su da gida da yiwa bakin sannu da zuwa duda bata san daga inda suke ba

Matar ta janyota kusa da ita sosai ta dan shafa gefen kuncinta ta ce" Da ace na samu D'a namiji a duniya, tabas da koda matansa uku sai ya kara da wannan babyn, an bata baci ba, yarinyata zaki zauna da ni a matsayin mamanki? "

Sai kuma ta maida dubanta wajen Mama da Tati ta ce" wayo Hajia ku bani ita, ina son y'a mai baby face jibi dimple dinta masha Allah "

Mama ta yi dan murmushi da yannayin raha ta ce" wai wacece mai kyan? Wannan mai munin yar? Cen ku je ku tafi ni dai na yafe Hajia "

Tati ta ce" Aa fa, muni fa? Kina cewa a tafi d aita so kike yaronki ya bi mu aunty? Ai inaga ko aure ya yi ba zai bara maki kanwar nan tasa ba"

Ita dai Bilkisu kanta sade yake, hannunta cikin na bakuwar nan

Tati ta ce" Yauwa tashi ki je ki yi wanka ki cenza kayan nan ki dawo maza ga abinci,"

Kamar jira take ta yi saurin mikewa ta kama hanyar zuwa dakinta, sai dai bata kai ga shiga ba Tati ta yi kiran sunnanta hakan ya sa ta dakata ta juyo tana kallonta ba tare da ko ta kifta ba

Tati ta ce" Ga yar uwarki nan, ku je tare ta yi wankan itama ta cenza kayanta sai ta adana kayan nata a dakin ki , Aisha ta shi maza ku je "

Mama dake idasa hade kwai din da ta yanyanka mai yawan gaske cikin salak din ta kai dubanta fuskar Bilkisu, ba dan komai ba sai sannin wacece Bilkisu, a rayuwarta yarinyar akoy shegen kyankyami, Bilkisu tana da wani irin Kyankyami na mamaki, a duniyarta bata son a shiga bayinta, ita kanta tana yawan wanke bayin ne ko gajiya bata yi a kai a kai, idan aka yi baki ita dai kar a yi mata anfani da abubuwan anfaninta da kuma bayinta ,

Ita Bilkisu rasa me zata yi ta yi tana nan tsaye kamar bakuwar waje har Aisha ta karaso kusa da ita

Tsayawa ta yi itama tana facing dinta, a hankali ta ce" Bilkisu, Sannu "

Ajiyar zuciya Bilkisu ta sauke , da kyar ta iya ciro murmushi a kan lebunnanta ta sakar mata sannan ta juya ta dan fara tafia , sai kuma ta ja ta tsaya muryarta cen ciki ta ce"


🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾
*DUK NISAN JIFA*
_(K'asa zai dawo)_
🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾

_RUBUTAWA_

*SAJIDA*

*SADAUKARWA*

*GA*

*MASOYA NA*


πŸ’«βœ¨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🀝

β˜† *[ T.M.N.A]* β˜† πŸ“–πŸ–ŠοΈ

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_


12

Muryarta cen cikin makogwaronta ta furta" Sannun ki "

Daga haka sai ta yi gaba

Murmushi Aisha ta yi tana bin ta a baya, a kasan zuciyarta kuwa fadi take ai gwara ke da shi, ke din da sauki sauki jan ajin a kansa , mutumen da ko kallon arziki ban samu ba da na gaishe shi?

A haka suka karasa dakinta

Bilkisu ta nemi waje ta zauna bayan ta nuna mata bayin

Ajiye kayanta ta yi nan kasa bayan ta ciro brosh da soson wankanta sannan ta nufi bayin

A hankali Bilkisu ta kai dubanta wajen jakarta
Tsai ta yi na dan lokaci a kasan zuciyarta ta shiga ayanawa 'Du dakunnan gidan nan a rasa inda zata shiga ta zauna sai nawa? Bayan mama ta san ba zan taba sakewa da wata haka a cikin dakina ba? '

Bakinta ta kara tabewa tana zaunen nana ta kuma tambayar kanta 'Yaya aka yi batai min ba a zuciyata? Yaya aka yi yannayinta bai min ba? '

Jin alamun za'a fito ya shaida mata cewar ta gama abinda take dan haka da sauri ta cire dubanta a wajen kayanta

Tana fitowa sanye da sket din da ta yi wanka da shi ta ja shi cen saman kirjinta

Sai a lokacin Bilkisu ta mike bayan sun yi ido hudu da Aisha ta sakar mata murmushi

Itama murmushin yake ta mayar mata sannan ta nufi bayin

Bata iya koda cire tufafin jikinta ba sai da ta wanke bayin kal kal sannan ta bude tagar ta saka turare watau air freshener

Wajen da tawuls dinta suke ta bude ta ciro ninkake wankake ta rataya

Tana cire tufafinta sai da ta wanke su ta matse su da kyau sannan ta saka cikin bokici ta ajiye gefe

Ta zo daukan soson wankanta ta ga na Aisha ajiye nan ba cikin abin kilacewa ba hakama broch dinta gashi ba mai murfi bane nan ajiye

Daukansu ta yi tana yatsine fuskarta ta kai su wajen pampo ta kunno ruwa masu dumi ta shiga wanke su cikin nutsuwa da ruwan zafin nan

Sai da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login