Showing 132001 words to 135000 words out of 180809 words
ciki abinta
HISHAM ya talabe habarsa ya ce" Toh fa, aman Billy ka ga karamima wahala yake bata, ita kam kashinta bai yi kwari ba, bata son abu mai wahala komai a hankali take yi bata son ta sha wuya "
Kader ya gyada kai ya ce" Hakane "
Hisham ya sake kallonsa ya yi murmushi a hankali ya murza yan yatsunsa na tsakiya ya ce" Ka ga, ka kiyayeni daga nan har a dauara aurena da Bilkisu, walahi kaina hade min komai yake, na kasa tsayawa waje daya, na kasa yarda wai ni zan malaketa ni din nan, to hakan ya sa ko tiyata ba zan yi ba har a daura mana aure dan bana son manta alura a kwakwaluwar wani, kai kuwa idan kana min surutu baban abinda zuciyata ke fada shine na kama wuyanka na karkatar da kanka na dali jijiyar nan dake bayan kanka kusa da wuyanka dif ka dauke sai na tabata ka dawo, yanzu haka saura kiris wacen mai karfin mazan ta katse ni"
Kader da ya zarro ido sai ya kuma gyada kai bai ce komai ba, hakan ya sa Hisham gyara zamansa da kyau du suka yi shiru kamar ruwa ya cinye su
A kdan sun dauki minti talatin kafin Hisham ya bude motar ya fita ya dan tsaya bai rufe ba ya ce" kuma mun kauro ne in kuwa bai maka ba ka maida mu gida!"
Kader dai bai ce komai ba sai da ya rufe masa motar ya ja madubin da kyau ya dan leka lokacin Hisham ya fara yin nisa da motar ya ce" Gabjejen banza mai cin zalin yara, Allahn da yasa ai inada kafa bare na tsaya ka summar da ni dan kawai ana bakin cikin bakina ya fadi magana sahihiya ta gaskiya, to ta Allah ba ta mutun ba yanzu Kadiri ya fara magan, kuma in ka kuma ce min kadiri sai na fadawa Bilkisu kana tsoronta, sannan in dai mata ne ka bi su a hankali da kake tafe kana rangaji da abu a hannu sai sun tsotse kaf madarar ka dawo kana ihun azaba kak!"
Ikon Allah kawai Hisham ya tsaya kallo sai da ya gama sannan ya shiga kokarin yin ribossssssssssssss ta hanyar kai hannunsa dan murda ky din ya kunnu gaba daya domin da farko kunnawar fari ce, hakan ya sa ya iya tada madubin ba tare da ya kunna motar gaba daya ba
Gannin wayam ba kys din ne ya saka shi kallon wajen Hisham da sauri
Ai kau Kys din ya ganni a hannunsa hakan ya saka shi dora hannayensa a kansa a bayane ya ce" Ashe kader baka da hankali? Watan cin yan garinku ne ya kama ko tsautsayi ne wannan tashin hankali yana gudu kana binsa?, to sai ka je ya ragargaza kasusuwanka da dukan wani abu haka idan ya so sai a kaiwa Farida sauran......."
......................BILLY
Murmushi kawai suke yi sunna sauraron magangannun Gimbiya, a sanyaye ta ci gaba da fadin" Ba wanda ya isa ya tsara wani abin har ya kai da wanzuwarsa face idan Allah ya bashi wannan dama, matsalarki ba matsala bace idan har kika bi hanyoyin da suka dace, shin bakya sonsa ne har cikin khalbinki ko fushin zuciya ne ya saka shi zama haka kin san hakan na iya sakawa ki ji kin tsane shi....."
A hankali yannayin fuskar Bilkisu daga yannayin murmushi ya ringa rikidewa yana komawa bacin rai, muryarta a yannayin fushi fushi ta ce" Du irin yadda yake nuna damuwarsa a fili sai na same shi da aikata abinda bana tunanin zai iya da watana!"
Murmushi Najeeba ta yi kamar ba zata yi magana ba, cen ta ce" Kamar me fa? Meye ya aikata da watan ki? "
Sai a lokacin suka zarro ido ita da laila, da sauri ta rintse idannuwanta dan jin kunya sannan ta shiga inda inda ta rasa ina zata saka ranta dan kunya
Najeeba ta kuma yin murmushi ta gyara zamanta ta ce" Baki sani ba, ai ba soyaya ba, ko me yake ji a game da ke yana iya zubar da damuwarsa a jikin wata, wannan abin da kika gani tabas baki da yadda zaki iya hanna shi duban watanki, komai karfin soyayar nan kar ki yaudari kanki da kannanun shekarunki ki sakawa ranki dan ana sonki ba za'a kalli wata ba, wata ba zata birge shi ba, idan kika sakawa ranki haka zaki cuci kanki da kanki, domin shi wannan lamari da baki kaman sunnansa ba abu ne mai bijirowa, yanna kamawa ne, sannan kar ki yi mamakin ya tashi a kan wace bata kamo koda farcenki a hafuwa ba........., Bilkisu na fi so ki yi kishi mai aji ina so ki yi kishi irin na amintaka, baban kuskurensa yin shiru da soyayarki a zuciyarsa wadda Mai martaba ya fara ganni kafin ya nuna mana, jikinsa bari yake idan kina gabansa, jarumtarsa na beman bijiro masa a lokacin da bai shirya ba, zufa yake dan yakar bakinsa kan abinda yake son amayarwa, bai san ya tafkawa kansa kuskure ba, zamu yake shi da makamansa zamu yake shi da kalaman kurma da makaho......",
Shiru ta yi na dan lokaci ta kuma yin murmushi ta ce" Zan shigi gidan naku kafin daurin auren in sha Allah "
Gaba dayansu da mamaki da kuma murna suka kasa rufe baki sai godiya suke da haka suka yi salama da Gimbiya daidai lokacin wani kiran ya kuma shigoea na mama
Bilkisu na dagawa mama ta ce" Na kawo maki gadonki ne? "
Daria ta yi tana jin kaunar mahaifiyar nata a ranta ta ce gatanan zuwa........m
A tsakanin kwanaki ukun nan da suka gabata Bilkisu ta yi su ne cikin wani irin yannayi mai wuyar fasara
Ko a lokacin da aka sanar mata daurin aurenta da Umar bata tunanin ta shiga hali na zulumi irin wannan
Rabonta kuwa da wani abu ya shiga tsakaninta da hammanta koda kallo mai tsayi ne tunda ta hango shi ta windows dinta shi da kader sunna nununawa wasu mutane guraren da ta ga ana kafa manyan runfunna a yau da yake saura kwana daya tak daurin aurenta, sam bai nemeta ba, ita kuwa ta cire shi a babin wanda zata nema a kwana kusa bale da tati ke fada mata sun tare, domin Tati na shigowa wajenta a kai a kai tana kawo mata maganin sanyi da sauransu sannan ta zauna ta yi mata hira wada hakan ke sakata jin sanyi a zuciyarta duda cinkushewar da zuciyar ke yi lokaci zuwa lokaci
A al'adance wasu na shafawa amarya lale tun sauran sati daurin aurenta, wasun kwana uku saura wasun ana gobe wasun kuwa da asubar daurin auren
Kamar yadda Mama da kanwarta suka shirya shafawa BILKISU lalle duk kuwa da irin yadda mahaifiyar Aisha ke kallon ikon Allah na sabon lamarin wai za'a shafawa bazawara lale, aman bata tofa ba domin so take ta idasa gane alkibilar tati, shin tana yin haka da biyu ne kamar yadda ta saba ko kuwa da gaske take ta dauki maganar auren nan?
Yama na yi waya ta same su daga masarauta, sosai abin ya ba mama mamaki a lokacin da ta ji sakon, hakan ya sa ta sanarwa tati
πΎπΎπΎπΎπΎπΎπΎπΎπΎπΎ
*DUK NISAN JIFA*
_(K'asa zai dawo)_
πΎπΎπΎπΎπΎπΎπΎπΎπΎπΎ
_RUBUTAWA_
*SAJIDA*
*SADAUKARWA*
*GA*
*MASOYA NA*
π«β¨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*π
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_π€
β *[ T.M.N.A]* β πποΈ
https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/
_Bismillahir rahamanir rahim_
47
Kasancewar sun yi gayya, gidan a cike yake makil da mata ana dore dore yan anguwa manyan mutane da masu dafe dafe ya saka nan da nan mata suka kirawo maza aka fitar da manyan kujerun fallon mama tsakiyar gida aka zagaye su a cikin runfar nan
Basu gama shirya wajen ba domin harda su kafet suka fitar daga dakin Hisham suka shinfida sai ga manyan motoci na ratsowa sunna shigoea fila fila da su
Dogarai ne ke firfitowa da gudu sunna kara zagaye motar da take ciki, sai da suka gama bada umarnin a saki hanya sannan suka bude mata gefenta
Cikin nutsuwa ta fito, cikin wani irin rantsatsen lesh fari kal da bakar alkyaba a sama mai duhu da duwatsu farare a jikinta, kanta dauke da simple dauri sai hular alkyabar a jikinta
A motar dake bayan tata yan mata ne har hudu suka fito kowace da alkyabarta sannan sunna rike da akwati da wata roba fara mai dauke da kaya
Irin yadda dogaran nan ke kara tatarewa ne ya sakata ja ta tsaya bata motsa ba har sai da ta yi niya da hannunta ta yafito baban dogarin wato sarkin bulala
Yana zuwa ya duka gabanta yana kwaso kirari, hakan ya sakata dan yatsina bakinta domin har ga Allah ta kasa sabawa da abubuwan nan, cen kasa kasa ta ce" Ku fita, nan gidan ba yan ta'ada ku daina hantarar mutane masu daraja"
Muryarsa sama sama ya ce" An gama gimbiya uwar gida kuma amarya a wajen mai damgaram, Allah ya huci zuciyarki mama a wajen yari da saraki ikon Allah, Allah ya fitar da ke lafia uwar gijiyarmu"
Da yannayin gajiyawa ta kara tamke bakinta cike da jin haushin wannan kirari fa abubuwa da ake mata, ta tsani wannan abu, ita bata son abin nan tana so ta shiga inda take so a lokacin da take so kai tsaye irin na kowa, sai dai kash daraja da girma na tare da zanen kadararta
Bata motsa ba sai da baki daya suka yi waje suka layu ta ga mai gadi ya rufe kofar sannan ta juyo wajen su mama ta saki murmushi a bayane ta ce" Asalamu alaikum "
Ai kam wajen du suka amsa salamar , Tati na yi mata murmushi tana mata barka da zuwa
Basu tsamaci haka ba sai gani suka yi tun daga yan matan da bayi matan dake ririke da abubuwa a hannu sun duka sunna gaishe da tsofafin wajen uwa uba Gimbiyarsu wace ita ta fara dukawa har kasa kanta a kasa ta gaishe da tsofafin nan ba dan komai ba sai dan ta saba da hakan sannan irin yadda dogaran nan suka yi masu ba zata so su juya su bar abin fada ba
Wannan abin ya saka wajen kwasar guda har sai da Najeeba ta ji wani shauki, cike da farin ciki take kallon mama wace ta mikar da ita tana sakin murmushi ta ce" Allah dai ya sa ba'a shafa mata lalle a filin nan ba mama? "
Mama ta girgiza kai da sauri ta ce" Ai tatinta ta hanna tunda na fada mata sakon masarautar damagaram ta ce mu jira"
Murmushi Najeeba ta yi tana kallon tati ta ce" Na gode Tati"
Tatima tana yi mata murmushi ta amsata
Najeeba ta juya ta amshi robar dake hannun kanwarta ta bude farin kyalen dake sama ta ce" Na kwaba lale, sai dai na yi wani garaje domin na saka an tatsa min nonon rakumi ina so a fara yi mata wanka da shi sannan a shafe jikinta da lale, sai dai ban san ko zaku yarda da hakan ba? Duba da irin hatsarin dake tatare da wanka da nonon rakumi "
Tati ta yi tsuru cike da tsoron hakan a zuciyarta, a sanyaye ta ce" Ba har mutuwa ake yi ba? "
Najeeba ta gyada kanta ta ce" Makarin samu ne, sai dai idan ka kasance kaima mai yiwa mutane abin na kume maka zuciya ya hanna numfashinka fita, sannan idan har sammu ya yiwa jikinka yawa shima yana kashewa, anfaninsa kuwa shine dumama jikin mace, idan gar budurwa ce ke kika damu gatan wanka da nonon rakumi sabuwar haihuwa wanda bai shayar ba yana gama haihuwa a tatse shi a maki wanka da shi a shada maki lale jikinki ba zai taba rabuwa da dumi da danshi da ni'ima na mata ba, koda kuwa kin haihu"
Su dukansu kall9n junna suke ga robar a hannun Najeeba tana nazartarsu
Tati ta kama robar ta ce" Mu je"
Mama ta sakar yi murmushi ta koma ta zauna tana kallo su biyu kawai suka shige ciki
Sunna shiga dakin Bilkisu suka tarar da ita kwonce saman gadonta tana cikin blanket ga wayarta a hannunta tana vidio call da Laila da farida wa'inda suka tafi saloon sunna mitar su fa gaskiya zasu dauko mai sallon din sun kada gane a kan me mama ta ce ba zata je saloon ba bayan gobe gobe daurin aure
Janye blanket din nata da aka yi ya sakata tashi da sauri domin daga ita sai yar rigarta ta barci fara wace yau fa ita ta tashi kuma bata cenza ba domin kasala da fargaba sun sakota a gaba
Murmushi Najeeba ta yi gannin irin yadda ta zarro ido tana kallonta da mamaki, hakama su laila harda ihu suka saki na murna hakan ya sa Najeeba saka hannunta ta kashe kiran da suke kafin ta fuskanci tati ta ce" Tati zaki yi mata ko? "
Tati ta gyada kanta ta dauki kwaryar sannan ta kama hannun Bilkisu suka yi ciki
Najeeba ta kwabe alkyabar jikinta ta koma fali ta amso sauran kayan hannun kannenta sannan ta fada masu su shirya fa
Tana komawa ta ringa jiyo Bilkisu na fadin" Kuma duka zan cire tati? Menene za'a min? "
Murmushi ta yi ta gyara tsayuwarta tana jiran fitowarsu, yau gata zata darji amarya
Cikin ikon Allah akai mata wanka da nonon nan mai karni da dumi domin baya hucewa da sauki
Nan da nan jikinta ya dauki wani irin dumi haka kuma ta fara jin juwa na neman kadata ita
Tati ta tareta a jikinta ta yafa mata katon tawul ta rikota ta fito da ita
Sunna fitowa Najeeba ta kamata suka zaunar da ita Tati ta riketa da kyau domin rangaji take abin daukanta yake sama sama
Najeeba ta bude lallen nan ta shiga shafa mata kamar yadda ta koya ake yiwa amare tana adu'a a bayane
Sai da ta gama shafa mata sannan ta juye sauran saman gashinta dake kunce yana digon abin nonon nan ta shiga murza mata shi sosai a jikinta tana kara murza mata sauran jikin nata da shi hankali kwonce fuda irin yadda jikinta ke rawa domin tsigar jikinta tashi take
A hankali tati ta fashe da kuka a lokacin da Bilkisu ta kifa kanta a kirjinta ta saki kuka mai shiga zuciyar nan gaba daya jikinta na rawa sakamakon abinda take ji ilahirin jikinta na dauka ga karatun da Najeeba ke yi ga murzartar da ake yi
Najeeba ta gama murzata da kyau domin ita kanta sai da hannunta ya ringa sulbi dan kuwa gaba daya suka cire tawul din suka darji jikinta
Fita ta yi ta amshi kaskon turaran wutar da suka hada mata ta dawo suka jibga mata katon barko fuskarta kadai ke waje suka aniya bambada mata turaran wutar nan yana ratsa gaban jikinta wanda kamar da wasa wannan karni da lale ya kora ta kuma bubude kofofin jikinta kanshin nan ya maye gurbinsa dan kuwa ba'a koma aka wanke ba aman gaba daya jikin ya dauki wani irin sansanyan kanshin turaran wutar
Sai da ta gamsu sannan ta kara dora kan Bilkisu a jikin Tati ta shiga yi mata tufka da gashin kanta ta yi mata rankwala rankwalan kitso kwaya hufu suka tafi har gadon bayanta suka ja fuskarta da kyau har kamar an yi mata kitso irin kananun nan
Madarar dake cikin gora mai hade haden tsumi kala daban daban da makari na asirai wanda ya zame mata jiki ta girgiza da kyau ta mikawa tati ta ce" Ta shanye duka tati, karfin jikinta zai dawo bara na amso kayan da zamu saka mata"
Tati ta gyada kanta a sanyaye sanadiyar kukan da ta yi na shafa lalen Bilkisun wace ita kuwa har yanzun take kukan ta ce" To aman ba zamu wanke mata nonon ba? Na ga kamar yana kara kashe mata jiki kar ya ilatata"
Murmushi Najeeba ta yi a lokacin da ta maida alkyabarta bayan ta kakabe jikinta ta ce" Da yana cutar da ita da ya kasheta tun kuna ciki tati"
tati ta talabeta a jikinta a hankali ta ce" Menene na kukan yar albarka? Ya isa haka mana kar ki kwonta rashin lafia kuma, kin ga fa kowa fa ta nan ya bi kin ji?, ki yi hakuri kukan naki na tayar min da hankali"
Bilkisu da kyar ta iya bude bakinta tana amsar madarar nan, du yadda ta so kin sha sai da suka tirsasata ta shanyeta tas , du kuwa irin yadda ta ringa yinkuri dan amayarwa abin ya gagara domin ya je ya zauna a cikin ba zai fito ba
A haka suka saka mata wata doguwar bakar riga mai laushi da santsi sannan bata da nauyi ko dis, suka saka mata bakar hula suka boye gashinta a ciki sannan suka dora mata alkyaba wata rantsatsiya sai walwalwal take
Ana dora mata hular tamkar wata gimbiya haka ta fito Najeeba ta saki murmushi a ranta tana ayanna 'Yanzu zaku yi kuka'
A hankali suka shiga janta suka nufi baban falon da ita, sunna fitowa kannenta suka saka su a tsakiya kowace da alkyabarta da turaran wuta gefe da gefe sauran ukun kuwa sunna watsa fulawa dayar kuwa na dauka a vidio da watsetsiyar iphone dinta
Sunna daga labule sunna fitowa sarewa ta shiga tashi , nan da nan kowa ya juyo hankalinsa wajen
Irin yadda busar ke tashi dole ta daga hankalin mutane da dama, shauki ya ringa debar da yawa wasun kuwa haka kawai suke jin hawaye na zuba ta gurbin idannuwansu
Abinda ta yi niyar yi ne ta dauki hanya, watau gaban Mama da ta kasa motsi suka nufa
Sunna zuwa suka kama Bilkisu suka tsugunar da ita gaban Mama, a nitse Gimbiya ta ce" Mama, ki yafewa Bilkisu ki yi mata adu'a zata shiga dakin miji, mama ki saka mata albarka zata je ta ga sabuwar rayuwar da bata