Showing 42001 words to 45000 words out of 180809 words
idasa faduwa ba sai da ta ganshi a irin wannan yannayi, baki daya jaruminta ne tsaye dukan halita ta kakarfan jarumin da ransa ke bace hankalinsa ke tashe sun bayana a tatare da shi.
Hawayen da take zubarwa ya saka shi k'ura mata ido yana kallonta.
A hankali ta dan rike gefen sket dinta sai kuma ta saki tana kallonsa.
Bata taba zato ko tsamani ba, bata yi aune ba, bata kawowa ranta ba sai jinta ta yi a cikin kirjinsa.
Wata irin wawuyar runguma ce ya bata wace ta sakata sakin kara domin ji ta yi zai karyata zai rabata biyu.
Baki daya jikinta ne ya dauki bari ta fashe da matsanancin kuka tana jin yanda jikinsa ya dauki zafi da kuma irin yanda k'irjinsa ke bugawa.
A hankali ya ringa sasauta rikon da ya yi mata a jikinsa, muryarsa a sanyaye ya ce" Ki ci gaba da rufe jikin ki du inda zaki je, ki ci gaba da kare mutuncin kanki Billyna, ki ci gaba da tsarewa kowani shara gida ki rike mutuncinki Billy, ki ringa cin abinci dan Allah, ki kula da shan magani idan baki da lafia, kin ga a cikin dakina babu wajen da zaki bude ba auduga idan kina da bukata ki je ki ciro adadin da kike so, Billy kar ki min bincike dan akoy abubuwan da nake jin kunyar ki gani kin ji? Billyna ban so kin ji komai a kan shirmen nan ba, idan kika yarda kika kuskure umarnin mamana du inda nake zan zo na sab'a maki ne, ko me ta ce ki yi , ki yi kar ki k'iya."
A hankali ya lalubi hannunta bayan ya ciro kati na banki a aljihunsa ya saka mata a cikin hannunta ya ce" ko nawa kike so, ko a wani lokaci kike so, ki je ki saka ki ciri abinda kike so, cod din number wayarki ce, kar ki yarda ki tambayi wani namiji abin hannunsa kin ji Billyna?"
Da sauri ta dago tana kallon fuskarsa, irin yanda ta yi ja har abin tsoro, haka kuma idannuwansa sun yi jajajir sai irin yanda jijiyar gaban goshinsa ke harbawa tana dik dik dik.
Da sauri ta kai hannunta wajen fuskarsa cikin muryar kuka ta ce" Me menene yaya? Ina zaka je? Kake min magana kamar zaka fita? Ina zaka tafi? Ka san a gari ana tsoron taba ni ne dan an san kana tare da ni yayana, ina zaka je?"
Da sauri ya cireta a jikinsa yana kallonta ya ce" Allah yana tare da ke, tsaro zai ninku a kanki domin ina tare da dukan motsinki, Billyna ko gawarki ba dai mutun ba sai dai Allah."
Yana gama fada ya saketa a wajen nan ya yi gaba.
Da sauri ta dnaga k'afarta da niyar bin sa sai dai kiran sunnanta da Mama ta yi ne ya sakata juyowa da wani irin sauri.
Da gudu ta fad'a cikin dakin ta je ta fada jikin Mama ta fashe da kuka mai karfin gaske tana girgiza kai ta ce" Mama ina zai je? Mama hala tafia zai yi? Mama a kan me zaki ce da shi haka? Me ya sa zaki ce da shi haka? Mama me yasa zaku yi mana haka? Mama tati ce? Dama bata so na? Me muka yi mata?"
Mama ta riketa da kyau a jikinta da yannayin fada fada ta ce" Yaushema aka haife ki Bilkisu? Kuka ne kike kan namiji ko kukan rabuwa da yayanki? Ya ce maki zai je wani waje ne? Ba inda zai je yana nan tare da mu, maganar soyaya ce babu na soketa ko akoy abinda zaki yi ne? Karya kike nufin mun yi maku ko me? "
Da sauri ta ringa girgiza kanta tana kara kwontawa a jikin mama.
Mama ta lumshe idannuwanta hawaye masu zafi suka kuma zubo mata, bata taba sakawa zuciyarta cewa wai zainab zata iya aikata mata haka ba, bata san dalilinta na aikata haka ba, aman sai take gannin koma meye hujarta idan har ta sameta ta nuna mata cewar ta tsawatar a kan wannan take taken yaren ai daa ta tsawatar ba tare da ta saka su yin karya ba, yanzun meye hakan? Wannan abin yana mata ciwo a kasan zuciyarta, sai irin yanda ta fahimci irin ciwon da Hisham yake ji a kasan zuciyarsa, sai ga Bilkisun nan itama ashe abin na iya tabata haka? Irin magangannunsa da irin yanda ya nuna a gaban kowa ba zai iya boye kaunarta da abinda yake iya yi a kanta ba ta hanyar rungumeta a gaban mama ya tsaya mata a rai ya bata tausayi ya sakata tuhumar kanta, magangannunsa sun tsoratar da ita, aman bata tunanin in dai HISHAM dan hakal ne zai gujeta a kan wannan! Ba zata daina hawa kan decision dinta ba, ta hau ta zauna ba zata sauka ba kuma domin Hisham sonsa take tamkar dan da ta haifa ba zata barshi ya bijirewa mahaifiyarsa ba dan ba riba
A hankali ta ce" A islamiya, yaya aka fasarta maku girman uwa Bilkisu? Wanda ya bijirewa mahaifiyarsa yaya Allah zai hukunta shi? "
Bilkisu dake jin numfashi ya yi mata karanci a hankali ta ce" Mama, zai kasance a gaban hukunci mafi muni, domin wuta ce makomarsa, an ce mu yiwa iyayenmu biyaya da dukan karfinmu in dai ba a kan sabon Allah bane."
Mama ta ce" zaki so ya sabawa tasa mahaifiyar da ta haife shi?"
Kanta take girgizawa a hankali bata ce komai ba
Mama ta kara riketa ta ce"...
*ASALAMU ALAIKUM JAMA'A, DU WANDA KE KARANTA WANNAN LABARI NA TABATA NA TABA ZUCIYARSA A KAN WANNAN LAMARI, SAI DAI KU SANI SAKONA DAKE CIKI BA ZAI ISA GARE KU BA HAR SAI NA GABATAR DA LABARINA YANDA NA TSARA SHI, INA MAI BAKU HAKURIN KU YI HAKURI KU BI ZAKU JI DADINSA IN SHA ALLAH, π taku ce yar mutan niger*
Mu je zuwa mutanena mor cmmnt mr pags in sha Allah
[7/24, 10:18 AM] BAK'A CE: πΎπΎπΎπΎπΎπΎπΎπΎπΎπΎ
*DUK NISAN JIFA*
_(K'asa zai dawo)_
πΎπΎπΎπΎπΎπΎπΎπΎπΎπΎ
_RUBUTAWA_
*SAJIDA*
*SADAUKARWA*
*GA*
*MASOYA NA*
π«β¨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*π
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_π€
β *[ T.M.N.A]* β πποΈ
https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/
_Bismillahir rahamanir rahim_
16
Mama ta kara jurewa a hankali ta ce" To ki taya shi yin biyaya dan samun aljanarsa, hakan shine so, ki taya shi Khalb hakan shine zai saka kema naki y'ayan su ji kanki, ku kadai gare mu, idan kuka fara botsare mana mun shiga uku uktie, mun shiga uku"
Bilkisu kam ta rasa kalma, bata da bakin furta koda A ne, hawayenta ya kasa tsayawa, ta rasa me zata yi tunani, eh lalle ta girma ba laifi domin shekara goma sha tara ba wasa ba, aman shekarunta basu kai daukan wannan firgici ba!
A hankali mama ta mike da ita a jikinta
Dakinta ta nufa da ita ta shinfideta a saman gadonta
Mikewa ta yi ta dauko mata litafi da carbi ta dawo ta ajiye mata a gefen kanta, a hankali ta ce" Kin ga maganin nauyin zuciyarki, kin ga maganin damuwarki, kin ga mafakarki, kin ga mai share maki kukan ki, ki fada masa, ki kai masa kukan ki, shine gatan ki Khalb"
Rana gama fada maimakun ta tsaya itama sai ta fice a dakin
A hankali ta nufi ainahin dakin Bilkisun
Budawa ta yi ta shiga da bismillah sannan ta mayar da kofar ta rufe
A hankali ta zauna bakin gadon ta saka hannayenta biyu ta dafe gaban goshinta
Fashewa ta yi da wani irin kuka, kuka mai zafi da ciwo, tana yi dukan gabanta na amsawa kanta na sarawa
A bayane ta ce" Ya Allah, ka sa ba abinda shedan ke rada min bane ya saka yar uwata guduna, ya Allah ka sa Zainab ta zo ta dubeni ta bani kyakyawar amsar da zata saka ni farin ciki da kara damarar yakin yaren nan kan soyayar junnansu, ya Allah wannan karya da na yi ka yafe mani, na yita ne dan na taya yarona biyaya, na yita ne dan kar d'a ya kalli mahaifiyarsa makaryaciya, idan har wannan karya da na taya zata kasance babar damuwa a garemu duniyarmu da lahirarmu Allah ka saka ya fahimce mu ya yafe mana, ya Allah ka dafa mana , bamu da madafa sai taka, bamu da madogara sai taka, bamu da mafaka sai taka" sai ta karashe da kara fashewa da kuka
Sai da ta yi ta koshi sannan ta ringa sauke ajiyar zuciya ta daga kanta tana bin dakin Bilkisu da kallo
Murmushi ne ya subuce mata gannin irin yanda dakin yarinyar yake, yarinya ce aman ba zata taba gannin dakinta da dati ba, kafin ta fita daidai da zannin gadonta sai ta cenza da gudu gudu ba da wasa ko sanya ba
A hankali ta daga matashin kanta, dan kuwa ta tabata a nan zata boye wani abin sirrinta dan haka suke daga ita maman har yaran , a wajen maman da suka gani sai suke yi
Wani dan litafi ta ciro an saka takarda an nadidiye shi sannan an rubuta masa kalamai kamar haka *SIRRINA*
hannunta ta dora samansa tana ta kallo
A kasan zuciyarta ta furta" SIRRINA "
Meye sirrin Billy? Wanene sirrin Billy? Billy tun da ta kai shekara goma sha hudu na gane cewa sirrinta HISHAM ne, HISHAM tun Billy nada shekara bakwai na fahimci cewa sirrinka BILKISU ce, na yi shiru na yi gum , na yi taka tsantsan ban barku ku kadai ba, na kuma ringa bugun cikin ku dan ku furtawa junna aman kun kiya, kai da ya dace ka jima da fada sai ka adana sirrinka a zuciyarka, ka tanadi rana Hisham, shi ai sirrin dake rai yakan falasa kansa a lokacin da ya yi niyya ne Hisham, na so ku da alkhairi,.......aman haka haka Allah ya hukunta hakan na nufin haka ne alkhairin ku.....
A hankali ta mike ta ringa nazarin wajen da ya dace ta kai litafin ta boye
Da kyar ta iya samun wajen da take hasashen Bilkisu ba zata je kakale kakalen cen ba ta boye sannan ta fito
Ido hudun da suka yi da Zainab ya saka Zainan saurin sada kanta daga duban Mama ido cikin ido
Fuskarta ta saki ta ce" Aa, har kun dawo ban zo ba? Ni kam akoy shiririta abincin ne nake karasawa na zo kuma har kun shigo, yaya mai jiki ina fatan komai ya je daidai "
Matar dg dake neman shigewa daki ta yi wanka ta ce" Alhamdulilah maman Hisham komai kam ya je daidai sai fatan samun lafia, domin an fitar da shi tun dazun, bara na watsa ruwa na fito na kwashi dadadan girkin nan naki mama Hisham "
Murmushi mama ta yi mata
Aisha ta ce" Mama ina mutuniyar ko ba'a sauko ba?"
Mama ta dubeta ta ce" ta sauko y'ata, yau dakina take tana baci "
Murmushi Aisha ta yi ta mike nan saman kujera ta shiga latsa wayarta tana jiran mamanta ta gama itama ta shiga bayin
Juyowa Tati ta yi ta nufo wajen Mama
Hannunta ta kama ta nufi Dakin Bilkisu da ita domin dakin du ya fi na kowa dan nesa da dakunnan dakin
Sunna shiga ta saki hannun tana kallonta ta ce" Aunty, Hisham ya zo nan kuwa? "
Mama ta kama hannunta ta nufi wajen kujerun dake ajiye biyu gefe guda ta zaunar da ita itama ta zauna tana kallonta ta ce" Ya zo "
Gaban zainab sai da ya fadi aman sai ta daure ta dan kakaro murmushi ta ce" Uhum, kin san magana muka yi da mai gidan nan namu na wajen aiki kan zai bani AISHA, shine fa nake dan fada masa zancen kafin na zo na fada maki "
Mama ta kara kureta da ita ta ce" Ah masha Allah, wannan ai abin murna ne "
Tati ta rasa yanda zata dago su yi ido hudu da Mama, sai kakawar da kai take tana ta dan murmushin yake, karshe dai ta kalli Mama ta ce" Kennan ba abinda ya ce da ke da ya zo? "
Mama ta gyara zamanta ta ce" Aa, ba abinda yake boye min komai gigitar furuci "
Ras gaban tati ya kara faduwa, hakan ya sa ta kamo hannun mama tana kallonta ta ce" Alkawari na yi aunty, ban rigaya na sanar maki ba nufina sai an yi aikin nan zan tunkare ki da maganar ki yiwa yaronki magana, sai kawai zumudina ya kaini na fada masa abinda ya faru, shine fa muka kama ja in ja da Hisham kamar ni din sa'arsa ce, karshe Hisham har cewa ya yi wai mahaifinsa na raye, abin ya caza min kwakwaluwa na ga nema ne yake ya bijirewa umarnina kuma ya nuna shi fa babyna kadai yake so, shine dan na tankwasa shi ya yi min biyaya na ce da shi kin shayar da shi , baki ga yanda ya fito ya bara min dakin ba, shi har ganni yake ko dan son raina na aikata haka"
Mama ta lumshe idannuwanta tana maida kwalar da ta taru a ciki, a hankali itama ta juyar da hannun Tati ya kasance hannun Tatin ne a kasa na mama a sama tana kallonta ta ce" AURE ai taya shi ake, Aure alkhairi ne Zainab, sannan ke din yanke hukunci a rayuwar HISHAM girmanki ne, haihuwa ba wasa bace! Ya yi ganganci da har ya daga idannuwansa ya so saba maganarki, aman zai gyara ta hanyar amsar umarninki, sai dai ina rokon ki abu daya, dan Allah koma meye nufinki a kan hirar ki da *YARON KI* ki daina sako karya a gaba Zainan, Hisham baya mutunta makaryaci komai kankantar karyar, yana iya ko me zaka fada masa gaba ya kalli tsabar idannuwanka komai girmanka ya yi maka tambayar shin na dauka ne ko na ajiyewa? Hala yake, haka halayansa suke, na yi iya yina dan gannin ko zai ringa kawar da kai a irin haka aman baya iyawa, ban san ko yanzu ke zaki iya ba...." ta karashe tana murmushi ta dora da fadin" In ba Hisham ba ai Bilkisu kanwarsa ce, duda ba haramun bane aman raini na iya shiga, in sha Allahu zai zo ya baki hakuri kuma za'a yi a lokacin da kika yanke Zainab "
Baki daya ita zainab sai take gannin kamar magana ne Mama ke gaya mata, bata ankara ba ta ga mama ta mike zata fita da sauri ta dago kanta ta ce" Amma Asma'u me yayi zafi haka? "
Mama ta juyo a dan zazafe ta ce" A kan me zaki saka na masa karya nima? A kan me ba zaki iya tunkarata da magana ba? Kin san cewa makarantar boko ce kawai ban je ba hakan ba yana nufin cewar ni din jahila ko mahaukaciya bace! A haife na girke ki da shekaru hudu a duniya , ko da ido mutun ya yi magana ina mai tabatar maki zan iya gane yarensa sai dai na yi anfani da nawa girman da datako na nuna cewar ban fahimta ba! Me kike tunani Zainab? Zan kama yaro ne na yanke hukunci a kansa bayan na san kina raye? Duda kin bani wuka da namar yin hakan tun a ranar da kika kawo min shi aman ba zan taba aikata haka ba domib kina raye a duniya! "
Sai kuma ta fashe da kuka ta kai zaune a nan wajen tana jimke hannayenta ta ce" idan baki cire ni a rudanin dake cikin zuciyata ba, ina mai tabatar maki ba zan iya yi maki duban da nake maki tun zuwanki ba! Zainab ina ce kin dawo gareni zamu zamewa juna uwa da uban da muka rasa ne, ina ce kin dawo kusa da mu ne a yanzun dan kin gane naka naka ne, har ina murna idan Mai gado na murzarki a kasan zuciyata na ce ko yau na mutu na barsu a hannu mai kyau! Zainab HISHAM, da Bilkisu ni su ne duniyata, au ne burina, dan Allah ki ce min baki katse masa hanzari a kan yar uwarsa ba sai dan kar irin aurwn hadi ya lalata zumuncin nan, ki ce min kema su ne duniyarki ba wani buri na daban ba, ki kaleni ki fada min kina tare da mu dan mu kasancewa junna zuri'a daya "
Zainab hawaye take ita kanta, kukan kuma daga zuciyarta yake fitowa, yaya aka yi ta zama mai bambancen hali da yar uwarta? Yanzun ta hanna ta gila karya gashi kuma ya zama wajibi ta kara yi mata wata, zata yi mata karyar nan ta biyu ne itama dan kare kanta, zata yi mata ita ne san kar ta rasa yardarta a kanta
A hankali ta sauko ta karaso kusa da ita ta zauna
Kamar wata yar yarinya ta dora kanta a gefen kafadar Mama , muryarta shake ta ce" Ni ina zan shiga da halayana? Ni butulu ce Asma'u, dan Allah ki yafe min domin ke uwa ce a wajena, ki sani na yi haka ne dan kawai na guje mana hade haden auren nan na cikin gida, ke kin fi kowa sannin me ake kira da aure, ina so kowa ya kawo nasa ta yada du wada ya so cutarwa yarinyata sai inda karfina ya kare"
Mama ta ringa sauke ajiyar zuciya, ba dan komai ba sai dan jin dalilin kanwarta, duda dalili ne karara marar ma'ana, aman sai ta haye sama ta zauna dan kawai ta samu nutsuwar zuciya
A hankali suka fuskanci junna, ba su su fito a dakin ba sai da kowace ta wanke fuskarta suka fito tamkar ba abinda ya faru tsakaninsu
Tsaye yake gaban baban ruwan dake kwonce a kanya, wajen ya yi shiru domin ko tsuntsaye babu, ruwa ne mai kyau mai dauke da kifaye duda zamanin ba na damana bane kifayen sun yi nisa, aman lokaci zuwa lokaci zaga ga sunna wutsil wutsil dinsu