Showing 96001 words to 99000 words out of 180809 words
baki sanni bane wallahi gani na kawai kike, amma ba komai yarinya damata kika samu."
K'aramar wayarshu ta ga ya d'auka alamar sak'o ya tura kafin ya zauna d'abas akan kujerar da bak'o ke zama, wani kallon ya sake jifanta dashi yana tunanin shi kam me zai mata idan yaje gida? Ya zaiyi da wannan gimbiya ne wai? Gaba d'aya daga jiya zuwa yau rayuwarsa take nema ta ko wane hali.
Shigowar Kader yasa shi d'auke kanshi daka kanta ya kalleshi, wani Murmushi ne ya shiga dokawa yana kallon Bilkisu da satar kallon Hisham yana fad'in "K'anwarmu ya ya? Kin samu kud'in wannan wankan ko?"
Kallonshi tayi a ranta tace "Zai kuma tsokana mana shi."
Kamar yasan me take fad'a sai kawai ya kalleta da idonshi ya mata alamar fita waje, ai da sauri kamar zata fad'i ta fita tana jin Kader na fad'in "Docter lafiya? Naga kanata muzurai kamar ka had'iyi kunama."
Da wani k'arfi ya mik'e ya nunoshi da yatsa yace "Kader ban san iskanci, ba wasa na kiraka ka min ba."
K'amewa yayi tare da sara mishi yace "Yes sir."
Cikin nuna mishi da hannu ya shiga fad'in "Ka mayar da yarinyar can gida, kayi duk yanda zakayi ta goge kwalliyar fuskarta sannan ta saka hijabinta, Kader idan baka sa tayi haka ba Allah ya bi min hakk'ina."
Ja baya yayi yana fad'in "To me yayi zafi? Wai ni ban gane ta goge kwalliya ba, yanzu kwalliyar nan ba tayi kyau ba kake nufi? Ai ko naga wallahi ta fito cas da ita, kamar z..."
Yanda ya zuro hannu zai shak'i wuyansa yasa shi cikin sa'a da dubara ya zille yayi hanyar k'ofa yana fad'in "Bani na kar zomon ba likita, kullum yarinya ta kunnaka ka sauke a kaina, tafi can jarababbe kawai, kuma na k'i nace ta goge kwalliyar."
Had'e labb'ensa yayi tare da komawa ya zauna ya girgiza kan shi, kai amma Bilkisu ta shawo kan shi da babban ludayi! To wai ko ta fahimci me yake dannewa ne a kan ta shiyasa take wani abun? Cike leb'e yayi tare da jin k'wafa alamar zata sani d'in nan idan suka had'e gida, dan sai yayi zama na musamman ya shirya kalar yaren da zai mata ta fahimta,
Sai kuma ya ringa cicije lebensa na kasa a kasan zuciyarsa ya kuma ayana 'Ka fadi ba nauyi Hisham, yar jaririyar kanwarka ce kake yiwa haukan nan? Kai Hisham kai Hisham"
Assalamu Alaikum
Da fatan kuna lafiya masoyanmu.
Ina son in fito maku a mutum don in maku bayanin abunda ke faruwa.
Da farko mun ce zamu aje rubuta *DUK NISAN JIFA* saboda mu maida hankali kan littafin *AUREN YAK'IN MATA* na *KUD'I* da nike rubutawa, amma da yawa daga cikinku sun mana korafin kada muyi hakan don Allah saboda littafin ya dauko dadi kuma anyi nisa ba laifi, ni kuma dalilina nayin hakan shine
1. Na fiddo littafin kudi, kalilan ne suka siya
2. Ina son maida hankali wajen na kudi domin fita hakkin mutanen da sukayi mun kara suka siya
3. Hankalina na karkata kan na kyauta alhalin na kudin ne hankalina yafi kamata ya karkata a kai.
Idan har zakuyi patronizing dina ana kudin da nakeyi insha Allah zan hada duka biyun in dinga maku posting akan lokaci, idan kuma hakan ya gagara dole in aje daya inyi daya wanda kuma dole na kyautar zan aje in maida hankali a kan na kudin.
Ina fatan zaku fahimceni, ba nayi hakan da niyya bane ko don in bata wa wasu rai, yin hakan ya zame mun dole ne duba da yadda na fiddo littafin kudi amma mutane kalilan mafi karancin kalilan ne suka siya. Ina fatan zaku mun kara ta dalilin kaunar da kuke mun ku sayi littafina.
Ga mai bukatar siyan littafin yana iya tuntubata kai tsaye ta wannan number din
*+277-93811618*
Mun gode sosai
Muna sonku domin Allah
[7/24, 10:19 AM] BAK'A CE: 🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾
*DUK NISAN JIFA*
_(K'asa zai dawo)_
🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾
_RUBUTAWA_
*SAJIDA*
*SADAUKARWA*
*GA*
*MASOYA NA*
💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝
☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️
https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/
_Bismillahir rahamanir rahim_
37
Alhamdulillah, munsan Allah ya azurtamu da masoya masu d'umbin yawa a k'asarmu Niger da d'ayar K'asarmu Nigeria harda ma sauran kasashe na nahiyar Africa.
Ina masoyan *Sajida* da *Samira* littatafansu??? Marubutan nan masu rubuta littafin *Bak'a ce, Mage* da *Badak'ala, Allura ta tono Galma* wanda kuke kauna har cikin ranku. Ku matso kusa don nuna musu d'umbin soyayya da kaunar da kuke musu inda suka zo maku da sabon littafinsu mai taken *AURE YAK'IN MATA* daga jin sunan kunsan cewa littafin kunshe yake da darussan rayuwa wadanda suka shafi rayuwarmu ta aure,kalubalen da mata ke fuskanta a gidan aure da kuma yanayin zamantakewar aure na zamanin yanzu, duk da ba sabon abu bane, amma namu ba irin nasu bane, sai an gwada akan san na kwarai.
Ga mai bukatar wannan littafi *Farashin mai sauki ne* naira dari uku (300) kacal ga yan Nigeria, yan Niger kuma dala dari ne (500)👌 zaka samu wannan littafi mai dubbin darussa a cikinsa.
_Domin tura kudin siyan littafin ga yan Nigeria sai a tura ta wannan account number din *2377403479* Khadija Umar Abubakar. Zenith Bank. Kuma akwai damar tura kati ta wannan lambar *081-686-594-14* IDAN KA YI TRANSFERT SAI KA TURA SHAIDA TA WANNAN NUMBER +227 93 81 16 18._
_'Yan Niger kuma sai ku tura katin MOOV ko Airtel ta dala dari watau 500 francs ta wannan lambar *+277- 94-98-56-52*_
Mun yadda daku, mun aminta da irin kaunar da kuke muna don hakan muna da yakinin cewa zaku siya don nuna mana kalar soyayya da kaunar da kuke mana da littafanmu.🥰
Kader na fitowa ya ringa neman ta inda zai ga Bilkisu aman cikin ikon Allah ba ita ba labarinta ba babur dinta
Wajen mai tsaron kofar ya je fuska a hade ya ce" Kai ina kanwar Docter? "
Daria ya yi yana dan tafa hannu ya ce" Oga Kader yau kaima ka ga mace ko? Walahi ni da kake ganina a nan kasa ganeta na yi tsabar kyan da ta yi, wai ashe tana da kyau har haka? Kai masha Allahu, yanzun ta fice a babur dinta aman gaskiya babur bai dace da hajia ba idan an tashi auren naku ka siya mata mota"
Kader ya gyara tsayuwarsa yana kallonsa cike da mamakin wanda ya fi shi gyara zance a yada ya ga dama, bai san lokacin da ya ce" Da ni din, da kai din idan muka yarda muka yi wasa da garwashi sai ya batar da mu, shege baki uwa kalangu daga tambayarka ka kama min zancen da idan a gabansa ne laifina zai gani, to wannan da kake gani matar Oga ce in sha Allah "
Ido gaba daya ya zarro ya ce" Ce Allah? "
Kader ya yi sakalau da bakinsa yana kallonsa, kai shi mantawa yake Kaca fa ruwa biyu ne, dan haka sai ya juya wajen motar yana kokarin shiga dan ya bi bayanta sai ga HISHAM ya fito dan zuwa amsar shayi wajen samarin sojojin dake dorawa duda mika masa nasa suke aman shi da kansama yana fitowa ya amsa bale yanzu da yake jin kansa na neman fashewa shayin kadai zai sauke masa da ciwon kan nan
Da sauri Kader ya duke dan ya labewa ganninsa, ya san dai ba zaman shan shayi yake yi na tsayin lokaci ba
Hisham ya amshi shayin yana dan murmushin gaishe shin da suke yi, sai da ya sha ya dan lumshe idannuwansa sannan ya yi masu salama
Tsayuwa ya yi wajen motar ya dan kwonkwasa
Kader sai da cikinsa ya dan murda ya dago da sauri suka yi ido hudu, da mamaki ya ce" Da ka ganni? "
Hisham ya masa alamun ya cire lk din da ya saka sannan ya zagaya ya shiga ya zauna yana ta sauke ajiyar zuciya a hankali ya ce" Tana ina ? "
Kader ya sauke ajiyar zuciya ya ce" Kaca ya ce ta tafi wai, shine zan bi bayanta da gudu aman kuma ban san ina ne wajen auren ba"
Hisham ya dan yi shiru yana jin takaicin ratsawarta titi a haka, aman kuma ya san koma meye yanzun ta kai gida dan kuwa ya mata kashedin zuwa wajen auren ya tabata ta tafiarta gida tana hutawa hakan ya saka shi cewa Kader" Mu je gidan nan da aka gyarawa ita dayar "
Kader ya gyada kansa dan ba sai ya nemi karin bayani ba, da ace dai ba a sama yake ba da sai ya tambaye shi wace dayar kuma?
Haka suka kama hanya cikin nutsuwa suka je gidan da aka yiwa Aisha Jere
Mai gadi da mai bawa fulawowi ruwa sai matar da mama ta dauka kan ta ringa gyaran fallo da kula da kayan dake ciki kafin amarya ta tare ne suka zo suka gaishe shi
Da kulawa ya amsa masu yana dan bin gidan da kallo, wai shin zai iya rayuwa kuwa a gidan da babu mama bayan ya san maman na raye tana kuma cikin gari guda da shi? Ya yi wata irin shakuwa da mama fiye da tunanin bawa
A hankali ya kalli Kader dake kashe selfi yana murmushi ya ce" Kader, ka san idan Aisha ta yi nesa da Billy zata daina fushi ko? "
Tausayinsa ne kader ya ji ya lulube shi, hakan ya saka shi zagayawa wajen da yake zaune kafarsa daya cikin mota dayar a waje ya rike hannun motar ya yi kalar serious ya ce" Hisham, ya dace ka ajiye tunanin Billy baby ce, ya dace ka cire du wani dar da tsoron kar ta ce da kai bata son ka, ya dace ka farka tun da wuri, Hisham idan har Bilkisu ta ci gaba da tafia wajen Najeeba ina mai tabatar maka zan karo maza biyun da zasu taya ni kulawa da kai domin ba zan iya daukanka ni daya ba idan ka suma, Hisham ka ga ka daina wasa da abinda ke iya tsayar da numfashinka ka ji?"
Murmushi Hisham ya yi yana duban agogon hannunsa ya dago kansa yana kallon Kader ya ce" Na kasa yarda, Kader ban yarda cewa ina iya sabe suturata a lokacin da ban shirya ba a gaban yarinya sai da ya faru da ni, abinda ya fi tsaya min a raina shine shin ta yaya, ta ina zab iya sabe tawa suturar kuma a gabanta, Bilyy ce fa, yar billyna ce fa? "
Kader ya tabe bakinsa ya ce" To idan kai ba zaka iya ba ai wani zai iya, in ka san tsoronta kake ba maza waje malan"
HISHAM ya yi shiru kansa a sade har Kader ya kai karshe
A hankali ya dago yana dubansa ido cikin ido, hakan ya saka kader dan matsawa kadan yana dan kikifta idannuwansa
Hisham ya maida dubansa wajen mai gadi dake tsaye cen kofa ya kuma maidowa kan Kader, a hankali ya ce" Kader, wai me na yi maka ne? "
Kader ya kikifta ido yana dan matsawa ya ce" Allah dai ya baka hakuri "
Hisham ya dan yi kwafa a bayane ya ce" Ya bani "
Kader ya kale shi da mamaki, ya ce" Kai, ba abinda zaka ce min? Ni walahi wannan abin ya fara bani tsoro ka daina biye min mu yi jaraba yau kusan sati hudu ko ka dauki zahi da ni sai ka wani yi hakuri, ni kam bana son haka"
HISHAM ya yi murmushi ya kyake shi yana maida kafarsa dayar ciki a kasan zuciyarsa yana ayana 'Zaka yi bayani ne'
Kader ya kara gyara zaman bindigarsa karama ya zagaya ya shiga ya tayar da motar yana alamun shi fushi yake irin Hisham na neman bata masa ran nan
Shi dai burinsa ya ganshi a gida
Sunna tsayawa ya sauka direct ya yi bangaren Mama a lokacin tuni magariba ke sanyo kai aman ba'a yi kiran sallar magaribar ba
A hankali ya ja ya tsaya sakamakon ganninsu da ya yi su hudu zaune saman shinfidar tabarma sunna hira cikin raga da sakin fuska da farin ciki
Amsa sannunsu ya ringa yi yana dan wara idannuwansa dan son ganninta
Gannin bata nan ya dan yinkura da niyar tambayar inda take sai jin karar babur dinta
Da sauri ya juyo , mamaki ke neman halaka shi ganninta saman babur dinta ta saka abin tsayawar nan da waya a kunnenta
Da sauri ya juya wajen Mama dake masa maganar ya zauna mana ga ruwa ya sha ya dan huta ko ya je bangarensa matarsa ta kawo masa ruwa
Katse mama ya yi ta hanyar fadin" Ita kuwa daga ina take a haka? "
Yannayin da ya yi tambayar a kausashe ya saka mama dakatar da abinda take ta dago da dubanta ta sauke kansa, haka kuma ta sauke kan Bilkisu da ta sauka kamar kwai ya fashe a cikin kaza tana dan matsowa tana ja ta tsaya
Mama ta kafeta da duban da ya sakata sada kanta da sauri tana wasa da yan yatsunta
Mama ta ce" Ba tace daga wajenka take ba kuma ka san da fitarta zuwa wajen auren gidan su Farida kawarta? Sannanma wayar nan dake hannunta kai ka yarje mata anfani da ita? Wace Umar ya bata "
HISHAM dake tsaye sai ya samu kansa da tsura mata ido irin yanda take kikifta ido tana son yin magana aman ta kasa
Tati ta dan yi gyaran murya ta ce" Nice ta fadawa zata je fa, dama ta san ba zaki bari ba in ba cewa ta yi shi ya bari ba "
Juyowa ya yi yana kallonta ya maida dubansa kan Bilkisu ya kausasa muryarsa ya ce" Daga ina kike? Wa kika tambaya? Yaya muka yi da ke ne? Ba cewa na yi kar ki je wajen auren nan a haka da kwaliya ba ki dawo gida? Yaushe kika fara karya? "
Bilkisu na jin kamar zata fashe da kuka tana ta kallonsa hankalinta a tashe ta rasa da wace zata fara bashi amsa a cikin tambayoyin nasa, cike da tsoro da dana sannin fara bijire masan da ta yi yau, ta budi baki zata yi magana ta ji muryar Aisha a sanyaye tana kallonsa ta ce" Me ya sa ba zata yi kwaliya ba idan zata fita Docter? Inace sai an gyara ake samun miji a wannan zamani namu in dai ba ka yi mata miji ba? "
Da wani mamakin ya kure fuskar Aisha da kallo, sarai ya san meye nufinta domin ya fi a irga tana nuna masa ta san wace yake so, me zai hanna ya yi bayani ya fada mata? Tunma kafin a daura masu aure ta yi rubutu a farar takarda ta ba kader ya bashi wanda take fadin sai yaushe zai furtawa Bilkisu kalmar so? Cire dubansa ya yi ba tare da yace da ita ufan ba, aman kwarai ya ga kokarinta, itace har ta iya yi masa tambayar da ta san yana iya rikicewa? To idan haka ne ita Bilkisun makauniya ce ko kurma? Har kowa ya gama sannin abinda yake ciki banda ita?
Yana kallonta da wayar dake hannunta aman ta kasa yin magana, sai kallonsa da take tana kwal kwal kwal da manyan idannuwanta
A hankali ya ringa saukowa, wanda du saukowarsa daya sai gabanta ya mulmula ya yanke ya fadi har ya idasa saukowa gaba dayansa tana mai binsa da kallo
Hannunta ya kama ya shiga tafia da ita, tafiar da kamar janta ne yake domin gaba daya kafafuwanta sun mata nauyi bata iya daga su da kyau har sai da ya karasa shiga da ita katon falonsa ya tsayar da ita tsakiyar falon
Kai kawo ya shiga yi hankalinsa a tashe, fuskarsa na nuni da yannayi na tashin hankali kafin ya tsaya yana sakin wayar dake hannunsa tasa kasa yana kallonta
Muryarsa a sanyaye ya ce" Rabonki da gyaran dakina an kai sati hudu, Billy am rabonki da damuwa da na ci ko ban ci ba an kai sati hudu, rabonki da damuwa da damuwata har kin manta, Bilkisuna ke kin san idan ba ke kika wanke min ba bana iya sakewa yanda nake so domin ko mama bata min wankewar da nake so
Bilkisu kin ga wajen suturuna yanda suka dawo? Na rasa yaya kike kina min kilacewar nan da na kasa koya har yanzu"
Kuma sanyaya muryarsa ya yi ya ce" Kin ga kwaliyar nan banda rigima ba abinda zata jaza min, banda tayar min da hankali da dauke min nutsuwata ba abinda zata haifar min, Billy dan Allah ki shafa abubuwan nan ki fita ki yi me a wajen? Wa kike son birgewa ne? Dan Allah fada min kin ji? "
Bilkisu ta lumshe idannuwanta masu dauke da gashin idon nan ta kuma aro jarumta tana kallonsa duda irin yanda tsayayen namijin nan ke halaka dukan wani kuzarinta ta cije ta cije sosai tana kallonsa ta dan yi dan murmushi itama muryarta a matukar sanyaye ta ce" Mijin aure mana Hamana "
Da sauri ya kara kallon lebenta dake motsawa, ita kuwa zuwa lokacin ta gama niyar idasawa tunda ta fara dan haka ta kara kallonsa tana dan motsa lebenta a hankali ta ce" Mijin aure nake son birgewa Hamana, ka ga a yanzu bazawara sunnana, an daura min aure ko tarewa ban yi ba an sako ni bayan ana daura min auren da shi sai da ya zo ya ganni, ganni mai girman gaske, gannin da inaga ya gama cutata....." dan dakatawa ta yi gannin a yanzu kuma ba wai lebenta yake kallo ba, kwayar idannuwanta ya tsayar da dubansa tarrr a ciki hakan ya saka ta ji kamar ta rasa muryar fadin kalma a bakinta
Kundunbala ta yi sannin cewa a yau ko yayane ikon Allah ne zai raba su da shi ta sada kanta ta fara shashekar kuka ta dago hannunta fari tas tana dan nunowa wajensa ta ce" Hamana,