Showing 21001 words to 24000 words out of 180809 words
bai taba daina zafin jiki ba, idan kin ganta tana fama da jiki hakan ya tayarwa da oganmu hankali
Yana ta neman likitan da ya kware ne aka ce masa ya zo damagaram
Baki ga irin farin cikin da na yi jin yana maganar cewa damagaram, ai ban san lokacin da na dira na ce garinmu ne, zan yi masu jagora, yanzu haka maganar da anake maki cen na baro su na gudo na zo dan na ganku "
Mama da wani farin cikin da ya rufe mata dukan fahimta a zancen yar uwarta, da murnar ganninta ta ce" aa, likitan kai? To HISHAM ne fa in dai baban likitan kai ake fada na niger din baki daya "
Kamar bata san da zancen ba ta zarro ido da mamaki ta ce" kika nufin HISHAM din ne ya zama likita? Likitanma baba? "
Mama ta yi murmushi ta ce" Shine, likitan kwakwaluwa, likitan mata kuma soja a cikin gidan sojoji "
Wani irin girma ta ringa ji kanta na yi mata da wani irin abu da ta rasa ko na meye, a zumudance ta ce" Auntu na barsu a cen, muna cen mun kama layi ko zamu samu ganninsa ashe Hisham ne? Sai dai ina cike da tsoron ta yadda zaya kale mu, shin zai iya dubana kuwa? "
Mama ta dan yi tsam na wani dan lokaci, ba dan komai ba sai dan irin yanda tun yaron na zumudi a da idan aka ce mahaifiyarsa ce a waya, har ya dawo ya ringa rage zumudin amsarta a waya, tun idan ya ce da ita Mama? Tana kwabarsa cewa ni ba mamanka bace, wannan ta kusanka ira ce mamanka ni tatinka ce, har ya dawo ya daina kiranta da mama sai dai ya ce da ita tati, kai sannu a hankali amsar wayartama sai ya zamana sai maman ta yi masa jan ido kan cewa mahaifiya ba abin wasa bace, sai ya ce Mama ki yi hakuri a kulun idan muna magana da ita a gagauce take, takan ce min karma na yi gigin cewa zan ringa tambayarta kudi domin itana ta kanta take, bata san kina siya min komai ba? Wai mama yaya aka yi wata ta haife ni ba ke ba? Da zan iya kwace a duniya da zan yiwa BILKISSUNA kwace ne, zan kwace mata tsaftataciyar uwa ne, zan hanna mata mamana ne na rike abina ni kadai, ita kuwa mama sai ta yi kici kicin da rai dan ya baiwa maganarta mahinmanci domin irin kalaman nan nasa sukan bata tsoro ainun
Ajiyar zuciya ta sauke ta mike ta ce" Bara na saka hijab dina mu tafi "
BILKISU kam hade haden kayan ciye ciye da shaye shaye ta baje ta yiwa Tatinsu
Cike da katon faranti ta shigo ta dire mata komai a gabanta tana ta murmushi tana kallon matar, irin feeling din nan mai girman gaske na yau kaima gaka ga wani naka na danginka bayan ka cire rai da gannin hakan
Zeinab cike da jin kaunar yarinyar ya mika hannunta ta kamota ta tsayar da ita kusa da ita sosai, a sanyaye ta ce" U'r cut babyna masha Allah"
Bilkisu ta ringa murmushi ta tsiyaya mata jus na kankana da peak sansanya ta mika mata tana kallonta ta ce" Tati, ina yini, yaya hanya? "
Zeinab ta sha tana lumshe idannuwanta hakan ya saka Bilkisu kallonta da mamakin irin yanda take lumshe ido, a hankali ta sauke ajiyar zuciya ba na komai ba sai na gannin yannayin yayanta , irin yanda yake da sarar lumshe ido a dukan motsinsa
Fitowar mama sanye da dogon hijab dinta har kasa rike da yar pos dinta ya saka Bilkisu dan dakatawa da harhadawa Zeinab abinci a plat
Mama ta ce" Bilkisu zamu je asibitin wajen yayanki, ki dora sabon girki kafin mu dawo "
Bilkisu ta ce" Ayah mama zan bi ku, na gama girkina fa tun da safe "
Mama ta yi murmushi ta girgiza kai ta ce" Ba guduwa ba zata yi tatinku, zamu dawo tare in sha Allah "
Ita dai Zeinab yannayin innocent face din yarinyar, da fatar jikinta, da tsarin halitarta uwa uba irin tarbiyarta ta birge ta, hakan ya sa ta yi ta janta a jikinta sosai tana jinta har cikin ranta, dan haka ta kamo hannayenta a hankali ta sakata cikin jikinta ta rungumeta sosai, muryarta sanyaye wace dukan abubuwan da ta tarar suka sanyayar mata da ita ta ce" zan dawo, ko da ke babyna "
'Kai wani dadi take ji gide idan tana ce mata babyna din nan iyeah, yau ga sha'ani sabo a gidansu da ganni tatin nan tata zata daure mata a Damagaram' Bilkissu ke ayannawa a kasan zuciyarta sai kuma ta saki murmushi ta masu rakiya har kusan motar kader
Kwarai ta yarda cewa ta bar waje, waje ya barta..........................
A matsayinsu na masu takardu da aikin yi sun zo asibitin nan duda babar kalmar da ta fada cewa a je a ce masa *mahaifiyarsa ce* sai kawai a bita da kallo aman ba wani rawar jiki ko wani bada girma kamar yanda a yanzun da suka zo da Mama take gannin ikon Allah
Jin cewa ya shiga tiyata mai tsayin lokaci sai kawai mama ta nemi da gannin doctor din da baya cikin tiyatar tare da shi
Nan da nan ya zo cike da girmamawa ya gaishe da mama,
Mama ta shaida masa cewa marar lafia ne suke tafe da shi,
Ta yi nuni da Zeinab dake tsaye ta dora da fadin" Mahaifiyar Hisham ce a garin Niamey take aiki "
Da mamaki ya bi mama da kallo, dama ba ita ta haifi Boss ba? Sai ya kasa jin wani farin cikin gannin maman Boss, sai kawai ya tsinci bakinsa da fadin " Aya, ina yini yaya aiki "
Daga haka sai ya maida dubansa wajen mama ya ce" Mama, ku je ku zauna ku huta zamu kula da marar lafiar har ya samu ganninta"
Godiya mama ta yi ta ja hannun Zeinab suka nufi office din HISHAM
Ba'a dakatar da su ba, saima bude masu da sekatariarsa ta yi suka shiga
A hankali take bin office din da kallo, kwarai ta so ta ga hotonsa a wannan tankamemen office din, sai dai babu, shin wace kama yake da ita a yanzu?
A hankali ta zauna saman kujera tana bin office din da kallo, so take ta tinano a cikin manya manyan da ta shiga offishinsu na wa ya kai na D'Anta kyau?
Hira suka ringa yi da Mama, duda yawancin hirar mama ke bata labarin irin abubuwan da suka faru bayan bata nan, sai tambayoyin da take yiwa maman wa'inda du yawanci a kan HISHAM ne
A kadan sun kwashe awani shida a office din nan domin har magariba ta kawo kai, sallah kadai ke tashinsu sai su koma su dora daga inda suka tsaya
Karar bude kofar shigowa ya saka su waigawa a tare
Da yannayin tafiar nan tasa kamar ya gaji yana jefa kafafunsa a hankali, da farar rigar likitoci, wuyansa dauke da abin tsinkayo numfashi, hannunsa sanye da safar likitoci, kafarsa sanye da farin takalmin likitoci, fuskarsa dauke da face mask manyan idannuwansa a fili yana lumshe su yana karrawa
Da dan sauri ya cire idannuwansa a kan fuskarta, irin kallon da ta kafe shi da shi da mikewar da ta yi tsaye da sauri ya saka masa bugawar zuciya
Ya kasa yarda da abinda yake ganni a gabansa
*MAHAIFIYA* Kalma mai girma da daraja, kalmar da ba kowa zai amsa idan aka kire shi da hakan ba, abinda duban jama'a ke kai goshinsu kasa su roki Allah ya sa zasu ga ranar da zasu kasance *MAHAIFIYA* Girma, daraja, daukaka, irin na Mahaifiya, yau shima gashi tsaye a wajen da wace aka ce ita ce ta yi nakudarsa ta kawo shi duniya
*ASHE TANA RAYE?*
*ME YA YI MATA DA ZAFI?*
*KO ZAFIN NEMA NE YA SAKATA YIN FATALI DA SHI?*
*SHIN IDAN YA KALETA YA KIRETA DA MAHAIFIYA BAI TAFKA KUSKURE BA KUWA?*
*UMANSA ASMA'UL HUSNAH CE, UMANSA NURIYAH CE, WACE YA JI DUMIN JIKINTA ASMA'U CE MAMANSA ITA CE ASMA'U*
A hankali ya karasa kusa da mama sosai har kamar zai zauna jikinta irin kusancin da ya hadasa a tsakaninsu
Dukawa ya yi kamar yanda ya saba a hankali ya dora kansa saman cinyarta, muryarsa sanyaye ya ce" To yanzu da kika fito tun dazun wa zai tirsasata ta ci abinci bayan kin san bata ci Mamana?"
Mama ta yi wani iri, du sai ta daburce ta kasa bashi amsa, hannayenta ta saka ta dago fuskarsa a tafin hannayen nata ta sauke dubanta a saman fuskarsa, nan take ta karanci irin bacin ran dake tatare da shi bayan tarin gajiya, haka kuma ta karanci wani yannayi mai nuni da tsoro da fargaba da tashin hankali a tatare da yaron nata
Muryarta ta sanyaya sosai ta kara rike Fuskarsa a tafin hannayenta duda nauyin da ta masa kuwa ta ce" Ban horeka da haka ba, kai ka san me ya kawo ni , ko kamaninmu zai shaida maka , ka kiyaye kar bacin rai ya saka ka aikata aikin da Allah zai kona ka HISHAM!"
ZEINAB dake tsaye baki daya abubuwa ne suka dagule mata, tambayar kanta take hala fushi yake da ita? Mamakin girman yaronta take, mamakin irin nutsuwa da tarin lafia dake tatare da shi take, a kamanin mahaifinsa lebe ne da manyan idannuwa kawai suka bambanta
Baki daya hannunta ne ya dauki rawa a hankali ta karasa ta dora hannun nata gefen kafadarsa muryarta na rawa rawa ta ce" HISHAM, baka gane ni ba ? Ni ce Mamanka fa? "
Da mamaki matuka ya buda jajayen idannuwansa ya sauke a saman fuskarta, mamansa? Yanzun ita ne ta budi baki a gaban Mama ta furta cewa ita ce mamansa? Ita dake kwabarsa ta ce da shi kar ta ji kar ta gani ya kireta da mama ne yau take fadin ita ce mamansa? Sai kawai ya yi tunanin yanzun da a wani mumunan Hali ta same shi anya zata so a rabata da shi a matsayin d'a? Waima me ya mata ne?
Nan take ya ji duniyar ta yi masa zafi, a hankali ya kai dubansa wajen Mama, ya kuma mayar kan Zainab, sai abu daya ya shiga cikin kwakwaluwarsa, kasancewarsa mutun mai saurin fadin abinda ya tsaye masa a kasan zuciya sai ya kara gyara tsugunnonsa sannan ya dan zame hannunta dake gefen kafadarsa a sanyaye ya ce" Ina yini? Ya hanya? Yaya aiki? "
Dubansa ya mayar wajen mama ya kara sanyaya muryarsa ya ce" Ki tashi Kader ya maida ku gida dan ALLAH mamana ko zaki matsa mata ta ci abinci, ina ji a jikina tana cen tana gadin zuwanku, zan je na kula da marar lafiar da ta kawo domin na san tati bata son wasa da aikinta, na yi maza na gama masu komai su juya "
Yana gama fada ya mike tsaye ya juya da sauri hakan ya saka Mama wangalar baki cike da mamaki
Da sauri ta mike tsaye da niyar binsa dan kuwa ita bata ga wani damuwa dan Zainab ta kire shi da D'Anta ba, ai danta ne, kuma uwa ta fi gaban haka, bata kai ga fita ba Zainab ta saka hannayenta ta rikota
Da sauri mama ta juyo tana kallonta, tana shirin yin magana Zainab ta ce"
Aiwah
[7/24, 10:18 AM] BAK'A CE: πΎπΎπΎπΎπΎπΎπΎπΎπΎπΎ
*DUK NISAN JIFA*
_(K'asa zai dawo)_
πΎπΎπΎπΎπΎπΎπΎπΎπΎπΎ
_RUBUTAWA_
*SAJIDA*
*SADAUKARWA*
*GA*
*MASOYA NA*
π«β¨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*π
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_π€
β *[ T.M.N.A]* β πποΈ
https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/
_Bismillahir rahamanir rahim_
9
Muryarta raunane tana jin wani irin abu , wani irin baban lamari mai wuyar fasara, a k'asan zuciyarta take jin ciwon irin abinda ya yi, sannan wani irin shayinsa ya d'arsu a zuciyarta, a sanyaye tamkar zata fashe da kuka ta ce da mama "Ki barshi Aunty."
Mama da gaba d'aya hankalinta ya gama tashi ta ringa girgiza kanta ta ce "A'a, ba zan barshi ba, ba zan iya barinsa ya saka kansa a halaka ba, ba zan iya baci ba bayan na san cewar idan har ya yi wasa da lamarin uwa sai ya tozarta a duniya kafin ya tozarta a lahira, ba zan iya rintsawa ba bayan ya yi abinda nake ganin kamar tarbiyata ce ta zo masa a haka! Zainab ba halinsa bane hakan, mai yafiya ne shi, mai bin umarni ne, mai ladabi da biyaya ne, mai jin k'ai ne, ba fushi yake da ke ba, na tabbata yana cikin kokontonki ne a zuciyarsa, ki barni na je na fad'a masa cewar ko me kikai masa tsakaninki ne da mahalicinki , aman idan shi ya yarda ya yi maki Allah zai yi gagawar la'antarsa ne, ki barni na ceci yarona tun kafin fushin zuciya, rudani su saka shi halaka kansa."
K'auna, da soyayar da ta gani a idanuwan Mama na yaronta ya saka Zainab jin jikinta baki d'aya ya yi nauyi da sanyi.
Ashe haka mama ke son HISHAM? ashe haka take motsawa idan abu ya shafe shi ne?
Da sauri zuciyarta, mai kwad'aita mata duniyar ta ce da ita "Ke kuwa idan bata so shi ba ai akwai matsala, ko dan irin daular nan da yaronki na cikinki ke ciki za'a rab'e shi! Dan haka karma hakan ya saka ki jin kamar zaki aikata ba daidai ba."
K'ara cijewa ta yi ta ce" Aunty, ki ji da kyau, in dai ni na haife shi da cikina na yafe masa, koma me ya yi min a rayuwa na yafe masa, zan yi ta yafe masa dukan laifukansa a gareni, fatana ya yafe min, hakan kuma ba zai faru ba har sai kin kama min, har sai kun kama min, na yi nadama, ba zan kuma ba."
Ajiyar zuciya mama ta ringa saukewa sannan ta ja hannun Zainab.
Suna fitowa sai da suka je ta wajen marar lafiar, nan ta ga sai matarsa da yarta zaune. Irin yanda suka ringa yi mata addu'a da nuna mata farin cikinsu a fili uwa uba irin yanda matar ogansu da kanta ta nemi da ta bata numberta zasu ringa gaisawa ya sakata jin zata k'ara d'aurar d'amarar yak'o zuciyar yaronta! Nema ta je ba yawon ta zubar ba, ba a kanta aka fara fita nema ba duda a yau ta ga wata kalmar malan bahaushe ta tabbata a gareta watau *Zafin nema baya kawo samu*.
Suna kowama suka tarar da abinci, girki mai rai da lafian da Bilkissu ta girka.
Sosai Zainab ta ci abincin nan domin kuwa yunwa take ji.
Tana cikin ci Mama ta fito da wata kula ta mik'awa Bilkissu dake zaune kusa da Zainab ta ce maza ta kaiwa Kader ya kaiwa masu zaman jinyar.
Ita dai daga zaunen nan take kallon dukan abubuwan dake faruwa.
K'warai ta ji dad'in irin shak'uwarsu, kuma bata da wata damuwa da hakan, damuwarta d'aya ce tak yaro ya san da ita ya dubeta.
Hira suke har wani lokaci inda su dukansu suka fara jin baci na neman d'aukansu, a cikin hirarsu kuwa sosai suke jajanta irin yanayi da Hisham ya nuna wanda baki daya BILKISU ta ji jikinta ya mutu, haka kuma burinta ta ga shigowarsa gidan aman har Mama na neman korata d'akinta bai shigo ba.
A karro na biyu Mama ta ce "Bilkisu."
Baki d'aya ta yi takwaf takwaf da fuskarta tana kallon mama haka kuma ta turo d'an bakinta kamar wace aka yiwa wani abu mai cin rai.
Mama ta yi murmushi ta ce "Ki tashi ki je ki kwonta ba zai dawo da wuri ba fa."
Bilkisu ta ce " Mama, dan Allah ki bani wayarki na kire shi na ji yaya jikinsa, sannan na ji shin ya ci abinci? Sai na je na kwonta."
Ajiyar zuciya mama ta sauke ta k'i bata wayar.
Zainab dake hankalce da wata irin shak'uwa ta daban tsakanin yaronta da Bilkisu ce ta ciro tata wayar ta mik'a mata tana fadin "Ban san ba ko yana daga bakuwar number? Yi kiransa babyna."
Amsa Bilkisu ta yi da hannu biyu tana kallon yannayin fuskar mama dan kar ta yi laifi.
Gannin mama bata d'aure Fuska ba sai ta yi murmushi ta ce" Na gode Tati, bara na fara yi masa mesage zai d'aga idan ya gani."
Hakan ne kuwa mesage ta tura kamar haka " Asalamu alaika yayana, ina yini, ina gajiya? Ina son kiran numberka Bilkisu ce."
Rik'e wayar ta yi a hannunta da niyyar idan aka d'auki kamar minti goma sai ta gwada kiran ta san zuwa lokacin ya karanta mesage din.
Sai dai ba'a kai ga yin minti goman ba wayar ta d'auki kuwa.
Da sauri ta duba mai kiran, sai da ta gyara zamanta, ta gyara nutsuwarta....baban abinda ita kanta bata san ta gyara ba shine muryarta ta d'aga kiran muryarta a mace ta furta "Yaya."
Muryan ba nata kad.ai bane a mace, duda tasa na fita ne da yanayi na ransa a b'ace, ga d'an zafi zafi da son sanin amsar tambayarsa ya shiga fadin "Wa ya baki waya? Me kike da waya? Wani kika kira? Ashe ba zaki ji maganana ba? Ba zaki kwantar min da hankalina ba? Bilkis da wa kike waya a irin wannan lokacin?"
Da sauri ta ce "Yaya, aa, ba waya nake da kowa ba na kasa kwantawa ne ganin zaka kuma kwana a wajen aiki bayan duk tsaurinta baka kwana biyu a waje, shine na ce tati ta bani wayarta na yi kiran ka."
"Wacece Tati kuma?" Ya kuma tambayarta a d'an hasale.
A hankali ta raunata muryarta ta ce" Mama 2 " domin du a tunaninta ko laifi ta yi da ta kirayi mahaifiyarsa Tati?
Dan shiru ya yi, hakan ya saka ta sare ta k'ara nutsuwa tana