Showing 141001 words to 144000 words out of 180809 words

Chapter 48 - DUK NISAN JIFA COMPLETE HAUSA NOVEL

sajida   

02 Feb 2025

12990

dan kankancewa ga wani cenza kala da suka yi sannan suka bushe , sai dai ta dake sosai tana sauke boyayiyar ajiyar zuciya

A hankali ya dauke hannunsa ta ringa ja tana rufewa tana kara jan rigar tana ta jimke hannayenta

A sanyaye ya muke tsaye sannan ya saka hannunsa ya kamo tafin hannunta a hankali ya janyota ya fitar da ita

Kanshin turaren da take ya rasa wanene , haka kuma sosai kanshin ke shiga jikinsa bai san dalili ba

A nitse ya shiga tafia da ita sunna jere yana rike da hannun nata yana dan murzawa yana jin zafin jikin nata ta haka

Gidan take dan bi da kallo , irin shuke shuken gidan kwarai ya bata sha'awa, haka kuma ta kasa hanna kanta bin bayansa har sai da suka zo kofar baban falon ya saka hannunsa a wajen budewar ya bude ya fara shiga a lokacin ne da ya sakar mata hannu ta iya ja ta tsaya ba tare sa ta bi shi ciki kamar rakumi da akala ba

Daga inda take tsaye sansanyan kanshin turaran wuta da sanyin AC ne ya huro mata, hakan ya saka ta kara zuba ido tana kallon yadda yake tafia, tsayinsa fafadan samansa wajen kafadunsa, rikaken kugunsa ginanun kafafuwansa, dogayan hannayensa da ko a cikin rigar basu boye kansu ba gashin da ya dan fara fito masa irin ya fara taruwa da dan yawan nan sai shadar jikinsa dake maiko

Ja ya yi ya tsaya a lokacin da muryar mace ta fara amsa salamarsa a sanyaye hannunta rike da jug

Da sauri Bilkisu ta dan rike wajen garun tana jin yadda zuciyarta ke dokawa da karfin balaki kamar zata balo kirjinta ta fito haka take ji

A sanyaye Aisha da ta wuni cikin yannayi na rashin jin dadin ranar haka kawai sakamakon sannin da ta yi cewar mijinta ya tafi daurin auren abar kaunarsa ta ce" Aa, Docter gajiya ce ta koro min kai tun yanzu?"

Hisham dake kallonta ya kai kugunsa zaune da dan murmushi a fuskarsa ya juya dan bai ji ta yi magana da Bilkisu ba bayan ya san tare suka shigo

Hango Bilkisun da ya yo tsaye tana kallonsu ne ya saka shi shan jinnin jikinsa, aman sai ya dake ya ce" Ki shigo mana Billy ?"

Aisha gabanta ya fadi ta juya wajen da ya kalla ya yi magana a hankali ta ce" Billy? "

Sai kuma ta yi gagawar cijewa tana dan fitar da idannuwanta na mamakin nan ta ce" Aa, amaryarmu? Ya haka zaki coge a kofa kamar ba gidanki ba? Shigo mana..... ta faada tana nufo kofar da Bilkisu ke tsaye wace gaba daya komai a kan idannuwanta haka kuma a cikin kunnayenta

Da karfin hali Aisha dake sanye da atampa golding an mata dinkin riga da zani sosai sun karbi jikinta ta kamo hannun Bilkisu tana fadin" Aa, ya haka jikin nake ji kamar da zafi likita lafia? Daga kuke haka ka ji jikinta da zafi fa?"

HISHAM dake zaune ya gyara zamansa yana aikin da ya fi kwarewa a shi watau kallo, ya zuba masu maganadisu yana mai binsu da kallo uwa uba fuskar Bilkisu yake kallo yana so dole dole ya ganne yannayin da take ciki bayan sam ta ki bada damar haka, hasalima tun ihun da ta yi ya ji muryarta sai shahsekar kukan da yake ji nata shi kansa ya ji muryarta sai inda ta cewa tati a maidota da wuri

Aisha ta zaunar da ita saman kujera tana fadin" Aya bara na dauko maki magani wannan zafin jiki ai sai ya ilata mutun

A sanyaye Bilkisu take binta da kallo ta ce" Aa, ba sai kin dauko ba Aisha an min allura"

Aisha ta ja ta tsaya ta juyo tana sakar mata dan murmushi ta ce" To bara na kawo maki jus ki sha ki ci abinci ko zaki ji sauki "

Bilkisu da ta fara kosawa da bada amsar ta dan rike lafayar dake son sauka daga saman kanta ta shiga kiciniyar tashi har ta mike tsaye ta ce" Aa fa, kin ga ai na karya kuma gida zan koma yanzun ki barshi walahi na gode sosai"

Kara gyara zamansa ya yi yana kallonta da gannin iya gudun ruwanta

Aisha kuwa itama ta dubeta da mamaki ta ce" Gida kuma? Daga zuwa sai tafia? Na zatama ko kin zo ne irin nawa? Ke da gidanki kuma daga zuwa sai tafia ?"

Bilkisu na kallonta tana jin dukan magamgannunta kamar da biyu ne sakamakon haushonsu da take ji su dukansu ta dan kalli yannayin katon falon mai dauke da manyan labulaye da katuwar TV da kafet tafkeke mai kwai, da table da tsakiyar falon da manya manyan po na gilas masu wani irin ado ta maida dubanta kanta , a hankali ta kakaro murmushi ta lumshe idannuwanta ta ce" AA, wannan din gidanki ne "

Aisha bata dadara ba domin ita ta yi mamakin ya ce yau ne daurin auren harma ya hannata zuwa ya ce ta zauna ya je ya dawo kuma sun dawo tare ga kuma maganar da take fada sai take son sannin shin an daura din ne ko yaya, dan haka sai ta ce" Gidan mijinki ai gidanki ne kanwata, ki zauna ki huta ko lafia baki da kin gani"

Bilkisu ta kuma sakar mata murmushi wannan karron amsar ta mijinta ce ba tata ba dan haka a gajarce ta ce" Mijinki dai, ni bani da miji, ya sake ni sai na samo wani"

Tana gama fada ta sauke dubanta a kan fuskarsa kafin ta juya a hankali tana jin wani irin daci a zuciyarta ta shiga tafia

Bata san yaushe ya mike ba, batama san ya iso inda take tafiarta ba sai ji ta yi ya kama hannunta ya juyo da ita gaba dayanta ta yada tana kallon kofar shigowa sai da ta dawo kallon TV cen falon

A hankali ya dora hannunsa a kan habarta ya dago da dubanta ido cikin ido muryarsa a sanyaye ya ce" *NI NE MIJIN KI BILLY AM, BAKI ZAMA DAYA DAGA CIKIN SHAIDUN DA MUHAMMAD YA AMSHI AURENKI A HANNUN ABA JAURO BA?* "

Idannuwanta ta lumse, du irin yadda gabanta ke faduwa, hankalinta ke tashi, tsoronsa ke shigarta duda a sanyaye yake mata magana a nitse ba tare d aya mata hargagi ba ko muguwar magana ba aman a hankalce take da girman bacin ransa kuma a sgirye take da ta dakatar da neman fitinarsa a kowani lokaci idan har ta gane lokacin hakan ya yi ta hanyar cenzawar yannayinsa
Fuskarta ta kwashashagwabe sosai ta dora dubanta a kan hannunsa da ya riketa da karfi a cen kasan makoshi ta ce" AUSH zafi hama am, ka sasauta min rikon kar na ji ciwo"

Irin yadda ta ajiye maganar ta hanyar kara jan kalaman sai da tsigar jikinsa ta tashi, ya shagalta kwarai da kallonta yana jin inama inama, inama a duniyar baki daya daga shi sai ita ne, da yana tunanin filin da wuya ya iya isasu zagaye, da yana tunanin lokacin ba zai ishe su zama ba , gadajen duniyar da sun masu kadan, shi yasa yake auna kalamansa yana tunanin ta inda zai fara?

A sanyaye ya ce" ME YASA KIKE SON WAHALAR DA NI BAYAN KIN SAN RAGO NE NI A GABANKI, ME YASA KIKE SON KI BANI WAHALA BAYAN KIN FI KOWA SANNIN BANI DA WANI KUZARI A GABANKI?"

Sosai ta cije ta samu kwarin gwuiwa da karfin jiki tana dubansa a hankali hawaye suka shiga zarya a kumatunta ta ce" HAMANA ina cikin tashin hankali da rudu ne, shin ina maganar MUN SHA NONO DAYA da Hammana ne?, shin ina maganar da kake fada min kaine magabacina kai zaka sama min miji ne ? Wai an daura min aure da yayana?, yayana fa? Hamma am ina zan shiga da wannan abin tashin hankalin abin kunyar?, kawayena fa ce masu nake ubana ne hammana uwarmu daya ubanmu daya ina zan shiga da wannan nauyin, aure fa? Wani kalar zamu raya da hammana ko bani da rabon zaman aure ne ni?, hammana tausayinka nake ji gannin tun ban kai ko'ina ba za'a fara irga min aure idan ka fita cikin mutane a ce shine wancen ne aka kuma yiwa auren da kanwarsa shima ya sauta, Hammana har an fara tunanin ko wani lamari ke tatare da ni marar kyau?, hammana yaushema ka santala aurw da auntyna?, ina zaka shiga da mace biyu, hammana mijin Aisha ne ba Bilkisu ba, tunanina na neman tsayawa ne bayan na san a yanzu na fara raja'a alkibilata a kan wanin hammana sai suka yi maka haka?, Hammana ba laifina bane, kuma ka tambayi Aba, hammana ka sawake min a laluma zan je na fadawa Allah ya shiga lamarina ina da damuwa Hammana gani zan zama bazawara ta biyu bayan ni ba zan taba hada miji da kowa ba?, ni bana son mijin wata ko wanene............nawa nake so hammana kuma zawara ta ina zan fara nema?, wannan shine ya hadasa min ciwo, ciwo na damun zuciyata hammana............." ta karashe tana mai rintse idon matsar dake kara shiga hannayenta da wani irin zafiin da bata shirya ji a yadda jikinta ke dandatsarta ba, sai dai ta dauri niya daga shi har matarsa sai ta karyata masu tunaninsu a kanta, idan tunaninsu ta mace a soyayar Hammanta ne? To bismillah

Dan ihu mai hade da dan kuka tana fido idannuwanta ta nemi saki da dan karfi ta ce"






😁😁😁😁😁😁😁
[7/8, 5:15 PM] +234 816 920 1901: 🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾
*DUK NISAN JIFA*
_(K'asa zai dawo)_
🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾

_RUBUTAWA_

*SAJIDA*

*SADAUKARWA*

*GA*

*MASOYA NA*


💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝

☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_



51


Da dan karfi ta ce" Yaya zafi ka matse ni "

Da wata irin inda inda har yana rufe idannuwansa ya ce" Billy ni......ni....ni din menene makusata? Ni din ai ina iyawa da ku na rantse maki, kin ga dan Allah ki daina min irin haka, kar ki tayar min da hankali na Ksa zama, na sha fada maki bana taba hada rigimarki ko da aikina bale wani abin, bana iya barkata komai hade da rigimarki, jibi fa duba ki ga yadda na rame, yanzun ba ruwanki da ni, na taro na taro kina zile min shin menene makusata?, yanzun da kike cewa wai na sake ki sai kace mahaukaci?, ni fa ba mahaukaci bane, ba wawa bane, kuma na yi girman da na san ciwon kaina, ba nono daya ba tare aka haife mu Billy am, dan Allah kin ga ba lafia gareki ba mu je ki kwonta ki huta kin ji? Idan kin samu sauki sai mu yi maganar nan kin ji? "


Bilkisu ta tabe bakinta ta kawar da dubanta tana son hango Aisha sai dai wayam bata nan, ba ita ba labarinta

Tabas magangannunsa na son su tankwasata kamar yadda suka saba karfi a tare da ita, a hankali take cicije lebenta na kasa har ta samu ta iya fin karfin emotion dinta, sosai ra cije ta yi kamar bata san abinda ya fada ba ta hanyar mayar da magangannun gefe guda tamkar yarinya karama wace bata gane yaren da ake mata sai iya abinda ta saka a gabanta kawai ta sani, da wani yannayin shagwabar ta
ta kuma tabe bakinta ta shiga kiciniyar ya saketa a hankali ta ce" Gida nake so Hamma am, ka mayar da ni gida ko na shiga taxi na koma "

A hankali ya ce" Ki yi hakuri, ki zauna da ni a nan kin ji? Ba zan iya mayar da ke gida ba"

Ido ta zarro tana kallonsa ta ce" Hamma am me hakan yake nufi na zauna da ku a nan? "

Hisham ya gyada kansa ya ce" Ba gidan mijinki bane?, ki zauna tare da mu mana, tare da ni mana kin ga Aisha tana son ki sosai da sosai zata kula da ke da lafiarki "

A hankali ta ringa dan girgiza kanta ta kuma kallonsa ta ce" Kamar wata wace aka jefo? Kamar ba jinnin filani ba? Idan na yi haka koda auren soyaya ne ai sai na koma ga mahalincina ban hada ido da iyayena ba Hammana, ai da na siyawa kaina ko a wajen mutane gari, ni dai aa gida zan koma ka je ka huta sai na shiga taxi "

Ransa fa ya fara baci, gaba daya magangannun da take fada masa shi kuwa yana rarashinta yana tarota sun fara kada masa zuciyarsa, ransa ya fara kunna fa , a harzuke ya saketa ya wuce gaba ya rufe kofar harda ky ya dawo ya tsaya a gabanta muryarsa a kausashe ya ce" Sai ki koma na gani !"

A fusace ya wuce d'akin data tabbatar na shi ne, yanda ya rufo k'ofar tare da murd'a mata key yasa ta k'ure k'ofar da ido, shiru tayi tana kallon wurin kamar an dasata, ganin babu motsin kowa saai ita kawai yasa ta zaman dirshen a k'asa ta had'a kai da gwiwa ta fashe da kuka, cikin kuka mai tab'a zuciya take fad'in "Na gaji Hamma am, na gaji da wannan dakon na wahala, na gaji wallahi ba zan iya ba."

Hannunta da taji an tab'a yasa ta zabura ta d'aga kanta da tunanin shi ne, ganin Aisha ce yasa kawai ta d'auke kanta ta kawar, wani malalacin murmushi Aisha tayi tace "Kuma kika ce ba kya son shi?"

Da sigar yanayin jin haushi tace "Ni ba kukan son shi na ke ba, taya zai min wannan rashin gatan ta hanyar kawoni gidanshi ni kad'ai."

Ba tare data daina Murmushi nan ba tace "Bilkissu k'arya kike Nina son Hammanki, wacece ke da zaki ce baki son wannan had'ad'en saurayin, zaune da kyau a tsaye ma da kyau fari mai farar zuciya, miskilin yaro mai dukan zuciyar matan da suka amsa sunan mata, ingirman namijin da komai kyawunki da ajin ki indai kuka had'u zai kaiki k'asa warwas, shi ne zaki ce ba kya son shi bayan tare kuka rayu a gida d'aya, ai Bilkissu idan akwai wata mace da *Hisham* ya ma illa da soyayarsa to ke *ce*."

Mik'ewa tayi tsaye a hassale tace "Na fad'a miki bana son shi, ni babu wata illa da ya min, ki rabu dani mana haba."

Kawar da kai tayi cikeda b'acin rai, murmushi Aisha tayi tace "Idan kin yardada kanki kuma kin tabbatar baki son shi to miye na damuwar? Kinga Billy ba zan b'oye miki gaske ne ina son Hisham so mai tsanani, saidai daga ranar dana fahimci ke ce a birnin zuciyarshi sai na k'uduri niyyar zama dake da kyautatawa, hak'ik'a ina sonki saboda ke ce farin ciki kuma muradin wanda nake so, Billy ki kwantar da hankalinki ki nutsu mu zauna a matsayin yan Uwa ba wai kishiyoyi ba, idan mukayi haka farin cikin mijinmu ne kuma jin dad'insa."

Tana gama fad'a ta juya zata koma d'akinta, galala Billy ta bita da kallo da jin matsanancin haushinta tattare da kishi mai zafi. Ganin ta sake komawa ita kad'ai a falo yasa ta ji lallai yau zata nunawa yayanta ba fa Bilkissun daya sani ba ce, d'akin dzya shiga ta nufa da d'an saurinta, bata yi k'asa a gwiwa ba wajen tattara k'arfinta ta bubbuga k'ofar d'akin dan ya bata makulli ta bar gidan nan.

Hisham dake zaune bakin gado ya jimk'e hannaye ya duk'ar da kai yana tunanin tashin hankalin da Billy ke nemanshi da shi, jin bugun k'ofar yasz shi mik'ewa ya nufo k'ofar, yana bud'ewa suka had'a ido a tare dukansu suka gimtse fuska, dan ji yake saiya dawo mata a Hisham d'inshi na gaskiya kafin su zauna lafiya.

A dak'ile fuska a had'e yace "Lafiya?"

Gabanta ya buga da k'arfi ya fad'i, dan da gaske ya bata tsoro sosai yanda ya mata yanzun, duk yanda ta so jajircewa tayi ta maza ta kalleshi tace "K'ofa zaka bud'e min." Sai ta kasa, sissinne kai ta fara yi tana d'an motsa ba tace komai ba, da d'an k'arfi ya rik'o wuyan hannunta ya jata da k'arfi zuwa d'akin ya maida k'ofar ya rufe da key.

Juyowa yayi da karfi ya nunata da yasta yace "Ke Billy ki fita idona na rufe, ba dan na fad'a miki ni gajiyayye akan ki ba hakan na nufin ki raina ni, idan kika ce haka zaki ci gaba da yi min to fa lallai zamu saka k'afar wando d'aya dake a garin nan."

Yana gama fad'a takawa ya fara yi zuwa ban d'aki ya nuna mata bakin gado yace "Maza zauna min a nan."

Rab'ata yayi zai wuce kawai Billy ta ga bata da wata mafita data wuce kuka, a gaskiya ba zata iya kwana a gidan nan ba, to kenan ta kawo kanta da kanta? Yanda ta fashe da kuka yasa shi juyowa yana mata kallon mamaki, rikicewa yayi tare da gigicewa, matsowa yayi da sauri da niyyar saka tafin hannayenshi ya share mata hawayen, sai kuma ya tsaya cak saboda tuna yanda yake so ya fara tafiyar da ita, da k'yar y'a iya zaro idannuwanshi dake tattare da tsantsar tausayinta ya sake nina mata gadon yace "Ki zauna na ce."

Da sauri ta zauna bakin gadon jikinta na b'ari amma bata daina kukan ba sai ma Kiran sunnan mama data shiga yi.

Juyawa yayi ya shige ya barta a nan yana jin sautin kukan, gaban madubi ya tsaya tare da dafe saitin zuciyarshi, lumshe ido yayi a hankali ya furta "Billy am me yasa? Da kinsan yanda nake azabtuwa da kukanki wallahi da ko na farin ciki ba za ki yi shi a gaban idona ba."

Wani k'akk'arfan numfashi ya sauke yana bud'e idonshi...

Alwala ya d'ora ya fito yana goge fuskarshi da k'aramin farin towel, jefoshi yayi kusa da ita

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login