Showing 24001 words to 27000 words out of 180809 words
jiran jin abinda zai fad'a , a hankali cikin wata sansanyar murya ya ce "Kina son ta ne?"
Bilkisu ta k'ara saurarawa , bata fahimci tambayarsa ba sam , hakan ya hana mata bashi amsa.
A hankali ya kuma fad'in "Kin ga baki santa ba fa, kar ki shak'u da ita ta tafi ta barki Bilkisuna, idan ta yi tafiarta tana d'aukan lokaci bata waiwayi masoyanta ba, a kad'an tana d'aukan shekaru masu yawan gaske, mai yiwuwa sai kin mutu ko ta mutu labari ya tardo ki, kar ki shak'u da ita Bilkis dan kuwa ko kiranta kika yi ba d'agawa zata ringa yi ba, ko ta d'aga a gagauce ta kashe maki kira, idan kika shak'u da ita zaki zo kina damuna da rigimar ina take? Yaushe zata zo? Ko a kaiki ki mata hutun makaranta, kinga damar kwantawa rashin lafia a kan rashinta, idan hakan ta faru ina zan shiga na ji sanyi?"
Ita kanta bata san cewa idanuwanta a lumshe suke a irin wannan lokacin ba, sauraron kalamansa take d'aya bayan d'aya tana yi masu waje a wajen da bata san akoy gininsa a cikin k'irjinta ba tana adanawa, bata san cewa da hannu bibiyu take rik'e da wayar a kunnanta ba, bata san cewa irin zaman da ta yi na nuni da irin yanda ta tsumu ta gama fita a hayacinba ba.
Kunya ce ke lulub'e Mama sakamakon ganin irin yanda Zainab ta mayar da Bilkisu tamkar wani abin karanta na makaranta wanda take son had'a kalmomi dan ta fahimci abinda yake nufi, irin haka d'in nan da take amsa wayar yayanta ko kai makaho ne idan kunnayenka suka jiyo maka irin muryar da aka yi anfani da ita dan amsawar in dai har kana da k'arfin ji to fa tabbas zaka dasa ayar tambaya koma ka gama yanke hukunci a kan lamarin
Bare da idanuwansu, haka kuma Allah ya hore masu k'arfin ji sosai.
D'an gyaran Murya mama ta yi ta ce "Bilkisu kin same shin kuwa?"
Firgigit ta yi kamar an watsa mata ruwa ta d'ago shanyayun idanuwanta da suka d'auki launi a yanzu yanzu suka dan cenza kala sannan suke d'auke da ruwa ruwa a cikinsu.
A hankali ta ringa girgiza kanta muryarta sanyaye ta ce " mTa ce min ba zata kuma barinmu ba, ta ce min mu kad'ai gareta, ta ce min mu ne duniyarta, ta ce min nima yanzun ina da tati kuma Mama 2, yayana ba zata kuma barinmu ba."
D'an murmushi ya yi yana girgiza kansa kawai ya ce "Kin ci abinci?"
Bilkisu ta d'an yi shiru sai kuma ta shiga kame kame ta ce " Eh, am Eh na ci sosaima."
Murmushi ya kuma yi yana jin kewarta na k'ara shigarsa na iya jiya da yau kawai, hakan ya saka shi mik'ewa daga zaunen da yake ya ce" Gani nan zuwa, ki cewa cikin ki na ce yama shirya domin kuwa zan k'ara loda masa cima."
Ido ta zarro sai kuma ta yi yar daria tana rike da wayar, sai kuma ta yi shiru tana kallon su Mama.
Ido cikin ido ta ga du sun kura mata ido hakan ya saka ta dan daburce a hankali ta ce "Au, sannun ku su Mama"
Mama ta kawar da kanta tana ta tunanin wannan ikon Allah, ta kasa cewa komai, wai sannun su, sannunta dai ita da ta gama makalkale waya, matse jiki da murya, sannunta dai ita uwar mararsa kunyar dunia.
Zainab ta raka Bilkisu da kallo.
Tana tafia d'akinta ta kai dubanta wajen Mama da yannayi na ayar tambaya ta ce " Aunty, ko dai soyaya ake Babyna da Hisham? "
Da sauri mama ta girgiza kanta tana kallonta ta ce" ko d'aya Zainab, kawai shak'uwa ce tsakaninsu, domin nima da na ga wasu abubuwan na sha titsiye su aman ba wanda ya nunan da maganar wata aba wai soyaya, kawai shak'uwa ce na san dan basu da yawa ne"
Murmushi Zainab ta ringa yi bata kuma cewa komai ba ta mik'e ta nufi d'akin Bilkisu.
Tana zaune bakin gado Bilkisu ta fito daga wanka d'aure da tawul a jikinta.
Sam bata lura da mutun zaune ba ta nufi wajen kayanta da sauri ta ciro doguwar riga da Pant.
Pant d'in ta fara sakawa sannan ta zira rigar ta shanya tawul din.
Ta juyo da niyar d'aukan abin busar da kai da ga Zainab zaune tana binta da kallo tana murmushi.
Gaskiya tsarin halitar yarinyar ya firgitata fiye da tunanin bawa, tabas yar na kama da su, sai dai tsarin halitarta ta dame su ta shanye, bata tab'a hasashen ta kai haka ba, uwa uba gashinta ya had'u na filanin usil baki sid'ik da shi ga gyara da yake samu.
Sai da Bilkisu ta zaro ido sannan ta dan rufe fuskarta na kunya sai kuma ta ce "Lah , Tati ban ganki ba walahi, wani abu zan kawo maki sauri nake kar yaya ya tardo ni da wancen kayan na makaranta ya min fad'a, ya hanna min zama da kayan makaranta a gida."
Zainab ta mik'e ta d'auki abin busar da gashin tana murmushi ta zaunar da ita ta ce" zauna na busar maki da kan naki "
Ai kau zama ta yi tana murmushin itama.
Zainab ta jona ta shiga busar mata tana caje mata kan domin abin busar da gashin mai hade da macaji ne.
A hankali ta ce" Babyna, na tambaye ki mana ko zaki taimaka min?"
Bilkisu ta dan dago da kanta ta sakar mata murmushi tana kallonta.
Zainab ta mayar da kan nata kasa ta ci gaba da busar da gashin nata ta ce" yayanki ya yi fushi da ni, ya tsane ni, ya kasa gafarta min, ko zaki taya ni lalaba shi ya yafe min? Na jima ban dawo ba, na gane kurena ba zan kuma ba, ko kina fahimtar yarena? "
Ta fad'a tana k'ara kallon Bilkisu.
Bilkisu ta yi murmushi
tana cire dubanta a kanta, kwarai ta san me take nufi kuma ta san ta batawa yayanta rai, ta san yana cikin halin fushi ne dalilinta, kuma ita bata ga laifinsa ba, abu daya zai sakata dagewa ta saka shi saukowa shi ne "Mahaifiya" , Uwa uwa ce, bata tunanin a nan gidan duniya akoy abinda Mama zata yi mata ta kasa yafe mata komai girmansa, koda kuwa yankata ta yi
Zagayowa Zainab ta yi ta rage tsayinta sosai tana kallon Bilkisu ta dago habarta ta ce" yannayinki sai ya fara bani tsoro, shin kema zaki taya yayanki yin fushi da ni ne? "
BILKISU ta lumshe idannuwanta ta bude tana jin kaunar matar a ranta, wannan uwa ce ga yayanta, wannan ita ta haifi yayanta, itace jefi jefi suke ji a waya, yau gata a gabansu tun da rana har yanzun bata tafiarta ba,
Murmushi ta sakarwa Zainab a hankali ta ce" Ba fushi yake yi ba, zai yi hakuri ne ni na sani Tati "
Zainab ta lumshe idannuwanta ta juya wajen kayan Bilkisu
Kayan kwakiya ne cike da wajen sai dai bata ga alamun ana anfani da su ba
Jan baki mai ruwan ja mai haske ta dauko
Bilkisu na kallonta ta bude ta dan dago habarta a hankali ta rike ta shafa mata shi a lebenta baki daya, shafawa irin na kwararu , shafawa daidai da lebunanta
A hankali ta mayar ta dauko jagira
Umartarta ta yi kan ta sada idannuwanta
Bilkisu kam abin bako ne a rayuwarta, hakan ya saja cike da zumudi ta sada idannuwan nata
Saman idon kadan ta shafa mata ja girar baka watau ta yi mata eye liner da shi sannan ta bata ta ce ta sakawa idannuwanta
Abinka da wace ba kwaliyar take ba sai fuskar tata ta fito a iya wannan kawai da akaiwa fuskar ta yi wani irin kyau da ita
Gashin kan nata ta kai mata shi kasa sosai ta saka mata dan ribom karami sannan ta dauki dan kwali ta shiga warwarewa zata d'aura mata kennan suka ji buga d'akin a hankali.
Da sauri Bilkisu ta kai dubanta wajen k'ofar, sai kuma ta kalli Zainab, a hankali ta ce "Waye?"
Shirun da ya yi ya sakata gane shi ne, ya tsani ya bugan nan ta wani ce masa waye kamar wani sa'anta.
Da sauri ta mik'e tsaye da niyyar zuwa ta bud'e, sai dai Zainab ta rik'o hannunta ta k'i bata damar yin hakan.
Turare ta juya ta d'auko mata ta shiga fesa mata shi , sai da ya shiga suturarta sosai sannan ta saketa bayan ta yi mata murmushi ta juya ita ta je ta bud'e k'ofar maimakun ta bari Bilkisun ta bud'e.
Ido hud'u suka yi shi da ita, kallon cikin ido na wasu yan sekwani kafin ya yi gagawar cire idanuwansa a cikin nata ya sada dubansa.
Sai da ya lumshe idanuwansa sannan ya ce " *Barka da warhaka Tati*."
Ajiyar zuciya ta sauke tana kallon wannan zaratan namijin wai nata ne, danta ne, da ta san abinda ta kunce a zanin goyo ta yar zai zama haka da bata yada ba.
A sanyaye ta furta "Yaya gajiya HISHAM?"
bai bata amsa ba sai k'ara sada dubansa da ya yi yana jin zuciyarsa na bugawa.
A hankali ta rab'a gefensa ta wuce.Tana yin gaba ya bita da kallo har ta k'arasa kusa da d'akin Mama.
Juyowa ta yi dan ta k'ara kallonsa, idanuwansu suka kuma had'ewa.
Wannan kallon ita ta fara cire dubanta a hankali ta shige d'akin Mama.
Bai san wani tunani zai yi ba dan haka ya juyo da niyyar kuma buga d'akin Bilkisu, domin rabonsa da shiga d'akinta kai tsaye har ya manta.
Turus ya yi da dubansa a saman fuskarta, cenjin da ya gani ya girmama a idanuwansa domin ita din ba ma'abociyar shafa jan baki da kwali bace.
Ido cikin ido yake jifanta da wani duba wanda bata san fasararsa ba.
A hankali ya kai dubansa saman leb'enta da ya sha jan bakin nan ja
"Ya salam." Ya ji zuciyarsa na fad'a a hankali.
Da sauri ya so juyawa sai dai sam k'afafuwansa da dubansa suka kek'yashe knasa suka ce basu san zancen ba.
A hankali ya ringa jin k'afarsa na son yi masa rawa hakama dukan wata jarumatarsa.
Murmushin dake tsayar da numfashinsa ta saki tana kallonsa muryarta a shagwab'e ta ce "Yaya ko? Tambayi mama wollah na tab'a aman ba da yawa ba."
"Wayo Allahna, na shiga uku, waye ya mata kwalliyar nan? Wa ya ce da ita ta yi magana a haka?" Ya ringa fad'a a k'asan zuciyarsa idanuwansa na k'ara tsayawa k'yam a kan leb'unanta.
Kin girma ne? Kin kai ne?' Ya kuma tambayar kansa.
A hankali ya ciro tishu daga aljihun dogon wandon dake jikinsa na geans.
Yana kallonta ba tare da ya yi mata magana ba ya shiga goge mata jan bakin yana kallon yanda ta mik'o masa bakin ba tare da ta yi gardama ba.
Abinda ya kawo shi ya kasa yi, ledar dake hannunsa ya iya mik'a mata ba tare da ya ce komai ba, dama ledar hud'u ce aka masa, d'aya ta Mama, d'aya ta Kader, d'aya ta Bilkisu, d'ayar kuwa tasa.
A hankali ya saka hannunsa ya rik'e nata ya kuma kalleta, d'an mak'oloton wuyansa ne ya ringa d'an kai kawo, kamar wanda ke had'iyar yawu kamar wanda ke had'iye magana yana hanata fita 'karfi da yaji.
Da k'yar ya iya cewa "Ki yi karatu kin ji?"
Ajiyar zuciya ta sauke tana gyad'a masa kanta, juyawa ya yi yana tafiar nan dake halakata.
K'uri ta bi shi da ido, sam ta k'i shiga ciki ko ta je wajen su Mama.
A lokacin da ya k'arasa kusan k'ofar fita ya ja ya tsaya ya juyo gaba d'ayansa. Had'e bayansa ya yi da jikin k'ofar ya d'ago hannunsa na dama ya kai daidai k'ahon zuciyarsa ya rage girman idanuwansa sosai yana kallonta kamar yanda take kallonsa.
Hannunsa na hagu ya saka ya fito ta da shi yana sakin ajiyar zuciya yana k'ara bin rigar dake jikinta, tsarin tafiarta komai nata da kallo.
Ya sani sarai cewa kallon nan da yake mata ya zarce misali, aman cikin ikon Allah ya kasa cire dubansa a kan wannan yar ficiciyar 'yar.
A hankali take k'ara kusanta kanta da wajen da yake tsaye har ta k'araso ta tsaya tana kallonsa.
Muryarsa a sanyaye ya ce "Billyna, ki daina kwalliya."
K'ara kallonsa take da manyan idanuwanta tamkar na mage. A hankali ya k'ara furta "Kin ji?"
Kai ta ringa gyad'awa tana jin kukan na gaf da zuwa, ji take zuciyarta ta cinkushe wannan kukan da take yi ma gaf da b'arkewa a kowani lokaci.
A hankali ta juya da niyyar tafiya ya kuma fad'in "Bilkisu."
Cak ta tsaya tana haki dan mayar da kukan kuma ta kasa amsawa, kiran sunanta da ya kuma yi a cen k'asan mak'oshinsa ya sakata juyowa , sai da ta d'ago dubanta ta sauke saman fuskarsa, tun daga kan har takalman dake k'afafuwansa k'afa ciki ta bi da kallo sai kawai ta bud'i bakinta ta b'arke da kuka, kuka fa mai sauti , tsakaninta da Allah kuma tana kallonsa yana kallonta hawaye na bin gefe da gefen kumatunta.
Da sauri ya wara idanuwansa a saman kanta, nan da nan ya tuno irin yanayin da ya ke son jefa kansa a ciki a tsayen nan, had'e fuska ya yi kamar wanda zai shigeta da dukan mutuwa, ya had'e muryarsa sosai a dake ya ce" ...
*Masha'Allah.*
[7/24, 10:18 AM] BAK'A CE: πΎπΎπΎπΎπΎπΎπΎπΎπΎπΎ
*DUK NISAN JIFA*
_(K'asa zai dawo)_
πΎπΎπΎπΎπΎπΎπΎπΎπΎπΎ
_RUBUTAWA_
*SAJIDA*
*SADAUKARWA*
*GA*
*MASOYA NA*
π«β¨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*π
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_π€
β *[ T.M.N.A]* β πποΈ
https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/
_Bismillahir rahamanir rahim_
10
Muryarsa kausashe yace "Meye? "
Hannunta ta kai kusan rigarta ta rik'e rigar da kyau jikinta na rawa rawa tace "Nima ban sani ba, haka kawai sai na ji idan ban yi kukan ba zuciyata na ciwo, sai na ji ina hakki."
D'an k'ura mata ido ya yi na d'an lokaci sai kuma ya sauke yar k'aramar ajiyar zuciya yace "To koma d'akin ki, ki ci abinci, ki yi karatu, ki yi wanka, ki yi adu'a sai ki kwonta."
Kanta take ta gyad'a masa har ya gama sannan ta juya da sauri ta nufi d'akin nata.
Kansa ya langwab'e ya rakata da kallo, yarintarta, shagwab'arta, innocence d'inta na saka masa jin cewa dole ya bata kariya, dole ya rarasheta, dole ya k'aunaceta.
Juyawar ya yi shima ya fice ya nufi b'angarensa, ko da ya je wanka ya fara yi ya d'auro alwallah sannan ya dawo falonsa.
Sai da ya gama sallar shafa'i da wuturi ya koma k'uryar d'akinsa.
Maimakun ya nemi abinci ya ci ya huta sai ya samu kansa da zama kusa da gadonsa ya k'urawa waje d'aya ido
" *MAHAIFIYATA*." Y'a fad'a a cen k'asan mak'oshi.
Tabbas soyyayar uwa daban take a cikin zuciyar bawa, kuma tabbas ya ji soyayar wannan mata farat d'aya, sai dai wani baban lamarin da yake gani shine *MAMANSA* . Mama ita ta goya ta sauke, ba dare ba rana, ba zafi ba sanyi ba damana, bata k'yank'yaminsa tun yana hali na a kyankyamce shi, bata kyarar sa tun yana halaya na a kyare shi, bata jin haushin halayan rashin ji irin na yaron da sai uwa ya dace ta yi hakuri da abinta, haka take rungume shi komai datinsa ta sile shi tas komai kazantarsa
Zata iya hanna kanta ci ko sha idan har cikinsa da yinwa, Mama itace bata barci idan bai yi ba
Duka wannan abubuwan ita tana ina kuma tana me? Tabbas ba zai iya wulak'anta ta, ta kowace siga, aman kafin ya iya saka shak'uwa a tsakaninsu sai ya yi fama da kansa.
Dare ya cika sosai zaune domin kuwa har sai da kiraye kirayen sallar asuba suka riske shi ya lalaba ya d'aura wata alwallar ya gabatar da sallar a nan dakinsa ba tare da ya iya fita masalaci ba, ga gajiyar aikin da ya sha hakan ya sa da ya samu baci mai mugun nauyin tsiya ya yi awon gaba da shi.
Bai tashi farkawa ba sai da ya ringa jin kira sama sama.
Mamaki ya ji ya kama shi ainun domin kuwa karfe goma ce ta gota na safe.
Da sauri sauri ya shirya ya saka kayan hausa watau yadi riga da wando wanda akaiwa dinkin malan bahaushe dinkin ya masa das a jikinsa masha Allah.
A lokacin da ya tura baban falon Mama ya tsinkayo dariarta kasa kasa, hakan ya saka shi jin wani farin ciki na dirar masa a zuciyarsa.
Muryar maman ya ji tana fadin "Zainab ai kuwa bana tunanin wad'innan sababin lalen na zamani zasu kamo k'afar jan lallenmu na hausa, ke ni ko ciwon k'afa ya dameni ina k'unsawa nake jin na saku sakayau da ni , aman lallen nan naku na zamani wani lokaci da Bilkisu ta zo da wani ja na dan sakawa yatsutsaina sai na ji sunai min kaikayi da sauri na wanke kar su cire."
Itama dariar ta yi ta ce" Aunty, wai ina labarin mahaifin Babyna?"
Mama ta yi dan murmushi ta ce "Yana nan, yayanta na kaita gaishe shi k'arshen wata wata."
"Wai me ya raba zamanku ?" Zainab ta fad'a tana kallon mama da son sannin dalili.
Mama ta bud'i baki zata yi magana ya idasa shiga baki dayansa da salama a bakinsa.
Zai iya cewa Bilkisu ta fi kama da matar nan, sosai ta dauko kamanin fuskar Zainab.
Tsayinsa ya rage sosai yana gaishe su da kulawa.
Mama da Zainab suka amsa kowace hankalinta na kansa.
Zama ya yi a gefen mama yana dan fadin " Wash."
Mama ta yink'ura ta mik'e ta nufi wajen abinci hakan ya sa daga shi sai Zainab.
Kansa na kallon gefen dakin Bilkisu , fuskarsa tamke tamkar bai san kalmar daria ba.
A hankali take karantarsa, dubanta ta kai wajen da ya fi kurawa ido hakan ya sa ta budi bakinta a hankali ta ce " Ta tafi makaranta tun karfe bakwai da minti talatin, ta karya da kyar haka kuka bar min yarinya bata son abinci?"
Da sauri ya kalleta, murmushi ne ya