Showing 168001 words to 171000 words out of 180809 words
su suke ba wuta da dogarin dake gadinsu ba dare ba rana yana kula da harkar mansu da lafiarsu"
Tati ta kuma gyada kai cike da gamsuwa da bayanan
Tawul din Tati ta rike Najeeba na tafe da Bilkisu a hankali har wajen Injin dake ajiye mai farin gilas a man kuma ba'a gannin abin cikin
Sai da ta taka zata hau Najeeba ta ce" Pant din zaki cire ki safawa nan hadin sosai ya samu"
Sai da Bilkisu ta zarro idannuwanta, aman gannin iya gaskiyar kennan ya sa ta hadiye yawu ta zare din a nutse ta shashafa ko'ina tana gagawa sannan da sauri ta haye ta shige wajen da Najeeba ta nuna mata ta kwonta saman wani lalausan tawul mai kanshi
A nutse Najeeba ta daidaita komai Gilas din ya rufe aman banda fuskarta
A nan ta dawo ta zauna saman doguwar kujerar rike da auduga da abin goge fuska ta shiga goge mata wancen hadin da akai mata sannan ta shafa mata madarar peak kadai ta umarceta cewar ko daria kar ta yi
A nan suka barta , dadadan dumin wajen da bashi da zafi sosai yana ratsa jikinta tana jin kamar wada ake bin du wani kofofin jikinta ana murzata da murza dadadan da nan da nan ta ringa jinta a gajimare sai wani nanauyan baci mai dadi ya yi awon gaba da ita
A takaice dai ta dauki awani ukun a cikin abin nan har sai da Injin ya nuna blu cewar ya gama aikinsa sannan ta ji a hankali ana shafa gefen fuskarta, hakan ya farkar da ita a barcinta ta ga an bude gilas din a yanzun sanyin AC na ratsata hakan ya sakata sakin ajiyar zuciya
A hankali ta mike tana daura tawul din cikin dabara sannan ta fito a wajen
Gannin har an kunce mata kanta ta yi mamaki ainun na barcin da ta yi
Sosai ta huta kuma jikinta ya amsa
A yanzun Tati ce da kanta zata wanketa dan ta wanke mata kanta sosai
Sam bata yi gardama ba domin da pant dinta, mamanta kuwa tun daga ranar da tati da Najeeba suka mata murzar nonon rakumi ta fara gane cewa an gama zubar masu da mutuncinsu ba su ba rufa saima da Hamanta ya yi wasan kura da su kan jiya zuwa yau tsaf hannayensa a jikinsu yake
Wanka ta sha na mamaki Tati sai mamakin yada skin dinta ya koma, ya Allah ana gyara a duniya sai dai idan baka da kudin yi ko hanyar da za'ai maka
Sosai take kara binta da kallo har bata so ta kufta idannuwanta dan yadda ta mata kyau
Cikin ruwan hadin sasaken baure kuma yanzun aka sakata ta zauna, ruwan masu dumin gaske domin sai da ta yi da gaske ta iya zama
Aman tana zama ta ringa sauke ajiyar zuciya, a hankali ta jita ta dawo normal wani irin dadi jikin nata ya dawo yanai mata saima wani irin abu mai santsin da ya gayato kansa ba tare da ko an gayato shi ba dan kuwa zuba tare yarari take
Sai da ya salabce sannan suka fitar da ita
Wani pant din da rigar mama yar cicib aka bata ta saka sannan aka bata wata doguwar rigar ta auduga mai laushin gaske mai ruwan fari aman kuma tana da manyan fulawowi a jikinta haka kuma bata wuce gwuiwarta ba ta zauna saman shinfidar kafet mai duhu mai laushin gaske wanda aka dora masa bargo shima mai laushin gaske
Kayan kunshin da yarinyar Najeeba ta gama hadawa take bi da kallo, abin nasu komai special kuma tsaf tsaf tsaf
A nutse ta zauna ta shiga zana mata kunshi a hannayenta, Najeeba kuwa ta gama hada man gashi ta ajiye kujerar tayani tsegumi sannan ta dora mata abin zama mai laushi sosai ta haye ta kunce tawul din da ta daura mata a kanta ta jona abin busar da gashin nan ta shiga busar mata da shi
A hankali take tsatsagawa tana shafa mata man gashin ko'ina, sai da ta gama sannan ta dauki abin kitso ta yi bisimillah ta shiga yarfa mata wani irin kannanun kitso irin na garari na amare, amarenma masu gata a baki kirin din gashin kanta wanda a hadin da suka masa yanzun ne ya kara yin sidik da shi ya kara mikewa sosai................
Kusan a cen ya wuni, ya wuni ne tare da ita duda ba wani abu ne na a zo a gani ya shiga tsakaninsu ba domin ko hirar sama sama ne dai kamar yadda suka saba suke yi
Sai bayan sallar la'asar suka zauna dan cin abinci
A sanyaye Aisha ta ce" Ina kanwata? "
Hisham ya dago da cokalin da zai kai bakinsa ya yi murmushi ya ce" Tana gidan Gimbiya "
GIDAN gimbiya?, take tambayar kanta, sai dai ba zata iya tambayarsa me ta je yi ba, dan haka sai ta hadiye tambayarta a cikin ranta kawai
Wayarsa dake ringin ta mike ta dauko masa ta kawo masa ita
Yana dubawa ya ga sunnan mahaifinta ne rado rado da ya yi serving da Elhaj
Ajiye cokalin ya yi yana gige bakinsa da tissu ya katse kiran sannan ya bi
Cikin mutunta junna suka gaisa sosai da sosai sannan ya dakata tana saurare
Kallon Aisha dake kallonsa ya yi kafin ya kai dubansa kan agogo ya ce" Ina zuwa zan duba na gani idan yauma da halin hakan zata zo in sha Allah "
Yana kashe kiran ya danna kiran Tati
Tana dagawa ya tambayeta idan har sun gama?
A nan tati ke fada masa cewar gaskiya da sauransu sosaima a kadan zasu kai isha
Hakan ya saka shi yi mata salama ya kai dubansa kan Aisha da take ta kallonsa ya ce" Saka hijab dinki mu je Asibiti, papy ne yake ta son ganninki kina ji tun jiya kece a bakinsa "
Da sauri ta mike cike da farin ciki ta yi ciki ta dauko katon hijab dinta ta saka ta dawo
Nan suka fito Kader ya dauke su suka yi asibitin
A lokacin da suka shiga dogon coridor din Mahaifiyarta ce tsaye idannuwanta sun yi jajajir alamun ta ci kuka har ta gode Allah
Da sauri Aisha ta karasa gabanta na faduwa ta ce" Mama kuka kika yi? Me ya saka ki kuka? Jikin papy ne?"
Mahaifiyar tata ta kasa amsa mata sai dai ta girgiza mata kai, hakan ya saka Hisham daga kafarsa da sauri ya nufi dakin inda Aishar ta shige da sauri yana tunanin meye hakan? Jikin tsohon ne ya tashi ba'a kiraye shi ba ko meye? Ko iya gaishe da mahaifiyar Aishar bai yi ba ya kutsa kansa
Turus ya yi gannin Mahaifin Aishar zaune saman kujera kansa sade a kasa
Aishar ta haye saman gadon na marar lafia ta dora kanta saman cinyarsa tana daria hadi da fadin" Mama na gani tana kuka , har ta tayar min da hankali ashe a zaune kake da sauki? "
Yana daria ya daki bayanta a hankali ya ce" Ja'ira ashe ke aurenki ya kawo ni jinya Damagaram? Tashi nuna min wanda ya kwace min mata mu yi kokowa dan ba zan yarda ba"
Murmushi Hisham ya saki gannin tsohon ras da yannayi na yana jin karfi a jikinsa da kuma yannayin farin cikin gannin jikar tasa ya tsaya jikin garu yana ta murmushi, sai dai shima yannayin iyayen na Aishar sun saka masa ayar tambaya, balema mahaifiyarta dake rizgar kuka a corridor
A hankali ya yi gyaran murya ya ce" Ba kukan wani abu mahaifiyarki take yi ba sai dan na umarci mijinta kan ya je ya ajiye aikin da suke takama da shi har sunna neman kauce hanya da son zuciya a kan aikin nan, shine ta sako shi a gaba kan in dai nashi da aikin nan sun shiga uku karyarsu ta kare ita kuwa ba zata iya zama da shi ba, shine na ce ai ba komai sai na aura masa wata, domin macen da zata iya zama da kai a halin akoy dinka ko babunka itace mace, shine fa ta fita tana rusa kuka sai hakuri ake bata ji ake majinyacin nata ne ya mutu....." ya karashe yana sakin murmushin da ya saka Hisham tsura masa ido, hakama Aisha ta dago tana kallonsa
A sanyaye ta ce" Me yasa zaka hanna su aiki Papy? Idan ka hanna papa aiki me zai yi ya ciyar da iyalinshi ya yi bukatunsa da namu? Papa ka fi kowa sannin menene rayuwar Niamey, idan ka hanna shi aiki ina zai kama? "
Hisham dake tsaye ne ya dan yi gyaran murya ya ce" Zan je na dawo"
Da sauri kakan Aisha Ya ce" Aa dawo, maganar ta cikin gida ce, kai kuwa ka zama dan cikin gidan"
Wajen zama ya nunawa Hisham, du sai ya kasa sakewa da kyar ya zauna ya kawar da kansa a kansu , sam baya so su tatauna abinda ya shafe su a gabansa gaskiya
A nutse kakan Aisha ya ce" kudi? Da mulki, ba abinda ke daukan dan adam ya kaishi wuta cikin sauki sannan ya kaishi aljannah cikin sauki irinsu Nana Aisha, shin kin san kafin ya samu wannan matakin me ya faru da shi? Bara ki ji abinda ya ringa faruwa har ya kai matakin da a jiya zuwa yau da bakinsa yake zayane min wai shi din nan da bakinsa har ya nemi da sirikin da ya aurawa yarsa jiya jiyan nan kan ya saka baki kar a kore shi a kujerar da wani aka tayar aka dora shi, shi din nan ya sauki yar ya badata ba tare da ya san takamaiman halayan waye ya aurawa dan kawai ya san cewa wani ne wanda suke iya mora, Nana Aisha da ba dan Allah ya sa matsayinsa bai saka shi alfahari ba da tuni kin ga abubuwa, Nana wai yau har mahaifiyarki ta iya buda bakinta ta nuna min ita din ba mutun bace butulu ce ta hanyar sakawa wa'inda suka amsheta da ita da yarta, suka ba yarta miji, suka kula da lafiar mahaifin mijinta, suka dauke mana abinci abin sha dukan bukatu tamkar wasu shakikanmu cewar an yi maki kishiya ba zata yarda ba mahaifinki ya samu mahaifiyar Mijinki ya fada mata ko ta sa a saki yarinyar ko ya koreta a aiki, bayan ita ta san alfarmar yaron take ci, su dukansuma suke ci, rigimar ce har ta kawo su nan gabana , wai duka a kan kudi da mulki? NANA AISHA shin ina duniya zata da mu ne?"
Ya karashe a zafafe kafin ya dago da kakausan kallo ya ce"
π
πΎπΎπΎπΎπΎπΎπΎπΎπΎπΎ
*DUK NISAN JIFA*
_(K'asa zai dawo)_
πΎπΎπΎπΎπΎπΎπΎπΎπΎπΎ
_RUBUTAWA_
*SAJIDA*
*SADAUKARWA*
*GA*
*MASOYA NA*
π«β¨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*π
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_π€
β *[ T.M.N.A]* β πποΈ
https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/
_Bismillahir rahamanir rahim_
62
Happy sallah yan uwa
Ya ce" Ai ba dole sai ta aikin gwomnati zai nemo ya ciyar da mu ba, shago nawa gareshi a kasuwa? Idanma bai iya ba ai sai ya koya, in dai aikin gwamnati zai ci gaba da yi sai na yi nazari a kan abinda yake tare da shi, domin kuwa ni ban ga ci gaba ba a rayuwar da zata kai mutun ga halaka, sam bana son butulci da son kai, ni ba jahili bane ba zan lamunci hakan ba, ai ya tara ya je ya juya ko ya bari ya ringa gurgura idan ya kare sai mu dawo mu zauna du ruwansa aman abinnan da na ga shine yake basu damar jiji da kai, yake basu damar aikata abubuwa kansu tsaye ba tare da shaka, kunya , ko jin tsoron Allah ba na soke shi domin ni tunda na gane cewa ana mutuwa ana kwonciyar kabari, akoy ranar hisabi, na zubar da duniya!"
A hankali Hisham ya kuma yinkurawa zai tashi dan ya basu wuri, domin kwata kwata bai ga dalilin da zai zauna a irin wannan issu na famillu dinsu ba, wannan abu ne da ya dace daga su sai su, abu ne da iya su ya shafa , tabas yana auren yarsu aman ba hakan yake nufin ya zauna a yi irin wannan maganar a gabansa ba
A hankali tsoho ya kai dubansa kan fuskarsa ya ce" Ka koma ka zauna, sarai na san abinda nake yi yaron nan, ka koma ka zauna ina yin haka a gabanka ne dan ka gane cewa ba duka dangin mayar da aka aura maka bane masu son zuciya duda wa'inda suka fi kusanci da ita ne suka zamanto haka, ka koma ka zauna domin so nake na fahintar da kai cewa ni kakan Aisha da ina cikin hayacina haka ta kasance sai na jinjina na san ku kuka hada kanku, kafin na kaiwa Allah zabi idan har alkhairin junna ne ku ya tabatar min, ka zauna yaron nan domin so nake kamar yadda ka fada aka barshi a wajensa ina so ka bi ta hanyar a sauke shi, ka sani ba tona sirrin iyalina nake dan na wulakanta su ba, aa , hasalima sun gama wulakanta kansu daga bakin lokacin da suka dauki abin duniya dawamame!"
Hisham ya koma ya zauna yana sada kansa, dan Allah yana gani sosai yake jin nauyin tsohon
Kiraye kirayen sallar magariba ne ta saka mahaifin Aisha kara risinawa yana neman afuwar mahaifinsa sanann ya yi bayi ya hado robar da yake masa alwallah da ita ya zo da buta dan ya masa, sai dai sam ya ki hakan ya umarce su da su je masalaci shi da Hisham din sannan ya saka Aisha ta dauki butar ta tara masa robar tana tsiyaya masa ruwan a hankali yana daura alwallar
Sai da ya gama ta taimaka masa sosai ya fuskanci gabas sannan itama ta daura ta dauki abin sallar dake ajiye ta shiga gabatar da sallarta
Tana gamawa tana shafa fatiha ta mike ta koma kusa da kakanta ta zauna wanda yake jan carbi idannuwansa a lumshe
A sanyaye ya ce" Kina son sa? "
Aisha ta dago da sauri ta kale shi, sai ta ga ita yake kallo hakan ya sa ta sada kanta cike da kunyar tambayar da ya yi mata
Murmushi ya dan saki a sanyaye ya ce" Tabas so halita ne jikata, sai dai ban so ba naki ya fi na mijinki karfi ba dan komai ba sai dan irin yadda rayuwa ta zama yanzun,"
Ya nisa a hankali ya dora da fadin" Shin kina tare da maganar mahaifiyarki dan an maki abokiyar zama kan sai ya saketa ko a kori mahaifiyarsa daga wajen aiki?"
Da sauri ta girgiza kanta ta dago ta kama hannun kakanta muryarta na rawa ta ce" Papy, tun da na gansu tare na gansu, aman kamar yadda ka fada a waya MATAR MUTUN bata auren mijin da ba nata ba, Papy yayama zan kawowa raina raba Bilkisu da Likita?, na tabata mutuncina da yake gani zai daina, Papy .........." ta shiga shashekar kuka ta daga hannunsa ta kai wajen kirjinta ta ce" Nan dina sai ya ringa zafi yana ciwo yana damuna idan na tuna cewa mijin da aka aura min ba asalin sona yake yi ba, aa biyaya da kawaici ya saka yake zaune da ni, bai taba fada min magana ta kiyaya ko ya aikata aikin kiyayar da zai kara tabatar min da hakan ba, asalima ban taba gannin namiji mai dama irin tasa aman kuma yake da sasaukan hali irin nasa ba, Papy itama na girmeta sosai, ba zan ce ga ranar da ta fito dan na aure mata mutumen da ta buda ido da soyayarsa ta min wulakanci ba, a irin wannan zamani daya daya ne ba zasu tafka wulakanci a kan haka ba, Papy na so kwarai a hada mana gida da ita ba dan komai ba sai dan na karra nuna masu ina son su, zan zauna da su da zuciya daya, papy ni bana cikin maganar saki, wani irin saki? Shin mama ta manta dan matar da nake aure na rike da igiyar aurwn yarta ne da kuma kujerar wajen aikin mijinta? Ni ban san ta yaya take da saurin mantuwa ba, sai ta yi tunanin ai ita ko dan ni an sasauta mata aman ita bata sasautawa mutun dan ni din ba? Papy idan tunaninta ta saka an saki yar wani ita tata yar ta fi karfin sakin ne? Ko a tunaninta kyauna, dirina kamar yadda take fadin ba namijin da ba zai soni ba su zasu saka a yi zaman aure da ni? Idan ta kula ai itama ba haka ba take, yau da gobe ta saka fatar jikinta ta ja baya, komai nata ya ja baya bale zaman yau da gobe? Papy........." sai ta fashe da kuka ta dora kanta a hannunsa tana yi sosai
A hankali ya ringa yin murmushi, murmushi ne yake na godiyar Allah da halin jikarsa bai zamo abin Allah wadarai ba, tabas ya godewa Allah da tunaninta bai zama cinkusashe ba
Dan haka ya dafa saman kanta duda hijab dinta ya tare a sanyaye ya ce" Ki je ki zauna da mijinki da kanwarki, raba maku gida ba wani abu bane idan yana da hali rabawar ita ta fi dacewa hakan zai saka du wace yake gidanta to fa ita ce sarauniya, matsalar raba gida daya ne kwal zumuncin y'aya ....shima idan har tsayaye ne hakan ba zai haifar da matsala ba, Aisha na ji dadi sosai sannan zan baki shawara, ki yi masa biyaya, ki kasance mai hakuri da kawar da kai a kan lamuransa, ki bi shi domin ya isa da ke, ki duka masa dan ya isa da ke, ki so yan uwansa domin Allah ki ki na ki domin Allah,