Showing 63001 words to 66000 words out of 180809 words

Chapter 22 - DUK NISAN JIFA COMPLETE HAUSA NOVEL

sajida   

02 Feb 2025

12976

Allah ya yi ko? Ina fatan ba zaki yi fushi da hakan ba "

Mama ta hadiye abinda yake tsaye a kirjinta ta ce" Da me kake bayanin na yi fushi? Da isar da ka nuna ka isa da yarka ko da me? So kake na yi magana bayan ana cikin zulumin rashi? Jauro wa ka aurawa yarinyata? Shin shi yace yana so ko zuwa zata yi ta fuskanci rayuwar wulakanci? Ka san wacece y'ata? Ko tsuntsu daga sama gasashe ka cafka ka cakawa wuka? "

Aba ya sanyaya muryarsa ya ce " Ban sanki da haka ba Asma'u "

Da sauri Mama ta ce" Ba zaka sanni da haka ba dan bata kama ba Jauro! Ka san me ta tsalake ta tardo nan? Ka san me ya kawota gudun hijira har ta samu sanyi a tare da kai tana murnar ubanta? Ka san wani irin abu take ji sakamakon rasa gudan jinninta? Ka san meye a zuciyarta? Ai baka yi laifi ba ubanta ne kai kana iya hanna ni tafia da itama ko yanzu"

Kansa ya sada yana dan shafa furfurar gemunsa hakan ya saka Mama juyawa ta karasa ta buda gidan baya ta saka Bilkisu sannan ta je gidan gaba ta shiga ta zauna tana kallon kasa

Tayar da motar ya yi duda irin yanda jikinsa yake bari ya kama hanyar gida da su, gidan da a yanzu yake ganninsa bakin kirin, ya masa kadan ya masa duhu ya masa daci bai san dalili ba

Sunna karasawa Mama ta fita ta fitar da Bilkisu ta nufi cikin baban falo da ita

Tana shiga ta zaunar da ita kusa da Tati sannan ta juya ta koma

Kansa kife a saman sitiyari ta bude motar ta shiga ta rufe

Da sauro ya dago kansa suka yi ido hudu, a hankali ta ce" Mu je "

Kallonta yake bai iya cewa komai ba, sai da ta kara nuna masa hanya sannan ya tayar da motar ya shiga kokarin juyawa ya fita

Tafia suke a hankali yana sauke ajiyar zuciya mai zafi har suka zo kasan wata babar shuka a bakin hanya cikin layin nasu

A hankali ta ce" Tsaya "

Ja ya yi ya tsaya kansa sade yana mai ci gaba da sauke tagwayen ajiyar zuciya

Juyowa ta yi ta fuskance shi ta sanyaya muryarta ta ce" Me ka fahimta a abinda ya faru tsakaninka da kanwarka? Me ka fahimta a wannan lamari?, shin yarona ka gane cewar hukuncin Allah ne ya tabata a gare ku ko har yanzu kana da ja? "

HISHAM ya juyo ya sauke jajayen idannuwansa a kan fuskarta, a hankali ya dora kansa a kan kafadarta ya janyo hannunta ya kai wajen kahon zuciyarsa ya ce" Mamana nan zafi, ciwo mama"

Mama ta lumshe idannuwanta ta fashe da kuka tana fadin" Nima tawa zafi Hisham idan kana haka, tawama ciwo take idan na ganka a irin wannan halin, Hisham dan Allah ka rufa min asiri kar ka ruguza min duniyata, kar ka kulace ni, kar ka ruguza taka duniyar, Hisham haka Allah ya tsara kai halitar da aka halita wanda a yanzu ana iya amsar ran da aka baka aro har kake wata takama da shi kana da ja da hukuncin mahalicinka? Hisham dina idan baka kama min ba zan iya ba, idan baka talabeni ba zan fadi"

A hankali ya kara riketa da kyau a jikinsa sai kawai ya saki kuka, kuka marar sauti aman gaba daya jikinsa jijiga yake, yana yi yana kara rike mama da itama take kukan, a cikin kukan ya ce" To ni ai sonta nake "

Mama ta ce" Ta haramta a gareka tunda ta zama malakin wani "

Hisham ya kuma cewa " Mama mutuwa zan yi "

Mama ta ce" Ba wanda ya kashe Hisham, idan so cuta ne, hakuri magani ne, mai hakuri shi yake da riba a duniya"

A hankali yake gyda mata kansa hakan ya sa take rage sautin kukanta

Muryarsa cen ciki ya ce" Mamana, ban taba gannin kina kuka haka ba, ki yi shiru kin ji? Ba zan kuma ba in sha Allah, na hakura mamana, na hakura, aikin gama ya riga da ya gama aman dan Allah mamana kar ki kuma ce min wai Bilkisu malakin wani, na sani aman kunnayena basa son ji kin ji mamana?"

Mama ta ringa sauke ajiyar zuciya a hankali ta ce" Yaushe matarka zata tare? Hisham wai baka gannin tsufa nake kara yi ne? Sai na kai ga durkushewa sannan zaka gane cewar mamarka ta buga ba wani sauran abu? Ina son gannin yan jikokina na yawo sunna ja min dan kwali da kafa " ta karashe tana shafa gefen fuskarsa da yannayin rarashi

Hisham ya kaleta da kyau , haka kawai ya ringa hasashen yana da ikon yin yanda yake so da Aisha kamar yada wani kato bakon mutun yake da ikon yi da Bilkisu? Shikenan? Wai da gaske shikenan? Bai san sadda ya sauke kakarfar ajiyar zuciya ba, lalle lamarin Allah shi ke tsara abinsa, shi yasa ba'a so bawa ya cika alfahari a kan komai na gidan duniya, ba'a so ka cika soyaya kamar yanda ba'a so ka cika kiyaya

Motar ya tayar ya kuma daukan hanyar gidansu Mama kanta kukan nan da ta yi wani irin sakayau take jin zuciyarta, kamar yanda shima ya ringa jin salama na mugun nauyin zuciya

Sunna zuwa ta sauka ta nufi ciki, shima ya nufi bangarensa

Mama na shiga ta kai dubanta wajen Aisha da su tati dake mata sannu da zuwa yannayinsu su dukansu ba a cikin nutsuwarsu suke ba hankulansu a tashe ta ce" Aisha tashi ki je ki kaiwa mijinki abinci "

Gaban Aisha ya fadi ta kalli mama bakinta na dan rawa rawa ta ce" Mama ni kuma? "

Mama ta ce" Akoy wata Aishar ne a nan bayan ke?, look Aisha ki zagine ki tarbi mijinki tun kina da damar haka!"

Da dan sauri ta juya ta fita a fallon ba ta dauki komai ba domin ta fuskanci kamar mama a hasale take

Mama ta kai dubanta wajen su Tati

Tati jikinta a sanyaye ta ce" Wai Mami ta rasu? "

Mama ta cire hijab dinta ta zauna tana fuskantarta ta ce" Mami ta amsa kiran ubangijinta, a daidai lokacin da bata shiryawa hakan ba, Zainab Mami ta amsa kiran wanda yake da karfin iko a kanta a irin wannan lokacin da take kara daukar aniyar shiga wata sabuwar rayuwa ta farin ciki, Zainab Mami an nanadeta an dadaureta, an saka mata farin tufafi an fita da ita...........a gaban Mahaifiyarta, yan uwanta, mijin da zai aureta ne da mahaifinta suka rike gawarta suka nufi wajen da aka kebance dan birne yan uwanmu, Zainab an tafi har an yiwa Mami sutura an dawo an daura igiyar auren a kan Bilkisu, Zainab wanda yake da babar guduma mai dokawa ba waiwaye ba gyara ba korafi ya wanzar da irin nasa ikon a lokacin da babu wanda ya hasaso ko ya yi tunanin yanzun haka zai faru! Ga yarki nan, matar aure sunnanta, a yanzu kuma ke ce zaki dauki kurumcinta ko maganarta, ke zaki san yanda zaki yi da irin halin da take ciki!"

Mama na gama fada ta mike ta nufi dakinta,

Gaba daya da kallo suka bita jikinsu ya mutu, mutuwa irin babar mutuwar nan, basu da wani kuzari ko tunani a kusa da kwakwaluwarsu,

Zainab sai ta ringa tariyo magangannun Mama, kwarai wanda yake sa iko ya wanzar kuma mun gode, ashe rai ba komai bane? Ta rasa uwa, ta rasa uba, ta rasa miji su dukansu a sun rayu ne sun haihu harma iyayenta sun yi ciwo, aman sai rasuwar wace ake shirin daura aurenta ya daketa

A hankali ta kai dubanta wajen Bilkisu

Mikewa ta yi ta kamata ta mikar da ita ta nufi dakinta da ita, watau dakin ZAINAB din ba na Bilkisun ba

A hankali take cire mata suturuta bayan ta dauko tawul ta daura mata tawul sannan ta idasa cire mata sauran kananun kayanta

Bayi ta nufa da ita ta sakata cikin jakuzi ta kunna ruwa

A hankali ta wanketa tas sannan ta cika a buta ta bata muryarta cen ciki ta ce" ki yi alwalah "

Bilkisu ta kama butar ta yi alwallah sannan ta mikar da ita ta fito da ita

Zaninta ta daura mata sannan ta dorata saman salaya ta nuna mata cewar ta yi sallah

Bilkisu ta shiga gabatar da sallah Zainab na zaune tana kallonta tamkar wace ke yin salolin sati guda

Sallar kawai take daga ta salamce sai ta mike ta kabarta wata, haka kuma karatun sallar a bayane take yin su sai da ta kai sujadarta ta kifa kanta a bayane ta shiga karanta *LA'IKA HA ILA ANTA SUBAHANAKA INNI KUNTU MINAL ZALUMINE* yi take ba kakautawa ta haka ta saka wani rikitacen kukan da ya saka Tati furta "Alhamdulilah"
[7/24, 10:19 AM] BAK'A CE: 🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾
*DUK NISAN JIFA*
_(K'asa zai dawo)_
🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾

_RUBUTAWA_

*SAJIDA*

*SADAUKARWA*

*GA*

*MASOYA NA*


💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝

☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_


24




Ta jima tana rizgar kukan nan har sai da Tati ta karaso ta duka a hankali ta ce" Ki tashi haka babyna dan Allah "

Bilkisu ta dago kanta sade tana gama tahiya ta salamce

Tati ta janyota ta rungumeta a jikinta ta fashe da wani irin kukan da take jinsa daga cen kasan zuciyarta
Bata taba jin ciwon wani ya gigita mata nutsuwa irin ta yarinyar nan ba, yaushema ta san yarinyar? Aman wani irin abu take ji ya tsaye mata a kasan zuciyarta yana sukanta sakamakon irin kukan da Bilkisu ke yi

Tati ta ce" Dan Allah, dan annabi ki yafe min, hasbunnalahu wani'imak wakim, walahil azim damuwarki na dukana fiye da tunaninki, ban taba jin ciwo a zuciyata irin na yau ba, Bilkisu ki daina kukan nan haka dan Allah ki daina , auren ne bakya so? Walahi zan raba shi , Bilkisu zan raba auren nan koda kuwa zamu tsaya gaban alkali da mahaifinki da mijin, zan raba auren nan na aura maki wanda kike yake kuma son ki, na hakura da komai, na hakura da dukan wani burina da komai , ki daina kukan nan haka kar ya lahantani"

Bilkisu ta dora kanta a saman kirjinta ta ce" Inata, mamin fa tare muka kwonta, inata ta ce na kyaketa ta huta da safe mu yi zance innata sai kawai ta mutu? Yaushema na san Mami? Yaushema ta lakata min dadin zama da ita da har zata barni? Innata sanadiyarta na hakura da komai na zubar da komai, innata ni kam ba dan auren nan nake kuka ba, ina kukan rashin farin cikina ne, innata na rasa Mami yarinya mai kunya, mai fara'a , mai tsoron Allah, mai nuna min hanya, Mami na rungumeni mu yi baci, Mami na sosa min bayana har na yi baci, Inata sati uku kawai na yi da mami ban taba jin nutsuwa irin ta lokutan da muke tare ba, wayo Allahna mutuwa, wayo mutuwa baki da adalci!"

Tatima kukan take tana kara rungumeta a jikinta, sai da ta yi mai isarta sannan ta ringa shafa bayanta ta ce" Kin ga, ban san cewa Mutuwa bata da wayau ba sai yau, kin ga na rasa mahaifiyata, na rasa mahaifina, na rasa mijina Bilki am, aman da yake ban san zafin zama da su ba sam ban ji radadin da nake ji a yanzu ba, Bilki auntyna ta ce wai Mami ta amsa kiran Allah sai na hasasa haka a kanki, Bilki am ashe mutun ba komai bane? Kin ga na rasa a saman me nake rayuwa tsayin lokacin nan, anya ina da hankali kuwa? Anya duniya bata gama yiwa rayuwata illah ba kuwa? Mami ta tafi ta barmu da datin cikin duniyar, mun shiga uku da ranmu sai ya fita ya barmu, ......"

Bilkisu ta ce" Innata, da ranmu sai mun wayi gari babu, kamar yanda muka zo a hannu haka zamu koma a hannu, innata na tsorata da duniya wayo Allahna yar uwatah"

Tati ta ringa shafa bayanta a hankali ta ce" Ban iya yanda zan yi na kwatanta maki wani abin mai daraja ba, hasalima yanzu na fara gane cewar lalle babu abinda ya kai so daraja Balki am, aman zan fada maki cewar mu yi mata adu'a kin ji? Mu yi mata adu'a shine zai kai haske gareta"

Bilkisu ta ringa gyada kanta tana kara rungume tati

Tati ta kara sasauta muryarta ta ce" Babyna? "

Bilkisu ta dago dubanta a hankali ta amsa kamar haka" Um? "

Tati ta ce" ki yi tunani a kai, idan bakya son auren nan ba mai maki dole kin ji? Sai na raba shi walahi koda mamanki ta hanna sai na bijire mata"

Ita abinma na tati sai ya daina bata mamaki, to an yiwa namijima auren dole ya hakura bake ita mace? Kuma itace zata ce zata bijire? Uhum.....


Kamar yanda ta san ba amsata zai yi ba bayan ta gama salamarta sau hudu sai kawai ta afka

Jikinta na dan rawar tsoron da ta fito da shi na mama ta duduba katon falon baya nan sai ta zarce cikin dakansa

Daidai Lokacin da Hisham ya fito daga wanka jikinsa iya kugunsa daure da tawul zai durfafi wajen madubi

Gaba daya ta zazarro ido tana kallonsa haka shima ya ja turus yana kallonta

Kanta ta cire a kansa muryarta na rawa ta ce" Wai mama ta ce na zo na tarbeka, na kawo maka abinci"

Takaici ne ya dirar masa na yanda ta shigo masa daki kai tsaye haka, wai wani ta tarbe shi ta bashi abinci

Kansa ya cire ya nufi wajen madubin ya dauku turarensa ya shiga shafawa

"Ina yini? " ta kuma fada tana kallon tsayinsa ta baya

Sai da ya shafa sosai sannan ya juyo ya nufo inda take tsaye

Kikam ya tsaya a gabanta a yannayin da yake kafin ya sauke dubansa a kan kirjinta ya kai har wajen kugunta

Bakinsa ya tabe a bayane ya ce" To "

Idannuwanta ta dago jin daga to din ya gama magana ko me? Ido hudu suka hada da shi hakan ya saka shi fitar da idannuwansa sosai yana kallonta ya ce" Maman ce ta ce ki zo dakina ? Ina abincin yake? "

Rikicewa ta yi tana kallon hannayenta ta kale shi tamkar sakara ta ce" Ban dauko ba ashe "

Hisham ya kara kureta da kallo ya ce" To je ki tafi"

Kallonsa ta kuma yi lokaci daya hawaye ya cika idannuwanta ta ce" Dan Allah ka sasauta mini, yau sati guda da daura aurenmu da kai aman ki kallo ban isheka ba, dan Allah ka daina hukunta ni da laifin da ba nawa ba, idan Bilkisu ce ka aureta, ka aureta ni bana kishi da ita ka hada mu walahi zan yi maka biyaya"

Agogon dake hannunsa ya saki da karfi ya dokata a kasa ya tako inda take tsaye ya damki damtsen hannunta ya turata saman bed dinsa

Kafarsa daya ya dora daf da cinyarta hakan ya saka shi take zanin dake jikinta da kafarsa yana kallonta ya ce" Anya zaki iya laya kishi da ita? Da ace zan samu damar samun nata bana tunanin zan iya yiwa wata mace adakci idan tana gefena! Shin baki san an daura mata aure da wanina ba? Bilkisu yanzun matar aure ce wani ya samu damata! Wace irin kulawa kike so? Irin wannan? ......" ya fada yana mai kai hannun nasa wajen rigarta ya kama hannun rigar ya ja kasa da dan karfi hakan ya sa yadin dake da santsi bin hannunsa ya sauka

Gaba daya ta tsorata da wannan lamari hakan ya sakata son mikewa sai dai dane rigarta da ya yi da kafarsa ya sakata komawa dabar ta zauna jikinta na rawa tana kallonsa tana girgiza kanta ta ce" Wani irin an daura mata aure? Kuma walahi ni ba wannan nake nufi ba, ina nufin idan na maka magana ka amsa ni"

Kansa dake dan sara masa ya saka shi cije lebensa na kasa, ko ba komai yarinyar ce ta ji duwawu ga shegen surutun tsiya duda yan mamanta bashi fi ya rike da yan yatsunsa biyu ba, kai shi uwa uba tunaninsa wannan yar zata iya da shi? Shi da ko biye biyen mata yake ya tabata sai dai ya ringa bin irin kartin matan nan , su zasu iya da wahalarsa,

Mikewa ya yi ya saketa ya juya mata baya a hankali ya ce" ki daina matse min waje , bana son na yi barna kin ji? "

Mikewa ta yi da sauri tana gyada kanta tana maida hannun rigarta sannan ta juya ta fice a dakin

Tsaki ya ja mai karfi ya karasa ya kashe fitilar dakinsa ya kwonta ya lumshe idannuwansa

Du zaune suke bayan salar isha'i , ba wani hira suke tsakaninsu ba aman kowa na dan tsakurar abincin dake gabansa,
Tati na diva a cikali tana sakawa a bakin Bilkisu wace ke kwonce a jikinta tamkar wata mage

Mama ta gama hada na saman faranti ta kali Aisha ta ce" Tashi ki kaiwa mijinki abincinsa"

Daga ita har Bilkisu a zabure suka dago da dubansu suka dora a kan Mama, sai dai irin yanda take kallon Aisha fuskarta tamke ya saka Aishar mika hannu ta dauka ta mike jikinta na rawa ta fita

Bilkisu ta lumshe idannuwanta a hankali ta mike daga zaunen da take ta nufi dakinta hakan ya sa Tati rakata da ido sannan ta sauke dubanta a kan Mama

Allah yana ganni bata taba shayin yiwa yar uwarta magana kai tsaye irin na wunin yau ba gaba daya ba fuska, ta tantanke ta hade fuskarta ba fuskar da zata dubeta ta yi mata wata maganar ko korafi, aman ba komai zata sauko ne ta tabata idan ta saku zasu tatauna ne, wannan abubuwan sunna damunta, so take ta yi dana sani har ta hayana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login