Showing 99001 words to 102000 words out of 180809 words

Chapter 34 - DUK NISAN JIFA COMPLETE HAUSA NOVEL

sajida   

02 Feb 2025

12997

ya sake ni, ya sake ni a haka? Idan ban yi da gaske ba ina tsoron na zame maka katuwar mace a gabanka, ka ga gari ya dauka, labari a damagaram in dai ka yarda ya mutun daya ya ji shi an kare, lungu lungu , sako sako sai ya zagaya a lokacin da baka shirya ba, Hamana makadi ya ce min wai Bilkisu bazawara......"

Sai kawai ta idasa fashewa da kuka gaba daya tana yin irin har jikinta na rawar nan

Walahi kafafuwansa ya ringa jin sunna son tika shi da kasa a lokacin da ta ce ya ganta gani irin baban nan, shifa bama fahimtar sauran bayanin ya yi ba hakan ya saka shi jurewa, ya gyara tsayuwarsa da kyau ya dan daga kafarsa ta dama ya kara karasawa sosai gabanta

A hankali ya dago da habarta wace take kusa da kusa sosai da kirjinsa
Kanta ta dago hakan ya bata damar zuba idannuwanta da ko digon hawaye babu a kan lalausan sajen fuskarsa sai kuma idannuwan nata suka sauka a cikin jajayen idannuwansa wa'inda sukai wani irin ja sosai
Da sauri ta cire ta shiga bin dogon karan hancinsa da bakinsa mai ruwan pink color da kallo

A hankali ya kuma dan girgiza habarta hakan ya saka ta kara dora dubanta tar a cikin idannuwansa harma ta ji kamar zai dauketa da idannuwan baki daya

A hankali ya shiga yin baya baya da ita har ya kaita saman doguwar kujerar dake wajen

Bai yi mata magana ba, sai wani kokari da ya shiga yi wanda ya sakata zazaro ido domin gaba daya ya aniya neman inda zif din doguwar rigar dake jikinta yake

A firgice ta ce" Hamana "

Bai saurareta ba sai ya bar neman aman kuma sai ya dawo wajen kasan rigar ya shiga nuna alama na kamar zai yaye mata baki daya

Wannan karron da ihu ta ce" Hammmmmmmana! Hama Nice fa!"

Hannunsa ya dago da karfi ya mikar da ita tsaye daga irin kwoncin da ya yi mata ido na cikin ido ya ce" wani irin gani ne ya maki? Me ya gani? Baban gani? Wani irin gani ne na ce!" Ya garashe da wata irin tsawar da ta sakata jin alamun ta fara sakin fitsari a dan wandonta........... .... .




Nima ji na yi na saki wayata domin gaba daya Hisham ya birkice , kamar ya haukace, ya kasa gane wani yare, kamar yana gannin aisha ne faπŸ˜’πŸ˜²πŸ˜²πŸ˜², kai ku zo mu je wollah kar ya afkawa yar baby🀣🀣🀣🀣🀣🀣🀣🀣🀣🀣🀣




πŸƒπŸ»β€β™€οΈπŸƒπŸ»β€β™€οΈπŸƒπŸ»β€β™€οΈπŸƒπŸ»β€β™€οΈ to madallahπŸƒπŸ»β€β™€οΈπŸƒπŸ»β€β™€οΈπŸƒπŸ»β€β™€οΈπŸƒπŸ»β€β™€οΈ
🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾
*DUK NISAN JIFA*
_(K'asa zai dawo)_
🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾

_RUBUTAWA_

*SAJIDA*

*SADAUKARWA*

*GA*

*MASOYA NA*


πŸ’«βœ¨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🀝

β˜† *[ T.M.N.A]* β˜† πŸ“–πŸ–ŠοΈ

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_


38



Gaba daya irin yanda ya saki tsawar nan sai da jikinta ya kwashi rawa, bakinta har hadewa yake dan tsoro domin ba zata tuna ranar da ya taba mata haka ba koda ya matan to bata malaki hankalin kanta da zata iya ganewa ba

Idannuwansa sun kade sun yi jajajur uwa uba santaleliyar cinyarta guda a bude take sakamakon kafar guda dake saman kujera kuma shi ya yi tsayuwar da kafarsa daya ta yi alamun shiga tsakanin kafafuwanta

A tsorace ta ce" A lokacin da aka daura mana auren ne ya ganni ya ce koda ba mami zai rike amanar mami yana so na kuma ya ji dadin aurenmu"

Wata wawuyar bayananiyar ajiyar zuciya ya shiga saukewa a hankali ya ringa sasauta rikon da ya mata kafin gaba daya ya saketa ya yi baya saman kujerar nan yana rike da kansa da hannayensa bibiyu yana rintse idannuwansa

A tsorace take, hakan ya sa daga tsayen da take jikinta bari kawai yake

A hankali ya dago rinanun idannuwansa da yan yatsunsa ya mata nuni da ta tafi

Sai da ta lumshe idannuwanta ta hadiyi busashen yawun dake makogwaronta sannan ta juya jikinta baki daya a mace bayan ta kuma kallonsa ta kama hanyar fitar

Da ido ya rakata har ta bacewa ganninsa kafin ya jimke hannunsa daya ya daki table din dake gabansa muryarsa a raunane ya idasa sauka kasa a hankali ya ce " INA SON KI BAN SAN YAYA ZAN YI DA SOYAYARKI BA "

tana fita kukan da take rikewa wannan karron ya kwace mata, da sauri ta ringa hawa matatakalar da zata sadata da bangaren su Mama

Tati dake tsaye tun tafiarsu tana kai kawo ce ta juyo da sauri ta riko hannunta tana kallonta hankalinta tashe ta ce" Dukanki ya yi? Dukan ki ya yi? "

Bilkisu ta kasa amsata, inama ace dukan nata ya yi? Inama a ce a jikin fatar jikinta ya daka ba a cikin wajen da warkewarsa ke iya zama abu mai wahala ba? Inama ace wannan duka nasa na bulala ne ba na aman jinni ba? A hankali ta janye jikinta daga na Tati ta juya ta yi ciki da gudu domin Allah yana gani gaba dayansu har maman sai ta ringa gannin laifinsu, baki dayansu sai ta ji zuciyarta zata buga a kan irin abinda suka aikatawa rayuwarta

Tati ta juya da sauri ranta bace zata nufi bangarensa Mama dake saka hijab dinta domin ta dauro alwallah ta ce" Ina zaki je? "

Tati ta juyo ranta bace ta ce" Ina zan je kuwa banda wajensa ya fada min a kan me zai daketa? Me ya yi mata? "

Mama ta yi dan murmushi tana kallon Aisha dake tsaye itama hankalinta tashe aman mamanta ta shiga ta yi sallah ta ce" Aisha je ki yi sallah kin ji? "

Aisha ta juya jiki a mace ta nufi ciki, mama ta kalli Tati ta ce" Baya dukanta, du abinda ta aikata bai taba dukanta ba, ita din ce ko yaya ya mata fada tana daukan abin da girman gaske, Bilkisu shirme ke damunta wanda da ace zata nutsu ta farka daga abinda take tunanin mai yiwuwa ne da ta farka ta daina wahalar da kanta domin abinda take yiwa din ba zai taba kasancewa ba! "

Tati ta yi tsam da jin furucin mama, a hankali ta ringa takowa har wajen da mama ke tsaye tana shinfida salayarta ta tsaya tana kallonta ta ce" Ni ban fahimci kalamanki ba Asma'u, dan Allah ganar da ni meye ne ba zai taba yiwuwa ba? "

Mama ta kuma yi mata wani murmushi mai bada tsoron nan sannan ta kafeta da ido tana kallonta ta ce" KIN TABA GANNIN SHIRMEN SOYAYA TSAKANIN MUTANEN DA SUKE MUHARAMAN JUNNA? "

Tati ta kuma kallonta gabanta na faduwa da yannayin na mama ta ce" Wani irin muharaman junna? "

Mama ta kara tsaida dubanta tar cikin nata ta ce" KIN TABA GANNIN AN YI MAGANAR BANZAR SOYAYA TSAKANIN WA'INDA SUKA TSOTSI NON DAYA? "

Tati ta kara tsare mama da ido, wada itama tar take kallonta ido cikin ido kafin a hankali ta ce" Zainab zan yi sallah kar magariba ta shige "

Jiki a mace tati ta matsa daga gaban mama still tana kallon fuskarta sannan ta juya ta nufi wajen pampon dake cen kasa dan ta dauro alwallah

Samun kanta ta yi da zurfafa tunani a kan maganar yar uwar tata, tabas akoy abinda mama ta rike a ranta, wanda ta tabata tana daf da fashewa, ta san wacece asma'u, ta fi kowa sannin wacece asma'u, ita nata wasa ne, sai dai koma meye ta san ba zata iya jurar gannin Bilkisu a damuwa ba ko dan son da take yiwa Hisham zata sadaukar da komai ta yi hakuri

Wannan tunani ya sakata sakin murmushi ta yi alwalarta cikin nutsuwa hankali kwonce


Mama na gamawa ta shige dakinta ta rufe ita daya ta ringa kai kawo, a hankali ta zauna bakin gadon dake dakinta ta fashe da kuka, tunda abin nan ya faru take son zubar da hawayenta har haka aman abin ya gagara, tana ji tana gani take kawar da kanta ta yi shiru, sai dai a yanzu an zo gabar da take gannin idan aka ci gaba da haka lalle lalle ita din ta tashi daga sunnan mace ta zama solofiyo, sam bata ga ma'anar wannan kwabar ba, idan har ta yi shiru ta kawar da kanta kuma toh tabas ta cuci kanta, haka kuma kanwarta da aminiyar da ta yi sabuwa ba zasu taba fahimtar cewa rayuwa ba wai iya kudi bane farin cikin dan adam, a hankali ta sada kanta tama tunanin BILKISU, asalima damuwar Bilisu shine, farin cikinta shine, to tabas zata daki rayuwar yarinyarta a lokacin da bata shiryawa hakan ba, zata zowa yarinyarta da abinda zai girgizata sosai, fatanta Allah ya bata ikon jurewa, ta daure, ta kawar da kai, ta jajircewa wannan lamari

A wannan rana a dakinta ta gabatar da sallar isha'i har bayan sallar tana iya jiyo muryar maman Aisha na amsa kira tama ta daria sama sama tana amsar sakon barka daga mutane daban daban na mayar da mijinta kujerarsa da aka yi,

Ajiyar zuciya ta sauke tana kuma tunanin Aisha, yarinyar mai sanyin hali da tsoron shiga hakkin wani, sai dai iyayenta sam basu da wannan a gabansu, tabas sai ta yi duka da bulalar da take rike da ita wace zata girgiza kowa sannan ta farkar da kowa, bata tana tunanin zata iya fuskantar butulci irin wannan ba, bata taba tunanin a duniya zata wayi gari ta ga haka ba, duda dan Adam na tafe da lamura na mamaki, dan ya wulakanta ka ba wani abu bane, aman bata taba kawowa ranta cewa hakan zai faru da ita ba

Cikin nutsuwa take dan bugawa har aka bude mata

Shiga ta yi ta samu waje ta zauna yannayin fuskarta a daure, hakan ya saka Bilkisu zama a darare tana kallonta

A kausashe ta ce" NANA BILKISU "

BILKISU ta dago kanta da sauri jin mahaifiyarta ta kama sunnanta complet ta kasa amsawa saima bakinta da yake dan bari a hankali a hankali

Mama ta kara gyara zamanta tana kallonta ta ce" Tabas abubuwa sun same ki , ko na ce sun same mu a cikin kwanakin nan, sai dai zan fada maki cewar wannan abu sune abubuwan da suka kaini ga yanke hukunci a kanki, Bilkisu ni na haife ki da cikina, dan haka nake baki umarni guda uku!
Na farko shine, maganar koyon kwaliya na soke ta, ba shawararki nake nema ba, umarni ne na baki idan dai zaki je gidan mai martaba sai dai dan ki yi zumunci ba dan ki je ki koyo kwaliya ba, kwayilar wacece baki iya ba? Iya tafiar da rayuwarki ne baki iya ba!,

Abu na biyu shine, daga yau na soke maganar saka kannanun kaya ko tafiar da lamarinki dan kisanci da mutumen da yake ba muharaminki ba!, idan har kika yarda Bilkisu kika kuma shiga harkar HISHAM da wani niya na daban banda dan uwanki yayanki walahi sai na saba maki, sai kin kasa yarda cewar nice mahaifiyarki!"

Shiru mama ta yi tana dan saurarawa gannin irin yanda Bilkisu ta yi mata tsuru tana kallonta, sai da ta hadiyi dukan abinda take ji sannan ta ce" BILKISU, umarni nake baki a maganata ta uku da ke shine, ki fitar da mijin aure a cikin satin nan na gaba, ko ki je ki samu mahaifinki cewar ya fitar maki da mijin aure, ko na same shi da wannan magana aman a cikin mazan duniya banda HISHAM!,"

A zabure Bilkisu ta kuma kallon mama hakan ya saka mama kara kaisasa muryarta ta ce" Bilkisu idan haka bata samu ba, ina mai tabatar maki ba zaki kuma gannin farin hakorina ba, ba zan maki baki ba, aman na rantse maki zan shafe ki a babin rayayun dake gefena! "

A zabure Bilkisu ta mike tsaye tana kallon mahaifiyarta wace ta mike da niyar juyawa ta tafi

Da gudu Bilkisu ta rukunkumeta ta baya ta fashe da wani irin kuka mai karfin gaske tana dora kanta a saman bayanta , muryarta a rikice ta yada dukan wanda bai yi baci a bangaren na mama zai iya jiyo wannan kuka nata ta ce" Mama, me aka yi? Innalilahi wa'ina ilaihi raj'ume, mama ashe rikicin zuciata bai kare ba? Ashe tashin hankalin rayuwata bai kare ba? Mama ashe na daina dariar kalamansa da yannayinsa mafarki ne? Mama me muka yi da zafi haka? Me ya sa ba zaku barmu mu rayu da junna ba? Mama kin tsani hamana ne kema? Mamana kin tsane shi ne kema? "

A firgice mama ta juyo ta bambareta daga jikinta, ba zato ba tsamani ta dauke fuskarta da gigitacen marin da ya sakata yin baya ta yi luuu ta fada saman bed , a zabure ta tashi a tsorace tana kara zarro ido kukan ya dauke dif

Mama muryarta a sama sama itama ta nunata da yatsarta ta ce" Bilkisu? Har kin yi idon da zan yi magana a kan da namiji ki nuna min ba haka ba? Bilkisu har zaki ce na zani yaron da na rayi da soyayarsa a zuciyata irin ta da da mahaifiya? Bilkisu ashe dan na cutar da ke na haife ki na baki tarbiya? Ashe baki da hankali? Soyayar banza soyayar wofi? Wace soyaya kike jira a duniyar da take da duhu a gare ku? Ba so, ba maganar soayya ko ya taba furta maki gaki ga shi? Dan ubanki me kike tunani da rayuwa da har zaki dube ni ki ce min na barku ku rayu? Ina ce da kunnayenki kin ji lokacin da mahaifiyarsa ta ce kum sha nono daya? Ke din kin zama koma baya a cikin mata da har zaki tashi ki kuma nacewa? Bilkisu idan har Hisham ya gane abinda kike ciki koda ace zan iya bari ki aure shi a gidan duniya ina mai tabatar maki sai kin ga wulakanci! Duniyar ce ta cenza, kidanta ya jima da cenzawa shi yasa rawarta ta cenza! Da sai ya ja gashin kanki a kasa tsabar ya san kina sonsa ba inda zaki je ba abinda zaki yi sai hakuri! Ke aure ibada ne ba bauta irin ta bayi mararsa yanci ba! Aure ana raya shi ne bisa tafarki na gaskiya, amana, soyaya ba wai a fara dora karya a kai ba, idan baki fita a harkarsa da iyalinsa ba sai na maki tijara Bilkisu! Idan baki fita a sakarci ba sai na ilata ki kin ji na fada maki! Ni ba mahaukaciya bace, fahimtar d ana yi shiruna ya fi maganata kawo alkhairi ya saka na yi gumm ba wai dan ban san abinda nake ciki ba! Idan hauka ne ake shukawa ba damuwa a girba aman ba da ni ba! Ya isa haka! Ya isa na ce!"

Ta karashe da kuwar da ta saka Tati idasa shigowa a tsorace gaba daya yannayin tashin hankali ya bayana a tatare da ita

Sai da suka hada ido hudu da Mama gannin irin hawayen dake zirowa ta idannuwan Mama aman sai ta saka hannunta ta goge tana kallonsu ta mayar da dubanta kan Bilkisu da gaba daya hannayenta ke saman kanta ta ce" idan har baki bi umarnina na wanke ki da hannuna na mika ki dakin miji nan da sati daya ba, ki dauka cewar na mace a duniyarki! "

Da sauro tati ta ce" Hasbunnalahu wani'imal wakim, Asma'u menene haka dan girman Allah? Meye ya faru har haka? Kina irin wannan furucin me kike nufi? Zaki shiga tsakanin soyayar Bilkisu da Hisham? Duma wanda ya ce baya tare da soyayar nan sai dai a yi dayan biyu, ko ya mace a yi ba shi ko Allah ya san yanda zai yi da shi, haba Asma'u da kike fadin hakan shin koda hakan na nufin bacin ransu na har abada? "


Mama ta juyo tana kallonta cike da wani sabon mamakinta duda ta yi niyar Mayar da maganar mamaki a kan Zainab, sai dai yanzun tana gannin dole ta ji mamakin furucinta, a kausashe tana danne damuwar irin yanda yarta ta zama kamar mutun mutuni binta kawai take da duba harda dan habo din da ya zuba daga hancinta sakamakon marin da bata taba yiwa fuskarta ba yau ya sauka a furkar tata da magangannun da bata shiryawa hakan ba ta kara kollon Tati ido cikin ido ta ce" ni umarni na bada ba magana na tsara dan nawa burin ba, abin duniya kuwa a lokacin da wani ke gannin ya tara wani yake barin duniyar! Karshen alewa dai kas, kuma duk nisan jifa kasa zai dawo! ZAINAB du dukiyarka du izgilancinka dai zaka kare kafafuwa a dadaure hannuwa a dadaure cikin farin likafani a haka rami a birne , idan wai kana da wannan sa'ar kennan domin wata gawar ba ita ba burbushinta! Fatanmu mu cika da kyau da imani ne! Sannan eh *KODA HAKAN NA NUFIN MUTUWARTA!* "
[7/24, 10:19 AM] BAK'A CE: 🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾
*DUK NISAN JIFA*
_(K'asa zai dawo)_
🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾

_RUBUTAWA_

*SAJIDA*

*SADAUKARWA*

*GA*

*MASOYA NA*


πŸ’«βœ¨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🀝

β˜† *[ T.M.N.A]* β˜† πŸ“–πŸ–ŠοΈ

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_


39




Mama na gama fada ta juya zata fice a dakin ,

Tati da gaba daya hankalinta ya so fin na maman tashi ta kamo hannunta da sauri ya ce" Aunty ,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login