Showing 117001 words to 120000 words out of 180809 words
dawo kuna masa abubuwa sai yau yana labarta min bayan na matsa masa cewar ita tana yi batama san mijin nata na nan raye da ransa ashe a nan din dai cikin garin damagaram din da bata da wani wawan girma ko mutanen cikinta basu da yawan da balarabe zai bace cikinta, aman balaraben nan dai da na sani Elhaji balarabe shine ashe mahaifinsa? Ai sai ki katse maganar da ta kula tun farko ki nuna masu ba haka bane sannan ki tirsasa su yi mata biyaya domin ta isa da su ba wai ki hau kan zancen ki zauna dan kawai kina gudun ki saki jiki a kan maganar yaron nan, Asma'u idan ba abinku na mata ba har a maki kallon wace ta saki jiki a kan yaron da tun yana zanin goyo take amsa kiran mamansa? Ai ba sakin jiki zaki yi a ciki ba, karbe komai zaki tunda dama naki ne ki aura masa zabin mahaifiyarsa sannan ki aura masa zabinsa, kin ga maimakun hakan sai kika ce da shi shi din aban Bilkisu ne? Abanta fa? Baki ga yanda ya ringa maimaita wai shi abanta, kin yiwa kanki adalci ne ?"
Mama ta ringa sauke ajiyar zuciya tana kallonsa ta ce" To To ni ba zaka ce ba'a min adalci ba tsakani da Allah? Ka duba fa ka gani uwar yarinyar nan a nan take a tare da yarta, ba hakan na damuna bane sai dan irin yanda nake so ya yiwa yarinyar nan adalci domin baka ga yadda take yi masu biyaya ba har shi din, basa tsoron gori ko banzatarwa irin ta d'a namiji sanadiyar wannan abin da suke a kan yarinyar?, ai sai ta koma wani wajen daga bakin lokacin da yarta ta zama matar gidan, ni ba zan kuma zama a wajen da Bilkisu ta zama matar gidan ba ko na wuni ne bale kwana!"
Ta karashe tana cire dubanta a kansa
Aba ya ringa murmushi ya ce" Yar fari ce kike kama sunnanta anya filatanci bai yi maki kaura ba kuwa Asma'u? "
Mama sai a lokacin ta tuna, da sauri ta sada kanta tana jin bakinta ya mata abinda ba shi ba
Aba ya kara yin murmushi gannin ta fara saukowa ya ce" Ba'a yi maki adalci ba Asma'u, ai akoy karra, akoy kunya, akoy cire kai a kan abubuwa, yau koda ba kowa bane a matsayin kudi yaron nan ai bai dace a yi haka na, aman kuma ke din dama dole ki ringa shanye bugu sakamakon darajar da Allah ya baki ta zamowa baba, kina hakuri sosai Asmana ni shaida ne aman kuma haka zaki kara hakurin domin mai hakuri mawadaci ne, baya taba tabewa sai dai ya samu nasarar rayuwa ko yayane, mahakurci zai kai ga ci ne Asma'u"
Mama ta kara sada kanta tana jin sanyi sanyi na shiga zuciyarta
Aba ya ce" Yarinya kuwa mai biyaya, Allah zai dubeta, matarsa ce kuma dan mahaifiyarta na nan sai banzan namiji zai mata gorin hakan duda na san bamu da kirki aman bana tunanin yaron nan zai yi haka sam sam"
Mama ta dago tana kallonsa irin yadda yake bayanin a sanyaye sai ta ji tana samun nutsuwa a kan tashin hankalin da ya dirar mata dazun
Aba ya ce" Kira min Bilkisun kin ji? "
Mama ta gyada kanta a hankali ta mike daga zaunen da take ta je ciki ta yi kiran Bilkisu cewa mahaifinta na kiranta
Bilkisu tana zuwa bata zame ko'ina ba sai daf da kafarsa ta duka kanta a kasa ta raba kan nata da jikin kafarsa muryarta a ciki sosai ta shiga gaishe shi
Bai iya amsa gaisuwar ba sai harara da ya aikawa mama wace ta cire kanta tana tura bakinta gaba , ya girgiza kansa kadan ya ce"Mai gado, ina son na tambaye ki, shin kina son hamanki kuwa? Zaki iya aurensa? "
Bilkisu bata san lokacin da ta dago da dubanta ba, a tsorace ta kale shi, sai kuma ta kalli mama ta ga kanta a kasa yake ta kuma kallon Abanta
Nan da nan ta afka tunani 'Shin kin tabata shi din yana sonki ko kawai shirme baki tafasa bama bale ki kone har kike kokarin nuna shirme a gaban mutane a kan wata wai soyaya? To bari ki ji zamanin da da yanzu ba daya bane, idan kika yi sake sai hamanki ya ja gashin kanki a kasa ya kirta maki abinda baki taba tunani ba domin ya san ke kike sonsa ba inda zaki je ba abinda zaki masa!'
"BILKISU?" Aba ya fada yana taba gefen fuskarta hakan ya sakata dan zabura tana kuma kallonsa ya ce" Kin yi shiru ina magana"
Bilkisu a hankali ta ronga girgiza kanta tana kallon mahaifinta kafin ta buda sanyayar muryarta ta mayar da idannuwan nata kasa a hankali ta ce" Aba bana son sa, bana son Hammana ko kadan, ba so irin na soyaya nake yi masa ba, ina masa so na dan uwantaka, Abana ka duba ka zaba min koma wanene zan zauna da shi aman banda Hamana"
Mama ta ce" Karya kike, hamman ne bakya so kuma? "
Bilkisu ta dago dubanta tana kallon mamanta, a hankali ta gyada kanta ta ce" Mamana, ba zan taba zama da hamana ba, na rantse maki bana so kar a min!"
Tana gama fada ta mike da sauri ta fice hakan ya saka suka rakata da kallo a bayane mama ta ce" Ka ji wani sababin "
Aba ya ce" Kya ce haka mana, ta yaya kike so dama yar ta nuna tana so bayan kin gwagwabran min bakinta, Asma'u haka rikon amanar yake? Gaskiya a bani y'ata na tafi da abina domin a yanzun kin ganta nan mace daya kwal uwa rai ita me da ni kuma ina son abina, ina dalili ji yadda yarinya ke sauke ajiyar zuciya ko tausayinta bakya ji? An ji kunya a gidan nan za'a kashe min yarinya? "
Mama ta saki baki harda dan tare habarta tana kallonsa ya dage bilhaki fada yake an tarru za'a kashe masa yarinya
Aba ya ci gaba da fadin" Dama ta yaya kike so ta fito tana kallonki ta ce tana son wane ai tashin kunya ne, wannan sai ke idona idonki yanzun kin nuna min soyaya?, kin ga ba zata iya haka ba sai dai ta nuna bata so idan ya so ni sai na gane yarenta"
Mama ta ce" Kai aban Mai gado dan Allah ka girma fa kake irin haka"
Aba ya tabe bakinsa sannan ya sasauta muryarsa yana kallonta da yannayi irin na maganar bakinsa mai mahinmanci ce zata fito ya ce" kamar yadda kika ajiye maganar daurin auren yaronyata nan da kwana shida magana na nan, sai fai da yaronki, shin kina da ja da maganar nan har cikin zuciyarki ko kin barwa Allah komai? "
Mama ta sada kanta cike da jin kunyar irin yadda yake dadaureta da magangannu yana sako Allah ciki hankalinsa kwonce bata iya cewa komai ba
ABA ya yi murmushi sannan ya kara sasauta muryarsa yana ta yi mata nasiha ya kara dorawa da fadin" Zumunci? Daga sallah sai zumunci wanda ya yi wasa da shi shi da allahnsa"
Mama ta dan girgiza kanta a sanyaye ta ce" Ni kam na yafe mata, bana so Allah ya kamata, ko kadan, abinda nake so yar uwata ta gane rayuwa ta gane mahinmancin dan uwa da kuma meye datin duniya"
Aba ya ringa gyada kansa kafin ya mike da takalmansa a kafarsa yana fadin" Nima na yarda a maida auren namu rana daya kawai ba komai "
Mama ta mike da sauri tanaai jin matsananciyar kunya ta ce" Jauro aa ni ban ce ba.....
"
Katsewa maganarta ta yi sakamakon gannin motar da Tati ta fita da ita ta dawo ta ajiyeta ba ainahin wajen da ake ajiye motocin ba ta fito ko takalmin kafarta bata saka ba ta nufo su hijab dinta a hannunta
Tana zuwa ta kama hannayen mama dake tsaye turus ta fashe da kuka a rikice take fadin" Da gaske yana raye, da gaske yana raye? Tun yaushe kuka sani, yana kuma cikin garin nan baku fada min ba? Ashe namiji kanin ajali ne ban sani ba? Ashe namiji bashi da amana ban sani ba? Me na masa da zafi? Baro dangina da na yo na zo ma zauna da shi na haihun masa ne laifina ko me? Ko karya yake baya son haihuwar ne ya saka min sonsa ya tafi ya barni? Ashema a cikin garin nan yake? To ta yaya aka ce ya mutu har aka nuno shi da iyayensa sunna kuka? Shin gwomnatim sojoji ta san da wannan maganar cewa yana raye daure masa ta yi ko suna karyar ya masu? Ni ni ni ya wulakanta ya cuta yanzun yake zaune hamshaki da matarsa jinsinsa? Ta yayama aka yi har Aka hasko shi a TV a mace? "
Mama ta dan tsaida yadda take girgizata tana kallonta cike da tausaya mata ta ce" Zainab akwatin gawarsa kika gani a TV ko har shi din aka gwado a cikin akwatin da ake saka su? "
Tsai Tati ta yi da kukan nata tana tunano ainahin abinda ya faru
Gaba daya ta ringa jin iska na yiwa kofofin hancinta kadan
Wani irin jan numfashi ta yi ta so kara fashewa da kuka aman abin ya gagara domin gaba dayanta ta yi baya luuuuuuuuuuuuu
Nace ba yau juma'a ce ko? Dan haka sai atinin ni da ku in sha allahu watau kwana biyu na hutun weekend saura na ji wani ya ce min na yi gagaπππ»ββοΈ
Assalamu Alaikum
Masoyanmu da fatan kuna lafiya.
Muna miko maku godia da fatan alkhairi masu matukar yawa a yadda kuka nuna mana kara da kauna wajen siyan littafinmu na kudi.
Alal hakika munji dadi kuma mun gode sosai Allah ya saka da alkhairi ya kara budi.
Ina kuma kara kira ga masoyana wadanda basu siya ba dasu garzayo su siya domin muhimman darussa rayuwa, ilmantarwa da nishadantarwa dake cikin littafin. Dukkan wanda yaji taken littafin na *AURE YAKIN MATA* yasan littafi ne mai cike da ilmantarwa da bude ido akan irin rayuwar zaman auren da muke a zamanin yanzu don haka babu danasani a siyan littafin.
Yadda kuke siyan littafin yana kara mun kwarin guiwa wajen yi maku typing din littafina na *KOMIN NISAN JIFA* ina fatan zaku cigaba da siye don in samu kwarin guiwar yi maku typing din littafina na kyauta akan kari ba tare da bata lokaci ba.
Na yadda daku na aminta da irin kaunar da kuke mun, nasan kuma zaku siya littafinmu mai take *AURE YAKIN MATA*
*INA SONKU SOSAI INA ALFAHARI DA KASANCEWA A CIKIN DUNIYARKU.*
Ga mai bukatar wannan littafi *Farashin mai sauki ne* naira dari uku (300) kacal ga yan Nigeria, yan Niger kuma dala dari ne (500)π zaka samu wannan littafi mai dubbin darussa a cikinsa.
_Domin tura kudin siyan littafin ga yan Nigeria sai a tura ta wannan account number din *2377403479* Khadija Umar Abubakar. Zenith Bank. Kuma akwai damar tura kati ta wannan lambar *081-686-594-14* IDAN KA YI TRANSFERT SAI KA TURA SHAIDA TA WANNAN NUMBER +227 93 81 16 18._
_'Yan Niger kuma sai ku tura katin MOOV ko Airtel ta dala dari watau 500 francs ta wannan lambar *+277- 94-98-56-52*_
Na yadda daku, na aminta da irin kaunar da kuke mun don hakan ina da yakinin cewa zaku siya don nuna mun kalar soyayya da kaunar da kuke mun da littafainaπ₯°
[7/4, 7:43 PM] +234 803 885 6944: πΎπΎπΎπΎπΎπΎπΎπΎπΎπΎ
*DUK NISAN JIFA*
_(K'asa zai dawo)_
πΎπΎπΎπΎπΎπΎπΎπΎπΎπΎ
_RUBUTAWA_
*SAJIDA*
*SADAUKARWA*
*GA*
*MASOYA NA*
π«β¨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*π
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_π€
β *[ T.M.N.A]* β πποΈ
https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/
_Bismillahir rahamanir rahim_
42
Ba edditing fa
Mama ta raka shi da kallo tana jin gabanta na faduwa da sauri ta dauki wayarta dake ajiye gefe ta shiga latsawa ta danna kan sunnan yaronta wanda ta dora yarona a sama ta shiga kira tana jin hankalinta na neman kara tashi kan na da
Ringin take tana karawa ana kashewa ita kuwa ta ki daina kiran sai cen aka daga muryar cen ciki ya ce" MAMANA "
Gaba daya sai da mama ta ji hankalinta ya idasa tashi, jikinta ya gama mutuwa, a sanyaye ta ce" Kana ina ne? "
Hisham ya dan yi tari kadan ya kara iya yinsa dan fitar da muryarsa ya ce" Mamana lafia? Akoy abinda zan yi ne? "
Wasu zafafan hawaye suka shiga biyowa ta gefe da gefen idannuwan mama a kan yaron, a hankali itama muryarta bata fita da kyau din ta kuma fadin" Nace kana ina ne? "
Hisham ya daga kansa kadan ya ce" Mama na je wajen Aba ne , daga cen na zo office ina kan aiki ne "
Mama ta fashe da kuka ciki ciki ta kashe wayar a bayane ta ce" Makaryaci, wai yana cikin aiki makaryaci! Wayo Allahna ka dafa min Allah ka kama min, yarona bashi da lafia kuma? "
Mikewa ta yi hankalinta ba a jikinta ba ta yi dakin Bilkisu
Rana zuwa ta tarar da ita a kan salaya watau ta farka ta yi sallar azahar tana jan carbi kanta a sade
Jin budewar kofar ya sakata dago kanta da sauri
Gannin mama ya sakata jin wani karfi karfi ya shigeta da dan sauri ta kara gyara zamanta a samyaye ta shiga fadin" Mama, ban je ba dan kaina ke min ciwo banza banza ya kama min ciwo, ina ta so na zo na gaishe ki, mamana ina kwana, an tashi lafia? Yaya gajia, mama dan Allah ki yafe min, walahi koma da wa kika nuna min zan je na zauna na yi biyaya, aman na rantse maki da Allah na hakura da maganat Hamana, daga yau ba ni ba maganar hamana na ajiye shi bana sonsa ko tak a raina, bana sonsa mamana ko kadan na daina kar ki yi fushi da ni, son nasa bai isa ya sakani saka uwata zubar da hawaye ba, mama na san meye hukuncin wanda ya yi sanadiyar bacin ran iyayensa a kan abinda ba wani ba, na hakura har a gaban Allah"
Mama ta lumshe idannuwanta zuciyarta tai mata nauyi, ta kasa furta komai ta juya da sauri ta fita a dakin ta rasa ina zata nufa ga hijab a jikinta ta fara jiyo salama
Muryar da ta ringa jiyowa ta sakata jin kamar ta samu salama, da wani irin saurin da ita kanta bata san cewar a shekarunta zata iya hakan ba ta juya ta fita a dakin
Hannunsa ta damka wanda hakan sai da ya saka gabansa faduwa ta yi baya da shi bata ce da shi komai ba ta nuna masa wajen zama
Aba ya bi hannun nasa da kallo a zuciyarsa ya ce 'To fah' a bayane kuwa sai ya ringa binta da kallo bai ce komai ba har sai da ta kara nuna masa wajen zaman sannan ya ce" ASMA'U hannun mijin mutane kika kama haka kawai? Ko dai soyayar ta motsa ne kin yarda a maida auren yanzu na je na samu man liman a taru a daura mana? "
Mama dake tsaye tana kallonsa kanta na mata ciwo sai kawai ta sada kanta ta fashe da kuka
Shiru Aba ya yi gaba daya yannayin da ya zo mata da shi na su yita ta kare ya ji ya nema ya rasa, du wani tashin hankali da ya shigo mata da shi kwata kwata ya nema ya rasa, a yanzun a tsayen da yake idan bata yi da wasa ba zata saka tsohon gashinsa ya jika shi da kasa, da ta san yanda zaman mutunci da mutuntawa ya saka shi kasa mantawa da ita da irin yadda koda yanzu aka ce su koma zai iya maida igiyar aurensa da ita ta bine shi ko ya bineta cikin daraja da amincewar ubangiji
A hankali ya zauna a wajen da ta nuna masan domin da farko kin zaman ya yi ya so ya sauke mata vishiyar dake tsakiyar kanta wace ta zuba mata aljannun yi masa fitsara
Yana zama jikinsa a sanyaye yana kallonta ya ce" Asma'u zauna mana ki bar kukan nan haka ya isa "
Mama ta saka hijabinta tana ta goge hawayenta da hannunta mai dauke da zobunnan azurfar da Hisham ya yi mata masu kyau ta zauna a kasa maimakun ta hau dayar kujerar muryarta na rawa ta ce" Ka min fada, dan Allah ka min fada, na shiga uku, na rikice na rasa ina zan kama, yaron nan ashe bashi da lafia nake faman na rike shi na ganar da mamansa cewa abinda ta yi bai bashi da kyau itama ta ji idan da dadi? Ka ga sai ya min biyaya, gana ganni yarona bai taba bijirewa umarnina ba, sai ya min biyaya ya tafiarsa koda kuwa hakan zai cutar da shi, itama kanta mai gadon a wannan abin da na san muna iya fito na fito da ita idan na yi wasa ya saka ni yi mata magana da tsaurin da ya sakata yi min biyaya harma ta shiga tsorona? Ka ga zan kashe y'ayana da kaina wa'inda basu taba guje min ba du kangin talauci da rashin lafia da bacin rai, kaga gannin kamar wace na haukace na hada kan yaren na zauna abina ina kallonsu, na cika son zuciya ko? Na cika son zuciya jauro? "
Aba ya sauke ajiyar zuciya a sanyaye ya ce" Menene ya samu zumuncin naku da har haka take faruwa a tsakaninku baku yi gagawar zama kun fuskanci junna ba bayan kun san kun haihu y'ayan da koda babu maganar soyaya ya dace su rayu tsintsiya madaurinki daya ko so kuke su dawo kowa na jin haushin kowa sanadiyar haushin abinda ke tsakanin iyayensu? "
Mama ta ringa dan girgiza kanta , kanta a kasa tana kara