Showing 150001 words to 153000 words out of 180809 words
aman so din nan tsaf zai goge, shin baki san kyautatawa na janyo soyaya ba? Ko baki san munanawa na kore soyaya ba?, oya kafin na irga Uku Nana Bilkisu Jauro ki kamo hanya ki fitar a gidan nan da suke wani kama maki dan sunna gannin ke auta ko me? Figigiyar kawai!"
Da gudu Bilkisu ta ratsa su ta yi waje tana mai sakin kuka a bayane
Daga Aban har Hisham din sai aka rasa waye zai fara riketa, da sauri Hisham ya rintse idonsa yana gannin yadda mama ta fito da kokara a hannunta ta ja ta tsaya ta nuno su ta ce" Daga kai din, har zainab din, har du wani wanda yake gannin ya tsufa a wajen nan ya ce zai kamawa yar nan rashin kunya da tabara sai na san yada na yi da mutun!, ke wuce ki bi shi ko na babala ki"
Da namaki Aba yake kallon Mama tati ta turo bakinta tana kallon mama ta ce" Kuma aunty uwa wata yar tsana inace mun yi da ke zan yi gaya a rakata dakinta ko? "
Mama ta ce" Ai na zata ita din yar kirki ce, aman tunda haka ne ta bi shi ba an gama gyara mata gidan ba? Ta tafi Allah kiyaye hanya!"
Aba ya ce" Ke asma, ina tunanin mantawa kike yarnan ba ta ke kadai bace, yaya zaki dakar min ita bayan rarashinta nake bata da lafia fa aman dan rashin tausayi kokaran nan kika kofa mata ko me? "
Da sauri tati ta ce" Ai marinta ta yi "
Daga Aba har Hisham basu ji dadin wannan magana ba, Hisham yanzun ya kasa daina kallonta, wani irin kallo mai dauke da so da tausayi da tsoron lamarinta
Aba ya girgiza kansa ya kalli Hisham a nutse ya ce" ina son zama da iyayenka, ka dauki matarka ku tafi, nan da sati daya ku dawo ina son ganninku, abinda nake so da kai ahine ka kasance mai adalci a dukan lamuranka Hisham, ka zama uba, yaya, miji, abokin wasa a gareta, Allah ya baka ikon riketa da amana,"
Ya juya dubansa wajen Bilkisu da har yanzun shashekar kuka take ya ce" A yanzu ban san me zan ce da ke ba auta, abinda na sani na kuma maki wani auren a karo na biyu, sannan ban san takamaiman abinda ya saka ki kuka ba, aman ina rokon ki da ki yi hakuri kin ji? Ki je ki yiwa mijinki biyaya ki yiwa yar uwarki adalci ku zauna lafia, duda sun jajirce min kan ba gida daya zaku zauna ba kan nasu dalilin mai karfin da ya saka na gamsu aman ina so ko nan gaba ku hade kanku a muhali daya ko dan idan kuna da rabon zuri'a su tashi tsintsiya guda, Auta am, ki yi biyaya kin ji? Ki yi hakuri"
Yana gama fada ya juya wajen su mama fuskarsa daure ya ce" Asma'u sai ki yarda kokaran mu je ciki!"
Mama ta juya kanta sade tana kokarin mayar da hawayen dake son konce mata cike da damuwar rabuwa irin haka da cilon yarta, sai dai ta yi haka ne dan so da kauna, ta tsawatar ne tun kafin abin ya fi karfinsu baki daya, ta fi so Bilkisu ta zamo wace zata tsaya a yi sama a yi kasa da ita aman a dakinta ba wai wani abin ya firgitata tun yanzu ba!"
Tati kanta ta sha jinnin jikinta haka tana ji tana ganu suka shige ciki Bilkisu kam tana kuka ta je ta bude motarsa ta shiga
Gaba daya wani irin haushinsa dama tsanarsa take ji a zuciyarta! Lale Hisham ya rainata ya raina darajarta, ba zata ce komai da Aisha ba aman shi ya gama wulakantata
A hankali ya tada motar ya dauki hanyar Jeune kadre, gidan Bilkisun wanda akai mata jere a ciki
A lokacin da ya zo kofa masu gadin suka bude masa ya shiga
A hankali ya tsaya yana kallonta muryarsa sanyaye ya ce" Me ya sa kika fita a irin lokacin da na hanna kika hau acaba Billy? "
Bilkisu ta dago da idannuwanta da sukai mata jja tana kallonsa ido cikin ido, a kausashe ta ce" Dan bana ra'ayin shakar numfashin da kake shaka Hama HISHAM!, DAN bana son ka kuma fitowa da irin yannayin da ka fito a ranar da ta cencenci ka fito a hakan da kuma rana irin ta yau wace ba haka ya dace ni na ganka ba Hamma am......" Ta karashe muryarta na matukar rawa cike da rauni sannan wasu zafafan hawaye suka kuma silalo mata ta gurbin idannuwanta
Gaba daya wata irin kunya ce take neman lulube shi, a hankali ya mika hannunsa zai dora saman hannunta wace ta gane hakan da yake shirin yi dan haka a hankali ta......
π kai, wannan comment ai dolema na karo pages na kara harzuka ku π
[7/8, 5:15 PM] +234 816 920 1901: πΎπΎπΎπΎπΎπΎπΎπΎπΎπΎ
*DUK NISAN JIFA*
_(K'asa zai dawo)_
πΎπΎπΎπΎπΎπΎπΎπΎπΎπΎ
_RUBUTAWA_
*SAJIDA*
*SADAUKARWA*
*GA*
*MASOYA NA*
π«β¨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*π
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_π€
β *[ T.M.N.A]* β πποΈ
https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/
_Bismillahir rahamanir rahim_
54
Janye hannunta da take son yi ya yi saurin dora nasa hannun saman nata, muryarsa na rawa sosai ya ce" I can't, i cant Billu i bg u ki sasauta min ba dan ni ba, kin ga ina kike so na saka raina da dukan wani guzurina?, Billy ban san wani yare a duniya ta kadaituwar zuciya da zuciya face naki ba, Billy tun ban gane me ke dorani gadon asibiti ba har na zo na gane cewar idan na yi garaje tsaf zan rasa numfashina a kan kanwata, Billy menene a ciki dan na jewa matar aurena? Shin ban baki tausayi da mamakin irin yadda na iya rike kaina tsayin shekarun nan ba?, Billy mu yi maganar gaskiya da gaskiya tunda har kin gane irin abinda na fito daga shi na tabata kina hira da kawayenki kuma kina gane wani yaren, Billy namiji ne ni mai rai da lafia, tun ban kai girman da ya dace na kai ba nake sin kadaicewa da mace, aman sakamakon irin yadda na tsani zinna, ya sa da na yi irin tunanin nan sai na kadaice kaina na roki Allah kan ya kama mani ya hane ni fadawa halaka, Billy sha nawa nake gudunki, nake tsayar da ke daga iya abinda Allah ya halata min a kanki?, a yanzun dan na jewa matar da aka daura min aure da ita shine zaki fita ki hau mashin din wani kato ya tuka ki fisabililahi? "
Dan murmushin da ita kanta bata san zata iya yi ba ta yi tana kallonsa a hankali ta ce" Ba damuwa bane , sam ban ji haushinka ba kar fa ka yi tunanin haushinka na ji ka ji?, ka bude min na fita na je wajen da akai min umarni na tatali rashin gatana na kowace mace , ka bude min na je na adana kaina ka koma wajen aunty Aisha ina matukar bukatar na huta Hamma !"
Hannun nata ya dago a hankali yana kallon fuskarta ya kai wajen lebensa ya lumshe idannuwansa ya sumbata sannan ya kara rike shi da kyau yana kallonta a sanyaye ya ce" *INA SON KI* "
Abu ne ya zo mata a ba zata, abu ne da bata taba tunanin zai iya buda bakinsa wata rana ya fada ba, irin yadfa yake tafe da ragamar rayuwarsa bata taba tunanin zai iya fada ba, sai dai kash a irin wannan lokacin gaba daya sai wani abu ya shiga fada mata magangannu kamar haka' Shin mema ya ce? Shin shi din nan kansa wanenen shi? Meye a kalamansa gaskiya ko karya? Meye hujarsa mecece soyayarsa?, shin da gaske yana iya so ko me?, a hankali ta dora ayar tambaya a kan kankin kansa, sannu a hankali ta idasa zubar da yardar da ta fara ji a kasan zuciyarta, du irin yadda abin nan ya daketa ya shigeta ya so sakata zunduma ihun murna sai wani duhu ya lulube shi a hankali ta ture, ta ture furucin da ta jima tana dakon son jinsa, furucin da a dalilinsa har kadarar rayuwarsu take afkuwa ta gama afkuwa ta wanzu, a hankali ta kurawa fuskarsa ido da shanyayun idannuwansa suka gama kankancewa suka kara yin ja sannan suka cika da wata kwala aman basu zubo ba
A hankali ta dube shi a sanyaye ta ce" SO? NI? SO NA?, HAMMA AM NI BILKISU? "
Idannuwan da ya kura mata ya sakata kara cijewa tana kallonsa cike da bacin ran da ya bata karfin gwuiwa da yaren filatanci ta ce" (Ashe soyayar ba zata hannaka ka dane yar wani a ranar da take haramun kadaicewa kai da ita ba? Ko ban cika mace ban kai wajen da zan san hakina da ranata ba? Ashe so din ne ya hannaka kasa dubana? Ko ni din ba mutun bace irin kowa? Ashe so din nan bai saka ka dubeni da idon rahama ba ka cencaneni ka hanna a doran wata igiya a kaina ba? Ko dan ni din yar jaririya ce rainona zaka yi? Hamma am na san komai, ka tsayar da tunaninka a kan kar na ji ko na gani na lalace na jima da lalacewa! , walahi sai na kasa yarda da yaren nan , sam na karyata soyayar nan! Ko dan ni bana jin ko digonta taka a zuciyata?)"
Ta fashe da kuka mai tsanani ta dora da fadin " Ni bana son naka!, na tsani jikin nan da ya je ya gogi wata a ranar da ba nata ba! Dan ni *DUSTE CE?* (Sabon labarina), dan ni SHASHASHA ce?......(taken ta cikin), Dan ni makauniya ce? (LABARINA), ko dan yan magana na fadin *DUK NISAN JIFA KASA ZAI DAWO?* Hamma na tare shi jifan, na dakakashi ta inda tsuntsu ya hadiye shi ya ci gaba da tafia!"
Da sauro ya saka hannunsa ya cicibota daga wajen da take zaune saman kujera ya dorata saman cinyarsa ya kara matsa kujerar sosai ya juyowa gaba daya jikinsa na bugawa hakama hannayensa na bari ya nunata da yar yatsa da yaren filatanci ya ce" Ke!, soyayar tawa kike karyatawa?, a yau da na kasa dane harshena har na fada shine kika kalli tsabar idona kika karyata min? Ba zan taba sasauta maki ba, yan mata ba zan taba sasautawa zuciyarki ba! Sai na saka maki bugun zuciya da tunanina, sai na hadasa maki motsi da numfashina a tare da ke, sai na gigita zuciyarki ta haukace a kaunata! Ba kin kaleni kin ce min ke bakya sona ba? Sai bakin nan ya furtan so da kansa, shi yasa nake jinkiri! "
Ya sada kansa da hausa ya dora da fadin" Shi yasa nake ta hakuri har ki girma, dan kawai na kwonta da wata shine na yi sabo? Billy kema na yi mana? Na yi idan zaki huce? Sai na kwana ina yi na wuni ina yi na kuma kwana ina yi in dai zaki sasauta min? Kin ga ki sasauta min haka mana? Haba yar aljana, haba auta, dan Allah kar ki dora da haka, na yi laifi aman ban ziyarceta a lokacin da yake naki ba domin baki hau lokacin tariyarki ba, ke kika kunna ni na sauke a kanta, kuma matata ce ai!, dan Allah ki bari haka ya isa kin ji? " ya karashe yana son rungumeta a jikinsa aman ta kiya a hankali ta ce" Bude min kofa "
Kallonta yake irin yadda ta tsatsare gira sai da ya sauke ajiyar zuciya, a hankali ya mika hannunsa ya bude mata yana kallonta ta zira kafarta ta sauke ta kama kujerar ta sauka da kyau ta juyo tana kallonsa ta ce" Ni tantamama nake idan ba wani abin kake so na jikina ba!, kuma idan ka mata ciki ka je ka tambaya shine shege idanma ka ki yarda da sannin da ka yi"
Yana kallonta har ta nufi katon wajen da sai an ratsa shukoki kafin a shige wajenta ya cira kai yana shafa gaban goshinsa da daidai kahon zuciyarsa
'ASHE haka take?, meye a ciki dan ya kwonta da matarsa?, Ashe zata iya tsayawa ta yi masa haka dan kawai ya ziyarci Aisha?, ashe zai ga ranar da zai furta mata kalmar nan aman ta kasa yarda? Ashe zata yi tunanin har ta tara abinda zai sota dan shi?' Hakan shine yake ta yawo tsakanin kwakwaluwarsa da zuciyarsa
A hankali ya iya lalubo wayarsa ya dannawa Kader kira
Ko ringin biyu bata yi ba ya daga ya antayo doguwar salama a nutse
Hisham ya ce" Wai cewa ta yi wai bata sona "
Kader ya gyara tsayuwarsa a ransa yana girmama so, lalle so mugu ne, so bashi da tausayi, a hankali shima ya ce" To kai ka ce mata kana sonta mana"
A hankali ya kuma fadin " Ai fada matan ne na yi sai tace ita bata sona "
Kader ya zarro ido da sauro ya ce" Na fada maka ka bude kanta, ka bude kanta ka kiya ni sai na rantse in ba Bilkisu ta fara shaye shaye ba in zama magi dan biyu naira biyar a kadani a miya a shanye, yanzun kaine ta ce bata so? "
HISHAM ya kara sanyaya muryarsa ya ce" Kader cewa ta yi dan wani abin na jikinta nake sonta "
Kader ya dan rike habarsa ya ce" To ko dai fyade ka mata?, hasbunnalahu wani'imal wakim a dawowarku ka afka mata? Na fada maka a yadda kake girmmaa soyayar yarinyar nan idan ka san zaka yi ka fada min mu zauna na maka nasiha aman kawai dan jaraba sai ka auka mata ka kasheta ko? "
Hisham ya lumshe idannuwansa Kader ya kasa gane abinda yake fada ne ko meye? Me yasa shi kulun cikin wasa yake? A sanyaye ya ce" Kader ban yi nata komai ba, ta fita ta hau mashin dan kawai ta jini da Aisha shine fa ta fafada min magangannun da yanzun ka ga zuciyata sai nauyi take kara yi na sanma mutuwa zan yi"
Kader ya dan zarro ido ya ce" Kai ina ba yauba ai nake cewa ka mutu mana na haye motar nan ka kiya sai yanzu dan bakin ciki? Ka ga kana ina? Walahi Hishamu ka saurareni kar ka bari mata su saka maka hawan jini ka zo a kwonce baki ya jirge barin jiki ya shanye magana bata fita da kyau kana kwonce da kyar ka iya kama sunnana ka ce *ADIYI UMA* (KADIRI RUWA) na rana yaya zan yi da kai su kuwa su fara takaba tun kafin ka mace su fara murza motocin nan dan tsaf zata yi bazawaro ya kwasheta da kudinta su kaura dubai, walahi ka mike ka tarda ita ka zare mata ido in da halima ka tsayar da ita ka fala mata mari na wahalar da zuciyarka da take, haka kawai ko na zo na maka ne? Kuma walahi ka ga ka ringa jin tsoron Allah da ta jikunma kuna me? "
HISHAM ya cije lebensa a hankali ya ce" Dan Allah ka zo jeune kadre ka ji Kader? "
Kader ya kara yin jim sai kuma ya kalli wayar jin tana tutututu ya kai dubansa wajen Fareeda dake tsaye kusa da motar tana kallonsa ya dan matse fuska ya ce" Ke bari ki ji faris Allah in wancen kawar taki ta kashe min abokina nima sai na kashe mata kawarta danma ki ji da kyau! Kai ina dalili mata baku da tausayi ne? Tun bata saka hoda yake kwonci a asibiti idan suka yi fada, yanzunma tana karkashinsa sai na je na kara masa ruwan? To wai sai ta kashe shi?"
Farida ta tabe bakinta ta ce" Kadiri to a kawayen wace zaka kashen? Shi da yake sakata kuka kamar zautaciya ta ce tana sonsa ta dawo ta ce bata sonsa shi baku ga laifinsa ba? Ya wani tatare ya ba samari ba komai sai shi shi kuwa ya kasa yi mata kalaman soyayar? Ai wollah akoy cutarwa kuma da kace zaka je ka saka masa ruwa yaushe ka fara saka masa ban sani ba? "
Kader ya rike tsatso ya ce" wai mijin da zaka aura kake son cewa ya yi karya, to in ban iya saka ruwan ba ni makaryaci ne ko me? Ke matsa min a jikin motar ogana na tafiata malama kar kuma ki saki ki kirayeni dan ni ya zun tsoron kawayen Bilkisu nake kar ku kashemu a banza!"
Sake da baki tana kallonsa ya shige motarsa ya yi gaba, kanta ta girgiza tana tabe baki a fili ta ce" zaka dawo ne Kader in na kulaka ni ba Farida bace! Malan kamar wani mai almutsutsai a kai dan wulakanci!"
Kader na zuwa gidan ya sauka a motarsa kasancewar fitilu fu a kunne suke ya sa ya iya gannin Hisham zaune saman kujera yana dafe da kansa
Sauka ya yi a motar ya nufe shi gadan gadan ya zauna a gefe ya ce" Fada min yaya aka yi dala dala"
Hisham ya dago yana kallonsa, to mema zai ce masa? Ya kwonta da Aisha a kunnenta a kuma ranar daurin aurenta? Aa ba zai iya bada wannan detail din ba
Kader ya wani kauda kai ransa a bacen nan ya ce" ka ga yanzu kuka fara, idan baka zame masu kura , ka zame masu zaki ba walahi sa sakaka kana tafe kana magana kai daya, ita kuwa wancen ta dakin idan ka tashi ka shiga yanzun ka kirta mata rashin mutunci ka nuna mata ka fa iya idan ba haka ba walahi sai ta jaka a