Showing 57001 words to 60000 words out of 180809 words
ciro ambulope din da ya shigo da ita ya mika masa yana kara tsatsare shi da ido, watau du abinda ya san baya so ne yake yi masa dan kawai su raba hali
Bai bude ba sai cewa ya yi" Menene a ciki Kader? "
Kader ya kara kallonsa da dan mamakinsa, sai kuma ya dan tabe bakinsa ya buda ya ciro katin gayatar da ya je aka buga, bugawa irin ta kwaliya mai shegen kyau ya miko masa ya gyara zama ya ce"
[7/24, 10:19 AM] BAK'A CE: πΎπΎπΎπΎπΎπΎπΎπΎπΎπΎ
*DUK NISAN JIFA*
_(K'asa zai dawo)_
πΎπΎπΎπΎπΎπΎπΎπΎπΎπΎ
_RUBUTAWA_
*SAJIDA*
*SADAUKARWA*
*GA*
*MASOYA NA*
π«β¨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*π
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_π€
β *[ T.M.N.A]* β πποΈ
https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/
_Bismillahir rahamanir rahim_
21
Ya ce" Yanzu na bugota, ka san kuwa du irin kudin da du daya ta kama min? Sannan na yi postern news din cewa ga ranar daurin aurenka a dukan grups na manyanmu, haka kuma na turawa abokananka da kuka yi karatu tare suma sun ce sunna ta neman layinka wai ko baya shiga ko me, harma da wanda ya ce ko amarya ta rike wayar " ya karashe yana yar dariar shakiyanci du burinsa ya kular da shi
Sai dai abin mamaki sai ya ga Ya yi masa dan murmushi yana ajiye ambulope din ya ce" Ka yi kokari sannu "
Kader ya yi sakayau da baki yana kallonsa, da sauri ya ce" ka kuwa ji me na ce? Takardun gayatar aurenka na bugo fa? "
A hankali Hisham ya dafe gaban goshinsa , muryarsa a sanyaye ya ce" Eh na gane Kader, bana son hayaniya ne ya sa ban karanta ba aman na san ai zaka rubuta komai yanda ya dace "
Kader ya ringa kallonsa, cen ya ce" Hala wani abu kake shirya yi mana ranar auren da zaka saka mu sakankancewa kan ka yarda da auren dolen? "
Shi har ga Allah sai abin na Kader ya fara bashi daria, sarai ya san so yake ya kula shi su yi ta zuba hauka bayan shi a yanzun karfinsa ya kare a tunane tunanen da ya aurawa kansa, yau kwana uku kennan ruwa a jalo nemansa ake a asibiti aman ya yiwa sakatariarsa kwakwaran kashedin cewa baya nan, kar ta yarda ya ga wani ya zo gidansu nemansa, hakan ya sa takr cikin tsaka mai wuya domin ita ke tatare masu neman nasa
Komawa ya yi zai kwonta hakan ya sa jikin Kader ya mugun mutuwa, dama karfin hali ne yake so yake ya saka shi sakin jikinsa ta wannan hanyar, sai gashi ya ki yarda ya bashi damar da yake so
A sanyaye ya sauka kasa ya zauna yana kallonsa, muryarsa sanyaye ya ce" Ka ce ka hakura, ka ce ka barawa Allah komai , kuma sai kake wannan yannayin da bana so? Dan Allah ka mike , Hisham bayan Aisha fa kana iya kara mace uku domin hudu aka halasta maka, a kan me zaka ringa haka a gabana a gabansu ka ringa shuka masu iya shege? Yanzu dai a gidan nan ba wanda baya tsoron ta hado ku dan ka zama fitsararen karfi da yaji, sakin magana kawai kake son ranka, haba Hisham Bilkisu idan rabonka ce ko bayan Aisha bayan wasu matan zaka malaketa, kar ka shiga hakkin Aishar nan dan na kula tana da sanyin hali, kai maimakun ka ringa murna zaka rabu da kayar kwana rabin ido a bude rabi a rufe da nauyin mara, zaka samu falalar ladan mai aure, kuma shine kake irin haka? "
Hisham ya bade fuskarsa ya juya bayansa da hoton nan a hannunsa ya ki bashi amsa
Tun Kader na sa tan zai waiwayo shi har ya mike ya juya ya fice a dakin jikinsa a mace
Direct baban falo ya shiga, ya gaishe da mai aikin dake goge goge sannan ya nemi da ta masa magana da Mama
Mama cikin hijab dinta har kasa ta fito ta karaso wajensa da kulawa take amsa gaisuwarsa
Sannin cewa Tati da sabuwar kawarta kuma sarakuwarta sun tafi kasuwa ya saka shi zama a kasa ya sada kansa
Muryarsa a sanyaye ya ce" Walahi du yanda na so ya kula ni mu yi rigima ta gagara, Mama kina kallo za'a ilata maki yaro dan kawaici? "
Da mamaki Mama ke kallonsa, a sanyaye ta ce" sai nake gannin kalamanka basu dace da wanda kake yiwa furucin ba, dan zai yi aure shine ila a tare da shi ko dan zai yiwa mahaifiyarsa biyaya? Shin Aishar dauke take da wata cuta ko wata nakasu a tare da ita da zai saka ya ringa haka? Idan baya so ya gudu mana irin yanda yan mata ke yi idan za'ai masu auren dole sai na ga karshen rashin kunya, Haba Kader, yaya kuke so na yi ne? Rashin fara'arsa sarai ya san tana ilata ni, aman sai ya ringa wani shasha min kanshi? Wai idan ina da ikon hanna abin nan da ba tuni na hanna ba? Yaya kuke tunanin ina iya yin kokowa da abinda ya fi karfina? "
Zata ci gaba da magana wayarta ta dauki kuka
Tana dubawa ta ga sunnan mahaifin Bilkisu
Dagawa ta yi ta yi salama sannan ta dan saurara tana sauraron sa
A sanyaye ta ce" Ita Bilkisun ce ta ce zata zauna har a kusa auren yayanta? Auren fa sauran sati biyu fa , makarantarta fa? Yayan nata zai yarda ne? "
Dukan tambayoyin nan da ta yi na nuni da hankalinra ba a kwonce yake ba, hakan ya saka Mahaifin na Bilkisu kallonta a hankali ya ce" Asma'u ko da wata matsala dake faruwa da Balkina ne? "
Da sauri Bilkisu ta kalli mahaifinta, hakama Mama da dan sauri ta ce" Aa, aa fa ba komai ba abinda yake faruwa "
Aban su Bilkisu ya ce" To gani na yi kamar kin manta inda ta zo ne Asma'u "
Mama ta sauke ajiyar zuciya ta ringa motsa bakinta tana son cewa ya bata Bilkisun aman ta gaza
Bilkisu ce ta ce" Abana bani maman "
Abanta ya bata wayar yana kallonta
Mikewa ta yi ta matsa gefe ta zauna ta sanyayar da muryarta ta ce" Mama "
Mamanta ta ce" Ya maki kyau, na ce ya maki kyau, ahine zaki ce wani zaki zauna a cen me yake baki da ya wanda nake baki? Bilkisu am meye hakan? So kike karara a gane dan auren yayanki kika yi gudu daga gidan nan ko me? Shine zaki ringa hadani da wancen yana wani yi min dogon bayani kou? To ba ruwana zan fadawa yayanki idan ya zo ya taho da ke ai shikenan!"
Bilkisu ta sanyaya muryarta sosai ta ce" Mamana, ba haka bane, mama walahi ina samun nutsuwar zuciyata sosai tare da Mami da Abana da Hamana na nan gidan, mama kin ga mu yi karatun sade mu yi da yama, mu zauna mu yi hira da Abanmu, mama zan dawo aman so nake sai auren ya kusa sai mu zo da Mamina a yi bikin da ita, ta ce zata zo ta kwana har mu yi shagalin bikin, Mama itama aurenta saura sati uku yanzun aman haka ta ce zata biyo ni, dan Allah mamana kar ki ce aa "
Mama ta sada kanta a hankali ta ce" To karatunki fa? "
Bilkisu zata yi magana mahaifinta ya janye wayar domin dama biyota ya yi ya kara a kunnansa ya ce" Kin ji kunya, haihuwarki ta farki kina irin haka da yarki ta farko Asma'u, to karki manta nine ubanta kuma karatun nima na yi, abin alfaharina ne ta zama likitan nan domin tun yanzu da ina ciwon kai ita ta rubuta magani aka siyo kuma na warke, ki fita a harkar y'ata da ni ko na amshe abata ai kin san na maki kara, kuma dama dama ni ba marar kunya bane "
Mama ta yiwa wayar kit tana zaro ido,
Ido hudu suka yi da Kader da komai a kan kunnayensa ya wani yi mata kuri
Fuska ta kara hadewa tana cije lebenta ta ce" Tashi ka tafi ka ji? Allah ua maku albarka baki daya "
Kader ya sada kai yana murmushin mama ya mike ya fita
Yana fita Aisha dake jiran ya tafi ta fito ta tsuguna gaban mama kanta sade ta ce" Dan Allah mama ki yafe min, walahi ni dai ba ruwana a cikin maganar auren nan, mama dan Allah ki yafe min ki hanna auren nan, walahi kina iya hannawa domin idan kika ce kar ya yarda ba zai yarda da maganar auren ba, du da kika ga ana wani ja'in ja dan kin hana shi bijirewa ne "
Mama ta kara dafe kanta tana kallon Aisha ta ce" Aisha bakya son yarona ne? "
Aisha ta dago ta kalli mama, da sauri ta sada kanta, dan Allah yana ganni idan kunya ce ta sarakunta ita ta mama take ji, hakan ya saka bata iya sakewa da ita
Mama ta yi murmushi ta ce" Tashi ki je ki sha maganin zahin da na dafa maki kin ji? ki yi ta adu'a domin wani baya auren matar wani"
Aisha ta gyada kanta itama jiki a sanyaye ta koma dakinta
Kwonci tashi kwana nesa
Wasa wasa auren Hisham har ya rage saura kwana biyu kawai
Yau tun da safe su Bilkisu suka zo ita da yar uwarta, tun da suka zo kuwa ta aniya lalaba mama har sai da ta bata ky din motarta nan ta dauki Mami da Atm cart dinta suka fita
Basu zame ko'ina ba sai shagon Elhaji Ayuba lhabille,
Zama suka yi Bilkisu ta ringa daukan masu rantsatsun lesuka da shadoji da mayafai yan madaidaita da takalma da jaka,
Aun cashi kudi a shagon nan wanda sai da Mami ta ringa rafka tagumi tana kallonta domin sai da ta hanna aman ta kiya
Daga nan suka mikawa tela Abdu da yake tsalake, ya kuwa zuga masu kudi aman ta tabata zai gama a kan lokaci sannan dinkin Abdu ba na yarwa
Daga nan gidan su laila suka wuce direct, wajen kwanar rahama
Laila ta girgiza jin jibi jibi Hisham ke daura aure, harda hawayenta, sai dai abin mamaki Bilkisu murmushi kawai ta yi ta ce" Haka Allah ya so Laila, ki daina damun kanki na barwa Allah komai"
Mami ta ringa murmushi tana jin kaunar yar uwarta har cikin ranta
A hanyarsu ta komawa gida ne Mami ta ringa jajen jikinta du ciwo yake sosai, hakan ya sa Bilkisu zuwa asibiti da ita duda ta nuna aa kar su je zai wuce aman Bilkisu ta kiya ta karkata ta kaita
An bata magani irin nasu sannan suka wuce gida
Duda abin ba a shirya masa ba, ba'a yi wani lamari na bidi'a ba kasancewar kakan amaryar na kwonce asibiti angon kuwa ba wanda ya san inda yake, aman gidan ya cika da manyan bakin da suka yi tataki tun daga garin Niamey dan halartar taron daurin auren
Ana gobe daurin auren gidan ya cika kowa da gayarsa ana ta shagulgula ciki kuwa harda Su bilkisu da kawayenta sun dinke a dakin tsakar gida sunna ta kunshi da kitso abinsu sunna shan daria domin akoy wace ta saka ado gwonja masu zaburi taka sai juyi suke abinsu
Sai kusan magariba kawayenta suka watse ya rage sai su biyu, an masu kunshi ya yi kyau sosai duda Bilkisu sai da ta hanna a yiwa Mami ta ce ita da aurenta saura sati daya tak ta bari a gwongwaje mata na aure aman fir ta kiya itama sai da akai mata harda kitso masu kyau
Sunna yar hira a gajiye bayan sun gama cin abinci Aisha ta shigo
Jikinta a mace ta samu waje ta zauna ta rakube jikin kujera
Bilkisu dake kallonta ta lumshe idannuwanta tana jin Mami na fadin" Aa, har an gama shafa lalen amarsunmu? Wai ina hamman yake? "
Aisha ta kaleta sai kuma ta dan saki murmushi bata bata amsa ba
Bilkisu ta sauko ta zauna a saman cafet din itama ta turo mata abinci a sanyayye ta ce" Aisha ci abinci mana? "
Aisha ta dago ta tsatsare Bilkisu da kallo, kawai sai ji suka yi ta fashe da kuka mai cin rai
Bilkisu ta rintse idannuwanta lokaci daya ta mike ta yi waje da sauri har tana hada hanya
Karron da suka ci da mutun ne ya sakata yin baya zata fadi, aman bata kai ga faduwar ba ta ji an wani irrin rikota, riko irin na zafi zafin naman nan
Baki daya ta rintse idannuwanta a lokacin da suka yi ido hudu sakamakon fadiwar da gabanta ya yi
Kallonta yake, jelar kitson da akai mata duda manya ne a bayane sai kunshin da ta sha ja wanda ya fitar da ainahin kyanta
A hankali ya ce" Kwaliya kike a aurena? "
Bilkisu ta tsurawa fuskarsa ido, hawayen da take na kara bin kumatunta
Wani irin haushinsa take ji na haka kawai, hakan ya sa ta tsatsare shi da idannuwanta tanai masa kallon eh din yi abinda zaka yi!
A hankali ya saketa ya raba gefenta ya wuce ciki hakan ya sakata nufar wani daki ta bude ta shige ta kwonta
Yanda ta ga rana haka ta ga dare, har kusan karfe taran dare idannuwanta bude suke a saman abin sallah tana kallon gabas
Shelar sunnan burinta hade da na watanta ana maimaita daurin aurensu ya sakata kwontawa a hankali tana sauke ajiyar zuciya
Wani murmushi mai ciwo ne ya kwace mata, a hankali ta kara gyara kwonciyarta kanta na sarawa tana jan carbi har baci mai nauyi ya kwasheta
Mami kawai ke kai kawo a dakin da take kwonce bayan ta samota da kyar, har sai da ta kusan wuni tana bacin nan kafin ta farka
Mami ta tsatsareta ta yi wanka ta saka shadar da suka yi iri daya
Mami ta sakata kimtsa fuskarta sannan ta kamata ta mike tsaye tana kallonta ta ce" Bamu yi haka da ke ba Balkisa"
Bilkisu ta yi murmushi ta ce" Nima ban yi haka da zuciyata ba, aman yanzun da na yi bacin nan komqi ya warware, na ji sauki sosai a zuciyata"
Mami ta yi murmushi ta ce" Kin ga cenjin da muka yi na kyautar da zaki ba amarya, kina tunanin zaki iya wannan jarumtar kuwa? "
Bilkisu ta ce" Idan kina gefena, ina mai tabatar maki har rawa sai na taka dan kuwa ina ji ana kidan larabawa kin san na iya kada kugu kuwa? "
Daria Mami ta yi ta ce" ba ruwana rasa kunya kawai "
Haka suka fito yan matan biyu, duda Mami bata da jiki sosai rashin lafiarta baya taba barinta yin gwabi haka ta yi kyau cikin dinkinta domin sai da ya auna su ya masu rantsatsun dinkunnan su
Bilkisu kam abin ba'a cewa komai, du irin yanda gurbin idannuwanta suka kunkumbura bai hanna mata zama wata tauraruwa ba
Walwal take walwali , haskenta yana cika ido
Maroka na ganninka suka shiga yi mata kirari, makadan da suka zo dan shafa lalen angon da har yanzu ba'a shafa ba domin wai yana asibiti tiyata yake da har uku suma suka shiga tarbota da kida da busa irin na barebari kasancewar damagaram gari ne na yawancin barebari
Murmushi ta yi ta karasa wajen Tati dake tsaye tana ta yi mata dariar oyoyo babyna ta ce" Tati bani mayafin naki na gani? "
Tati ta kuwa bata dan tana son gannin abinda zata yi sai kirarin ga kanwar docter, ga kanwar likita, ga yar shalele ake mata
Ai kau kamar da almara Bilkisu ta shiga taka rawar barebari wace suke yi da mayafin nan cikin kwarewa da juyi a hankali
Mama ta zarro ido da sauri ta labe cikin mutane tsabar kunya
Tati kam me zata yi banda daria da murna, ba shiri wajen ya kaure da karri domin kawayen maman Aisha da maman aisha da tati gaba daya suka shiga suka rufeta da karin mikakun manyan yayan banki masu maiko
Sai da Mami ta gaji da daria tana girgiza kai ta shiga ta fitar da kanwarta tana dungure mata kai ta ce" bakya jin magana auta, rawa ko? "
Bilkisu na daria ta ce" kema sai kin taka, wai ina uwar ango take bata taka ba "
Mama na ganninta ta kara guduwa ciki, dan ita kam yanzun daga Hisham har Bilkisu ta kula sun karro wulakanci bata cikin abin kunya ba da ita ba!
Haka aka gama tarron biki aka watse, ango tun wajen daurin aure ya fece wai yana da aiki daga nan ba wanda ya kuma ganninsa domin baya asibitin kuma baya gidan da akaiwa Aisha jere
...................
..
Auren Mami
[7/24, 10:18 AM] BAK'A CE: πΎπΎπΎπΎπΎπΎπΎπΎπΎπΎ
*DUK NISAN JIFA*
_(K'asa zai dawo)_
πΎπΎπΎπΎπΎπΎπΎπΎπΎπΎ
_RUBUTAWA_
*SAJIDA*
*SADAUKARWA*
*GA*
*MASOYA NA*
π«β¨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*π
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_π€
β *[ T.M.N.A]* β πποΈ
https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/
_Bismillahir rahamanir rahim_
22
A yanzu abinda take ta shige da fice shirye shiryen auren yar uwarta daya cilo mace
Domin kuwa a yanzun auren Mami bai fi kwana biyu ya rage ba
An bata wayarta, gidansu sawu ya dauke sai su tati kawai hakan ya sa take sha'aninta
Kasancewar komai a kure yake zuwa sai kawai saki kadai zasu yi ita da kawayenta watau kayan filani
Sosai take