Showing 84001 words to 87000 words out of 180809 words
sama kadan ya shiga kunce belt dinsa daga zaunen dan ya daidaita jikinsa kafin ya fita
Bai ankara ba ya ji an bude an shigo an rufe sannan kyan ya sauke dubansa a hannunsa dake cikin wandonsa ya sasabta belt dinsa
Dagowa ya yi da sauri suka yi ido hudu, sai kuma Kader ya cire dubansa ya maida gefe yana fatan Allah ya rabasu lafia
HISHAM ya kuma daure fuska ya saka hannunsa da kyau ya gyara jikinsa sannan ya ciro ya maida belt dinsa da kyau ya ja rigarsa
Sai da ya gama cikin nutsuwa sannan ya gyara zamansa ya kunna fitila ta yada zasu kalli junna da kyau ya juyo da Kader ya shaki wuyansa ya dan dago da shi daga zaunen da yake cimak
Kader da sauri ya ce" Dan Allah ka yi hakuri walahi ban san ta tabaka ba da ba zan shigo ba sai ka daidaita kanka, kuma tsakani da Allah Hisham baka wanke hannunka ba zaka taban rigata da nake sallah da ita? Kuma ka tsaya na maka bayani dala dala a kan Gimbiya Najeeba"
HISHAM cikin dakakiyar murya ya ce" Sex na yi da zan kwashi najasa Kader? Ka ga ka tako min falo da takalmi, ka zo office dina ka zauna min ka dora min kafa daya kan daya, uwa uba ka ce kwaliyarta ta yi kyau me ya kai idannuwanka cen? kana min shiga hanci da dukunkunne dan ka ga bana son damuwa ko? Ka fada min wacece matar nan? Mijinta ya ce kadan daga cikin abinda na siyarwa kaina ga Billy tana kuka dan zan hanna zuwa koyan aikin ka fada min tun wuri in na ga bai min ba na katse tun kafin ta jaza min fitinar da zan kasa tarewa! "
Kader gyada kansa yake tamkar kadangare har sai da ya cika shi da dan karfi hakan ya saka shi komawa dabar ya zauna yana sauke ajiyar zuciya ya ce" Ita din nan da ka gani itace ta yi wani irin yanmatanci a garin damagaram da ya gwara kawunnan samari, datijawa da yan yara dare daya aka ji daurin aurenta a ranar maza sun ringa sakin zance domin du sun ringa tona kansu ta hanyar bacin ran dake damunsu sai kawai su saki zancen hankali tashe, ba dai ka san oga malaika namu na gidan maza ba? Ai kuka wiwi ya yi da idannuwansa ya ringa masifar manyan kasar nan na fitowa sunna nuna karfi a kan mata sunna kwacewa!" Ya karashe yana yar daria domin hango lokacin yake a idannuwansa dan sa bacin rai Malaika ya koma masu mugun bacin rai sai kawai aka ji wata irin murya ya shiga dagargaza kuka yana fadin kalaman nan
HISHAM ya kalle shi da kyau ya ce" sai na ga mutun ce kamar kowa, tara samarin bata rike mutuncin kanta bane ko meye? "
Kader ya kara gyara zamansa ya ce" taku ne nawa, taku ne Elhaji, da ka ganta a nan gayu ke shaidar du tsakaninta da kai kar ka nuna mata lalata domin komai na iya lalacewa, oga daba take hadawa a saloon dinta aman ba zaka taba jin an ce yau gata tana kawowa maza yan mata ko ita an kamata da mugun aiki irin na bin maza ko shaye shaye, su dai barsu da fadace fadace da tara samari ita da yan uwanta"
HISHAM ya kara gyara zamansa ya cije lebensa na kasa, Tara samari? Ai damuwar kennan, shin zamanta da wani halayarta take koya masa ko kuwa iya kwaliya zata koya mata ta sako masa abinsa? Idan halayarta take koyawa mutun babar matsalar kennan dan kuwa in ita ta iya takunta ba kowa zai iya takunsa ba, ita din kanta Allah ne ya kubutar da ita dan kuwa mazan yanzu ko yaya ka kai da iya zagayesu in dai ka ce tara su zaka yi barkatai tabas zaka hadu da abinda zai girgiza tunaninka da kai da ahalinka,
Kuma daure fuska ya yi ya juyo gareshi ido cikin ido ya sasauta muryarsa da yannayinsa ya ce" Look Kader, lalata abin nan nata za'a yi, walahi baka ga riginar ba daga cewa ta bani, ni ba zan iya amshewa ba aman kai kana iya buga sauko ka warce jakarta a zauna lafia !"
Kader ya yi shiru yana kallonsa, a kasan zuciyarsa kuwa a kulun mamaki yake irin yanda yake kiyaye bacin ran Bilkisu
Sai da ya gyara zamansa ya ce" SIR, dan kana tsoronta an ce maka ni din bana tsoronta ne? Tsakani da Allah da muka taba yin fada sai da ta kusan sati bata min magana daga ce mata ta daina fada a makaranta fa "
HISHAM ya ce" Ka ji kunya Kader, nine zaka zauna kana yiwa iskanci kennan ita tsorontama kake ko? Ni a gidan wa na taba nuna maka ina tsoronta? Zaka rufe fuskarka da konau ne ta yada zaka warce ka gudu ba tare da ta gane ba"
Ido Kader ya kwalalo ya ce" Na dai sace kake nuni? Ko na mata fashi da makami? HISHAM anya banda horon sojoji da abubuwa da akai maka ba harda na cin zalin ba? Tsakani da Allah Bilkisun taka za'a yiwa fashi da makami? Haba Hisham, haba Hisham idanma koya maka aka yi an kiya maka ne dan ka yi a wajen da za'a yi taimako a manyan kasashe ba ya kare a kaina ba ni bawan Allah "
Wannan karron Hisham rasa me zai ce masa ya yi hakan ya saka shi fita daga motar ya rufo masa ita da karfin gaske ya nufo fallon, kai ina, tara samari? Ba zai yiwu ba walahi! Ba zai taba yiwuwa ba sai dai idan bayan ransa haka kawai!
Yana shigowa ya tarar da su zazaune aman Aisha bata wajen
Direct kusa da Mama ya zauna fuskarsa a hade
Ita kanta tana kallonsa ta ce" Hisham lafia? Ko wani abin ya faru ne? "
Bilkisu ta ciciba da dan sauri dan fecewa domin haka kawai zuciyarta ta shaida mata yayanta bai hakura ba
Idannuwansa ya sauke a kanta ya ce" Ai dole ki tafi, dole ki tafi mana, Mama ba zai yiwu ba matar sultan din nan an ce ta yi zaman tara samari, kin ga daga zuwanmu ta koya mata saka jan baki da wannan daurin na kanta tsakani da Allah a tsaya iya hakama an gode"
Tati ce ta kara juyowa daga dane danen wayarta tana kallon yannayinsa kafin ta sauke saman Bilkisu da ta ja ta tsaya tana kikifta ido gaba daya tsoro ya bayana a tatare da ita
Dan murmushi ta yi ta ce" Menene a ciki Hisham? Gyara ai ba matsala bane, tara samari kuwa ai du budurwa a wannan zamani tana tara yan samarinta sai dai a ringa yi mata nasiha ana saka ido a kanta ana tunatar da ita mutuncinta shine gaba da komai, waima idan bata yi samari ba ta ina kake so ta samu miji ta yi aure ne? Mu dai danginmu ba yawa ne da mu ba bale na ce ka samo mata a cikin dangi, dan Allah ka daina daukan babyna jaririya ta kai wajen da zata iya yin saurayi, ka barta ta yi kwaliya ta isa ta yi zuwa yanzun "
A hankali ya kurawa fuskarta ido, a hankali ya ce" BANI DA RA'AYIN NAN "
TATI ta kura masa idon itama tana gyara zamanta ta ce" Hakan za'a yi, domin ba wani abu tsakaninku bale ka ce GAKA ko ba kai ka shaida min ba soyaya tsakaninku ba? "
Gabansa sai da ya buga, haka na Bilkisu , Mama kam cire kanta ta yi daga kansu su dukansu tana dan karkada kafafuwanta, sarai ta san so take ta kai Hisham ga buda aki ya fadi soyayar Bilkisu a gabanta da bakinsa, domin dukan abubuwan nan da yake fa a zagaye ne sai tafasa zuciyar yarinya da yake a koda yaushe yana kara tsumata da salon da Allah ya bashi yana haukatar da zuciyarta da zazafar soyayarsa, ita kanta tana tsoron a je gabar da Bilkisu zata ce da shi tana sonsa bayan shifa ba furta mata ba ya yi, su dai ya farfada masu aman ita bai taba fada mata ba sai wanda ta ji a bayan labule, boyayoniya da namiji bata da kyau,
Hankalinsa ne ya ji yana tashi daga zaunen da yake a kusa da ita, dubansa ya maida wajen Mama ya ga TV take kallo hakan ya saka shi kuma kalonta yana cije lebensa na kasa cike da bacin rai da takaici
Bilkisu kuwa gannun ba abinda ya ce ya sakata juyawa tamkar kwai ya fashewa kaza a cikin cikinta ta nufi dakinta hankalinta a matukar tashe, bata gane ba, an sakata a duhu, dama haka yace? Haka yace wai?
Sai da ya ga shigewar Bilkisu ya dawo da dubansa kan Tati dake shirye da jin amsarsa ya ce"
Morning alll
[7/24, 10:19 AM] BAK'A CE: 🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾
*DUK NISAN JIFA*
_(K'asa zai dawo)_
🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾
_RUBUTAWA_
*SAJIDA*
*SADAUKARWA*
*GA*
*MASOYA NA*
💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝
☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️
https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/
_Bismillahir rahamanir rahim_
33
Sorry fa ba edditing wollah
Yana kallonta ido cikin ido ya ce" Tati, dama akoy maganar soyaya tsakanin wa'inda suka sha nono daya? Ko wasa kike min da kika ce mun sha nono daya? "
Tsuru suka yi sunna kallon kallo Mama da Tati hakan ya saka shi mikewa tsaye yana kallon agogon dake daure a tsintsiyar hannunsa ya ce" Mamana na ci abinci a waje ina son na yi baci dan haka ba sai an aiko min da abinci ba "
Mama dake kallonsa baki bude ta talabe habarta tsabar mamakin iya shegen yaron nata
Ido hudu suka yi da Maman Aisha, matar da tunda aka tsiro da auren hadin nan tsakaninsa da ita gaisuwar kamar ta yan kwaya, domin yakan ce da ita sannu dai sarakuwata, ko yace da ita ana hutawa ? Ko ya ce yaya dai? Gaisuwarsa kennan da ita, ko yanzun dan murmushi ya sakar mata ya juya ya fice ransa na masa kunna
Ido hudu su Mama suka kuma yi, hakan ya saka mahaifiyar Aisha mikewa tana ce masu bara ta yi kira, dan ta basu waje su tatauna
Tana shiga Tati ta sauko kasa tana talabe kanta ta yi shiru, sai kuma cen ta ce" To ranar nan ai mahaifin Babyna ya so fadin zancen, tunda har ya tirke mu Aisha ta katse mu, walahi ya san gaskiya sone yake ya ringa zilemin ta haka , kin ga ilar karya ko aunty? Yana fadi na yi mukus bayan ni na so tsare shi, yaron nan baya jin magana ko kadan! Kuma walahi ko da me yake takama sai ta je koyon kwaliyarta, sannan maganar ya hannata kwaliyama bata taso ba, haka kuke zaune da shi ba maganar soyaya aman yana mata irin ikon nan? "
Mama ta yi murmushi ta ce" ai ba iko bane sai gaskiya, yar taki cema bata da farin jinni to idan har ka yarda da kanka har sai ka yi kwaliya za'a ce ana sonka? Kai ni wannan lamari nata na rasa kansa"
Tati ta ce" ta yaya kike son ta ba namiji fuska bayan ta san ga dodonta dake gadibra a gida wanda idan ya gani ya isa da ita yana iya daukan matakai a kanta ciki harda kilaceta da hannata zuwa makaranta? Gaskiya ya samu dama mai yawa da yake tunanin yarinyar nan a arha take a tafin hannunsa "
Mama dai sai kakare Hisham take da dukan karfinta, Tati kuwa tana fadin du laifinta ne da ta wani zuba masa ido yake abu uwa uban Bilkisun, duda shi ya raineta ba yana nufin ya haifeta ba duba da abinda yake ji game da ita
Mama ta dan kura mata ido, uhum dama ta san Hisham din na jin wani abu game da Bilkisun aman ta saka masu katangar karfe a tsakaninsu? Koda yake da wahala dama ya kasa fada mata irin yanda ya shigo mata haka
Ajiyar zuciya ta kuma saukewa tana tunani a kasan zuciyarta, ta kasa gane a wani muhali zata ajiye yar uwarta, idan yau ta yi wani abin sai ta ji gaba daya tamkar ba bahaushiya kuma bafilatana ba, idan ta yi wani gobe sai ta ga ta san halaci
A wannan dare Bilkisu sai da ta daura alwallah ra gabatar da salolin nafila sannan ta samu abinda ya tsaye mata a kahon zuci ya saketa duda haka tana kwonci shi ya fado mata a bangon idannuwanta,
Sosai take gannin cewar bata yiwa kanta adalci ba, haka ne fa bai taba duban idannuwanta ya yi mata magana irin ta soyaya ba, tsakaninta da shi sai dai umarni da kalaman da ba zata ajiye su a matsayin ya furta mata kauna ba
Ta yo tir da zuciya, ashe zuciya bata da hankali? Ashe zuciya wawa ce? Idan har dan ya fada a boye ya kasa fada a gaban idannuwanta to tabas soyayar bata kai wajen da zata falasa kanta a lokacin da vai shirya ba!
Lebenta ta dantse na kasa a lokacin da ta ringa tuna kalaman matarsa, irin yanda take nuna ita yake so ba ita ba kar ta bari a yi auren nan, a fili ta furta "WANI SO? MEYE SHI SO DIN? YAYA AKE A GANE IDAN BAKI BAI FURTA BA?"
Da kyar ta iya samun rintsawa hakan ya sa tana yin sallar asuba ta sakawa dakinta ky ta koma bacin danganar da ta sakawa kanta
Saai wajen karfe goma ta jiyo muryar Tati tana kiran sunnanta, aman sai ta yi kussss ta yi tamkar bata nan
A ciki ta yi dukan abinda take yi irin su wanka ta saka dan gaheran wando budade irin na basket din nan da yar rigarta mai siririn hannu sannan ta dauki litatafanta na makarantar da ta kwana biyu ko a leke bata leka ba ta dukuta ta sha karatu mai yawan gaske
Ta zuba madara da corn flaks ta wuni sha da yan chocolate dinta ,
Sai da yama ta dauki sabuwar wayarta ta shiga chating, ba da kowa ba sai da Umar, labari ne kawai suke sunna daria wanda yawanci takan masa tambaya a kan mu'amala da mutane, hakan ya ringa bashi daria yana bata amsa a sake shima da sakewar da ta bashi mamaki har kusan magariba ta tashi ta sake wanke bayinta ta yi wanka ta dauki gawayi na kwali ta kunna turaran wuta dan kadan ta ajiye a bayin tsakar dakin ta fesa airs freshener ta kuma saka wasu gajerun kayan ta haye gaban madubi ta buda kayan mak up dinta
Cikin nutsuwa ta shiga dan zannawa fuskarta abinda ta iya da ya shafi mak up, tun daga girarta dake cike da gashi irin na fulani, da shafa hoda ta ruwa ta dora da ta gari ta saka kwali ta zo ta shafa jan lebe
Gashin kanta ta warware haka kawai ta yi tsai tana binsa da kallo
Cikin nutsuwa ta kara caje shi da kyau sai kawai ta yi sama da shi sosai ta saka yar karamar tsinka ta soke shi
Turare ta kama fesawa fiiiiiiiii a jikinta sai kuma ta yi tsaye gaban madubin
Tudun mamanta ta ringa bi da kallo, wa'inda ko rigar mama bata saka ba tana kara binsu da kallo, basu da girma sosai aman asalin maman fulani su za'a kira da mama domin a cike suke dam uwa uba kawunnansu tamkar wa'inda ake dan mulmula tsinin kadan domin tsinnin baya risinawa yakan kasance a tsole a idon mutun
Tana da dan kashin wuya domin Bilkisu bata da jiki sosai kashin wuyan sai ya kawata halitarta sosai sannan jikinta daga saman bata da kauri mamanta ne kawai suke da cika da tumbatsa dan du cinta a nan da bayanta suke taruwa
Mazaunai ne da ita boyayu, irin mazaunan nan masu cika tam domin tana da mazaunai tana da cinyoyi abinta sai masha Allah, rashin tsayinta sosai ya kara daimakawa mazaunan wajen kara gyara zama a bayanta ya zamana da ta juya da bata juya ba su zasu juya ne sai dai idan bata mike ba, wannan ke saka Hisham yi mata dinki burum burum tamkar wata wace zata je makarantar islamiya kuma ya dora dokar hijab duda takan kauce dokar nan idan ta ga dama
Tana tsaka da kallon kan nata ta ji kwankwara dakinta a karro na uku kennan, ta tabata Mama ta fadawa tati ta kyaleta idan ta yi niya watarana haka take wunninta a dakinta ba mai ganninta domin da abincinta dangin su kifin gwongeani da su kazar gwangwani irin markadadiyar nan da su madara da su abubuwanta dai wa'inda take iya ci ta yi zamanta a daki , aman tati sai da ta dawo ta buga mata abincin rana yanzu kuma an buga duda na yanzun ta so ta cenki ko waye domin yakan buga sau daya ne sai kuma ya saurara
Shirun ta yi itama tana saurare har sai da ya kuma bugawa
Ba tare da tunanin komai ba ta tunkari kofar ta bude da kys din ta janyo sannan ta fito gaba dayanta da wannan gajeran wandon da ya bayanar da cinyarta da rigar nan tata
"Hasbunnalahu wani'imal wakim" Bakinsa ya iya furtawa a lokacin da ya sauke dubansa a kanta gaba dayanta
Gaba daya zuciyarsa ce ta tsinke gabansa ya yanke ya fadi ya ji harta da jikinsa ya dauki rawa
Da sauri ya rintse idannuwansa, ita kanta da gudu ta koma ta rufo kofar gabanta na faduwa ta jinginu da jikin kofar ta silale nan tana hade kanta da gwuiwarta tsabar kunya da tsoro da takaicin kanta na fitowar da ta yi