Showing 6001 words to 9000 words out of 180809 words

Chapter 3 - DUK NISAN JIFA COMPLETE HAUSA NOVEL

sajida   

02 Feb 2025

12948

sak'onsa.

*"MUTUNCINKI shine farin cikina."*

Da wani irin sauri ta d'ago da dubanta, gabanta ya bada wani irin bugawa haka kuma sukai ido hud'u wato idanuwanta cikin nasa, sai dai kash.....bata kai ga idasa fasarce kalamansa masu nauyi a harshenta ba ya taka mata birki, birki mai kauri da k'arfi, birkin dake farkar da ita, lokaci d'aya ya dora mata da fadin "Mutuncinki, shi ne farin cikin Mu! Ki gane u'r precious, ke d'aya k'walin k'wal nake da ita k'anwa a duniya, idan wani abu ya same ki bana tunanin zan iya yafema kaina Bilkissu!"

A hankali ta mayar da jikinta jikin kujerar ta jingina bayanta sannan ta lumshe idanuwanta tana sauraronsa...

Ya dora da fadin "Karatu na kaiki yi, ke kika zab'i kasancewa likitar mata, na yarje maki dan cikar burinki, shin so kike ki kaini wajen da zan dakatar da karatun naki ne dan kare mutuncinki?"

Da kakausar murya da d'an sauti ya k'arasa bayanin hakan ya sa ta buda idanuwanta da sukai mata nauyi ta girgiza kanta still kanta a k'asa.

Yatsar hannunta ta kusa da uwar yatsa watau manuniya ya nunota da ita ya k'ausasa muryarsa, du a maganar yanzun ne zai gindaya mata yin ko bari dan haka ta sada kanta tana sauraronsa ya ce" Ki saka sutura ki suturce jikinki, ki maida hankali a kan karatunki shi na tambaye ki! "

Kanta ta gyad'a kan nata a sade tana cije leb'enta, burinta ta ganta a waje, burinta ta daina shak'ar numfashi daya da yayanta, burinta ta yi nesa da wannan bawan Allahn ko zata ci gaba da anfanuwa, ko zata ci gaba da amsa sunan BILKISSU ba sakarai ba.

Hannunsa ya mik'a ya bud'e mata motar ta hanyar cire lock d'in da ya yi.

A hanzarce ta fita a motar, a gagauce ta yi cikin gidan bayan mai gadi ya bude mata tana b'alle botiran rigar tata da suka yi saura tana jin tamkar zafi zai halakata tamkar zata k'urma ihu dan wani irin abu da ya tsaya mata a wuyanta

Tana shiga d'akinta ta maida kofar da rufe, da sauri ta k'arasa wajen bed dinta ta kifa kanta ta jimke hannunta ta fashe da wani irin kuka marar sauti, kukan dake jijiga ilahirin jikinta tana k'ara cusa kanta a jikin abin gadon dan bata so sautin kukan ya fito har mamanta ta san da ta shigo gidan ta tambayeta ba'asi, abinda ya fi yi mata ciwo ita kanta bata san ba'asin kukan nata ba, idan an tambayeta Bilkissu kukan me kike daga yayanki ya maki fad'an gyara kayanka sannan ya gindaya maki doka dan ya isa da ke sai ki ce a kan wani dalili ne? Ita kanta bata san me ke damunta wanda ta ringa jin idan ba hawaye ta zubar ba tana iya bugawa tamkar bindiga ko bombe.

Yana kallonta har sai da ta bacewa ganinsa sannan ya sauke ajiyar zuciya.

Wayarsa ya d'auka dan kira, sai ya samu kira mai yawan gaske, wannin daga asibiti, wasun daga duniya ne kawai.

Yana shirin danno number wanda yake son kiran wayarsa ta kuma d'aukan tsuwa.

A hankali yake bin numbobin da kallo, kana ganinsu ka san ba number k'aramin mutun bane irin numbobin nan ne masu shige da juna
Uwa uba ita number nan tasa da akai kiransa da ita tabas wani wanda ya samu number ne a wajen wani makusancinsa, domin number yana anfani da ita ne kawai dan ajiye numbobin malaman Bilkissu, da number mamansu, da mutanen da baya so su neme shi bai d'aga kiran ba.

Kamar wani wanda baya so ya d'aga ya ajiye ya saka a handsfree yana sauraro.

Salama akai masa, da wata murya irin ta datijai kafin a ci gaba da magana kamar haka "Barka da warhaka Docter, sunana hajia Aisata Muhammad matar tsohon shugaban k'asa, yau kwana uku kennan ina neman layinka Allah ya sa kai d'in ne."

Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya amsa salamar, sai kuma ya k'ara yin gum yana sauraro.

Hajia aisata ta yi murmushi domin an fad'a mata yaro ne, mai aji ne, dole ta lalab'a shi ita dake so, dan haka ta kara tausasa muryarta mai cike da kamala ta koro masa bayani a kan rashin lafiar mahaifinta ta dora da fad'in "Ba zai iya jure doguwar tafia har kasar waje ba, na takaice maka yarona ni d'in mai kishin k'asata ce, a lokacin da na ji cewar akoy wanda ya jajirce ya zama k'wararre kuma har ake wawarsa sai na ce ba inda zan je, ina k'asata, sai dai damuwar ko zaka ganshi a cikin satin nan?"

Sai a lokacin ya bud'i bakinsa cike da girmamawa ya bata cikakiyar amsa da adireshin asibitin da lokaci sannan sukai salama.

Number mai Ipes ya dannawa kira ya k'ara gyara zamansa.

Yana d'agawa suka gaisa sosai da tambayar junna aiki.

Kafin ya yi yink'urin fad'in dalilin da ya sa ya kiraye shi sai kawai mutumen ya ce" Docter ka samu sak'ona daga wajen Principal ko? Ka yi hakuri muna yawan takura maka da kira kan Nana Bilkissu, yarinyar tana da ilimi sosai fiye da tunaninka sai dai matsalar tana yawan saka wasa a gabanta, maganar da nake maja yau kwata kwata bata shiga aji ba wai dan ta raina lesson d'in a cewar ta ita ko bata hau table ba zata iya cin jarabawar Psycho wai waye ba zai gane mahaukaci ko mai hankali ba, dan Allah ka tsawatar mata dan kuwa na rantse maka dalilinka da kuma k'wazon yarinyar ya sa na kasa d'aukan mataki a kanta da k'awayenta."

Ajiyar zuciya ya sauke a hankali yana d'an cije leb'ensa na kasa yana k'ara lumshe idanuwansa sannan ya bud'i baki ya ce" Kalar kayan makarantar nake so a d'inka mata yau kala hud'u, ina so a yi mata manyan d'inki sannan sket din a yi shi mai girma sosai iya tsatsonta za'a matse dan ya rik'eta sai a ba wani ya kawo gida."

Cike da murnar an karb'i sukarsa ya amsawa DOCTER HISHAM sannan sukai salama.

Kansa ya maida ya jinginar jikin motar yana shafa sajensa, ajiyar zuciya ya sauke a ransa yana tunanin yaushe za'a yi sati ba'a kawo kashenta ba? Sai kuma ya yi murmushi yana dan girgiza kansa, bai san me yasa a yanzu da ta zama budurwa idan zata fita baki daya yake neman nutsuwarsa ya rasa ba, ya kama bin k'ofar makarantarsu yana zirga zirga tamkar wanda bashi da aikin yi bayan shi din mutun ne mai aiyukan yi masu yawan gaske. Baya cikaken baci irin na kowa idan ba cewa aka yi weekdend ne ba, hana tare da dakarun dake saka masa tsoron barin k'anwarsa cilo ta fito yawo.

Nan ya yi ta rakiyar gawon shanu har sai da kiraye kirayen wayarsa ya ishe shi kafin ya daga ya shaidawa Kader wajen da yake.



Tunda ya ajiye ledar Mama ta buda tana dubawa take gumtse daria a cikin ranta.

Irin yanda Bilkissu ta zaro idanuwanta tana kallon d'inkin da ya shigo da su kai ka ce ta sume a zaunen nan ne.

Yanayin da ya yiwa fuskarsa kuwa tamkar bai san wani abu wai shi daria ko sakin fuska a rayuwarsa ba.

Wayarta dake ajiye gefen mama ce ta d'auki kuka, cikin sansanyar wak'ar celine dion mai taken my blood.

Maman ta kai dubanta ta karanta mai kiran, hakan ya sa ta tabe baki ta ce "Wai shi sojan nan bashi da suna ne? "

A tare zuciyoyinsu suka bada wani irin bugawa wanda har ya saka su kallon juna a tare.

Sai ta ji baki daya jikinta ya d'auki b'ari tamkar wata tsohuwa sai kawai ta ringa motsi daga wajen da take zaune ta kasa katab'us , ta sada kanta kasa sai ga zufa na neman wanke gaban goshinta du kuwa da irin sanyin acn wajen.

Irin yanda ya k'urawa fuskarta ido kai ka ce wani abin yake so ya karanta na halitar jikinta. A hankali ya ringa jin kansa na sarawa har ya ji idanuwansa sun yi masa nauyi.

Dogon hannunsa ya d'ora gefe ya samu ya cicib'a daga zaunen da yake ya maida dubansa wajen k'ofa, a hankali ya d'aga k'afarsa ya jefa da niyar tafia, sai dai muryar mama ta dakatar da shi a lokacin da ta ce " A'a, Hisham abincin fa? "

"Abincin fa?" Sai ya samu kansa da kasa fahimtar inda yaren ya dosa bayan yanzun a shigowarsa da wata yinwa ya shigo irin mai kad'a hanjin nan.

A hankali ya lumshe idannuwansa ya bud'e yana kallon Mama, wanda idan ya yi haka yana jiran k'arin bayani ne a kan magana.

Da mamaki Mama ta ce" aa, Hisham ba yanzun ka gama ce min a kawo abinci ba ga Umaimah ta je ta kawo kuma sai ka nuna baka fahimta ba?"

Wannan karron sai ya saurari cikinsa, sam ya nemi yunwar ya rasa, sai wani irin zazab'i da ya ringa jin na hauhawar masa kamar da wasa.

A hankali ya ce" A barshi."

Bai tsaya ba, ya yi gagawar juyawa dan ya san idan ya k'ara tsayawa zata iya cin galaba kansa ta hanyar tirsasa masa had'iyar abincin da baya jin idan har zai iya tauna shinkafa d'aya a bakinsa.

Baki bud'e Mama ta bi shi da kallo har ya fice a fallon, dubanta ta maido wajen Bilkiss, sai dai irin zaman da ta yi, kanta sade k'asa zaman k'warai ya sakawa mama ayyar tambaya a k'asan zuciyarta.

Kasancewarta mace mai fad'in magana kai tsaye, cike da tuhuma tace" Shin soyaya kuke ne?"

Kafin komai na jikinta ya yi magana cikinta ne ya fara murdawa ya bada wani irin sauti k'uuuuuuu kafin ta dago tana hakki tamkar wace ta ci gudu har ta gaji, abu d'aya ya hana mata sumewa ganin ba da shi mama take ba, ganin baya d'akin, da ita take tambayar , wata wawuyar ajiyar zuciya ta sauke sai kuma a hankali ta ringa juyawa mama kai watau amsarta kenan a gareta.

Mama za ta kuma yin magana ta ga hasken bud'e fallon, tana mai binsa da kallo har ya karaso kusa fa ita sosai, murmushin da ya sakar mata ita kanta ta san iya lab'ansa ne, ya rage tsayinsa a hankali ya dauki wayar sannan ya juya ya kuma ficewa.

Kamar an mintsineta ta fasa ihu tana mik'ewa daga zaunen da take hannayenta saman kanta ta shiga dira tana fad'in "Mama ki amso wayar nan tun kafin yaya ya shigeta, mama ya min kashedin samari ya ce na yi karatu idan yaya ya shiga wayar cen zai mayar da gabana gabas ya yanka ni a gidan nan, mama yaya bai taba dukana ba bana son ya dake ni na shiga uku na lalace."

Wata harara mama ta maka mata ta kausasa muryarta ta ce" Ke ni sakar min hannu bakya ganin kina min sama da kasa ne? Au kin san kina tsoron kika taka dokarsa? Ba ruwana yayankine idanma soya ki zai yo bayan ya yanka kin tsakaninku ni sakar min hannu."

A hankali take girgiza kanta gannin Mama fa bata fahimci yarenta ba, a hankali ta ji wannan murd'awa ta cikinta ta kara murd'a mata , maimakun ta kara samun kalaman bakinta ta amayar sai ta ji idan bata sada kanta da bayi a irin wannan lokacin komai na iya faruwa da ita ciki kuwa harda wankin fallon mama'

Kansa kawai ya jinginar da bayan mota a lokacin da Kader ke tuk'a shi
Basu zame ko'ina ba sai wajen aikinsa.

Nurse d'in dake gadi a ranar ta shigo da murnar ganinsa a irin wannan lokacin da tarin takardunta na mutanen dake son ganinsa, sai dai a irin yanayin da ta ganshi zaune saman kujera baki d'aya yanayinsa ya cenja, fatar jikinsa ta d'auki ja tamkar ba shi ba, gaban goshinsa jijiyar nan ta tashi sosai, jikin hannayensa haka du sun mike sun yi kalar kore abinka da farin mutun, k'wayar idanuwansa sun yi ja, hannunsa na dama rik'e da waya ya k'urawa wayar ido.

A tsorace ta tsaya bayan ta tambayeshi ko lafia?

Ya d'auki mintuna masu tsayi kafin a hankali ya ce"Ki kira min docter i'm seek."





*Hello mutanen barka da sallah.*
[7/24, 10:17 AM] BAK'A CE: 🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾
*DUK NISAN JIFA*
_(K'asa zai dawo)_
🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾

_RUBUTAWA_

*SAJIDA*

*SADAUKARWA*

*GA*

*MASOYA NA*


💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝

☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_


4




Da wani irin sauri ta juya dan zuwa kiran doctern da zata kwana a asibitin irin wannan ranar, wato wace zata yi gadi a asibitin.

*Docter RAKIA* likita ce a wannan asibiti sannan matar aure ce, matashiya ce ko na ce yarinyar mace ce mai ji da kanta, ita din yaren bahausa ce sannan tana auren bahaushe dan uwanta, tana da fara'a sosai da mutunci sannan tana son aikinta.

Bata wani jima ba ta bayanna a office d'in ogansu, ta gaishe shi da ladabi da biyaya sannan ta shiga gabatar da aikinta, sai dai kash ta kasa gano tak'amaiman matsalar dake damunsa dan kuwa gum ya yi mata da bakinsa yana mai bin wayar dake kuma shigowa da kukan kira da kallo, numbobin da a zaman da ya yi a wajen nan ya hardace su tas a cikin k'wak'waluwarsa tamkar karatu.

Kwata kwata ya k'i bata damar da zata gabatar da aikinta cikin nutsuwa hakan ya sakata gyara zamanta da abin d'aukan zafin zazab'in da ta d'auka tana kallo.

Da sauri ta mik'e ta fita
Bata jima sosai ba sai gata ta dawo da abin tura kayan magunguna d'auke da magunguna sosai.

Tana zuwa ta nemi da ya kwonta saman doguwar kujerar office d'in nasa.

A hankali ya cicib'a ya koma ya kwonta sannan ya lumshe idanuwansa da wayar nan a hannunsa.

Allurar karya zafin masasara ta fara yi masa, sannan ta saka masa abin karin ruwa aman bata saka ruwan ba domin ba zata saka masa ruwan komai ba kai tsaye bata san damuwarsa ba, ta d'ibi jininsa dan zuwa a auna abinda ke damunsa.

Tana rufe yan k'annanun kwalaben ya d'ago shanyayun idanuwansa ya sauke a kan fuskarta, muryarsa cen k'asa ya ce" Ki bani abinda zai sasauta min nauyin zuciya likita."

Gabanta ne ya yi kwonce kwonce ya bada wani irin ris ris ris sakamakon ido hudun da suka yi da shi.

Irin yanda idanuwanta suka sakata a wani irin yanayin da bata tab'a shiga a kan wani namijin da ba nata ba ya sakata saurin ambaton Allah da korar shed'an sannan ta cire dubanta a kansa da sauri ta duba takardar hannunta dan ganin idan har suna da likitan zuciyar da zai kwana yau?

Babu, domin dama manyan likitocin ba kwana suke yi ba, sukan zo dai su yi aikinsu cikin wuni sai kuma idan urgence ta samu ko zasu yi tiyatar tsakiyar dare, dan haka da sauri ta kuma tura abin ta fice dan zuwa ta saka a kiraye shi ko me yake ya bari ya zo!


Irin hirar da ta tarar likitocin na yi na d'akin kula da marar lafia ya sakata dan girgiza kanta, watau nurse d'in nan ce ta fad'a masu boss fa ba lafia, hakan ya saka du suka shiga a cikin matsananciyar damuwa, domin a cikinsu akoy wa'inda suna girmama boss fiye da tunanin bawa dan kuwa ya jajirce wajen ganin sun koyi aikinsu, akoy wa'inda ya masu rana fiye da tunanin bawa, sai kuma wa'inda ke dako da damuwar soyayarsa....

Sai da ta gimste fuska sannan ta basu umarnin fad'in rashin lafiarsa.

Kafin ka ce me du likitocin da suke ji da su sun halarta a kansa, kowa ya bada k'ok'arinsa abinka da masu abin nan da nan wani nanauyan baci ya yi awon gaba da shi.

Sai bayan ya yi bacin Kader ya d'auke wayar dake hannunsa ya bi number dake kira da kallo.

A hankali ya zauna cike da damuwa yana kallonsa, me hakan yake nufi? Shin ya shiga matsanciyar damuwa mai tsananin gasken da har ta fara taba lafiarsa a kan damuwar da bai san da ita ba ko yake danneta da k'arfi da yaji kan dalilinsa na banza?

Kiran da ya kuma shigowa ya saka shi mik'ewa a fili ya furta" Ka kai wajen da zan nemeka na ci uwaka ko dan yawan kiran nan naka yaro bale ka tabo wajen da dole sai na daki bakinka!"


Idan ta rintsa a wannan dare tabas b'arawon baci ne ya sand'eta ya d'auketa a saman dardumarta rik'e da tazbaha. Takan kali gabas, ta kali kudu, ta kai dubanta yamma , ta dawo da shi arewa, sai ta daga hannayenta biyu ta ce" Ya Allah ka kare yayana du inda yake, ka sa ya ci abinci ya koshi, ka sa ya daina fushi da ni ba zan kuma ba."

Sosai abin ke tab'a zuciyarta, ba komai ya fi tab'a zuciyar nata ba irin tunanin itane sillar b'acin ransa.

Kiran sallar farko ta farka da sauri tana mintsina ido.

Alwallah ta koma ta d'auro bayan ta yi wanka da sabuli da soso ta wanke bakinta sosai.

Sallah ta gabatar domin zuwa lokacin har an yi ta biyu an shiga masalaci.

Tana gamawa ta mik.e a hankali ta kai dubanta wajen agogo

Dakin mahaifiyarta ta fara shiga ta duk'a har kasa ta gaisheta

Mama dake haramar fita dan zuwa kicin ta ga abinda zasu dafa ta amsata cike da kulawa tana son gannin fuskarta da take kakarewa dan kar ta lura da kumburan da kumatunta sukai tsabar kukan da ta sha.

"Ki maida hankali ki gyara bangaren nan, idan haske ya fito sosai sai ki gyara na yayanku, bai kwana gida ba yau, tunda hawan karfe goma kike makaranta zan zuba abincinsa Kader ya fara kaiki ki kai masa sai ya kai ki makaranta" .....Mama ta fada tana mai ninke hijab dinta na sallah sannan ta saka wanda take fitowa tsakar gidan baki daya

Amsa mama ta yi ta mike tana jin damuwarta na kara hauhawa,

Gyare gyrare ta yi cike da rashin kwarin jiki, ta kunna turaran wuta mai kanshi sannan ta wuce

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login