Showing 78001 words to 81000 words out of 180809 words

Chapter 27 - DUK NISAN JIFA COMPLETE HAUSA NOVEL

sajida   

02 Feb 2025

12994

_RUBUTAWA_

*SAJIDA*

*SADAUKARWA*

*GA*

*MASOYA NA*


πŸ’«βœ¨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🀝

β˜† *[ T.M.N.A]* β˜† πŸ“–πŸ–ŠοΈ

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_


30



Da kyar ya iya ciro maganarsa yana kallon fuskarta ya ce" Na zata zaki kama min, na zata zaki ji tausayina, na zata zaki kasance mai talabeni a dukan halin da nake ciki, me yasa kike son idasa bayanar da cutata? Ashe idan na tashi da barin jikina a shanye gobe kiyama ba zaki ji ba dadi ba? Menene abin daukan fushi dan na aikata sunna ba zina ba? Ban cencenci ki yi farin cikin cewar ni din mai rike kaina ne har zuwa lokacin da na samu halalina? Shin ke makauniya ce da bakya gannin me nake ciki? Yaya aka yi kika gane yannayina bayan ba a cikin aikata hakan kika sameni ba? BILKISU ya taba taba maki koda hannu ne? "

Bilkisu ta lumshe idannuwanta hawayen azabar matsar da yake yiwa hannayenta na cinta da kuma hawayen magangannunsa, ita kanta ta rasa gane a kan me take wannan masifar, ita dai ba maganar soyaya suka furtawa junna da shi bale ta ce ya ce yana sonta a gabanta kuma ya je ya afkawa watanta ba ko jinkiri
Matar nan da ya jewa fa matarsa ce ba wata daban ba
Yaya aka yi take son zama wata wawa ta yanda zai gane abinda yake cikin ranta bayan ya dace ta boye? Me take so ya dauketa? Yana iya anfani da irin wannan damar da yake ganni a tare da ita gobe ya wahalar da ita cikin sauki

Ita kanta wace take yiwa fushin bata yi mata magana shin me ta yi mata? Idanma menene bafa ita ta roki a aura mata shi ba, kumama wai ita a su wa zata yi gaba da hukuncin Allah?


A hankali ta sada kanta muryarta a sanyaye ta ce" Hama, kana min da zafi "

A hankali ya sasauta rikon da ya yi mata yana kallon lebenta stil da baban burinsa shine ya kama shi ya saka shi a bakinsa yayi ta tsotsa har sai ya kara yin fari fat ta yanda zai tsotse jinnin dake saka shi zama pink

A hankali ta sauke ajiyar zuciya ta ce" Dan Allah ka yafe min, ba zan kuma ba "

Ajiyar zuciya ya ringa saukewa yana kallonta

A hankali ta dan matsa kusancinsu ya dan rage sannan ta hade hannayenta tana kallonsa ta ce" Hama am, ka yafe min ka ji? "

Wata ajiyar zuciyar ya kuma saukewa a hankali ya ja hannunta wajen kujera suka zauna yana kallonta ya dan sauke ajiyar zuciya a karro na uku ya ce" Ki daina irin maganar nan tsoro take bani Allah yana gani"

Wani dan galala ta kale shi, wai shi wannan gabjejen ne magana zata bashi tsoro?, hm,

Hannunsa ta kamo ta langwabe kanta ta sasauta muryarta ta ce" Hama am, dan Allah ka taimakeni ka rufa min asiri ka saka ni a wajen da za'a koya min mak'up, Hamana mak up shine baban burina na koyi yanda ake kwaliya da komai, Hamana idan kana tsoron na cikin gari kana iya kaini gidan sultan ka nemi alfarmar a koya min, dan Allah hamana kar ka ce min aa dan ni Gimbiya Najeeba nake so ta koya min, Hamana ba zan daina karatuna ba, zan yi sosai ba wasa a ciki, aman kuma dan Allah ina so nima ka cika min nawa burin"

Hannunsa da take dan masaging yake kallo jikinsa na amsawa, a hankali ya dan janye hannun ya daidaita muryarsa bayan ya dawo hayacinsa ya ce" Karatun likitanci ba burinki bane Bilkisu am? Yaushe ya zama ba burinki ba? "


Kanta ta sada kafin ta dago ta ce" Hamana na ga yana birgeka ne"

Dagowa ya yi daga jinginar da ya yi ya rike hannunsa daya cikin daya ya ce" Karya kike! Shin waye ya saka min ra'ayin yin karatun likitanci in ba ke ba? Me ya sa da muka je asibiti kika ce namiji mai kayan likitoci yana birge ki kina so na zama likita? "

Bilkisu ta yi tsuru tsuru da idannuwanta ta ce" Hama, ai namiji na ce, aman mace ta koyi mak up shine yake birge ni "

Hisham sasauta muryarsa ya ce" kennan a yanzu burina ba shine a gabanki ba? "

Gannin fa idan bata yi da gaske ba , ba zai barta ba , ba zai nema mata abin nan ba bayan ta tabata idan har shi din ya nemi hakan in sha Allahu zai samu ya sa ta duka a kasa
Fararan hannayenta ta dago ta hade tana kallonsa ta ce" yayana, koda ka ce a barshi zan bari, aman dan Allah kar ka hanna ni"

Zuciyarsa bugawa take da dukan karfinta idan yana zaune kusa da yar kanwarsa, kwata kwata mantawa yake cewar lokaci na tafia a zaunen nan da yake

Sanyayar da muryarsa ya yi ya ce" Ilimi kowani iri ne yana da anfani a rayuwar dan adam, neman ilimi sai mai hankali, Nana ilimi baya yawa, koda ilimin daure awaki be mutun ya ga wanda zai kara shi da shi ya tsaya ya koya domin kuwa zai anfana koda baya kiwo, bana son maganar barin karatu koda wasa kin ji? "

Kanta ta gyada masa kafin ta sada kan nata
Hawayen da take ta rikew ne wata kwalar ta ziraro mata ta gefe da gefen idannuwanta,
Bayan hannunta ta saka ta goge da sauri sannan ta mike da niyar nufar dakinta

A sanyaye yana biye da dukan motsinta ya ce" Ki kira min Aisha"

Cak ta tsaya da tafiar da take ta sauke ajiyar zuciya ta juya ta nufi dakin da Aisha ta shiga

Salama ta yi mata a sanyaye ta shiga cikin dakin

Aisha na zaune bakin gado hannayenta saman cinyarta tana kallon wajen madubi ta dago ta amsa salamar Bilkisu tana binta da kallo

Bilkisu ta karasa wajen da take zaune a hankali ta zauna bakin gadon sannan ta sada kanta, sosai ta ringa ba kanta shawarwari na rayuwa, shin meye ribarki Billy? Wannan yarinyar ta shigar maki hanci ta maki shigar wuri ta shige rayuwarki ta dira ta dire a wajen da baki taba hange ba, hasalima ko ganni da tawul din ranar kika taba gani dare daya ta zo ta gani...shin wannan ba ikon Allah bane? Ke Billy wannan ba hukuncin Allah bane? Ki cire komai da kowa a zuciyarki, kamar yanda kika rayu da naki ra'ayi ki yi wata rayuwar aman wannan ta hanyar baiwa wani damar shiga zuciyarki, ki barsu su rayu, ki basu space su ji dadin rayuwarsu

Ajiyar zuciya ta kuma saukewa a sanyaye ta ce" Ki yi hakuri, Aisha na san zaki daukeni mai son kanta da mugun hali ki yafe min dan Allah idan da hali komai ya wuce"

Da sauri Aisha ta juyo tana kuma kallonta, hannunta ta kamo tana kallonta ta ce" Ki daina bani hakuri Bilkisu, ni nan ni nake cikin damuwar shiga hakin ki da na......."

Bilkisu ta tari numfashinta tana kallonta ta ce" Ki dauka kan baki shiga hakin kowa ba, ki rayu ta hanyar tarban gaban abinda yake malakinki, Aisha ki daina ba kowa hakuri kan abinda kika tashi kika ganki a ciki, ki dauki cacar bakin da muka yi da ke a matsayin sabani ne ya dan samu tsakaninmu kuma ya wuce, in sha Allahu zan girmamaki da girman da Allah ya baki na auren yayana, ina fatan ki daukeni a matsayin kanwarki, daga wannan bana son wani abin na roke ki"

Aisha kallonta take, ita du gani take tana yin haka ne dan ta nuna bata damu da shi ba bayan kalamai ne kawai take saki daga bakinta aman abinda yake bayana a motsinta ba haka bane

A hankali ta mike tsaye ta mata murmushi ta ce" Ki tashi Hama na kiranki"

Aisha ta kasa motsawa daga inda take zaunen har sai da Bilkisu ta kuma kama hannunta ta cicibata da kyar tana nishi hakan ya baiwa Aisha daria har ta kara sakar mata jiki tanai mata daria

Itama dariar take ta ce" Waiwaiwai aunty Aisha sannu"

Aisha ta ce" Wani sannu, ke zan ma sannun ai"

A haka suka fito , Bilkisu ta nuna mata hanyar ta tafi

Tana kama hanya itama ta juya ta nufi dakinta wanda ya rakata da kallo har ta bacewa ganninsa

A hankali ya maida dubansa kan Aisha dake zaune dan nesa da shi ta sada kanta, dukan alamu na tsoro da rashin sakewa da shi sun bayana a tatare da ita

Yar ajiyar zuciya ya sauke muryarsa a sanyaye ya ce" Yaya jikin ki Aisha? "

Dagowa ta yi da dan sauri, sai kuma ta maida kanta ta sada tana jin kunyar tambayarsa har cikin ranta

Dan murmushi ya yi ya mike a hankali ya kama hannunta ya mikar da ita tsaye
Dakinta ya nufa da ita cikin nutsuwa har kusa da bed dinta ya tsaya yana dan kallonta kafin ya ce" Ki sha maganinki na yama ki ci abinci sai ki huta kin ji? Zan koma asibiti sai na dawo"

Aisha ta gyada kanta a hankali ta ce" Na gode sosai "

Dan tsai ya yi yana son ya tambayeta godiyar me take? Sai kuma ya fasa ya saki hannunta ya juya ya fice a dakin

Dakin Bilkisu yake ta kallo a tsayen da yake har mama ta shigo

Yana ganninta ya sauke ajiyar zuciya ya shagwabe fuska ya ce" Mama ni na gaji "

Mama ta yi murmushi ta ajiye kayan dake hannunta ta kama hannunsa suka fita
Sai da ta kaishi wajen motarsa ta bude masa da kanta ya shiga ya zauna sannan ta sanyayar da muryarta ta ce" A dawo lafia, zan dafa maka abinda kake so kana dawowa ka ci ka more sai barci ka ji yarona? "

Murmushi ya mata sannan ya daga mata hannu ya yiwa motar ky ya kama hanyar asibiti

Bayan salar magariba zaune take saman kujera kafarta daya sama dayar a kasa tana ta faman hada wayar da ta nunawa mama cewar Umar ne ya bata, mama kam ido ta zuba mata jira take su kadaice ta bata bayani domin a lokacin Aisha na zaune ne

Cen wajen diner su Mama ne zaune harda Aisha da mamanta da tati sunna cin salak din da Aisha ta kwada masu

Kanshin turaransa ya sanar mata da isowarsa aman bata dago dubanta ba ta mayar kasa tana dan dadannawa

A jikinta take jin ya bita da kallo har ta ji muryarsa yana ba mama amsa

Da sauri ta dago kanta jin yana fadin" Zamu je gidan Mai damagaram ne da Bilkisu mu dawo "

Da sauri ta mike tana ajiye wayar ta nufo wajen da yake tsaye ta ce" Yaya zamu tafi? "

Dubanta ya yi tun daga kasa har sama, ita kam me yasa take son saka wando ne?
Kawar da dubansa ya yi ya ce" ki saka sutura ki yi maza mu tafi ya ce akoy mai jiranmu a kofa da zai kaimu dakin bakinsa "

Ai tun kafin ya gama ta yi dakinta da sauri

Wani rantsatsen lesh ta saka ta daura dan kwalinsa irin daurin nan mai shige da fice ta dauki mayafinta ta kurma a saman kanta ta fito tana washe bakinta ta yiwa su Mama salama domin tuni yana cikin mota

Tukasu Kader yake inda motar ta dauki shiru sai sanyin Ac kawai dake tashi domin ko radio basu kunna ba

Ta madubi yake kallonta ta yafa mayafinta saman kanta ba kwaliya a fuskarta normal dai

Sunna zuwa aka shigar da su da motarsu har wajen ajiye motocin gidan

Tatare suka nufi wajen da sun tabata sai sun yi jira domin ba wanda bai san waye Mai damagaram da mulki ba

Abinda ya basu mamaki tarar da su da suka yi zazaune bayan jakadiya ta masu iso

Zaune yake cikin shigarsa ta alfarma kamar yanda ya saba kansa dauke da rawani
Gefensa NAJEEBA ce cikin shiga ta wani rantsatsen lesh ta sha alkyaba fara kal mai yalwatacen duwatsu, sai Nadia dake zaune a gefenta itama cikin shiga ta alfarma tana rungume da yaron da ba zai fi shekara biyar ba

A lokacin da su Bilkisu suka zauna a kasa Hisham na tsaye a kan kafafuwansa , shi bai zauna dandar a kasa ba, shi bai zauna saman kujera ba

Cike da isa Sarki SHAHEED ke kare masa kallo kafin ya yi murmushi ta cikin rawaninsa ya sasauta muryarsa ya ce da Najeeba" Ba zai duka min ba hala? "

NAJEEBA ta sasauta muryarta sosai ta ce" Ban kare masa kallo ba dan kar ya zama fitina, aman kar ka manta kowa sarki yake a wajen aikinsa, mun samu ya zo ya dace mu sauke kanmu kasa"

Dubanta ya yi ya dan daga muryarsa kadan ya ce" Da kallon tsaf kike son masa ko me BEEBAH? '

NAJEEBA ta dan yi shiru kafin ta kalli Nadia dake murmushi ta ce" Toh fa "
Sai kuma ta kale shi ta rage muryarta sosai ta ce" Allah ko ka yiwa bakinmu maraba ko na tashi na yi masu "

Da sauri Shaheed ya kaleta sai ya cire kansa ya tabe bakinsa sannan ya kai dubansa wajen da HISHAM ke tsaye yana kallon Bilkisu
Irin kallon da yake yiwa Bilkisu ya saka Shaheed yin murmushi ya kalli Najeeba ya ce" Na so na hora shi kan tsayawa da ya yi a gabana kikam, aman ba zan yi hakan ba da alama wannan da suke tare ko matarsa ce tana cin kaniyarsa ne"

NAJEEBA sai a lokacin ta kai dubanta kan Bilkisu, gannin yar budurwar ta sada kanta tana wasa da yan yatsunta sannan ta kai dubanta kansa, shi kuwa yanda ka san ya samu TV haka yake kallonta ya saka Najeeba sakin murmushi tana gyara zamanta da kyau

Sandar dake hannunsa ya dan bubuga a kasa hakan ya sa sarkin bulala shigowa da sauri ya zube a kasa yana kirari da fadin cewa gashi

Sai a lokacin ya kalli Hisham, da mamaki ya ce" Yaro yaya kake tsaye kikam gaban gurnanin zaki? Ka kuwa san cewa ka zo gaban mai wukar yanka? Zube a kasa ka gaishe da uban gidanka tun kafin ka ji kanka a kas!"

Da sauri Shaheed ya ce" KAR NA GANI, SHI DIN NINE NA NEMI ALFARMARSA GAYANA NE!"

Da sauri ya shiga neman afuwar Hisham wanda baki daya wannan abin da sarkin bulala yake yana bashi daria ne da mamaki, wai dama haka fadawa suke yiwa sarki? Lalle dole a kirki sarki da sarauta da kuma takama, tabas zai duka ya gaisar da shi dan kuwa ya cencenta

A hankali ya rage tsayinsa har ya kusan dukawa dan gaisar da mai damagaram ya dakatar da shi ta hanyar daga masa hannu sannan ya masa nuni kan ya dawo kusa da shi





................
[7/24, 10:19 AM] BAK'A CE: 🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾
*DUK NISAN JIFA*
_(K'asa zai dawo)_
🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾

_RUBUTAWA_

*SAJIDA*

*SADAUKARWA*

*GA*

*MASOYA NA*


πŸ’«βœ¨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🀝

β˜† *[ T.M.N.A]* β˜† πŸ“–πŸ–ŠοΈ

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_


31



Sai da Hisham ya mike tsayinsa da kyau ya dan gyara tsayuwarsa a kasan zuciyarsa kuwa fadi yake' Da ba dan Allah ya ce na girmama sarkina ba da na juya domin irin haka na hauda min jinina sama'

A hankali Bilkisu ta kuma kallonsa a karro na biyu, tsarin shigarsa sai yanzun take kara kawatuwa a cikin idannuwanta domin sanye yake da wani danyen yadi ruwan blue an masa dinki simple aman tsayinsa da tsarin jikinsa ya saka yadin wani irin daukansa, a kasan zuciyarta take fadin 'to shi hama a kan me bai duka ba tunda muka shigo?' Gashi dai da wannan mutumen ya yi ihu sai da ta ji uwa ta rukunkume yaya Kader, shima Kader din kallonsa kawai yake, anya Hisham bai shafi jinnin sarauta ba? Wannan na biyu kennan da ya ga irin haka, yau gashi ya yi a gaban mai kankat din watau mai damagaram, uwa uba irin yanda Hisham ke saka idannuwansa a cikin na Shaheed sai abin ya ringa bashi mamaki, idannuwan shaheed da ake tsoro? Shi dai fatansa su gama su tafi kar ya yi abinda mai damagaram zai kule su walahi!

Wajen da ya nuna masa ya karasa ya zauna saman kujerar

Muryarsa ya sanyaya ya ce" Barka da warhaka Sultan "

Shaheed ya saki murmushi a hankali ya dan gyara rawaninsa ta wajen bakinsa ya miko masa hannunsa ya furta" Barka da aiki likita, ya fama da jama'a? "

Hisham ya kuma dagowa ya kale shi sai ya sakar masa murmushin shima ya ce" Alhamdulilah "

Sultan Shaheed ya kai dubansa wajen da Nadia take sannan ya kai dubansa kan sarkin bulala

Da sauri sarkin bulala ya karasa ya duka daga nesa da ita kadan hakan ya sa ta mikar da yaron dake sanye da wani rawani a kansa ta matso masa da shi

Daukansa ya yi ya kaiwa Hisham shi

Hisham na kallonsa da tausayawa ya shiga warware masa nadin da aka dafka masa

Sai da warware masa shi tsaf, sannan ya cire masa katuwar rigar da aka saka masa mai uban zubi

Dubansa ya dan dago ya ga kowa shi yake kallo hakan ya saka shi yatsina kyakyawar fuskarsa ya kai dubansa wajen kader ya ce" Baka dauko jakar aikin ba "

Kader ya mike da sauri ya fita

Jim kadan ya dawo hakan ya sa Hisham shinfida rigar yaron a nan kusa da mahaifinsa sannan yana kallonsa da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login