Showing 15001 words to 18000 words out of 180809 words

Chapter 6 - DUK NISAN JIFA COMPLETE HAUSA NOVEL

sajida   

02 Feb 2025

12958

a barta a gurbin da mijinta ya barta ba zata iya fita ba.

Yanayin Inna ya saka dole ta je gidan mai gari ta kwana domin ba zata iya kwanan gidansu ba gaskiya.

A haka mijinta ya saka aka kawo likita ya duba Inna, aka ringa bata magani anna kara kulawa da lafiarta, sai dai cikinta ne ke kumbura haka kawai.

K'arshe dai wannan ciwon sai da ya kai Inna k'abari. Asma'u ta yi kukan da bata tab'a yi ba a rayuwarta, ta rik'e hannun k'anwarta da hannu bibiyu tana kuka ta ce" Zeinab yanzun idan kika tafi sai yaushe? Bani da kowa sai ke sai mijina Zeinab, kar ki tafi ki barni na rok'e ki"

Ita kanta wayar gari ba uwa ba uba ya saka zuciyarta tsintsinkewa, sai dai bata tunanin a yanzu wani abu zai saka ta dawo k'auyen nan da zama, hakan ya sa ta rarrashi Asma'u ta hanyar fadin" Asma'u inada wani ne bayan ke? Da mijinki zai amince da kun zo birni na baku gidana kun zauna, Asma'u aure ya kai ni birni, dole na koma, aman na yi maki alk'awarin wannan karon ba zan ringa jimawa har haka ban zo inda kike ba, ki siyar da gidan nan, ki gyara rayuwarki sannan ki saka mijinki ya ci gaba da nome gonar cen hakan zai sa ku ji sanyin rayuwa."

K'arshe ta bata kud'ad'e da suturu ta tafiarta ta barta da kewa sosai dan kuwa Asma'u kam akwai son mutane da son d'an uwa dan bata da yanda zata yi ne.


Haka rayuwa ta ci gaba da tafia, a shekararsu ta bakwai da aure Zeinab ta samu ciki.

Wannan ciki ya ringa kawo yan cenje cenje a zamantakewarta da mijinta, dan kuwa sai wani lamari na kusanci da bayyanar yan sirrika suka ringa bayyana a tsakaninsu.

Ya fara fad'a mata sirrikansa na irin dukiyar da ya mallaka, asalin shi d'in wanene, irin matsayin da ya taka a duniya da dai sauransu.

A ranar da ta haihu ta samu d'a namiji a ranar ya rungume yaron cike da damuwa da wani irin farin ciki ya kalleta yace "Kamar yanda na fad'a maki ni sunana Muhammad K'aribullah Zeinab, ni balarabe ne gaba da baya, kasancewar haka ya saka a danginmu muke da wata banzar al'adar auren jinsinmu, bama aure sai balarabiya yar uwarmu, ina da aure kusan shekaru goma sha takwas kennan a nan cikin damagaram matata da mahaifiyata suke, a lokacin da na ganki na jewa mahaifiyata da maganarki, sai dai tashin farko ta nuna karma na fara kar na jaza mata abin fad'e a cikin dangi, matata bata tab'a haihuwa ba, kuma na k'ara auren wata balarabar ya gagara dan kuwa na rasa me ya sa mahaifiyata sam ta k'i na k'ara auren wai yaro ne ni, kin ga na aureki ne a b'oye Zeinab, gashi a yau ni ne rik'e da gudan jinina, Allah ya raya min *HISHAM*."

Bata wani mugun damu ba, haka kuma bata yi wani uban taro ba, iya k'awayenta yan gayu da ta yi ta gayyata suka rak'ashe. Sai bayan wata biyu ta je ta kaiwa Asma'u Hisham, a wannan rana ta ga wani irin lamari wai shi son y'aya, dan kuwa Asma'u har fad'i take zata bita su dawo birni ta raini Hisham, dan Allah Hisham zai kirata da mama?.

Irin abubuwan nan suka bata daria, ita kanta da zata samu ta biyotan ta zo ta k'arata da wahalar jariri da ta so hakan, dan kuwa a gaskiya bata son takura duk da yan rainonsa hakan baya wani d'ad'ata da k'asa.

Hisham na da wata bakwai tafia ta taso wa mahaifinsa zuwa daji

Kafin ya tafi ya yiwa mahaifiyar Hisham alk'awarin yana dawowa zai d'auketa ya kaiwa mahaifiyarsa da abinda Allah ya azurtasu da shi.

Da wannan suka rabu da mak'udan kud'i da wasu gidajen biyu da motar da ya bar mata ko da buk'atar wani abin zai taso baya nan, sai dai bai tantance mata su waye iyayen nasa ba, a ina suke da sauransu, ko a larmé ba'a san da zamanta ba bale yaronta a haka ya tafi wannan dajin da bai dawo ba, wanna dajin da bata ga gawarsa ba sai a TV take ganin suturarsa da aka gabatar. Wato yak'i ya ritsa da mijinta, wanda bata ga iyayensa ba sai a TV aka hasko fuskar mahaifinsa ta mahaifiyarsa da wata a kusanta d'auke da nik'af.

Bata tab'a dana sanin auren nan nata ba sai a wannan rana, gata zaune a d'aki ita daya ba mai rarrashi ba wanda zai yarda cewar mijinta ne ya rasu sai wahalar rayuwa ta ci kuka har kamar za ta haukace.

A hankali abubuwa suka ringa rincab'e mata, ta rasa madafa, ta rasa shin idan ta fita dan neman dangin mijinta su wa zata ce? Iya sunansa ne kawai ta sani, idan ta je TV ana iya ganin dan ta samu kud'i ne zata yi masa sharri, idan ta je ma'aikatarsa zata iya jazawa kanta matsaloli ne da ba zata iya fitar da kanta ba.

Dan dole ta zauna a d'aki karatunta na neman lalacewa, komai nata na neman tsayawa cak a irin wannan lokacin da ta saba da kud'i da rayuwar kud'i.

Kud'ad'en hannunta duk ta kashe sai mota sai gidaje, gata ko acc bata da shi dan kuwa a hannu yake zuba mata ita kuwa ta kashe.

A hankali ta fara neman zaucewa da jigilar yaron da aka sabawa shan madara, madarar gwongwani ana bud'ewa bata rufe kwana biyu
Yaro jajajir da shi b'ulb'ul da shi sai k'ara k'iba yake yana yawonsa ko ina.

A ranar da ta wayi gari ba isashen cenji a jakarta sai kawai ta had'a dukkan abin had'awarsa ta shiga motarta dan kuwa ta sallami yan aikinta ta nufi k'auye.

Ta kuma zuwa ta zubawa yayarta dukan damuwarta sun yi kuka kamar me, sannan ta rik'e hannayenta tace "Aunty Asma'u ga Hisham, ba zan iya rayuwar karatu ba mai tallafa min ba ga kuma yaro, aunty Asma'u ki saka Hisham a makaranta, ki kula da lamarinsa, zan siyar da sauran gidajen da ubansa ya bari na je garin niamey na k'ara karatu na samu aiki, sai ku shiga d'ayan gidan ku zauna, aunty asma'u yaron nan naki ne dunia da k'iyama, Hisham ba *D'ANA BANE*, zai kira ki da Mama, ko da wasa kar ya kira ni da Mama, ga wayar nan zan bar maku ita ku yi anfani da ita, duk lokacin da na samu dama zan ringa kiranku, haka kuma sai dai na tabbata zaku wahala domin a yanzun bani da kud'in da zan ringa turo maku, idan na samu wani auren mai tafe da cenji zaku ji ni, idan zan dogara da kaina ne sai dai na k'ara baku hak'uri."

Sosai Asma'u ta so ta rik'e yar uwarta, ba irin abin da bata nuna mata ba kan ta zauna a gari ta gama idarta, ta kilace kanta ta samu mijinta, ta yi aurenta Allah shi keda komai.

Sai dai kash, hakan ya gagara, dan k'arara ta nuna mata wannan rayuwar ba tata bace, k'arshe dai tare suka juya ta nuna mata gida ta bata takardunsa , basu bar garin ba sai da suka k'ulla alak'a da mak'otan gidan ta bar masu amanar saka kunne a motsin gidan domin akwai kayayaki na anfani , kayan abincin ciki kawai ta fitar ta bayar sadaka, sun amshi number juna da matar gidan sannan suka yiwa juna sallama.

Asma'u ta yi kuka tana kallon yar uwarta ta tada mota ta tafiarta ta barta tsaye da yaron da bai san kowa ba sai mamansa aman rana tsaka ta cire shi a nono , ta cire shi a jikinta ta tafi nema kamar wani namiji ko waiwaye babu.

Abinka da k'auye sosai aka so sakota gaba dan wannan yaro, sarakuwarta ta so ta d'auki ziga cewar yaron shege ne aka kawo aka yarda masu, sosai ta fara nuna halayan da ba nata ba cewar dan d'anta yana zaune da ita a haka juya ba haihuwa shine za'a jajab'o masa wani jan d'a kamar d'an mai jan kunne a kawo masa ya ciyar. Sai da ya ga abin ba na k'arewa bane ya fayyace masu cewa shine baya haihuwar ba ita ba.

Tun daga lokacin sai ta samu sauk'i a wajen uwar mijinta, aman mutan gari sun kasa yarda cewaHisham ba shege bane, an d'ora cewa shege ne uwarsa ta kawo ta yardawa yayarta ta koma yawon ta zubar d'inta.

Haka tafia ta ci gaba da mik'a, a haka ajalin mai gidan Asma'u ya riske shi a hanyarsa ta dawowa daga maradi. Har sai da Asma'u ta yi jinyar wannan rashi, ta dawo zurum da ita, abu d'aya ke sakata sakin ajiyar zuciya idan Hisham ya rik'e hannunta ya kireta da " *MAMANA."*





Alhamdulilah
[7/24, 10:17 AM] BAK'A CE: 🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾
*DUK NISAN JIFA*
_(K'asa zai dawo)_
🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾

_RUBUTAWA_

*SAJIDA*

*SADAUKARWA*

*GA*

*MASOYA NA*


💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝

☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_


7


Ta zauna a tare da sirikanta har ta yi takabarta ta gama
Ta samu ta yi takabar cikin nutsuwa da kiyayewa

Bayan ta gama ne ta shiga tunanin sana'a, da kuma wajen zama domin ba zata iya zuwa gidan mahaifanta ba ta zauna ita daya sai dan yaronta mai shekara uku,
Haka kuma idan ta zaune a gidan sirikanta zata dora masu wani nauyi ne, su kansu sunna fama da kansu a gabannan zasu tsaya kan kafafuwansu ne domin dama mijinta shine komai na gidan, sai dai a lokacin da sarakuwarta ta ji bayaninta sai ta nuna mata sam ba inda zata je, ai su y'a take a wajensu zasu iya rike iyalin d'ansu ko bayan ransa, idan ta samu miji sai ta yi aurenta

Shawara kan shawara take tana kwoncewa kan sana'ar da ta dace da ita

A hankali ta fara yin awara tana siyo waken a pancas (wata yar kasuwa ce dake bakin hanya a garin damagaram)

A kafarta take zuwa da goyon yaronta ta siyo ta kai nikan abinta sannan ta koma kanya ta dafa ta matse ta fita waje ta shiga soyawa tana siyarwa

Ta iya gyaran awararta hakan ya sa ake siya ta ko'ina dan kuwa harda kwai take sakawa mai son da kwai

A hankali ta ringa fuskantar rayuwa, kafin yaronta ya kai lokacin shiga makaranta ta samu zawarawa uku sai dai kowa maganarsa a kan yaronta ne, wanda takan yi murmushi ta ce da mutun" Allah ya hadaka da wace bata da yaro, aman idan na yi aure yanzun ina zan barshi? Maraya ne"

Shakuwar dake tsakanin Asma'u da HISHAM shakuwa ce ta uwa da d'a, ta sadaukar da farin cikinta bila adadin dominsa, Nema take ido rufe dan shi, yaron idan ka ganshi ba zaka ce rayuwar kauye yake ba dan kuwa suturunsa masha Allah, jikinsa a tsaftace
Yana kai shekarun shiga makaranta ta je da kanta dan tana son saka shi
Sai dai damuwar da ta fara fuskanta shine ba zasu dauke shi a shekarunsa ba a kauyen sai ya kara girma

Ta ci burin karatun HISHAM, ta rayu da wannan buri a zuciyarta, domin kuwa karatun islamiya da na boko ta yiwa kanta alkawarin sai inda karfinta ya kare a kan yaron nan wanda take kallo ta ji sanyi a zuciyarta, dan shi kadai ne da ita gaba da baya, mahaifiyarsa tun da ta tafi bai fi a irga ba wayar da suka yi da junna har mamaki take bata

A haka ta zauna da mahaifiyar marigayin mijinta sukai magana, ta zo mata da maganar yaronta da kudirinta, duda ba a hakan ta fara aikata abinda bata taba aikatawa ba watau a kan rayuwar yaronta ta inganta ta koyi shiga kasuwa, ta koyi zama kofar gida ta toya awara, ta koyi kutsawa cikin mutane, ta koyi abubuwa da yawa a dalilin yaronta, sai kuma ga baban abin, a kan karatun yaronta zata koma birni da zama

Sun jima sunna tatauna maganar, har mahaifin mijinta ya zo ya saka baki
Gannin burinta kennan, kuma su, suke zaune da ita sun san wacece ita ya saka suka saka albarka da faran alkhairi

Mafarin kaurowarsu kennan birni, ta tare a gidan nan da makotanta

Ko a birni sana'a take ka'in da na'in

Bata shiga sabgar da ba tata ba, tana mutunci da mutan anguwa , tana shiga ta kamala
Bata wasa da adininta, bata wasa da shiga sabgar mazan anguwa haka kuma bata baiwa kowa fuskar da zai iya kawo mata lalata ba

Yaronta na karatu, yana da ilimi , domin Hisham ya kasance irin yaran nan da ake kira surdoué, tun yana kananun shekarunsa ake tsalake masa aji kafin kace me ya yi fice a harkar karatunsa yana zama zakara a dukan abinda ya saka gaba
Tun a kannanun shekarunsa ya yi sauka, ya ringa shiga litatafan adinni, sannan ya ajiye buri na zama soja

Yana kawo shekara goma sha shida a duniya mamansa ta yi aure, ta auri wani bafulatin mutun dan kasuwa mai mutunci
Dagewa ya yi kan su tare a gidansa da matarsa da y'ayansa biyu
Sai dai mama ta dage kan maganar yaronta fa? Idan ta je gidansa da d'anta shin za'ai zaman lafia da iyalinsa?
Ga Hisham wani irin yaro ne mai kafa kafa da mutuncin mamansa, a duniya zaka zauna kalau da shi idan zaka mutunta masa uwa, daga bakin lokacin da zaka nemi raina masa uwa zai daina gannin girmanka, sannan zai datse du wata alaka tsakaninka da shi, idan kuwa ka nace zai kirta maka rashin mutuncin da zaka manta hanyar garinku

Wannan tunannika suka saka mama kasa bin wannan mutun, sai dai ya zo ya kawo masu ziyara ya tafi

A haka kamar da wasa mama ta wayi gari da ciki, abin ya daketa ya bata mamaki, tana fahimtar hakan ne sai ta yi shiru bata fadawa kowa ba ta ci gaba da harkokin gabanta duda irin wahalar da yake bata a cikin gidanta

Mijinta ya yi murnar haka, ya kuma tado maganar komawa gidansa dan ba zai taba son gannin ya raba kawunnan y'ayansa ba

A wannan lokacin ne kuma wata rigimar ta kara barkewa, dan kuwa mama ta so komawar sai kuma matarsa ta yi yaji ta tafiarta gida

Abubuwa dai sun faru mararsa dadi , karshe sai kulawa ta ragu, a hankali ya rage yawan zuwa inda suke har Mama ta haihu yarinya ta ci sunnan *BILKISSU*

Tun yana waiwayarsu sau biyu a sati, ya koma sau daya
Karshe abin ya dawo wata, har ya koma idan ya tunna
A hankali dai bawan Allahn nan ya yi watsi da su ya bar mama da rainon yar jaririyarta da kuma yaronta

Daga wannan lokacin ne HISHAM ya kara zage dantse wajen taimakawa mamansa

Idan ba kira Zeinab ta yi ba, ko mama ta yi kiranta ta zaunar da shi cewar ga mahaifiyarsa su gaisa shi ba wani sanninta ya yi ba, sannan yana kara gannin girma da darajar mama a idannuwansa na irin yanda take sadaukarwa a gareshi a wannan zamani da zumunci ya yi karanci

Karatunsa na kara zafi tafe da shekarunsa, kwazonsa ya saka ya yi ta cin nasarar shiga manyan makarantu ba da ko sisinsu ba

A shekarar da ya zama zakaran zama na farko a kaf niger wanda ya fi kowani dalibi maki a matsayinsa na wanda ya karanci Serie C mai matukar wahala ya saka manyanmu zama na musaman a kansa

Daga wannan rana ne komai ya cenza masa domin kuwa gwamnati ce ta dauki nauyin fitar da shi waje, nauyin abincinsa, nauyin suturarsa, da wajen bacinsa, da litatafansa, komai nasa tare da albashi irin na mai burse mai tsokar gaske

Cike da farin ciki Mama ta zauna ta dannawa Zeinab kira dan ta sanar mata, cikin nutsuwa ta ce da ita" Dama albishir zan baki a kan HISHAM"

ZEINAB dake rubuce rubuce ta dan dakata ta lumshe idannuwanta ta ce" Asma'u, ni kam gaskiya sai na ce kamar baki gane yarena ba? HISHAM D'ANKI NE, dan Allah cen ku karata ni kam ku barni na yi abubuwan dake gabana dan idan har kudi ne zai fito daga wajena a irin wannan lokacin bani da shi, nima ta kaina nake"

Bata tsaya ta ji sauran zancen ba ta kashe ta ci gaba da rubutunta dan tana ta ajiye takardunta ne na neman aiki

Jiki a sanyaye ta dago ta kai dubanta kansa, yana gyarawa BILKISSU rigarta da ya cenza mata

Miskili ne na bugawa a jarida aman idan yanaiwa Bilkissu hira kai ka ce da wata katuwar budurwa yake

Mama ta dan gyara murya ta ce" Mahaifiyarka ce na yi kira Hisham , zata kiraye mu ta ce"

Irin yanda ya kurawa fuskarta ido sai ta samu kanta da kawar da kai tana dan dama bata ce haka ba,

Murmushi ya yi a fili ya ce" Mamana, likita zan karanta aman kuma na sojoji, ina da buri a cikin zuciyata sai dai ina tunanin barinki a nan, da kuma BILKISSUNA, ina tunanin wa zai kula min da ku? Wa zai ringa kai min ita makarantar islamiya? Wa zai ringa kaita na boko? Wa zai ringa hannata fada? Kar fa a dakar min ita mama, kar ki ringa hasala a kanta mamana, zaki rike min ita da irin rikon da kikai min kuwa? "

A hankali ta ringa jin kewarsa tun kafin ya tafi, a hankali ta sada kanta sosai tana jin yaron a kasan zuciyarta

Murmushi ta dago ta sakar masa dan kar ta sage masa gwuiwa

A haka ta rarashe shi da alkawarin yin iya yinta a kan amanar da Allah ya bata na tarbiyarsu baki daya

Daga bakin lokacin da ya daga ta fara azumin litinin da alhamis
Idan ta kai kanta kasa sujada bayan adu'ar gamawa da duniya lafia

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login