Showing 36001 words to 39000 words out of 180809 words
ce" Aman mama bata san cewa ke din mafad'aciya ce ba ko? Yanzun Bilkisu a kadan na baki shekaru hud'u a duniya shine kike min ihu haka daga tambaya? Ki yi hakuri dan Allah."
Bilkisu ta ringa sauke ajiyar zuciya tana cije leb'enta na k'asa, itafa bata huce ba sam neman wanda zasu yi sama su fad'o take ko zata ji sanyi a kasan zuciyarta.
A sanyaye Aisha ta d'ora da fad'in" Tun da ya fito daga d'akin tiyata kafin na san wanene shi , matsayinsa ko isarsa ni na kamu da son sa."
Ras ras ras gabanta ya ringa wani irin fad'uwar da ta sakata zabura daga juyawa Aisha bayan da ta yi ta juyi gaba dayanta tana kallonta.
Aisha ta kara gyara yannayinta ta ce" har gabana ya fad'i, na zata ko kema kina son sa ne? Da na shiga halin damuwa domin kuwa na tabata zai so ki fiye da ni idan har ya same ki duda so gamo ne na jini, na zata ko kina son yayanki ne, da na had'iye tawa matsalar dan na san ke d'in ke ce mai gurin ni kuwa mai tabarma ce sai..."
Giftawar hannunta da ta gani ne ya sakata saurin rik'e hannun nata ya zamana sunna kallom juna ido cikin ido.
Murmushi Aisha ta yi mata ta ce" Kar ki yarda yarinta, ko jiji da kai da kina mace ki hadiye damuwarki har ta yi maki illah, du wanda bai fahimci abinda ke damunku ba ya yi niyar makancewa a gabanku ne, ki sani Doctor namiji ne cikake duda ban san ainahin shi din namijin ne ko aa, abinda idannuwana suke iya gani nake kokarin fasarawa zuciyata, zan rantse maki da Allah idan na same shi zan amshe shi koda kuwa baya so na domin wannan ka samu yan dagwai dagwai irinsa sun isheka rayuwa, matsalar daya ce abinda na hanga a tatare da shi a kan ki! Bai yi mini duba na second biyar ba dan ya bambance ni din a wani jinsi nake cikin halita? Yaya yannayin halitata take? Aa, ko gaisuwata bai amsa ba, ama irin yanda ya kura maki ido daga farar fuskarsa ta nemi zama ja na hango abinda kike so sai ya furta maki! BILKISU duniya yanzu ta zama ki yi da kanki tun kina gane yare, na rantse maki abinda ya hanna yayanki a laya mace hud'u inaga jiranki yake, da ba dan shi ba akoy mata fa a waje kamar su suka tsara halitar kansu, kuma ko muni ne da kai baka da ko sisi zaka samu wace burinta kai, bale Elhajin ya tara ga kyau ga sarauta, ki yi hakuri ina son tunasar da ke ne cewar ke ki furta ku fuskanci juna kafin wata ta k'wace maki abinki, ko shi wani ya k'wace masa kayarsa!"
Tana gama fad'a ta saki hannun Bilkisu dake tsaye tamkar mutun mutumi ta k'ara rage muryarta sosai ta ce" Ni ina son ki da k'awance K'anwata"
Bilkisu ta lumshe idanuwanta ta kuma bud'ewa a kanta tana kallonta har ta fita ta bar ma ta d'akin.
Wata wawuyar ajiyar zuciya ta kuma saukewa kafin ta mike tsaye ta shiga kai kawo.
Babu abinda ya fi tsaye mata a cikin zuciyarta irin *Du wanda yake tare da ku ya gane sai dai idan ya yi niyar makancewa a gabanku ne* sai kuma *jiran ki yake*.
Tana fita suka ci karro da Tati tsaye, ido hud'u suka yi da ita , duba irin na kamar ta fahimci abinda yake faruwa.
Hannunta tati ta damk'o da sauri ta ja ta suka fita waje.
Tsatsareta ta yi da ido tana kallonta, da yannayi na tuhuma ta ce" Haka kika karanta a tatare da su? Sunna son junan su? "
Aishat ta kure fuskar Tati da kallo hakan ya saka Tati yin dan murmushi tana dafe gaban goshinta ta ce" da mun tafka kuskure bamu sani ba, da mun cuci kanmu bamu sani ba, dan kuwa akoy wani duhu a tatare da su!"
Kuma wara idanuwanta ta yi a kan Tati tana kallonta, kallo irin na son karrin bayani a kan furucinta hakan ya saka tati sakar mata murmushi tana kallonta ta ce" Ma kika karanta be Aisha?"
Aisha ta ce" na karanci fannin kasuwanci, ina aiki a Sonibank yanzu haka na saku zaman nan ne dan ina cikin hutuna na wata guda."
Tati ta kuma yin murmushi ta ce da ita" Masha allah, je ki, tafi ki huta."
Juyawa aisha ta yi tana tafia tana dan waiwayen Tati domin kuwa yannayinta ne sam bai kwonta mata ba, aman sai bata nuna ba ta tafi ta koma wajen mahaifiyarta tana latsa wayarta.
Zainab ta girgiza kanta tana kara bin ki bangarensa da kallo.
Bata kuma bi ta kan kowa ba sai waya da ta yi ta bugawa , ko da dare ya yi Kader ne ya tuka su su uku suka je gannin marar lafia suka dawo, a cen suka baro HISHAM da ya hau aiki domin yana da wanda zai yiwa aiki.
Murmushi mahaifiyar Aisha ta yi tana kallon Tati, sai da ta rage muryarta sosai da yannayi na farin ciki ta ce" koda shekara talatin za'a jira dan ganin sakamako mai kyau, tsadar abin jiran ya fi k'arfin haka, ya cencenci hakan ko a kan waye Hajia."
Murmushi tati ta yi itama tana mai tunanin lamarin.
Kwonci tashi ba wuya a wajen Allah, bawa kan dora hakarkarinsa idan duhu ya shigo ya kwontar da kansa, wanin a tashi da shi wani kuwa a dauke shi, tafia na tafia , bawa na kara kusanta kansa da burika da mafarkai bayan dukan awar da zata karu , dukan minutes ko seconds yana mai rasa lokaci ne a cikin lokutansa...wani ya fahimci haka , hakan ya saka yake rayuwa tamkar ba zai mutu ba, sannan yake tuna mutuwa tamkar yanzu zata zo masa.
A haka Cikin baban gidan Professor HISHAM MOHAMMAD KARIBULLAH ke tafe.
Hisham mutun ne mai tsananin biyaya, uwa uba ga matar da ta raine shi, daga bakin lokacin da ta zubar da hawayenta sanadiyar share bakin dake cikin gidansu masu mahinmanci sai Hisham ya zubar da dukan matakan gabarsa yake tafiar da lamura a saukake a ganninsa, domin kuwa yakan gaishe da kowa sannan ya amsa gaisuwar kowa
Tsakaninsa da kanwarsa zan iya cewa shi ke tafia da kafafuwansa aman ragamar rayuwarsa, nutsuwarsa, tunaninsa na makale da baiwar Allahn nan, ko me yake zai iya tsayawa na dan second idan sunnanta ya fado a cikin zuciyarsa, takan yi masa karan tsaye a kowani lokaci, sannan takan zo masa a mafarkinsa
Ya yarda cewa *BILKISU ITA CE BURINSA, TANADINSA, MAFARKINSA* bai raina shekarunta ba, bai raina yannayin jikinta ba domin shi likita ne ya jima da sannin cewa mace Rijiya ce komai kankantarta
Kwaliyarta, iya saka kayanta, jan ajinta, kamshinta, girkinta, murmushinta sun ci makin da ya tanadarwa mai dakinsa
Bai taba gannin karfin abin dake zubar da shi kwonce rashin lafia irin ya hangeta da wani ko ya ji tana da wani a duniya ba. yanzun a shirye yake da tunkararta a kowani lokaci duda ya kasance mai nauyin baki da nauyin furuci. Duda bai san ta inda zai fara ba, bai san me zai ce da yar kanwarsa ba, duda ya san cewa furucinsa abin sauraro ne a kunnayenta, ita din mai amsa masa ce, mai sauraronsa ce, mai yi masa biyaya ce.
Murmushi ya yi yana murza hannunsa saman kafet sakamakon jin yanda baki daya yannayin tunaninsa na wannan lokacin ke masa dadi.
Kwana biyu kawai, kwana biyu ya rage ya kirayeta, ko ya tarda ita, ya fita da ita wajen shan ice cream ko ya ritsata a kofar makaranta, ya tareta a cikin falon Mama ko ya tiso k'eyarta a tsakar gida, ya barta sai tana aiki ya furta mata ko ya barta sai tana tilawa?
Wani murmushin ya yi yana mai kai dubansa wajen agogo, bai fi sauran yan awani ba ya shigar da tsohon, yana fatan Allah ya bashi sa'a idan da sauran kwanakin tsohon aikinsu ya yi kyau a fitar da shi lafia, yana adu'ar cin nasarar aikin nan domin ana gamawa su Tati zasu juya bakin aikinsu, saga nan filin zai dawo masa irin na da, daga shi sai mamansa sai BILKISU.
A hankali ya daga kansa dan duba mai son shigowa bayan an tsaya an yi knowing.
Siririyar muryarta ce ta biyo baya cikin salama.
A hankali ta kuma yin wata salamar tana duban k'ofar d'akin.
Sai da ya kimtsa yannayin zamansa, ya had'e k'afafuwansa ya gyara zaman rigar dake jikinsa sannan ya amsa salamarta ta yada zata ji shi.
Tun da ta shigo ya kura mata ido kamar yanda ya saba, kafin ma ta kai zaune ya bud'i a sanyaye ya ce" Me ke damun ki?"
Dago dubanta ta yi ta sauke a saman fuskarsa, a hankali ta lumshe idannuwanta muryarta ciki ciki ta ce" Barka da yamaci yaya."
Bai iya amsa gaisuwar tata ba sai kara kura mata ido da ya yi a hankali ya ce" Baki da lafia ne? Me akai maki? A makaranta aka taba ki? Ko mama ce?"
Baki daya sai ta ringa jin sanyi sanyi a cikin zuciyarta, kuma dubansa ta yi ta raunana muryarta ta yi kwal kwal da idannuwanta ta ce" Nima ban sani ba, ka ga yaya tun jiya nake jin kamar bani da lafia, kamar lafiata kalau, haka na ringa jin faduwar gaba da ciwon kai."
Idannuwansa ya lumshe yana jin ba dadi yannayin da ta ce take ji a jikinta, a hankali ya mika mata hannu yana kallonta da kulawa.
Mikewa ta yi ta d'ora hannunta a cikin nasa tana mai rintse ido dan ta tabata abinda zata ji a jikinta mai girma ne.
Hakan take kasancewa a bangarensa shi yasa baya son ko da wasa kusantar jikinsa da nata.
Zaunar da ita ya yi face dinsa yana kallonta.
A hankali ya kai hannunsa wajen wuyanta ya dan taba sai kuma ya janye ya kai wajen idannuwanta ya dan duduba kafin ya kara kura mata ido
Ciwon kan da mutuwar jikin ba na wani abu bane na menstru d'inta ne dake hanya domin ya tabata yau komai dare yana iya zuwar mata, faduwar gaban da ta ce tana yi shine damuwarsa.
A hankali ya ce" An yi maku wata jarabawa ne baki yi aiki ba kike tsoron sakamako? "
Da sauri ta girgiza kanta tana kallonsa.
A sanyayen dai ya kuma fadin " ko fada kika yi da laila? Ko wani malamin aka tsokano min?"
Irin yanda ya karashe yana dage mata gira guda yana murmushi sai ta samu kanta da sakar masa murmushi har tana rufe fuskarta ta girgiza kanta watau ko d'aya.
Hannunta ya kuma rikowa yana kallonta , gabansa na faduwa da abinda zai tambayeta ya ce" Kin ga ni kuwa idan ina yawan faduwar gaba abinda nake so ke shirin bata min rai, ko saurayi kika yi ya bata maki rai?"
Da sauri ya d'ago ta kafe fuskarsa da kallo
*Abinda yake so?* kennan yayanta yana da budurwa? Abinda yake so? Mutun ko aikinsa?
Gaba d'aya sai ta ji jikinta ya fara d'aukan zafi mai sunnan zafi.
Shima dake kallonta sai jikinsa ya fara tauri daga laushi, a kausashe ya ce" Baki bani amsa ba, saurayi kika yi?"
A hankali ta sada kanta hawaye suka cika idanuwanta.
Dago da dubanta ta yi ta sauke a kansa a karro na ba adadi kafin ta girgiza masa kai tana kallonsa.
Kwarai ta ga ya saki ajiyar zuciya sannan ya sakar mata murmushi ya ce" ko yawaita innalilahi wa'ina ilaihi raj'une, ki saka a ranki ko menene Allah ya kawo maki shi da sauki, ki sakawa zuciyarki alkhairi ne koma meye yan matana."
Murmushi ne ya kwace mata a lokaci daya ta lalubi bacin ranta ta rasa dalilin yanda yau wai itace zaune gaban yayanta har yake kokarin kamar ya tsokaneta? Kamar yana zolayarta? Kamar yana mata rarashi cikin lalama ba da fada ko hayaniya ko tirsasawa ba?
Kawai sai ta nemi du wani bacin rai da mutuwar jiki da tashin hankalinya ta rasa, lokaci daya ta ringa haskowa zuciyarta dama a yannayin nan da suke ciki yannayi ne da suka gama aminta da abinda ke cikin zuk'atansu.
π
[7/24, 10:18 AM] BAK'A CE: πΎπΎπΎπΎπΎπΎπΎπΎπΎπΎ
*DUK NISAN JIFA*
_(K'asa zai dawo)_
πΎπΎπΎπΎπΎπΎπΎπΎπΎπΎ
_RUBUTAWA_
*SAJIDA*
*SADAUKARWA*
*GA*
*MASOYA NA*
π«β¨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*π
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_π€
β *[ T.M.N.A]* β πποΈ
https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/
_Bismillahir rahamanir rahim_
14
Farkar da ita ya yi daga dogon tunani da farin cikin da ta afka ta hanyar tunatar da ita cewar ta tashi ta tafi b'angaren su Mama domin baya tab'a yarda daga shi sai ita su kwashe lokuta masu tsayi a tare.
Sai ta ji kamar ta k'wala ihu ta ce da shi aa, ita ba zata koma ba har sai dare ya yi sosai tana ribantuwa da kalamansa da furucinsa da murmushinsa.
A hankali ta mik'e tsaye, mik'ewar ya yi shima ya k'arasa wajen table d'in dake tsakiyar falonsa.
Duk'awa ya yi ya ciro magani ya k'araso inda take tsaye, hannunta ya bud'a ya saka mata yana kallonta ya ce "zuwa an jima idan ya zo ki sha daidai shan ki kar na zo dubawa na ga baki sha ba fa."
Gaba daya ji ta yi kamar zata zura da gudu, wata irin kunyarsa mai tsanani ce ta lulubeta har ta ringa sinne kanta tana kawar da kanta tana d'an janyewa daga gabansa irin umarnin ta tafi take jira ya bata aman ya k'i yin hakan sai kara bin dukan motsinta yake da kallo yana sakin murmushi.
A hankali ya ce" Tafi... "
Da sauri ta d'aga k'afarta ta juya ta fice a b'angaren nasa.
Tana fitowa suka ci karo da Kader wanda ya zo dan kawo masa takardu.
Kallonta ya yi na yan seconds, irin yanda take fara'a ya saka shi jin dad'i a ransa.
Bata tsaya ta kula shi ba ta yi ciki da dan gudunta.
Kader kuwa ya shige da salama, hangam ya yi da bakinsa yana kallon yanda HISHAM ke murmushi yana dafe da daidai kirjinsa.
Kansa ya girgiza ya karasa ya ajiye takardun sannan ya ce" Ina tausaya mata, tsohon gwabron nan anya zaka yi hakuri da yar jaririyar nan?"
Da sauri ya kai dubansa wajen da yake jin maganar, hade murmushin ya yi ya ce" kai a kan me zaka shigo min daki ba salama hotel ne? Ko sai ka tardo abinda ba shi ba kuma ka ce ba'a kyauta maka ba?"
Kader ya yatsine bakinsa ya waiwaiga ya kara waiwaigawa ya ce" Ban ga kalabin matarka ba bale na ce kar na tardoka a hanyar keta gajimare, hasalima kai din mugun matsoraci ne da ya kasa fuskantar yar ficiciyar kanwarka da maganat dake iya tsinke maka numfashi, sai wani cicijewa a gabanta kuma ka je office ka kama haki sai mun dadane."
Murmushi ya yi yana shafa tarin gashin kansa zuwa sajensa da gemunsa ya zauna ya amshi takardun sannan ya kalli Kader ya ce" Ko ka tashi ka bara min dakina yanzu yanzu ko in tashi in dakaka da kasa sai ka ware matsoraci tsakanin ni da kai!"
Mikewa Kader ya yi yana tabe bakinsa ya nufi k'ofa, sai da ya bude ya juyo ya ce" AI tsoro kala daban daban ne, ni nan na yarda ina tsoronka, to ba dole na ji tsoronka ba dan jaraba kana kara mulmulewa uwa dan dambe, ga shegen karfi ga tsayi? Aman ni nan da ka gani a lokaci daya sai na ce da yan mata hudu ina son su, kuma su yarda da furucina harma su bani amsar eh suma sunna so na!, kai kuwa shekara goma sha tara ka dauka kana fama da kalmar nan har yau ka kasa fada malan!"
Daria ya yi yana kallon Kader ya ce" Baka sani ba, kalmar nan koda kuwa tunaninka haka ne, watau hasashenka hakan ne, idan har na furta ta ba irin yanda zaka furtata wa yan mata hudu bane, ni ba zan iya rarabata ba dan mai ita ta gama kwace abinta, zan bayana mata ne daga ni sai ita, kuma idan ta kuskura ta dayki rawar kai ta bani amsa tana rangadadi da kai gaskiya akoy matsala, domin kuwa idan har ta wani bani amsar tambayata a kan lokacin da nai mata ita zamu samu matsala ni da ita, ba zai yiwu bata jani a kasa ba, idan har ta ki jana a kas ta wani bani amsa nan take cewar itama tana so na akoy matsala! Domin kuwa hakan na iya nuna min ta saba baiwa wani irin amsar, hakan na iya saka min tashin hankali marar musaltuwa, zan iya kumewa da takaici har sai kun dadane ni! Kafin nan bara na ci yan gidan ku!"
Mikewa ya yi tsaye hakan ya saka Kader ficewa a guje ya fada mota ya tayar ya yi ribas.
Murmushi ya ringa yi yana girgiza kansa, a kasan zuciyarsa yana ayana" idan kika ji sakon zuciyata ya dace na ga tsoro, mamaki, firgici a fuskarki, ina son na ji muryarki na rawa sannan ki gudu ki barni nan tsaye, ida har kika min getsetse a gabana kika bani amsa zamu mutu ne daga ni har ke har dan iskan da ya lalata min tunaninki!"
*Washe gari* tun k'arfe shida suke asibiti
Sai kusan karfe goma Mama ta koma gida dan dora masu girki baki d'ayansu.
Karfe goma da yan mintuna aka fitar da marar lafian aka shigar da shi dakin kula da dukan yannayinsa
Kamar yanda ya saba yana tafe masu raka shi office dinsa na zagaye da shi cikinsu harda Kader dake lure da dukan motsin mai motsin dake kusanta kansa da shi
Wani irin dadi da farin ciki da wani irin girma da tsuma jiminta yake a lokacind a suke tsaitsaye sunna kallo aka raka shi aka shige da shi cikin office dinsa
Hannunta Hajia matar DG ta kama tana kallonta