Showing 111001 words to 114000 words out of 180809 words
a ji warim bakin nata shi yasa take ta kare fuskarta duda ba maganar ta yi ba.
Tati ta dan janyota jikinta a hankali ta dorata ta dauko kofin shayin nan tana dan juya shi dan ya rage zafin da yake da shi kafin ta kafa mata a hankali tana kallonta.
Da kyar Bilkisu ta iya surba du kuwa da irin yanda take son shan a ranta domin so take ta samu kwarin da zata iya zuwa wajen Mama.
A sanyaye Tati ta ce" Ki daina kukan nan da damuwa kin ji? Ki yi ta adu'a auntu zata sauko, cen dama bata iya fushi ba, shi yasa du abina bana so ta yi fushi, kin ga yanzun na kureta ta dauki fuahin da kowa kuma ina gudun sai ta hora kowa, aman na san ba zata raba ki da yayanki ba."
A hankali Bilkisu ta dago dara daran idannuwanta da suka dauki kalar ja suka kumbura saboda kuka da firgici tana kallonta, rabani da yayana abinda ta fara maimaitawa kanta kennan, waye ya raba ni da yayana? Ta kuma tambayar kanta, a hankali ta dan girgiza kan nata tana murmushin da iyakarsa kan leb'enta.
Muryarta a sanyaye ta ce" Inata, Uwa ce mama, tunda ba umarnin da ya sabawa musulinci bane zan yi biyaya, Walahi zan yi biyaya koda hakan shine sanadiyar barina duniya baki daya, Innata yau ina yar uwata Mami? Tabas Mami ta ci ribar biyaya ga iyaye domin Mahaifiyarta da mahaifinta asalin hawayen rabuwa da ita suka zubar kafin su cire da yi mata shinfida a makwoncinta, nu Bilkisu na hakura da yayana har abadan abada, daga jiya zuwa yau na yakice yayana a kundin tarihina, Allah shine zai dafa min na bar rayuwarsu kwata kwata in sha Allah "...tana fad'a ne idanuwanta a soye, tana bud'e su da k'yar, kalamanta da d'an k'arfi domin daga zuciyarta take k'wato su tana harhad'a su, hakan ya sa suke fita da k'arfin da ya saka Tati rintse idanuwanta, anya zata ci gaba da zubawa zuciyarta abubuwa na emotion haka? Ba zasu illatar da ita ba kuwa?
*Masha'Allah*
[7/24, 10:19 AM] BAK'A CE: ๐พ๐พ๐พ๐พ๐พ๐พ๐พ๐พ๐พ๐พ
*DUK NISAN JIFA*
_(K'asa zai dawo)_
๐พ๐พ๐พ๐พ๐พ๐พ๐พ๐พ๐พ๐พ
_RUBUTAWA_
*SAJIDA*
*SADAUKARWA*
*GA*
*MASOYA NA*
๐ซโจ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*๐
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_๐ค
โ *[ T.M.N.A]* โ ๐๐๏ธ
https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/
_Bismillahir rahamanir rahim_
40
Assalamu Alaikum
Masoyanmu da fatan kuna lafiya.
Muna miko maku godia da fatan alkhairi masu matukar yawa a yadda kuka nuna mana kara da kauna wajen siyan littafinmu na kudi.
Alal hakika munji dadi kuma mun gode sosai Allah ya saka da alkhairi ya kara budi.
Ina kuma kara kira ga masoyana wadanda basu siya ba dasu garzayo su siya domin muhimman darussa rayuwa, ilmantarwa da nishadantarwa dake cikin littafin. Dukkan wanda yaji taken littafin na *AURE YAKIN MATA* yasan littafi ne mai cike da ilmantarwa da bude ido akan irin rayuwar zaman auren da muke a zamanin yanzu don haka babu danasani a siyan littafin.
Yadda kuke siyan littafin yana kara mun kwarin guiwa wajen yi maku typing din littafina na *KOMIN NISAN JIFA* ina fatan zaku cigaba da siye don in samu kwarin guiwar yi maku typing din littafina na kyauta akan kari ba tare da bata lokaci ba.
Na yadda daku na aminta da irin kaunar da kuke mun, nasan kuma zaku siya littafinmu mai take *AURE YAKIN MATA*
*INA SONKU SOSAI INA ALFAHARI DA KASANCEWA A CIKIN DUNIYARKU.*
Ga mai bukatar wannan littafi *Farashin mai sauki ne* naira dari uku (300) kacal ga yan Nigeria, yan Niger kuma dala dari ne (500)๐ zaka samu wannan littafi mai dubbin darussa a cikinsa.
_Domin tura kudin siyan littafin ga yan Nigeria sai a tura ta wannan account number din *2377403479* Khadija Umar Abubakar. Zenith Bank. Kuma akwai damar tura kati ta wannan lambar *081-686-594-14* IDAN KA YI TRANSFERT SAI KA TURA SHAIDA TA WANNAN NUMBER +227 93 81 16 18._
_'Yan Niger kuma sai ku tura katin MOOV ko Airtel ta dala dari watau 500 francs ta wannan lambar *+277- 94-98-56-52*_
Na yadda daku, na aminta da irin kaunar da kuke mun don hakan ina da yakinin cewa zaku siya don nuna mun kalar soyayya da kaunar da kuke mun da littafaina๐ฅฐ
A yau gata zaune gaban yar yarinya karama tana fada mata maganar da take jin kamar da ita ake, ita fa kwata kwata ji take kamar da ita Billy take, kamar tana nuna mata mahinmancin biyaya ga iyaye ne, ya Allah, kwarai wani irin girman yarinyar da mamakinta ne suka darsun mata a zuciyarta, koda kuwa ta kasance mai biyaya ce to fa lalle tana cikin daidaikun yaren zamanin dake iya take soyayar da suke yiwa namiji su kawar da kai komai tsananinta, ko ita da take uwa a gareta ta tabata da ace itace ke cikin irin halin da take ciki da ta murje ido ta nuna aa ita fa a bata abinda take so ko ran kowa ya baci
Jikinta a sanyaye ta buda wajen kayan Bilkisun da ta nuna mata akoy maganinta ta balo mata da ruwa ta kuma bata ta sha sannan ta kamata ta kaita saman gadonta
Muryarta a sanyaye ta ce" ki huta, Allah zai sanyaya mana baki daya "
Bilkisu ta lumshe idannuwanta da take jin ba zasu hade da kyau su rufe da kyau ba a hankali ta shiga salatin annabi tana karawa idannuwanta lumshe, yi take yi daga cen kasan zuciyarta har ta budi bakinta tana ta yi ba kakautawa, a hankali ta ringa jin zuciyarta na rage mata nauyi har ta ji ta fara yinsa a rarabe rarabe , sannu a hankali gaba daya ta dauke sakamakon nanauyan bacin da ya fizgeta ta tafi bacinta
Tati dake tsaye tun dazun tana kallonta hannayenta rungume a kirjinta ta sauke ajiyar zuciya ta juya a hankali ta fita a dakin zuciyarta na kara tsintsinkewa
Hango shi kawai ta yi ya shige dakin mamansa hakan ya saka gabanta bugawa
Tsoronta daya, kar shima yau lamarin mamansa ya shafe shi, shin yaya zasu kwashe? Shin me zai ji? Me zai same shi? Yaya zai dauki abin? Wa zai tuhuma da irim duban nan nasa?
Tunanin mafita a gareta ta fara yi, shin ta gudu dakinta ne ko ta tsaya har ya fito ya sauke mata tashin hankalin a kanta? Shin yaya zai amshi sakon nan na mamansa? ?????????????
Yana shiga dakin mama da salama a bakinsa ya gantsa tsaye tana ninke kayanta da ta ciro sakamakon rashin abin yi ga tunani na neman tarwatsa mata kwakwaluwarta
Ido hudu suka yi ita da shi, baya shirya sakar masa da murmushi ba sai da ta ga gaba daya ya sakar mata da murmushi sannan ya nufota da yannayi na zumudi da soyaya irin ta uwa da d'a
Tsoro, kunya, fargaba, suka tarun mata suka dirar mata lokaci daya, ta rasa ta ina zata fara, da me zata fara
HISHAM na karasawa kamar yanda ya saba gaisheta sai da ya duka ya gaisheta sannan ya mike ya ajiye wayoyinsa nan gefe ya shiga ninke kayan da take ninkewa yana kallon yannayinta, domin a duniya idan matar nan na cikin farin ciki ko akasinsa daga ya kaleta yake ganewa
Yana ninkewar tana dan taya shi ta ce" Kai da zaka je wajen aiki ka ajiye ninkin nan Hisham "
Hisham ya yi murmushi a sanyaye ya ce" To koma wani irin aiki ne a bayan na mamana yake, "
Sai kuma ya kara kure fuskarta da duba a hankali ya ce" Me ke damun mamana ne? "
Mama sai da ta dan dakata ta kale shi, sai kuma ta jara sada kanta kasa
Ajiyar zuciya ta sauke kafin ta nemi waje ta zauna dan gabatar da shawarar da ta gama yankewa kanta ta inda zata biyo masa
Gefenta ta nuna masa kan ya zauna, hakan ya saka da sauri ya zauna yana kallonta
Mama ta mika hannunta a hankali ta kamo nasa dake ajiye a kan katifar ta sanyayar da muryarta a hankali ta ce" HISHAM yaushe zaka tare da matarka a gidanku ne? "
Hisham ya dago yana kara kallon fuskarta aman bai ce komai ba sai ya kara sada kansa kasa
A hankali ta ce" Hakkinta na kanka, Hisham ba iya haka bane hakkin aure, hakkin aure yana da yawa ciki harda kula da matarka ta yada zata ji dadin zama da kai , Hisham aure daraja ne da shi, yana da girman gaske, yana tafe da abubuwa masu adalci da daukaka, Hisham ta amsa sunnan matarka, harma ta je dakinka shin me zai hanna ka kilaceta kamar yanda kowace macen aure ke kilace a gefen mijinta sai dai idan wani baban lamari ya taso ya hanna hakan?, ka dube ni nan, shin so kake Allah ya tsayar da mu duka a gabansa kan hakkin yarinyar nan ne ko me? "
Hisham ya girgiza kansa yana kara sada kansa cike da kunyar mamansa da kuma jin nauyinta a ransa
Mama ta kuma dago habarsa ta ce" Ina baka umarnin a yau yau ka fara kilace matarka, idanma ni zan daukar maka ita na kaita ka bamu dama mu sadata da dakinta ka ji? "
Hisham ya dan gyada kansa a sanyayen dai sannan bai furta komai a kan maganar ba
Mama ta ja numfashinta domin yanzun ne zata fara maganar da take kayar mata da gaba, hakan ya saka ta kasa kallon yannayin fuskarsa koma wani abin da zai sakata dasa aya a maganarta tun kafin ta kai karshe ta ce" HISHAM sai maganar yarinyar cen, har yanzu na ga ka yi shiru a kan lamarin yarinyar cen, Hisham harma ka biye mata ka sakata koyon kwaliyar nan, Hisham har ta fara shigar nan ta fita waje bayan kwana biyu ta daina kwata kwata, idan da na yi shiru a matsayin budurwa take, a yanzu kuwa sunnan yarinyar nan bazawara!"
Yansun shi yake kallon fuskarta ita kuwa ta cire nata duban a kansa hakan ya saka shi gannin tsabar tashin hankali da gaskiya a furucinta
Mama ta dora da fadin" Hisham, ku biyu nan kawai, kune damuwata, kune rashin nutsuwata, kune ke iya tarwatsa kwonciyar hankalina, Hisham ka ga a zaunen nan da nake na gama yankewa kanwarka magana daya tak idan har bata fitar da miji nan da sati daya ba zan mugun saba mata, Hisham ni da kaina zan samu mahaifinta na masa maganar yarinyar nan, miji nake so ya zaba mata a matsayinsa na mahaifi a gareta ya daura mata aure ta tare a dakin mijinta, kaima ka dauki matarka ka je ka yi zamanka da matarka ko hankalina zai kwonta, sam sam ba zan iya ci gaba da walwala da irin tunanin abinda ke faruwa a kan Bilkisu ba!"
Idan ya fahimta da kyau maganar mamansa, nuninta Billy ta tare da wani zabin na mahaifinta shima ya tare da Aisha?
A hankali ya girgiza kansa dan ya karyata ya kara gyara zamansa yana kallonta ya ce" Mama, wani abin ke faruwa ne da Bilky?, wani abu yake faruwa da ita ban sani ba?, mama ba zamu barta ta gama karatunta ba duka duka shekararta nawa? Auren cen da aka daura mata ba kowa ya san da shi ba bale a ce har an mata aure ta fito, yarinyar da ko tarewa bata yi bale a mata wani sharrin?"
Mama ta yi murmushi tana karfafawa kanta gwuiwa ta ce" Ai damuwar kennan, rashin tarewar har auren ya mutu daga daura shi, sai kuma jin mutun daya dake zaga gari a lokacin da ba'a shiryawa hakan ba, Hisham kar ka yi mamakin a yanzu du wanda ya san Bilkisu ya san an daura mata aure har an saketa .....menene tambayar da mutane zasu ringa dorawa a kan dalilin sakin yarinya?, shin meye ya sa daurin auren ko tarewa bata yi da miji ba ya saketa? Wani mumunan hali ne da ita? Ko bata da lafia?"
Da sauro ya kara kallon mama hakan ya saka ta gyada kanta tana kara tabatar masa da yannayin idannuwanta ta ce" Babu abinda ba za'a ce ba, duniyar? Ba abinda ba za'a fada ba, haka kuma mutanen da basu san bama da maganar auren sunna iya tsara amsar da ta masu dadi daidai da irin mu'amalarsu da ita su bada, ba wanda bashi da mai juran ya ji lalacewarsa a duniya ba wani abu ka tsare masa ba kawai kai din ne baka yi masa ba, idan magana ta zaga kunnensa irinsa ba sai ya ji ba'asin sakinka ba, daga inda yake zaune zai ce to dama, me ake jira da wance?.....ta haka zai lauya tasa kalar karyar ya zarga, ba yanzu nake dubi ba, aa, magana bata birnuwa kwata kwata, tsiro take ta yanda bata yado sai an tashi abin arziki, ire iren haka sai ka ga yarinyar tun tana ganiyar yarintarta har ta kai wajen da tarmamuwarta zata disashe, Hisham Allah ya kiyaye idan tun akoy maneman har ya zamana an rasa sai ita zata nema yaya zamu yi da ita? A lokacin da y'a mace ta ringa samun manema ta kowani bangare ake gagawar wanketa a mikata, idan aka tsaya tsaye tsaye ana samun matsala"
HISHAM da kansa ke kasa yanzun a hankali ya ji bakinsa na fadin" To ni ai ba wannan yake gabana ba, koma me za'ace a kanta ba shine a gabana ba mama"
Mama ta yi gagawar tare maganar dan bata so ko da ya wasa ya maimaita mata kalmar cen, ta ce" AI KAI UBA NE, KAI ABANTA NE, KAI DAMA KO ME ZA'ACE DA KANWARKA TA INA ZAI HANNAKA GANNIN MUTUNCINTA? AMAN MIJIN DA ZAKA MIKAWA ITA, SHI NA FI TSORO, HISHAM BABAN WA UBA NE SHI YASA NAKE SO TUN WURI KA FITA DA NIYAR SAMA MATA MIJI WANDA KA GA YANA DA TARBIYA YA AMSHETA DA ZUCIYA DAYA TA TAFI DAKINTA ITAMA NA HUTA"
da sauri ya kuma juyowa, tun maganarsu ta farko hannunsa ke cikin na mama har yanzun kuwa
Kara tsatsareta ya yi da idannuwansa irin yanda gaba daya maganarta ba tsokana bane ya saka shi jin zai halaka
A hankali ya kara rike hannayenta yana kallonta, sai ya samu kansa da sada kansa yana jin irin yanda zuciyarsa ke wani irin tsalen albarka tana dokawa
A sanyaye ya kara rike hannayenta muryarsa cen cikin makoshinsa ya ce" Mamana, Ni din ina son Bilkisu, kuma ban damu da du wani abinda wani zai ce a kan billyna domin rainona ce, Mamana, idan yanzun kike so a yi da ni da ita sai a yi, ko yau yau sai a daura aurenmu mamana"
Mama ta rintse idannuwanta da kyar ta iya kakaro murmushin dole sannan ta kara gyara zamanta tana kallonsa ta ce" Maganar Zainab tashi ta yi ne?, ko so kake ka ce kin yar yarinyar da aka daura maku aure jiya jiya ake son a mata kishiya irin ta son kai? Bayanma wannan itama Bilkisun a jiya da ina mata fada na ce ko dai wani abin ke tsalaninta da kai sai cewa ta yi aa ina ba wani abu ko da wasa ita bata taba kawo hakan a tsakaninku ba, domin kai uba ne a wajenta"
Harta da lebensa rawa yake, sai ya ganshi wani jibgege kawai sakamakon maganar mama, UBA? a hankali ya dago dubansa a sanyaye ya ce" bayan nonon da muka sha tare yanzun kuma Uba ne ni a duniyar Billy? "
Irin maganar da ya yi gaba daya sai mama ta tsinci kanta da kikifta ido, tana kallonsa ta ce" Me kake nufi? "
A hankali ya girgiza kansa sannan ya duka a gaban mama gaba dayansa
Muryarsa a sanyaye ya ce" Mamana, ke kin san na rayu da soyayarta a zuciyata, kuma na san ke mai sona ce, ban san menene dalilinki na biyewa son zuciyar kanwarki, ban san me yasa har kike goyawa wannan lamari baya ba, mama hasalima ban taba dubanta ido da ido na furta mata kalmar so ba, sai kakarewa nake da dukan karfina kan kar wanda ya yi kokarin furta mata hakan, mama idan kika ce ta ce ni babanta ne abin ya min tsauri da yawa, abin ya min girman gaske mamana, ban san idan soyayar billy alkhairi ce a rayuwata ko akasinsa ba, abinda na sani shine nakan duka kaina wajen ibadata na fadawa Allah idan alkhairina ita ce ya nuna min, ya tabatar min, mamana gaba daya sai nake gannin kema yanzum bayan kin giyawa maganar da kika san ba haka bace baya kuma har kin yarda wai ni Hisham kamar baba nake a wajen Billy, mamana ita din ce ta ce bata so na? Me na yi? Mamana me na aikata mai muni haka? Dan Allah ki yafe min kar laifin kowa ya shafi yaronki, mamana ki yafe min kar ki yi anfani da karfin ikon da Allah ya baki na isa da kika yi kan saka mu ko hanna mu, mu bi umarni a rayuwarmu , mama koma menene Allah shi zai warware, mama aman ba zaki sasauta min ba? Na san cewa Allah ba zai dora min abinda ba zan iya dauka ba, aman ban san ta inda zan iya daukan rabani da ita ba, mama shin ba zan samu sasauci a wannan umarni mai shirin dauke min dukan wani kuzarina ba? "
Mama ta ringa sauke ajiyar zuciya wata na korar wata a hankali ta mike da hannayensa dake cikin nata kafin ta raba rikon ta shiga kwasar kayan muryarta na neman yin rawa ta ce" Ka tafi Hisham, ka tashi ka tashi abinda na yanke kennan!"
Hisham ya lumshe idannuwansa juwa na neman maka shi da kasa ya mike a hankali ya iya ciro kalamai kamar haka" A huta lafia "
Yana gama fada ya fita a dakin inda mama ta ja da sauri ta tsaya da jera kayan ta sada