Showing 123001 words to 126000 words out of 180809 words
wando irin na lalausan yadin nan da ake yin irin kaya dinkin turawan nan na mai yar ciki da ta sama da nekti, sai dai ita din ce kawai sai wata riga baka itama mai dan tsaba tsaba sai farar rigar likitoci wace take saman kayan nasa fara kar kar da ita a goge tas hakama sai daukan ido take tsabar tsaftar mai ita
Ginanen jikinsa ya baiwa kayan damar haskawa a jikinsa, farar fatar jikinsa ta dauki kalar bakin nan da farar rigar likitoci wanda damatsunan hannunsa du irin yadda suke cikin rigar nan ta likitoci ana iya gannun girmansu da cikarsu taf da su
Kanshin turaransa yana bude motar dama shi ya fara yin salama kafin ya fito din, zuwa yanzu da yake tsaye idannuwansa sanye da bakin gilas irin bakin nan mai madubi blu wanda ya rufe kalar kwayar idon hakan ya rufe ainahin yannayin da yake ciki
Fuskarsa a hade take ba alamun ya taba sannin kalmar daria a duniyarsa
A hankali ya sada kansa da dubansa a kan mamansa dake jan hannunsa kafin ta ja ta tsaya da sauri ta shiga masa bayanan da ciki abinda ya gane kadan ne , shima kawai ya gane cewar tati ta suma ne
Turus mama ta yi tana kallonsa ta ce" HISHAM, ya kake kallona cikin wannan gilashin ina maka bayani ka zo mu je ka kama min mu yi mata nasiha wai jinninta na hawa ina take so na saka raina ne? "
A hankali ya rike hannunta sannan ya shiga tafia da ita
Sai da ya kaita wajen zaman mutane ya zaunar da ita a hankali ya dan dafa bayan hannun nata sannan ya juya ya nufi cen cikin wajen likitoci
A hankali Bilkisu ta zauna itama a saman abin zama, kafarta ta ziro daga cikin zumbulelen hijab dinta wace ke sanye cikin baki dogon lalausan wandonta irin wanda ake kira da sigarette damamen nan daga kasa aman kasancewar mai jayuwa ne sai ta saka hannunta ta ja kafar damar sama kadan hakan ya ba saman kafarta damar dan fitowa kadan
A hankali ta dora kafa daya kan daya ta shiga dan balancing dinta sannan ta maida kanta baya ta jinginar da jikon garun wajen ta lumshe kyawawan idannuwanta da suka dan kumbura kadan ta afka a kogin tunani
Ya dauki dan lokaci a ciki kafin ya fito shi da wasu likitoci uku, dayan docter ne biyun kuwa infirmier ne
Da yannayin farin ciki a fuskar likitan ya kama hannun Hisham ya ce" Mun gode sosai Professor, Allah ya biya in sha Allah hajia na zuwa zamu kai mata wannan albishir Allah ya baka ikon zuwa muma kana duba mararsa lafianmu a nan"
Murmushi ya masa mai kyau wanda yanzun ba bakin gilas din a idannuwansa sannan ya nufo wajen mama dake zaune a nan din Aba kuwa na nesa da ita
Sai a lokacin ya dan rage tsayinsa yana gaishe da Aba, sannan ya zauna kusa da mama ya kamo hannunta cikin nasa ya rike a sanyaye ya ce" Mama yanzun sai ki ringa saurin kuka bayan kin san bana so"
Mama ta sauke ajiyar zuciya a sanyaye ta ce" Yaya jikinta? Ta tsoratani Hisham yaya zan fuskanceta na mata bayanin tambayoyinta? "
A sanyaye ya ce" Da sauki sosai, ta yi baci mama"
Sai kuma ya dan daga dubansa yana kallon wajen kofar da ma'aikatan ke ciki ya ki ba mama amsa a kan tambayar da ta masa na shin ta yaya zata bata amsoshinta, sarai ya san wasu amsoshi tati ke so domin a lokacin da ya shiga tana kukan ne kuma ta masa tambayoyin ne, aman sai ya share domin idan zai ba mama amsa zai ce da ita ne ki bata amsa kai tsaye shin kina da wata damar bata amsa ne bayan ta kai tsayen?, sai dai ya kyaleta dan baya son ranta ya zo yana baci saboda shi
Stil da yannayin sanyin da ya riski jikinsa a yau ya ce" Yaya aka yi kuka zo nan? Ko nisa cen ta yi sosai? "
Mama ta girgiza kanta ta kai dubanta wajen da Bilkisu ke zaune ta ce" Ga ja'irar da ta kawo mu nan ban san dalili ba "
Sai a lokacin ya kaleta, ya mata duba na kirki duda jikinsa na shaida masa cewar tana wajen tun da suka sako hancin motarsu aman sai ya share ya dake ya basar du a zuwansa na ya idasa yakiceta daga rayuwarsa kwata kwata dan ya gama yarda cewar mama bata son tarayarsu shi kuwa zai mata biyaya
Kasa kasa ya kare yiwa yannayinta kallo kafin ya cire dubansa a kanta ya lumshe idannuwansa
Sun dan dauki kamar minti biyar ya ji mama na fadin" Rikemu za'a yi ne? Idan rikemu ne na koma gida na harhado abubuwan bukata Hisham? "
Hisham ya kaleta kallo irin na girmamata har cikin zuciyarsa, lalle ana cewa tsakanin yan uwa ba'a shiga, shi shine kat, koda yake soyayar mamansa ce ta fito fili ita dayar ko zata iya duban maman bayan dukan abubuwan son kai da rashin adalci a bayane da ta aikata mata idan a kanta ne ya faru?
Kansa ya dan girgiza ya ce" aa "
Sai kuma ya kara yin shiru
Aba ne ya fara mikewa ya ce" Tunda da sauki bara na koma ga duhun magariba na karatowa "
Hisham ya mike da sauri yana kallon Aba ya ce" Aba tafia zaku yi? To bara kader ya mayar da ku gida "
Aba ya ce" Aa aa yaron nan ba za'ayi haka ba, ka ga shi din ba dorebanka bane? Kai kuwa baka da wasu aike daga nan har anguwarmu akoy nisa ga cen yan sahu da yawa sai su kaini mana"
Bilkisu da ta riga ta mike tun da Aba ya mike ne ta dan tabe bakinta gannin sunna ta gardama Hisham na fadin aa ya yi hakuri a kaishi gifa ba wani takura, shi kuwa ya dage irin kar ya shiga motar sirikin nan ta dan rage muryarta ta ce" Ma zan kai Abana gida "
Mama ta kaleta ta dan tabe baki tana kara kallonta, ita ta kulama kamar Bilkisu bata yi kukan sukar yar uwarta ba fa? , wai wani abana to da wa ya ce nasa ne? Mama ta kara tabe baki da haushi haushi ta cira kai gefe
Bilkisu ta yi murmushi ta juya ta nufi hanyar kofa bayan ta furta" Aba mu me"
Da ido du suka bita, hijab din lale yana da tsayi aman irin mai lafewar nan ne a jikin mutun, ga wando a kasa wanda tsaf ana gane wando ne wanda ya fitar da tsarin halitarta tana rausaya cikinsa ta yi waje
Sai kuma suka kalli junna Aba da Hisham, Aba ya yi dan murmushi ya ce" to ka ga, kasancewar kai.ke tsaye a kan Zainab ka koma Hisham, ita sai ta mika ni domin akoy maganar da zamu yi da ita, idan ka samu lokacin dai ka leko kafin nan zuwa gobe in sha Allah akoy maganar da zamu yi da kai "
Hisham dake tsaye hannunsa daya na cikin farar rigarsa ta likitoci dayan kuwa na cikin na aba a ransa fadi yake 'Shin gaba muke?', sai kuma ya sauke nanauyar ajiyar zuciya ya gyada kansa a hankali ya ce" Aba, dan Allah kar ta jima dare ya yi, idan kuwa ta yi dare ta kwana a cen bama son tukinta na dare"
Aba ya amsa shi cike da kulawa kafin ya juya ya tafi mama na masa Allah ya tsare
Kusa da mama ya koma ya zauna kansa sade, cen ya dago yana dubanta a lokacin da take fadin" Lah Hisham, kira min number Aisha na fada masu ga inda muke kar su dawo daga asibitin bama nan"
Dan tsai ya yi da tunanin da yake, numberta? To shi ina ya ga numberta?, a hankali ya ji bakinsa na fadin" Mama wa ya batawa Bilkisu rai ne? "
Mama ta kale shi, irin yannayin da ya yi tambayar kwarai ta kula kamar maganar cikin ransa ce ta falasa kanta ta fito a lokacin da bai shiryawa hakan ba, domin sai da ya yi tambayar ne kuma sai ya hade fuskarsa ya mike tsaye yana fadin" Mama tashi a maida ke gida, wajen nan yanzu sanyi ya sauko, idan maganinta ya kare sai na kawota"
Mama ta masa wani duba mai cike da tausayi kafin ta dan kauda kanta ta ce" Zo nan "
Wajen da ta duba masa ya tsaya ya kalla sai ya kuma dubanta
A hankali ya dawo ya zauna, tun kafin mama ta yi magana ya ce" Mama, ban tambaya dan wani abu ba fa, na hakura kamar yadda kika ce mama, ba zan kuma takurawa a kan magamar ba na barwa Allah komai, na dai ga ne kamar ranta a bace kuma idannuwanta sun kumbura sannan mama ko magana fa bata min ba shine hankalina ya tashi"
Mama ta yi murmushi ta ce" akoy wanda ya isa ya maka iyaka da ita ne? Ko ni nan sai dai na nemi shawara sannan na katse wasu abubuwa duba da yannayin rayuwa......"
Dan shiry ta yi tana tunanin shin wajen nan wajen yin maganar ne ko yaya?, aman gannin da sauki barcima take kuma tana son ya tayata rarashin kanwar tata sai ta kara gyara zamanta tana kallonsa ta ce" Harta maganar shan nono daya dan ka mana biyaya ne, kuma ka ga Abanta sai ya ce in dai kana sonta bata da miji sai kai "
Diro masa maganar ta yi hakan ya saka shi yin dan tsai yana kallon mama kafin da hannunsa ya nuna kansa muryarsa ta kasa fitowa sai idannuwansa da suke da ja da ya wara a kan mama still yana mai nuna kansa
Mama ta sauke ajiyar zuciya ta gyada masa kanta tana kallonsa a sanyaye ta ce" ko da ta ce ita bata so bai saurareta ba "
HISHAM gaba daya ji yake iska na neman masa kadan bayan wajen da wadataciyar iska ga sanyin AC na busawa
Da sauri ya mike ya yi cen ciki, ofice din doctern nan da suka shiga dazu ya shiga da sauri ya maida kofar ya rufe ya ringa kai kawo yana dan fifita wajen hancinsa yana rintse idannuwansa
Sai da ya cire farar rigar likitocin dake jikinsa ya bale botiran rigar sannan ya samu ya iya sauke numfashinsa yadda ya dace
A hankali ya dora jimkakun hannayensa saman table din nan ya lumshe idannuwansa kansa sade, ya kasa yarda da wadinnan kalaman da suka soki kunnayensa, fatansa Allah ya sa ba mafarki yake yi ba, haka kuma Allah ya sa a cikin maganar ta bata so din cen wasa ne, dan ya kula iyayen nasa na son yin wasa da rayuwarsa a cikin yan kwanakin nan
Buda kofar da aka yi aka shigo ne ya saka shi dan dago jajayen idannuwansa ta madubun dake jikin tagar ofice din ya zuba dubansa dan gannin ko waye
A hankali ya kuma maida duban nasa kasa sai kuma lokaci daya ya juyo da sauri ya damki hannunsa muryarsa wani iri ya ce" Mafarkin ne ko? Mafarkin ne? Me yasa? Me yasa ba zan daina wannan mafarkin ba? Ka ga fa ni ba shaye shaye nake ba"
Kader ya sakar masa murmushi yana kallonsa ya ce" Mama ta kirani, Hisham ba mafarki kake ba, Allah ne zai cika maka burinka domin da ka kai goshinka kasa zabi ka bashi a kan wannan matsananciyar soyaya taka duda kana taketa kana daneta, ka ga sai ya zaba maka Hisham alkhairin ce, soyayarku alkhairi ce"
Ajiyar zuciya a jere a jere yake saukewa, sai kuma ya ce" Wai cewa ta yi bata so in ji mama? "
Kader ya jinjina girman so idan ya yi wani rikon, a sanyaye ya ce" Ni tunda aka ce ta ce wai babanta ne kai na ce ya dace ka binciki kwakwaluwar, aman kuma wa ya sani ko Umarun take so? "
Hisham da gabansa ya buga yana kallonsa ya ce" Kader baka so na? Me na yi? "
Kader ya turo bakinsa ya ce" Ka ga ka sakeni Hisham, ni wannan abin ya fara bani tsoro rabonmu da mu yi rigima har na mance, ji wai bana sonka yo Aisha ce ni ko Billy? Ni kam kar ka tsoratar da ni na sakawa raina ko dai mala'ikun mutuwa sun shafaka ne kake kara zama wani kalau da kai ?"
Alhamdulilah Allah ya dawo da ni, Alhamdulilah jiki da sauki, in sha Allahu zamu dora daga inda muka tsaya, du ranar da ba posting to fa aure yakin mata ne zai hana sai ko jiki da jinni🤣🤣🤣🤣🤣🤣🤣🤣🤣💃🏾💃🏾💃🏾💃🏾💃🏾
[7/4, 7:43 PM] +234 803 885 6944: 🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾
*DUK NISAN JIFA*
_(K'asa zai dawo)_
🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾
_RUBUTAWA_
*SAJIDA*
*SADAUKARWA*
*GA*
*MASOYA NA*
💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝
☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️
https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/
_Bismillahir rahamanir rahim_
44
A hankali muryarta na rawa ta ce" Aba, ni sam ban taba sonsa ba, banma san meye hakan zai bada wata ma'ana ba, ni yayana ne, baban yayana ne, wanda ya rike ni tamjar yarsa, Aba kar ku min irin auren nan a karro na biyu, kar ku mika ni a sake ni ba tare da wata kwakwarar huja ba Abana"
Mahaifinta dake kallonta shima jiki a mace ya ce" Bilkisu am, to menene na zubar da hawayen? Yanzun hamanki ne bakya so? "
Bilkisu ta kara sada kanta tana tare kanta wa fashewa da kuka ta gyada kan nata ta ce" Bana so Abana, bana so kar a min, ya je ya karata da matarsa ba wani abinda zan iya so kuma a tare da shi"
Abanta ya kuma tsatsareta da ido ya ce" Kamar me fa? "
Dubansa ta yi ta ga irin yadda ya bada hankalinsa a kanta gaba daya, sai kuma ta sada kanta da sauri ta kasa cewa komai
Aba ya sauke ajiyar zuciya a sanyaye ya ce" Da farko kalaman bakina na bada ban rigaya na gabatar da istihara a kan maganarku ba, ki yi hakuro autana ko wancen na maki aurwn gagawa ne cike da tsoro da firgicin rasa yar uwarki ke kina kuka shi mijin da za'a aura mata yana yi, shine na aura da ku dan kowane ya rarashi dan uwansa, ashe ke ke yin kukan rasa yar uwarki shi kukansa ya fi karkata kan tsoron Allah da tunanin me zai cewa unangijinsa a kan abinda ya so boyewa a hadu da shi a cuci baiwar Allah, ba zan ce maki komai ba a kan auren nan, idan ya zama alkhairi za'a daura shi, idan ba alkhairi bane na tabata Allah ba zai bamu ikon kuma daura maki shi ba sai dai idan zanen kadararki ce a haka, raba aurenki na farko luwa shine huja, ba auren nan!"
Bilkisu kanta a kasa yake har yanzu, mahaifinta ya dauki shiru na dan lokaci kafin ya ce" Ki je gida ki huta, banda koke koke da tunani kin ji? Idan kuwa a nan zaki yi zamanki na bude maki gidan ki shigo kin ji autana? "
Bilkisu ta dan girgiza kanta tana jan hancinta har Aba ya gama mata adu'a ya juya ya fita a mktar sannan ta tayar da motar ta juya ta yi gama
Haka kawai daga kasan zuciyarta take jin tana hasala da lamarin nan, sosai take jin haushin abin harma take jin bata so har kasan ranta, du ta watsar da komai ta ture komai a me zata je? Ta biyu kuma ba shi ya nema ba! Shin yaya suke so su yi zaman fahimta bayan yana mata kallon yar jaririyar da bata kai wajen da namiji zai iya yi mata kalmar so ba? Sarai ta san dalilinsa na tatarewa da kasa fada, kai ita batama yarda ba domin sarai mama ta saka mata kokonta a zuciyarta
Maimakun ta je gida sai ta samu waje ta raba motarta tana ji ana kiraye kirayen sallar magariba
Gannin ita ba abin sallah ne da ita a motar ba sai kawai ta karkata ta nufi gidan su laila
A cen ta yi sallar magaribar, har isha'i ta shigo suka yi kafin ta kwonta lamo saman doguwar kujerar falonsu ta afka tunani
Mahaifiyar Laila ce ke magana ta hanyar fadin" Bilkisu Bilkisu? "
A zabure ta dago domin ta afka tunani ne
Maman Laila ta ce" Lafiarki kuwa?"
Bilkisu ta sauke ajiyar zuciya tana kallonta ta mike zaune
Mamanta ta ce" Waya ke kuka tun dazu shin lafia kuwa? "
Dan Murmushi ta saki a hankali ta mike wajen da ta jona wayarta a caji ta je ta dauka tana dan jan karamin tsakin iya shegen Laila wai wani ta yi bako saurayinta ne da abokinsa sunna cem sunna zance
Wayar ta duba , mama ce, sai kuma Yayanta
Tana shirin maida kiran a number mama wani kiran ya shigo a number yayanta
Tana dagawa ta yi shiru bata yi magana ba, shi kuwa muryarsa a sanyaye ya ce" Kina ina ne? "
Bilkisu ta lumshe idannuwanta ta dane bacin ranta sannan ta bude ta bi fallon su Laila da kallo tamkar wace ke son gane a inda take kafin ta ce" Ina gidan su Farida " sannin da ta yi cewar gidan su Farida na yanzu bako ne a wajensa domin bai san inda suka koma ba sai ta yi wannan karyar dan idan ta ce da shi gidan su Laila ta tabata yana iya zuwa inda take ya umarceta ta koma gida kamar yadda ya saba
Tana jin yadda yake dan sauke numfashinsa ya kasa magana sai kuma ta ji muryar mama tana fadin sannu da yannayi na kamar a mota suke
Cen dai ta gama gajiya da sauraron numfashinsa ta nemi kashe wayar tana ji ana bude motar mai yiwuwa fita ne suke a cikin motar su kuwa