Showing 81001 words to 84000 words out of 180809 words

Chapter 28 - DUK NISAN JIFA COMPLETE HAUSA NOVEL

sajida   

02 Feb 2025

13003

sakin fuska ya ce da shi " Zaka iya kwontawa na duba ka? "

Yaron dake ta langwabewa saboda azabar da yake ji na ciwo ya kama hannun Hisham ya taimaka masa ya kwontar da shi saman rigar

Sai da ya cire masa suturar jikinsa tsaf sannan ya shiga ciro abubuwan da ya zo da su dan auna yaron iya abinda ake iya dauka na aikin

Tun bai je ko'ina ba ya gane cutar dake damun yaron, hakan ya saka shi daukan takarda ya yi rubutu mai dan tsayi sannan ya mikawa sarkin bulala wanda ya duka ya mikawa Shaheed

A hankali ya ce" A kawo min ruwa da tawul,aman ruwan mai dumi, kuma a kawo min maganin da na rubuta a kasa, na samanma a samo su dan sai an yi kwana uku ana saka masa ruwa safe, rana , da dare sannan ya sha magungunnan nan in sha Allah ba sai an masa aiki ba dan ciwon bai shige shi sosai ba aman a maida hankali kan traitment din "

Da sauri Sarkin Bulala ya amsa ya fice da karsashinsa a falon

Yana fita Najeeba ta kasa hakuri ta kuma dago dubanta a karro na ba adadi ta ce " Kana nufin zai samu lafia irin na kowa?"

Bai kalleta ba, yana maidawa yaron kayansa ya gyada kansa kawai sai cen kasan makoshinsa ya ce" In sha Allah "

Sai da ya saka masa mararsa nauyin sannan ya dago suka kuma hada ido da Sultan, 'Ikon Allah, meye haka a idannuwansa shi kuwa?' Shine abinda Hisham ya fada a kasan zuciyarsa, aman ya basar bai wani nuna alamun tsoro ko cire dubansa a cikin nasa ba, ko ba komai shi mai buda kai da kwakwaluwa yana tunanin abinda zai saka shi firgita ba nan kusa ba

A hankali ya kara gyara zamansa tsaf ya sauke dubansa kan Bilkisu wanda hakan ke dadada ran Shaheed, sai kawai yake gannin kamar shi a da idan yana zaune haka kawai idannuwansa basu da wajen sauka sai kan abokiyar fadansa kuma farautarsa gabansa ya ringa faduwa kamar ya ga abin tsoronsa

A hankali ya ce" A daina saka masa rawanin nan da du wani abu mai nauyi, a barshi ya ringa samun iska har ya warke daga baya sai a masa koma menene "

Shaheed ya dan gyada kansa a hankali ya ce" Kennan ba sai mun kaishi asibitinka ba? "

Hisham ya dan juyo yana kallonsa ya ce" Akoy wanda zai ringa saka masa karin ruwan a nan? "

Nadia sai da ta saki baki dan mamakin mutumen, shima Shaheed sai ya samu kansa da sakin murmushi yana gyada kansa a ransa ya ce'Yau ga wani tsayayen irina, aman ba komai ni ke nema dole na yi hakuri kuma ko ba komai ga mai haukata tunaninsa'

Hisham bai san daga ina Shaheed ya samu tambayar nan ba, sai ji suka yi ya gyara zama cikin isar nan tasa ya ce" ITA DIN IYALINKA CE? "

Su dukansu kallonsa suka yi, ciki harda Bilkisu,

Hisham idannuwansa ya zaro yana duban Sultan sai kuma ya daidaita yannayinsa yana sauke ajiyar zuciya a hankali ya dan girgiza kansa ya ce" Kanwata ce, tana jin zan zo shine ta tada rigima ita dai burinta Gimbiya ta kiya mata mak up "

Kuma dubansa ya yi ido cikin ido ya ce" Kana nufin kanwarka uwa daya uba daya ko kai ba muharaminta bane? "

A hankali ya kara wara dubansa a idannuwan Sultan wanda ya tsatsare shi da duban da idan da ace sun san junna yana iya rantsewa da Allah sone yake ya kure shi ko dariarsa yake, sai dai ya san ba sanninsa ya yi ba, shima hakanan kawai wani lamari ne ko dai ta birge shi ne?

Gyaran Muryar da Najeeba ta yi ya saka sultan kallonta

Kasa kasa ta gala masa hararar da du wani wanda ya kaleta da kyau ya kula da hakan, sannan ta maida dubanta wajen Hisham ta dan gyara muryarta ta ce" Ai ba damuwa, dan makup akoy masu koyarwa sosai zasu kula da ita "

HISHAM ya maida dubansa kan Bilkisu ya ce" Haka na ce da ita, sai ta ce aa ita Gimbiya Najeeba zata koya mata, burinta ta iya daga hannunta"

NAJEEBA ta maida dubanta kan Bilkisu

Ido hudun da suka yi da Bilkisu ya sakata kara kallonta

A hankali ta kara gyara zamanta tana kallon Bilkisu ta ga baki daya tana irin yannayin nan da ake shiga idan ana matukar son wani abin

A hankali ta ce" Taso "

Bilkisu da ta san da ita ake ba wani yanga ba komai ta mike ta nufo wajenta

Tana zuwa ta nemi zubewa hakan ya saka Najeeba lumshe idannuwanta ta saka hannunta ta tareta

Bata bata damar zubewar ba ta matso da ita kusa da ita, muryarta ta rage sosai irin yanda du wanda ya ji maganarsu lale mai mugun ji ne ta ce" Shikenan daga cewa taso, ban ambaci sunnanki ba, ban nuna maki da hannuna ba, banma nuna alamun da ke nake ba sai ki taso ba tare da kin ja aji ba baki nuna ke din mace ce mai isa da takama ba kika zo kike kuma son zube min a gabama shin ni mamanki ce?"

Da mamaki Bilkisu ta kaleta hakan ya saka Najeeba kara rage muryarta sannan ta yaye mayafin da Bilkisu ta luluba tamkar wata matar aure ta shiga kunce daurin dake kanta

Mikewa ta yi tsaye ta zaunar da ita saman kujerarta hakan ya saka baki daya su suke kallo, Najeeba ta mikar da dan kwalin sosai ta dan ninka gabansa kadan ta kama hannayen Bilkisu da ta zama tamkar wata status dan mamaki da tabatarwa kanta abinda ake fada a kan Najeeba tana biye da ita sau da kafa

Najeeba ta dora mata shi gaba sosai da goshinta sannan ta yi baya da shi bayan ta yi sama da hannun hagu din ta bi kasa da na damar a hankali ta ce" Mace kike, a gaban magauta kike, kar ki ga yayanki ne, daukarsa a matsayin abin harinki, abin farautarki, aman ba ta hanyar rashin da'a ko rashin mutunci ba sai ta hanyar da zai kasa motsin kirki a kan gadonsa, koda kuwa duniya ya aura domin an fada mana ya yi aure shi yasa bai zo da wuri neman da sultan ke masa ba, rike da kyau kar ya kunce?"

Da sauri Bilkisu ta tare domin sauraronta da take ya sakata yin sakayau zata saki dan kwalin

Sai da ta nanade dayan hannun mai tsayi ta nuna mata shi da kyau sannan ta zagaya da shi bayan ta soke mata shi sosai ya shiga ya zauna das da shi

Dan baya ta ja ta dago habarta tana kallonta sai kuma ta kunce mata shi gaba daya ta bata a hannunta ta ce " Daura na gani "

Bilkisu ta hadiye yawu, hannayenta dake rawa rawa Najeeba ta bi da kallo

Habarta ta kuma dagowa tana kallonta tar ta ce" Kin aikata mugun laifi ne? "

Bilkisu ra yi gagawar girgiza kai tana kallonta ta ce" To a kan me jikinki yake bari bayan ke din budurwa ce dake iya tsaida jinnin tsoho ko yarro a lokacin da hakan ta raya maki? Samarinki nawa ?"

Bilkisu ta kuma hadiye yawu ta dan girgiza kanta ta ce" Ba ko daya "

Najeeba sai da ta zarro ido, a hankali ta saci kallon Sultan ta ga sai murmushi yake dokawa irin abin na saka shi nishadi, ta tabata dan ya ga irin halin da Hisham ya shiga ne abin ke saka shi nishadi ta dan yi murmushi ta saci kallon Hisham
Duda yana rungume da yaron aman gaba daya so yake ya ga me suke ko me suke fada

Najeeba ta ce" Hala tsoronsa kike? "

Bilkisu ta dan sada kanta da dan kwalin a hannunta ta ce" Yayana ne ai "

Najeeba ta tabe bakinta ta ce" Ki yi hakuri da maganar da zan yi walahi bana hanna kaina ko a gaban bako ne, yaya sunnanki dan Allah yar kanwata? "

Bilkisu ta ce" Sunnana Bilkisu "

Najeeba ta kara matsawa kusa da ita sosai ta ce" Kece fa mai gadon zinari, ke ce Nana uwar manya, kece mace mai sunnan mace, ke ce farar mace alkyabar mata, ke ce gold ke ya dace a haukacewa, da kike tsoronsa Ubankine shi? "

Sai da Bilkisu ta dago da sauri hakan ya saka Najeeba sakar mata murmushi ta ce" Sai da na baki hakurin zagin ai kau? "

Bilkisu ta sauke ajiyar zuciya tana sada kanta

Najeeba ta ce" Daura "

Bilkisu ta shiga bin yanda ta yi mata ta dora saman kanta ta shiga daurawa Najeeba na dan gyara mata wajen da bai hau da kyau ba

Sai da ya dauru das da shi sannan Najeeba ta juya ta dauko jan bakin cikin yar karamar jakar dake ajiye gefe ta bude shi ta dan murda shi ya fito

Habarta ta dago ta goga mata kadan sannan ta nuna mata cewar ta hade lebunnanta

Sai da ta hade da kyau ya hadu sannan ta saka mata shi cikin hannunta ta ce" Ko kina gudu ki ringa yi da shi, koda kin ci abinci sai dan gyagyara dan kuwa dama gareki wace idan kina da wayau zaki dama!"

Bilkisu ta ringa dan gyada kanta Najeeba ta dauki mayafin nata ta ce" Tashi tau daga kujerar tawa "

Bilkisu ta mike tana kallon Najeeba,

Najeeba ta yi murmushi ta warware mayafin ta yafa mata shi a kafadarta ta ciro mata gashinta dake kasan mayafin ya hau saman mayafin sannan ta ce" Ki daina sauri ko a gaban waye, ko wa ya yi kiran ki, sannan ki fara zuwa ranar litinin karfe uku na yama dan na san kina makaranta ko? Idan kin zo ki nuna wannan takardar za'a kawo ki inda nake"

Tana fada ne tana bata yar takardar gayatar aman wannan mai saka hannun Najeebar ne wanda idan an nuna irinta har wajen Najeeba ake kawo mutun

Gaba daya mutuwar zaune ne Hisham ya yi da kader, daidai lokacin da sarkin Bulala yake neman izinin shigowa aman Sultan bai buga sandarsa ba hakan ya saka shi dakatawa a waje

Murmushi Sultan ya kuma yi ya rage muryarsa ya ce" Kadan daga aikin da ka siyarwa kanka "




🤣🤣🤣🤣 sai atinin ko? Idan Allah ya sa muna cikin masu rai da lafia🤣🤣🤣🤣
[7/24, 10:19 AM] BAK'A CE: 🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾
*DUK NISAN JIFA*
_(K'asa zai dawo)_
🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾

_RUBUTAWA_

*SAJIDA*

*SADAUKARWA*

*GA*

*MASOYA NA*


💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝

☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_


32




Gaba daya idannuwansa ya kuma zarrowa ya kalli Sultan ya ga ya gyara zamansa a lokacin da Bilkisu ta koma wajenta ta nemi waje ta zauna

Kyam ya yiwa fuskarta lokaci daya gabansa ya fadi sakamakon murmushin da ya ga ta saki tana dan lumshe idannuwanta

SHAHEED ya dan bubuga sandar tasa nan dogarin ya shigo dauke da ledojin baki daya magungunnan da ya amso a pharmacy dinsu

Jikinsa a mace ya duduba ya kwatanta masu yanda zai ringa sha sannan ya basu na karrin ruwan ya ce" A tabatar an zo da wuri da shi asibitinmu, zan bada sakon yanda za'a saka masa, rike shi zamu yi na kwana uku har a gama in sha Allah "

Sultan ya gyada kansa ya kuma mika masa hannu ya ce" Jazakallah "

Hisham ya yi murmushi shima ya mika masa nasa hannun suka yi musabaha sannan suka mike

Har su Bilkisu sun fita Hisham ya dan juyo sakamakon abinda ya tsaye masa a zuciyarsa ya koma kusa da Sultan kadan ya dan rage muryarsa yana fadin" Ko zan iya samun katin numberka? "

Sultan ya kai dubansa wajen Sarkin Bulala dake tsaye yana jira dan ya dauki yaron da kayan ya masa umarnin ya bashi numbarsa ta sirri

Yana amsa ya juya ya fita shima

A hankali ya karasa wajen motar ya bude gaba ya shiga ya zauna da abin a hannunsa yana dan jujuyawa

Kader dake zaune ya ki tayar da motar ya yi gurum yana kallonsa hakan ya saka Hisham dagowa jin shiru basu fara tafia ba ya kale shi

Kader ya ce" Mu je ne? "

HISHAM ya kuma kallonsa ya ce" Ko su bamu gado a nan ne? "

Kader ya dan girgiza kansa ya ce" AA mu tafi gidanmu mu yi bacinmu a cen ya fi "

HISHAM ya kyale shi bai kuma ce masa komai ba sai madubin da ya gyara saitin Bilkisu dan kuwa abinda ke damunsama ya ishe shi

Daurin kalabin nan ya wani irin fitar da tsarin kyan fuskarta, kamarma wanda ya fitar da girman idannuwanta, sannan ya karawa fuskar tata kima kamar ba yar jaririyarsa ba

Sun hada ido ya fi a irga a hankali ya budi bakinsa a hada idannuwansu ya ce" Dan Allah goge bakin naki kuma ki rufe gashinki bakya gannin ba mu kadai bane? "

Daga ita har kader sai da suka kale shi da mamaki, ita mamakin da ta yi ba yau ne na farko da ya yi irin furucin nan na kar ta yi kwaliya aman na yau sai ta ji shi wani bambarakwai, to ta goge ta kunce dauri ta kimsa irin na uwayen mata ko masu auren nan ta dora mayafi kidim ta daure ko'ina dama ashe dan kar ta birge kowa ne ko me? To in ba yayanta ba ita ba matarsa ba budurwarsa ba me yake nufi da ita?

Kader ya dan yi gyaran murya yana yin kwanar da zai dauki hanyar gidansu ya dan kara gyara zama ta yadda zai ja balaki ya ce" Ni kuwa sai na ga ta mata kyau daurin da jan bakin....." ya ja sunnan jan baki har yana nunawa da hannunsa

Hisham ya kura masa ido cike da mamakin iskancin da Kader ke nemansa da shi

A kausashe ya ce" Tsaya "

Kader ya dan kalle shi, tabatawar da ya yi da shi yake ya saka shi tsayawa da motar yana cije lebensa dan kar daria ta fito masa

Hisham ya ce" Sauka ko? Mu hadu a gida na gode Allah ya saka da alkhairi "

Kader ya ce" Me zai hanna na kaimu gidan mu duka Sir? "

Hisham ya kara kure fuskarsa da kallon, sai da ya dan sado kansa kusa da nasa kadan ya rage muryarsa sosai ya ce" Idan ban nuna maka hauka a wajen nan ba ka ce min dan iska, yau na ga jaraba kai ka fitar min a mota ko na dirka maka kutufo da hanuna shegen kai mai shegen sa ido!"

Kader ya sara masa yana bude gefensa ya saka kafarsa guda waje ya dan leko ya ce" Kin hade kanwata "

Da sauri ya idasa ficewa a motar yana kara sarawa Hisham sannan ya tsaida dan acaba dan kar ya masa nisa ya hau ya tsaya yana jira har su daga

Hisham sai da ya gama cije lebensa na kasa sannan ya fito a motar ya zagaya bangarenta ya bude a sanyaye ya ce" Ki koma gaba "

Bilkisu ta ziro kafarta ta fito ta zagaya gaban ta shiga dan itama ba zata ja da maganarsa ba

Sai da ta rufe sannan ya shiga gaban ya tada motar ya fara tafia a hankali yana dan satar kallonta

A sanyaye ya ce" Baki goge din ba? "

Bilkisu ta kale shi gannin hankalinsa a kan tukin da yake ya sakata mika hannu ta cirro tishu ta karkato madubin ta ringa dan gogogewa
Sai da ta goge shi sannan ta rike abin a hannunta

Bai ce da ita komai ba har ya tsaya a cikin gidan bayan an bude masu

Hannunta ta saka dan bude bangarenta aman ya ki buduwa hakan ya sakata kallonsa

Irin yanda idannuwansa suke binta da kallo sai da ta ji gabanta ya fadi, kallon nan ne da ba a so, ya tsatsareta da idannuwansa kikam wanda hakan ya sakata jin kamar ta fice da gudu

A hankali ya ce" Bani katin da ta baki "

Bilkisu ta kura masa ido, a sanyaye ta ce" Ai da shi zan je dole Hamana "

Idannuwansa ya lumshe ya kuma budewa a kanta ya ce" ni, ni, to a Kan me zata saka maki jan baki ta daura maki irin daurin nan, kin ga yanda kika yi kyau kuwa? Yau kadai idan kika je jibi me zata koya maki? Ni bana son fitina ina zaman zamana kaina baya iya hada rigimarki da aiki sai dai a yi daya dan Allah bani kar a rikita min tunanina

Kallon katin ta yi ta kalle shi, ta kuma kallon katin ta kuma kallonsa

A hankali ta mika masa katin sai kuma ta kifa kanta a wajen madubin ta fashe da kukan da bata san ko na meye ba

Abinda dai ta sani hawayen kansa ba fita yake ba sautin kukan ne da take saki tana rera shi tana kara kife kanta

Hankalinsa tashe ya dan miko hannunsa zai tabata ya dan dakata ya ce" Billy "

Bata dago ba ta kara sautin kukan har tana shasheka hakan ya saka dan kwalin nata faduwa kasa

Hannunsa ya dora ya dagota gaba dayanta ya sakata cikin jikinsa yana bubuga bayanta yana furta" shuiiiiiiiiiiiiiiit "

A hankali ya lalubi hannunta ya saka mata katin, gashinta dake kusa da hancinsa kuwa yana ta sinsinar kamshin man gashin da take anfani da shi

Da sauri ya dan saketa sannan ya matsa daga jikinta idannuwansa lumshe ya dan daga mata hannu bayan ya cire lk din

Da sauri ta fita domin itama bata ji kukan na gaskiya yana son rufeta ba sai yanzu, tana fita da sauri ta nufi wajen dakin mama ta samu mafaka ta labe ta saki kukanta mai tsuma zuciya tana fadin" Me ya sa sai na hakura da kai sai ka kusantani da kai? "

Idannuwansa ya sauke a gaban wandonsa, a hankali ya dora hannunsa yana dane abin dake kara kumbura
Gannin ya ki dannuwa ya saka shi jan rigarsa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login