Showing 165001 words to 168000 words out of 180809 words

Chapter 56 - DUK NISAN JIFA COMPLETE HAUSA NOVEL

sajida   

02 Feb 2025

12998

je gidan Gimbiya za'ai mata kitso"

Galala ya yi da cokali a hannunsa ya ajiye yana kallonta ya ce" Sai da na ji raina zai kiya, wani irin a je a mata kitso bayan na kanta tati? Ina aka taba fita da amarya washe garin aurenta a zo nan a mata mana ko nawa ne zan biya"

Tati ta hadiye yawu tana tatara kalaman da zata yi anfa i da su dan ya yarda cikin sauki ta gyara zamanta ta ce" Ka gane, ka ga ba'ai mata gyara irin na amare ba, tana da bukatar a je a yi mata gyare gyare a mata kunshi a mata kitso, ka ga Gimbiya ba zata iya fitowa dan wannan ba koda kuwa tana so, mu kuma mu ke so dan haka zuwan ba zai haifar mana da matsala ba idan har muka samu gyaran nan ko kai ba zaka ganeta ba"

Ido ya tsurawa tati, shi kansa bai san lokacin da ya ce" Wai tati bayan yadda take din nan za'a kara gyarata? "

Sosai tati ta ji kunya, aman ganewar da ta yi shi din sai a hankali sai kawai ta gyada kanta tana kakauda kanta dan walahi yadda ka san sirikinta haka take jinsa

Wani murmushi ya yi yana komawa ya dauki cokalinsa ya ce" To bari na gama na kaiku "

Ai kam tati sai da ta ji daria na son kubce mata, lalle Hisham sai a barshi, hankali kwonce ya ji za'a gyara masa watau a yi?

Ita dai mikewa ta yi ta shige ciki wajen Bilkisu

Cike da wayewa ta sakata tashi ta cenza kayanta , katon hijab ta fitar mata sannan ta buda jakarta ta ciro nikaf da safa ta daura mata ta rikota ta ce" Babyna ki saki jikinki wannan kakame jikin bana so, kuma na san kina jin yinwa aman ki yi hakuri idan mun je sai ki ci dan ta ce kar ki ci komai wai"

Ita dai Bilkisu bata ce komai ba a hankali take biye sa Tati har suka fito fallo

Hisham ya tsura mata ido an lulubeta ruf sai idannuwanta kawai ake gani, sai ya ji ya gamsu da shigar tata har ya sakar masu murmushi

Abincin aka fitarwa masu gadi sannan suka shiga bayan motar ya nemo Kader ya zo ya shiga gaba ya tayar suka kama hanya

Shiru shiru kader bai ce komai ba ya saka Hisham jin ya damu, kallonsa ya yi da kulawa ya ce" Kai kuma lafia? Ko baka da lafia ne? "

Kader ya ya kale shi shekeke yana shan kwana ya kai hannunsa wajen bakinsa ya dan ciza ya ce" Han kak, Hisham futar rai ne nake ba bani da lafia ba, nace fitar rai ne nake !"

Tati ta ce" To fa, yau kuma me aka yi "

Hisham ya daga kafadunsa irin shi ya gano din nan

Kader ya dan waiwayo ya ce" Tati, wai muna zaune tare da mutumen nan ashe so yake na mutu? Kin ga jiya fa ashe ni fadan da na yi mata dan su gyara halinsu ita da kawayenta dan abokina na neman mutuwa a kan wannan ta kusankin nan ficiyaya da ita, nan har ce masa na yi ya shiga rai bace ya mata muzurai ashe ni a shashasha yake daukana, yanzun du ba wannan ba da asuba fa ina kiranta bata dagawa karshe sai kawai nake jinta tana waya, na rikice athsmata na neman tashi na fada masa mu je ya ce aa in je, shine na je ina zuwa na tarar da mamanta a tsakar gida tana wanke kaushi Tati idona idon mamanta na rasa ina zan yi, wai Farida na fitowa da wata gajartarta uwa inuwar magi ce min ta yi ba na ce kar ta saki ta kirayeni ba? Yo dan Allah tati sha nawa zan fadi abinda bai dace a kulani ba? Shikenan ashe ita ta ji haushi kin ji jikina har yanzu zafi Farida cewa ta yi na fita a idannuwanta ta rufe ni Kadiri ni ni?"

Tati ta ce" Asha subahannalahi kai basu kyauta ba su duka, to aman dama kana da ciwon huka ne? "

Kader ya dan waiwayo zai bada amsa Hisham ya ce" Ka ga a motar nan da Billy ce da inarta ka dauko, idan ka saba wasa da raina ka kula da rayukan nan biyu a kansu sai in yi wasan kura da kai, da farida, da danginta baki daya "

Kader ya yi wani shekeke yana kallonsa ya ce" Bari in ajiye su mu gama maganar, Tati zan zo mu zauna walahi a je gidansu tun kafin ta haukatani ina dalili ita ba wada ba ba mai tsayi ba garjeje da ni tana saka ni kwala, Allah dazu hawaye na ji zai zubo min na cije na daure na tsere kar ta ga kukana ta raina maza"

Tati daria na cinta balema da take jin Bilkisu na kilkila daria har tana dan rawar nan da daria ke sakawa ta cije dan tsakaninsa da Allah yake fada a dube shi

Harara ya wula ta madubi ya ce" Dama ina zaka zama matar maketaci kai ka rasa keta a jinninka? Ai abin dauka ake , Allah ya yaye maki kuma in kika fadawa wancen abin na yi kuka dan ta ce bata sona Allah sai na kaimu gegi mun wuni an rasa inda muke"

Hisham kam shiru ya masa yana kallon hanya har suka wuce wajen masu tsaron kofar saloon din gimbiya

Sai da suka dangana da kofar shagon sannan suka tsaya Tati ta fitar da ita ta sakata ciki ta dawo dan daukar jakarta ta ga Hisham tsaye jikin motar

A hankali ya kamo hannunta da jakar tata a hannunsa yana kallonta a sanyaye ya ce" *INA, NA GODE SOSAI, DAN ALLAH KAR KI YI NESA DA MU, KI ZAUNA DA MU*"

Kamar a mafarki take gannin wannan lokacin, hakan ya sa ta kasa cewa komai sai wasu irin hawaye da suka shiga bin kumatunta ba kakautawa

Muryarta na rawa ta ce" Ka yafe min? "

Hisham ya kuma sakar mata murmushi a hankali ya ce" Na jima da yafe maki "

Wata ajiyar zuciya ta sauke tana kara rike hannayensa ta ce" Na gode, sosai Hisham na gode "

Hishamma ya ringa mata murmushi yana jin wata madaukakiyar kaunarta a cikin zuciyarsa a hankali ya ce" Ki yi tunani a kan mahaifina Ina, kasancewarki a inuwar aure shine cikar kamalarki, zan samu kwonciyar hankali ne idan na ga iyayena na karkashin inuwar aure "

Wannan karron gaba daya ya gama dadaureta da igiyoyin jikinta, a hankali ta kara rike hannunsa a sanyaye ta kuma fadin" Jazakallah "

Hannayenta dake cikin nasa hade da jakarta ya hada a hankali ya sada lebensa da goshinta cikin nutsuwa ya mana mata kisss sannan ya dan matsa yana mata murmushi kafin ya daga mata hannu a hankali ya ce" Sai na dawo daukan ku "

Rasa me zata iya fadi dan tsananin murna ta yi, sai kawai ta bi shi da kallo har suka ja motarsu suka yi gaba

Wata wawuyar ajiyar zuciya ta sauke a hankali ta zauna saman kujerar dake wajen na zaman baki ta tsurawa waje daya ido, ashe aurensu da ta jinkirta ta nuna ba za'a yi ba shine sanadiyar kusantuwarta da yaronta?, lale Bilkisu alkhairi ce a rayuwarsu

Ajiyar zuciya ta kuma saukewa ta mike ta yi ciki wajen Billyn
[7/24, 10:20 AM] BAK'A CE: 🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾
*DUK NISAN JIFA*
_(K'asa zai dawo)_
🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾

_RUBUTAWA_

*SAJIDA*

*SADAUKARWA*

*GA*

*MASOYA NA*


πŸ’«βœ¨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🀝

β˜† *[ T.M.N.A]* β˜† πŸ“–πŸ–ŠοΈ

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_



61


A lokacin da ta shiga Bilkisu na sanye da doguwar riga baka saman wani gado gado, kamar irin na likitar hakorin nan aman na roma sannan yana da laushi wajen zaman da wajen kwonciya, tana reran tana kallon sama sunna darzar jikinta da hadin dulkar da karfi da yafi sai da matar nan ta saudiya ta koya mata kuma take siyo abubuwanta du idan ra je ziyara

Wajen idannuwanta an dora mata kokomber bayan an shafa masa abin gyaran wajen, sosai aka yaye rigar har cen saman cinyarta sannan hannunta Najeeba ke sakawa har cikinta da wajen mamanta ta murje da dilkar nan mai wani irin haske da santsin uwar madarar da aka maka mata

Wajen kanta kuwa yarinyar Najeebar ce ke lalabe kan da wani hadin mai, sai da ta gama ta saka mata hular wanka wace zata baiwa kan damar yin zufa sosai gashi dama sun kashe AC dan kuwa gyaran ba'a so sanyi ko iska ya busar da shi an fi so dumi irin na zafi ya dumama fatar ta yadda zai ratsa jiki sosai

Sai da ta gama zufar har zufar ta shige jikin ya shanye sannan ta saka ta zauna ta murje mata shi sosai ta karkade shi ba tare da an yi wanka ba

Somin tabi kennan domin bayansa aka kawo garwashin wuta tare da kujerar zama sai wani hadin a wata yar silba mai kyau wanda akai masa hadin zuma

Shafa mata ta yi banda fuskarta sannan ta dauko tsumin da take sha ta cika mata katon kofi ta bata ta sakata shanyewa tas dama shine na biyu domin kaza aka fara bata dafafiya da Tukunya ta cinyeta tas domin karama ce sosai dan ta iya cinyewar ta sha hade haden magungunnan sai dabri take aman a haka ta cinye tas sai yanzun kuma ta kira da tsumin nan

Cikin nutsuwa ta lulube mata jiki bayan ta saka pant ja hayakin nan ya shiga shigarta harta da tafin kafarta banda kanta domin kanta ne kadai a waje

Nan suka dora hira da Tati da Najeeba, inda Tati take tambayarta gyaran nan kowama suke yiwa?

Gimbiya ta yi murmushi ta bata amsar cewa eh a saloon din du wanda zai iya biya sunna yi masa, ita dai ce bata zuwa aiki sai idan kannenta za'a aurar ko wanda ta yi niya Mai martaba kan bata wannan dama ta zo ta gabatar

Tati ta gyada kai cike da mamakin tsarin saloon din ta ce" Kuma gyaran na kwana nawa ne? "

Najeeba ta ce" Ai iya yau ne tati, harda inji fa da zata shiga wanda ake saka mutun "

Tati ta yi murmushi sosai ta rage murya ta ce" Nima ina so wannan fata fata tawa da ta dan yakune a jata y'ata"

Najeeba ta yi murmushi ta ce" Tati, shi gyara fa da kika gani a wajenmu ne ya zama sai na yaran mata, shin iya yaran mata ne mutane ko iya sune suke da aure? Ko mazan manyan matan ce masu suka yi basa son gyara?, zaki ga tsohuwa sosai bama wai mai shekarunki ba ta je an gyarata da gyara na ban mamaki tati, shi yasa zaki ga shekarunsu na boyewa a jikinsu dan gyara na boye shi, mace idan ta san darajar kanta tati daga an kwana biyu ta ga ta dan fara fita hayacinta koda bata da kudin ta dan harhada kan sauran na cefane ne kan na dan baki na karin ne ke da kanki ki hada ki je su murje ki su gyara ki su yarfa maki dan kitson nan da dan kunshin nan ki fito das da ke kamar ba ke ba, shi da kansa zaki ga cenjin rayuwa a tare da shi, aman ya zamana mace ba kyau ba tsari baki kirin ina anfani? Gyara aka ce, kowace fata da irin gyaranta , ni yanzu ba baka bace? Bakina kuma mai yawa ne bama mai haske bane ai kau? To haka ake dilke ni a murje ni na shiga mashin na fito, Allah tati ina cewa mai martaba a karro min mashin irin ta gyaran nan da nake ko sisina bai amsa ba ya saka aka kawota bayan tsada ne da ita"

Tati sai ta ringa jin kamar wani tsuminta na tashi na yarinta , a sanyaye ta ce" Bale ni kishiyoyin da zamu zauna da su uku larabawa ne su dukansu dayar yarinya cema baki ga ni kaina sai da ta birgeni gasu da gyara kau?"

Murmushi Najeeba ta yi tana kallonta ta ce" A kowani yare akoy masu gyaran akoy wa'inda basa yi, zan iya fada maki ba sakarkarun mata irin farar fata, Tati dan sunna farare wasun ko wajen wanka suka zo basa tsayawa da sabulu da soso su darji kasan hamata da wajen dohi , sama sama suke wankawa su fitowarsu dan kar a ce basu yi ba , sun iya caba kwaliya aman kuma sunna tsami, Tati ai farar fata daidaya suka san cewar bayan farin nasu ana so su zama masu gyara, su ringa tsaftacewa jiki ya kasance cikin dumi, nawa suke fararan aman kuma su ba komai bane gaban bakaken? Ba dan komai ba sai rashin sa'ar da suka ci sun hadu da bakaken da suka san ciwon kansu suka san gyara, kin ga tiket zaki yanka a nan tati itama tuni na yankar mata, du wata uku uku ta zo dilka, a gida kuma ta ringa hawa hayaki komai da komai na gama packaging a rubuce zan rubuta mata komai a bayane na mata gwari gwari, a je a zauna Allah ya bada zaman lafia"


Wayo tati kam ba karamin dadi ta ji hira da yarinyar da a haife ta haifeta aman kuma a wannan fannin ta dameta ta shanye, sam bata ji wahalar dukawa wada dan ta san zata tashi da tsayinta ne, a nitse ta ce biyu take so nata da na mama, sai kuma ta samu kanta da yin daria dan ta tabata zasu kwasa ne da mama kafin ta yarda ta wani hau kujera, sai dai sam ba zata mata da sauki ba dan walahi in dai ta hau sai ta haudata, ita kuwa ta darmi niyar hawa tun daga gobe dan da alamu gyaran Billy zai kaisu dare

Tana saman wutar sau biyu ana bata wani hadin aman da ruwa masu dan dumi kadan ba masu sanyi karara ba

Sai da ta dauki awa daya sannan aka yaye mata rufar a lokacin ta gama dafewa fatar tata ta yi wani irin ja na zafin hayaki

Sai wani luuuuu take da idannuwanta a lokacin da Najeeba ta sakata cikin wani dan lungu ta saki labule ta cire mata abin cikin nata ta shiga murzarta daga ita sai pant

Nadia ce ta miko mata hadin sansanyan madarar da aka hada mata itama wani hadin ta bata shi ta ce" Shanye "

BILKISU ta ce" Aunty, na koshi fa "

Najeeba ta ce" Aa akoy waje ai kin jima da cin kazar shanye kin ji? Yi kokari gyara ne"

Ai kam ta rufe ido ta kafa kai ta sha sosai dan sai dan kadan ta rage ta kasa shanye shi ta mikawa Najeeba abin mamaki tana kallo ta kafa kai ta shanye sauran ta mikawa Nadia

A nan dai ta kuma murza mata dilka ta barta sai da ta bushe ta dawo ta murje mata ita sannan ta dora mata hadin kurkum da madara sosai ko'ina nata kunya kamar ta kashe Bilkisu haka take harhade jikinta ana murzarta ga tarin gajiyar da take shi

Wannan karron sai da ta bata kujera har ta bushe a jikinta sannan ta bata tawul ta umarceta ta shiga bayi akoy wajen wankan gyaran jiki ta yi wanka da ruwan da aka tanada

Bilkisu na shiga ta koma wajen hadin da ta yi na su turaran jiki sansanya mai sanyin kanshi, da man oliv da madara abin kitib da shi sai kanshi yake

Bilkisu kuwa dake bayi tana zuba ruwan nan masu dumi a jikinta tana lumshe idannuwanta cike da wani irin jin dadin ruwan
Ruwan wani kamshi yake fitarwa na turaran ruwa hadin wajen Hajia Binta (Babar yaya), garai garai da shi haka ta wanka tana ta zubar da ruwan kurkum din da komai

Da mamaki take shafa jikinta tana jin yadda ya yi wani irin santsi da haske a kan na da ga kanshin ruwan nan dake tsaya mata a jikinta sosai

A nitse ta gama ta daura tawul din da ta dauro ta shiga da shi ta fito

Tati murmushi kawai take doka mata cike da kaunarta a nan ne Tati ta mije tana gannin yadda ake shafa abin shigar

Najeeba nake dibowa da abin shafawa ta zaunar da ita ta shiga bin lungu lungu da sako sako da hadin nan tana shafa mata ta ce" Wannan injin da kike gani da irinsa ne ake saka mata masu bleating, hafin nan ake yi sai a shada maki a saka ki a daidaira duminsa ki dauki awani a ciki, a lokacin da aka ciroki kamar sabuwar haihuwar jariri , aman shi ba dawamame bane ana yi ana sake shiga ne, haka kuma manyan yan siyasarmu da manyan matan da suka san kansu sukan taka kasashe kasar waje su je gyara, to ba wani abu bane ake masu sai wannan, kowa ana tafe da shi ne da kalar fatarsa, idan fari kake son komawa sai ka koma "

Tati na gyada kanta cike da mamakin ci gaban zamani ta ce" To aman aka ce idan aka dauke wuta mutun na ciki mutuwa yake? "

Girgiza kai Najeeba ta yi ta ce" Eh na farko farkon an ce haka suka ringa yi, aman ai kin san tati ana yin abu ne ana kara kayata shi da gyaransa da komai, yanzun dai wadinnan basa yin hakan idanma aka dauke wuta abin ke budewa sai mutun ya farka ya fito har a dawo da wuta, bale nan bamu yi hadinsa da wutar Nepa ba duda ba'a dauke mana wuta nan aman sam bana son anfani da wutar baban gida dan gudun kar wutar ta masa kadan, shi yasa aka kawo mana manyan inji aka kafa su iya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login