Showing 135001 words to 138000 words out of 180809 words

Chapter 46 - DUK NISAN JIFA COMPLETE HAUSA NOVEL

sajida   

02 Feb 2025

12991

taba ganni ba"

Du irin kwarjini da irin yadda wajen ya cika bai hanna maman Aisha budar baki ranta na ci gaba da tafarfasa ta ce" Wani irin rayuwar da bata taba gani ba, shin baku san bazawara bace har kuka shafa mata lale?, ku kuwa mutane kun taru kuna taya abin bayan a wata daya ne tak take cenza maza uwa rigar mama ana daure mata? "

Sai a yanzu Najeeba ta sauke ajiyar zuciya, domin dama abinda take son ganni kennan kuma ta samu, mama kam tunda Najeeba ta gurfanar da Bilkisu gabanta zuciyarta ta karye hakama tati hakan ya sa ta rungume kanwarta tana hawaye ga kuma magangannun mahaifiyar Aisha dake nemanta da fitina ido rufe du kuwa da irin yadda take kauce mata dan bata sin fitina ta je ta iya da kanta aman sai haye mata take

Najeeba ta yi murmushi bata ce da ita komai ba, sannan da sauri ta dakatar da jakadiya uwar yara wace ke kula da dukan motsin najeebar a lokacin da ta zabura ta ce" Wace marar da'ar ce zata fada a kan maganar Gimbiya? "

Najeeba ta kuma gyarawa Bilkisu aljyabarta sannan ta rage tsayinta kasa kasa ta ce" MAMA zamu juya, mai Shaheed ya ce kar na yi dare, aman in sha Allahu zamu yi waya, a watse taro lafia, aman ina nan alfarmar a maifa ita dakinta kuma kar a mata wani wankan sai gobe "

Mama ta ringa godiya tana share hawayen idannuwanta suka tashi gaba daya mutane na yi masu godiya da adu'a duda iya mama da tati da Bilkisu aka bari suka rabe su

Sai da suka zo kusan motarsu Najeeba ta juyo ta kalli Maman Aisha wace tsabar rashin nutsuwar zuciya ta kasa tsayawa waje daya du inda suka yi tana biye da su sai waya take dokawa ta kasa tsayar da tunaninta da kalamanta a kan lamarin ta ce" Ki godewa Allah mata sun ji maza sun yi sanyi, sai dai ki sani mulki zamani ne, a lokacin da jaki ke neman kahon da zai kai tini rago ke hangen kafafunsa na baya domin bai san idan ya daga bindinsa kafafun na kai dukan da suke iya halaka bawa, ba rashin sannin ciwon kai ke saka bawa kawar da kai a kan wasu abubuwan ba, wani lokacin gardama da jaki ke iya sakawa ka zamo jaki!, sai dai ki kula da takunki bana fada mai daura zani ta fada idan ba ni na bata damar zama uwata ba, ......"
Yar yatsarta ta kada ta fitar da hakorinta ta dantse lebenta na kasa ta ce" Zan tafki fatar marar kunya komai tsufansa , zan hargitsa lisafin DG a lokacin da na bashi yar shila ya kara ta biyu, ki ce da shi NAJEEBA MUTALAB na gaishe shi, sannan ya shirya SADIYA MUTALAB ta warware ya je ya tara domin bana baiwa rago Y'A!"

Tana gama fada ta shiga motar tana hararen kannenta da suka tsurawa Mama Aisha ido , hakan ya sa da sauri suka nufi motarsu suka shiga summa sannan dogaran nan suka ringa shigowa da gudu gudu sunna shiga motocinsu kafin suke juyawa du suka fice

A gidan biki an samu abin tataunawa hakan ya sa gidan ya kara daukan haramar al'uma

*Babar rana*


A yau ne ta kama ranar juma'a, babar ranar da mutane da yawa ke jira

Tun karfe shida mama ta mayar da Bilkisu dakinta , Tati kuwa ba kanta cikin baki take tana ta saka gyare gyaren wajaje

A wannan lokacin aka yi baki manyan baki larabawa mutun hudu suka zo da tsohuwa da wasu mata uku

Tati ce ta ja su har wajen mama a lokacin da suka ce dan Allah a nuna masu maman Hisham

Mama kanta sai da gabanta ya fadi, a sanyaye ta nuna Tati ta ce" Wannan ai itace mahaifiyar Hisham, Zainab kin ga maman MUHAMMAD ce fa"

Itama da sauri ta kalli matar dake kallonta da wani yannayi kamar na tausayawa kamar na neman taimako gata sharaf cikin shiga ta alfarma sai kanshi take bazawa

A hankali ta ce" Wanene Muhammad?, Aunty kin ga ina zuwa bara na je na ga an gama daidaita kofar gidan cen? "

Tati na juyawa mama da mamaki ta bita da kallo

Mahaifiyar MUHAMMAD ta yi murmushi ta ce" Ki barta, fushi take da ni ko?, zata hadu da shi domin yana kofar kuma ya ce shi zai daura auren dansa"

Mama kam kunya ce ta hannata magana hakan ya sa ta basu waje tare da Bilkisu wace ke cikin abin rufa jikinta ya gama dumuwa da zafi ko idannuwanta bata iya dagawa
[7/4, 7:43 PM] +234 803 885 6944: 🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾
*DUK NISAN JIFA*
_(K'asa zai dawo)_
🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾

_RUBUTAWA_

*SAJIDA*

*SADAUKARWA*

*GA*

*MASOYA NA*


πŸ’«βœ¨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🀝

β˜† *[ T.M.N.A]* β˜† πŸ“–πŸ–ŠοΈ

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_



48


Mama na fitowa cikin shigarta ta shada kalar orange an yi mata zubi tun daga wuya har kasa na kore da fari ta sha yar madaidaiciyar sarkarta ta sha daurinta daidai misali da abubuwan hannunta ta fara cin karro da Tati tsaye da mahaifiyar Aisha

Tati ranta a bace ta ce" Saurara Hajia, wai me kike so da ni ne? Bari ki ji na fada maki idan baki san yaren shiru ko kawaici ba, gidan nan da kike cewa gidan dana ne dan nawa shi ya ginawa mamansa shi da sunnanta, idan ita bata fada min ba dan kar hankakina ya tashi a tunaninta ya jima da ja min kurtu a kan na kiyaye hakan, bari ki ji na fada maki a yanzu ke kadai ke kirana da uwarsa kuma ina jin kunyar hakan, haihuwarsa na yi aman uwarsa yayata ce, na ajiye aurensa da yarki a matsayin *MATAR MUTUN* (Na aminiyata Samira Harun, idan baka bi ka nema ka karanta domin dadi ya barka),
Ke baki san kawaici ba? Ina mai sanar maki kaina ya dauki zafi shi yasa na kasa tambayarki shin yaushe zaki koma garinku ne? Na ga dai ya ji sauki harma ana shirin sakinsa mijinki sau nawa yana maganar komawarki kina cewa sai ta tare ai ta tare din ko? Nima ina zaune ne kan alfarma ba wai dan na isa ba, ki kiyayi sakani yiwa yayata rashin da'a, ko wanda na mata a baya ya isheni aya!"

Da mamaki hajia ta ce" Aman Zainab baki da wayau ban sani ba? Ni kike fadawa haka yau kuma? Shin kin manta wacece ni? Kin manta a karkashin mijina kike aiki? Waye ya baki damar da zaki fada min magangannu haka? "

Tati ta yi murmushi ta ce" Dadina da wanda ya tsinta bai iya ci ba, natsalar yiwa matsiyaci aiki kennan, matsalar rabewa a karkashin innuwar wani dan shan iska"

Tana gama fada ta juya itama cikin shigarta irin ta mama ta nufi waje

Da sauri mama ta daga kafarta dan dakatar da ita, sai dai wanda ya shigo ne ya saka su dakatawa su dukansu, basu gama karewa yannayin fuskarsa kallo ba mai kama da shi sai dai datijonsa sak ya shigo shima cikin gidan

A hankali mama ta ce"Tashin hankali"

Ido cikin ido suke kallon junna lokaci daya gabansu ya buga su duka biyun

Matsananciyar kunya da tashin hankali ya bayana a tatare da shi, sai dai kasancewarsa jajirtacen namiji wanda ke tsaye kan kafafuwansa sai ya dake yana kallonsu su duka ukun

A sanyaye ya ce"Asalamu alaikum ahalina"

Mama kawai ta iya amsawa tana kallon yadda tati ta yi mutuwar tsaye a lokacin da ya kara kusanta kansa da ita muryarsa still a sanyaye kamar irin yadda ta hisham ke yi idan yana cikin halin zulumi ya ce" ZANNUB shin baki fadawa yaron cen cewa abin alfahari ne ubansa ya daura masa aure? "

Makwat ta yi da busashen yawun dake makogwaronta ta ce" Baka isa ba , waye uban nasa? A sanina uban yaron nan ya jima da mutuwa dan haka baka isa ka daura auren yarona ba!"

Mama a hankali ta ce" Zaunab kin ga ku mu shiga ciki mu yi magana kina gannin mutane na kallon mu"

Aban Hisham ya yi murmushi yana kallon tati sannan ya kalli Hisham wanda tunda ya shigo fuskarsa hade ya yi murtuk bayan ya sha dakakiyar shadarsa sai maiko take ta sha zubi ta bi lafiyar jijinsa dukan jijiyoyin jikinsa sun fito radau tsabar bacin rai ya ce" Zan je na daura shi yanzu, idan da mai ja ni ba ubansa bane ya zo ya cire jinina dake jikin yarona"

Har ya juya zai fita ya ja ya tsaya sakamakon gannin mama ta yi raf da ita tana maganar ta wuce su shiga

Wani murmushin ya kuma sakar mata ya fita abinsa

Daurin auren da aka yi niyar daura shi bayan salar juma'a sai gashi ya samu karfe tara na safe a lokacin da al'uma ke cike a anguwar dan ba'a fara shiga masalaci ba duban al'uma suka shaida daurin auren HISHAM MUHAMMAD KHARIBULLAH da BILKISU JAURO bisa sadaki mai daraja da adu'o'in manyan malamai

Shiru ya yi kansa a sade tunda aka ringa shelar daurin auren a wajen da ya zauna, manyan likitoci, manyan yan kasa yan kasuwa ne, manyan mutane ciki kuwa harda mai Martaba sai busa ke tashi tamkar dan sarauta

A hankali ya dora dubansa a kan fari kal din hannun da ya dafa gefen kafadarsa a hankali ya dago dubansa ya sauke a kan fuskar mutumen, MUHAMMAD KHARIBULLAH cikin shiga ta alfarma fuskarsa mai annuri sunna kallon junna

A hankali ya cire hannun daga nan ya dan daki kirjinsa ya ce" Mijin Bilkisu ko sai na samo maka maganin zahi ne zaka mike daga zaunen nan uwa filo bayan jinnin larabawa kake?"

A hankali ya lumshe idannuwansa yana gannin yadda KADER ke tsaye da wasu mutun hudu su dukansu cikin shiga ta aikinsu sunna kakare shi domin in dai tarro zai shiga mutun biyar ne ke tatare shi ya ga yadda mutane ke yi masa fatan alkhairi daga nesa sai wa'inda ya zama wajibi su gaisa da shi ake bari su karaso inda yake

A hankali ya budi bakinsa dan ya ce a daga shi, domin kwata kwata ya kasa jin motsin kafafuwansa a jikinsa gani yake mafarki yake da wannan rana wai ga abansa ya daura aurensa da Bilkynsa? Sai dai wayarsa da ta ringa tsuwa karfi da yafi ga kuma ta kader ya saka shi zubawa Kader ido

Ta yannayin da ya amsa ne ya gane ana tambayar ky din falonsa ne dan a kai Bilkisu cen wai bata da lafia

Bai san ta yaya kafafun suka samu karfin dagashi ba, sai mikewa ya ga ya yi tsaye kan kafafuwansa sannan a hankali ya juya ya bar abansa nan tsaye yana murmushi yana binsa da kallo da godiya ga Allah wai wannan namijin nasa ne, dansa ne, jinninsa ne ya nausa cikin mutane su Kader na tatarewa ya shige ciki

Bai tsaya ko'ina ba sai falon Mama, a nan ya samu su bakwai zagaye da ita tana kuka cen cikin makogwaronta ta ce" MAMA kar a daura min auren nan, mama baya so na, nima bana son sa kar a daura auren nan mama ki hanna dan Allah"

Mama dake cike da takaicin ta yadda Bilkisu ke wannan bori bata ko jin kunyar kakarsa da Tati da mutanen da suka zo da su ta ce" ZAINAB idan baki barni na daki bakin tsiwar yar nan ba zan kai maki duka, wai meye haka kina ganni tana yiwa mutane iskancin nan ba zaki tsawatar mata ba? !"

Da sauri ya daga kafafuwansa dake rawa rawa ya karasa wajen

Irin yadda jikinta ke rawar sanyi ga kakarsa rike da ita tana dan bubuga mata baya irin rarashin nan, ga Tati na tsaye da waya ta kare mama dake son dukanta ga wasun tsaye wa'inda shi baima san ko su waye ba kowace ta sha kwaliya irin ta larabawa sunna shan yare ya rintse idannuwansa jin kalmar ki daga bakinta na kuma fitowa

A hankali ya ce" Ku barta, ku saketa ku fita dan Allah"

Cike da takaici mama ta fara juyawa tana al'ajabin irin rikicin da ranar nan ta zo mata da ita

Sauran kansu da daidaya du suka fita, Bilkisu kuwa tunda ta ji muryarsa sai ta yi gum fa bakinta aman jikinta na rawar sanyi haka kuma idannuwanta rintse

A hankali ya rage tsayinsa yana kallon rufar dake jikinta, dangalgal a falo saman kafet tana turmuka kokowa da iyayensa

A hankali ya saka hannunsa ya yaye rufar a yanzun bakar rigar ce kawai a jikinta sai kamshin turaran wutar da ya ki barin jikinta gaba daya domin ko wankan ba'a samu an yi ba aka tashi da rigingimun nan

Irin yadda ta rintse ido yake kallo, a hankali ya ringa bin dogon karan hancinta da ido har ya sauke duban nasa a irin dunkulewar da ta yi

Sai da ya cije lebensa na kasa da dan karfi sannan ya bude bakinsa muryarsa a dan dake ya mika hannunsa yana son jin zafin jijinta ke sakata rawar sanyin nan ko meye lokaci daya kuma ya budi bakinsa ya ce" BILLY AM....." irin yadda ya so maganar ta fito a dake aman sai muryarsa ta cuce shi ta fito cen kasa sannan ya ja sunnan shi kansa sai da tsigar jikinsa ta tashi bale ita dake cikin bege da bacin rai da tsoro da firgici

A hankali ya janye hannunda jin yadda jikinta yake da zafi kafin ya dora hannunsa gaba daya ya mikar da ita tsaye

Abin rufar ne ya fadi kasa, shi kuwa da karfi ya bata wata wuwuyar runguma, irin rungumar da kana gani ka san an jima ana son aikatata ba'a samu ba sai yanzu, runguma ce da sai da ta sakata bude idannuwanta da sauri tana dan sakin kara , a tsaten da suke tsayinsa ya kere nata fadin jikinsa ya kere nata aman a haka ta jita lufluf cikin kirjinsa wani irin abu na ratsa ilahirin jikinta, hakan ya jara hadasa mata rawar jiki da digar hawaye

Muryarsa a shake ya budi bakinsa ya ce"







πŸ™ƒπŸ™ƒπŸ™ƒπŸ™ƒ i'm backπŸ™ƒπŸ™ƒπŸ™ƒπŸ™ƒπŸ™ƒ
[7/4, 7:43 PM] +234 803 885 6944: 🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾
*DUK NISAN JIFA*
_(K'asa zai dawo)_
🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾

_RUBUTAWA_

*SAJIDA*

*SADAUKARWA*

*GA*

*MASOYA NA*


πŸ’«βœ¨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🀝

β˜† *[ T.M.N.A]* β˜† πŸ“–πŸ–ŠοΈ

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_



49


Muryarsa a shake ya budi bakinsa a sanyaye ya ce" Kin ga fa yadda kuka ke mayar min da ke, dubi yadda jikinki ya dauki zafi kuma idan na ce allura ki tubure ki kiya, haba Mai gado me yasa kike son zame min rigimamiyar karfi da yaji ne?, yanzun ni ne ake yiwa kukan ba'a so har haka?"

Bilkisu idannuwanta ta rintse gam domin tunda ya fara maganar a kunnnenta bai sasauta mata rikon da ya yi mata ba, gaba daya mamaki, tsoro, kunya ta hanna mata dago idannuwanta bale har ta iya dubansa, irin yadda zuciyarsa ke bugawa da irin yadda hannunsa ke dan rawa ya sakata kuma lumshe idannuwanta ta rasa ina zata tsoma ranta

A hankaki ya dago habarta yana kallon kyakyawar fuskarta ya ce" Zaki min alfarmar dakatar da kukan nan haka?, kin ga an daura ba maganar kina ko so na, Billy auren nan da aka daura wanda ya busa min numfashi kawai ya isa ya kashe shi ta hanyar kashe ni, ba zaki gane ba, ba zaki taba fahimta cewar kalmar so na zuwa ne idan da hali, nw i bg u ki saurara min haka kin ji?, kin ga fa wai rigima ce ta barke tsakanin su kin ga mamana ta ja su bangarena, da wane zan ji?"

Bilkisu ta kuma lumshe idannuwanta tana sauraronsa tana kuma kallon kirjinsa duda a rufe cikin rigar shadarsa mai ruwan sararin samaniya hakan bai hanna mata gannin fadinsa a haka ba

A hankali take binsa sakamakon jan hannunta da yake cikin nutsuwa ya yi dakin mama da ita

Saman bed ya dorata ya gyara mata kafafuwanta a sanyaye ya ce" Ina zuwa "

Ita dai bata da wani ikon da gaban jikinta da tunaninta har sai da ya fice ya bar dakin
Huci ta sauke mai zafi a hankali wani hawaye mai dumi ya fito daga gurbin idannuwanta, yannayin da take ciki mai girma ne, godiya take tiwa Allah na gannin wata igiyar aure ta hau kanta, godiya take yiwa Allah na gannin igiyar wadda take kauna ce a saman kanta, sai dai sam jikinta ba karfi idan tana kallon yadda yake aikatuwa da jikinsa da aljihunsa a kanta aman bakinsa bai furta mata kalmar nan ba, shin me tasa wasu mazan ke tunanin wai ba sai an fada ba, fadan ya zama kauyanci? Wannan shirme kennan fada ba zai taba zama kauyanci ba domin da da hali a kulun ka furtawa matarka wannan kalma jadadawa ne da tunatarwa hakan zai kara dankon zaman amana soyaya, da tausayi

Ta tabata du inda su Laila suke sun kusa zuwa, su kadai take jira su kamata ta mike dan sosai take jin zazabin nan a jikinta

Yana buda falonsa ya yi turus yana kallon

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login