Showing 162001 words to 165000 words out of 180809 words
shi cike da nutsuwa da wani irin kwonciyar hankali da nishadi
Karfe biyar da rabi
Kader ne zaune da waya a hannunsa bayan ya daura alwallah ya shiga dannawa Farida kira
Habarsa ya dafe ya kara tura mata kira, aman sai aka kuma kashewa,
Kai daga karshema sai ya jita kamar tana tsaka da kira
Da sauri ya zarro idannuwansa yana kara tura kiran a bayane ya ce" To ita kuwa da wani shegen take kira a wannan lokacin da ta san ni kadai nake kiranta na tasheta ta yi sallar asuba?, Farida to wani abin na maki da kike kashe min kira?"
Kuma gwadawa ya yi, aman kamar da wasa baya shiga waya kawai take
Da sauro ya mike ya shiga kai kawo, ido hudu suka yi da daya daga cikin masu gadin gidan ya gaishe shi tare da tambayarshi kamar haka " Oga kader lafia kuwa? "
Kader ya rike tsatsonsa ya ce" Da aka yi me?"
Kansa ya girgiza ladan ya ce" Aa ba komai gani na yi kana ta kai kawo kamar an yi wani mugun abin"
Kader ya ce" aa ba mugun abu ba ka ce kamar ina zawo, kai Bukari dama tun jiya na lura ka cika sa ido na fita a gaban idannuwanka na dawo kake tambayata wai ko nine ko ba ni ba, to ina ruwanka, ka ga ka barni Farida nake kira idan bata daga ba yau ko uban gidanka sai na dada shi da kasa ba kai ba! Jira ni"........ya karasa fada yana nufar kofar su BILLY
TO FA BILKISU DA HISHAMU ANYA AMARCIN NAN DA KADIRI A KUSA ZAI DORE?
BARKANMU DA SHAN RUWA JAMA'A
[7/24, 10:20 AM] BAK'A CE: πΎπΎπΎπΎπΎπΎπΎπΎπΎπΎ
*DUK NISAN JIFA*
_(K'asa zai dawo)_
πΎπΎπΎπΎπΎπΎπΎπΎπΎπΎ
_RUBUTAWA_
*SAJIDA*
*SADAUKARWA*
*GA*
*MASOYA NA*
π«β¨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*π
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_π€
β *[ T.M.N.A]* β πποΈ
https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/
_Bismillahir rahamanir rahim_
59
Yana karasawa ya ja ya tsaya ya shiga dannan sonor din da zai sanar da mutun a kofa yana kara danna mata kira
Hisham dake tsaye da carbinsa ya yi wanka zai je masalaci ne ya juyi da sauri dan gudun kar karan ya tayar da Bilkisu dake dukunkune tana baci ya yi waje wadda tun dannawar farko a kunnenta domin sam bata da nauyin barci
Yana fitowa ya zubawa Kader ido, shi kuwa da sauri ya kamo hannunsa ya damka masa wayar hankalinsa tashe ya ce" Taya ni ji, to waima da uban wa Farida take waya da asuba? Tun dazun take kan wayar nan Hisham, saurara ka ji me na mata yo? Ka ji taba kirjina ka ji yadda yake sama yana kasa, ji nake numfashina zai tsaya kama kirayeta da wayarka mu ji"
Hisham Tsakani da Allah dariya ce ta ciyo shi duda irin lokacin da kuma son ya shigar masa lamari da ya yi, aman sai ya cije ya fara tafia yana fadin" Faridar banza faridar wofi da daren nan zaka zo ka wani bani waya na kireta ? Yo matata da nake jinya kake son na dagawa hankali ko hauka, Kadiri ka fita a idona na rufe Allah!"
Kader ya ringa binsa zungwai zungwai suka fita suka nufi masalaci
Sunna zuwa suka bi sallah har aka gama aka shafa fatiha suka fito suka nufo gidan kamar marar lafia ya kuma ciro wayar ya danna mata kira aman yanzun ma tana kan waya
Kader ya yi gagawar tarban gaban Hisham yana kifta ido ya ce" Ka ga Allah taba jikina ka ji zafi ya fara rufe shi , yanzu Hisham me na maka da zaka ki kulani fisabililahi? Nan kake sumewa in Bilkisu ta bata maka rai sai na kaika asibiti sannan in je in sameta in mata nasiha, aman shine kana ganni za'a kashe maka dan uwa kan laifin da ni kaina ban san me na mata ba shine kake share ni kamar ba ni ba ni dinka Hisham? "
Hisham ya ja ya tsaya gari ya fara haske kadan ya ce" To yanzu yaya kake so mu yi? "
Kader ya ce" Ka shiga mu je ta fadi me na mata sai mu bata hakuri"
Hisham ya gyada kai yana murmushi ya ce" To yau sai ka fada min a wawa dan fari ka daukeni ko a dan iska?, Kadiri ni idan muna fada da Billy kulun shawarar da kake bani shine na je na hauta da fada na mata kaca kaca in ba zan iya ba bara ka min, a jiya jiyan nan tana sabuwar amaryata na bara mata rai ce min ka yi na shiga fuska a daure na fatataketa idan ba zan iya ba bara ka je ka mana, shine yau zaka ce wai mu je mu ba farida hakuri, ai sai dai mu je mu fatataketa Allah walahi!"
Kader ya zarro idannuwansa yana fadin" Yanzun daga taimako sai ya zama matsala? Inace Bilkisu ai kanwarmu ce muna iya tsawata mata mu mata jan ido ta sauraremu kau? "
Hisham ya gyada kai ya ce" A gidan uban wa, kai da na je mata da hauka yaya zamu kwashe? To ita faridqr uwarmu ce ba zamu mata fada ba? Ka ga Kader tun yanzun kana nema ka zama wani solofiyo a kan mace ko? Ka je ka murje idannuwanka ka bata umarni ta saurareka ko a yi tashin hankali"
Kader ya yi shiru cen ya ce" Ba zaka gane ba, ita kadaima fada take jiyan nan fa daga fada mata gaskiya kan su daina wahalatar da mu, kuma idan ka mutu sai na kashe kawar Billy daya shine fa inaga ta ti fushi, to ai ba laifi na yi ba"
Hisham ya yi murmushi ya ce" To wa ya ce maka ana yiwa mace haka? Ai kadan ake mata fadan sauran sai a rike a kyaleta da halinta , ka ga yanzun ba inda zan je walahi idan muka je masu gida warhaka ai har Babanta ya hanna maka ita , ka ga ka rufawa kanka asiri ka ji? Ka je ka kwonta da na so na maka asubanci na kishi banza aman tunda faridede ta taimaka ta kama min ai shikenan, zan je na ga yar aljana yaya ta farka"
Kader tsaye baki bude yana kallo Hisham ya yi bangarensa hakan ya saka shi juyowa ya nufi mota suka kuma hada ido da mai gadi
Da fada fada ya ce" Meye? "
Mai gadi ya girgiza kai ya yi wajen kofa ya hangame masa yana rike dariyarsa domin tsaf ya tsaya ya ga diramarsu da ogansu har yana mamakin dama Hisham da magana haka, lale kuwa
A hankali ya rufe kofar dan kar ya tasheta, sai dai abinda ya bashi mamaki dadadan kanshib turaren wutar da yake dukan hancinsa a duk lokacin da ya shiga dakin mamansa ne ya daki hancinsa ya hadu da sansanyan sanyin falon
Da sauri ya shiga kale kalen falon gannin ba kowa ya taka a hankali ya nufi dakin da suka kwana
Saman kujera ya tarda ita tana shafawa jikinta mai, da alama daga wanka ta fito ta sauko da hijab dinta wajen wuyanta dan kar ta zauna daga ita sai tawul
Da sauri ta ja hijab din tana kokarin maidawa a wuyanta cike da kunyar yadda ya tardota
A hankali ya karasa inda take zaune yana gannin ta cenza zannin gadon sannan ta kwashe kayansu ta kuma saka turaran wuta
A hankali ya saka hannunsa yana dan janyota jikinsa cike da mamakin yadda ta iya mikewa har ta yi wani abu ita da bata da lafia
A sanyaye yake shafa bayanta bayan ya sakata a jikinsa
Ajiyar zuciya yake kwacewa yana sinsinar sansanyan kanshin turaran dake fita a jikinta
Irin yadda take nokewa tana mai nuna tsantsar kunyarsa a bayane ya saka shi sakin murmushi a hankali ya janyota ya nufi saman bed din da ita
Shi ya fara zama ya dorata saman kansa yana kula da yannayin tafiarta da ya ga ta cenza sosai ba kamar ta jiya ba, da alama har ruwan zafi ta shiga shi yasa ta ji saukin jikinta
A hankali ya rungumeta a jikinsa yana kara shafa bayanta cen kasa ya ce" Yaya jikin ki? Yaya nan....."
Ya karashe yana nuna wajen hakan ya saka ta kara sinne kanta cikin kirjinsa cike da matsananciyar kunyarsa ta kasa bashi amsar tambayarsa
"BILLY Am? "
Ya fada a sanyaye hakan ya sa cen kasan makoshinta ta ce" Na'am?"
"BILLY ina son ki" ya fada cen kasan makoshi kuma cikin kunnanta hakan ya saka ta ji wani irin yar yar yar gaba daya a sasar jikinta tana rintse idannuwanta
Bata dawo normal ba ya dora da fadin" Billy dadi, dadi na sha jiya kuma ina marmarin karawa, sai na ga kamar kin warke na kara?"
Sai da ta zabura ta dago tana kallon fuskar sabon yayan nata da sam bata san shi ba, wannan mutumen mai sakin magana du a yadda ta zo masa bako ne a tare da ita, ya cika sakata jin kunya da jin wata irin bakuwar duniya a duniyarta kamar ba jikinta ba, kamar ba ita ba haka take ji, komai sabo, komai na taba ilahirin jikinta da duniyarta
A hankali ta shagwabe fuskarta ta maida kanta saman kirjinsa ta shiga dan girgizawa cen kurya ta ce" Ban warke ba walahi zafi sosai "
Hisham dake shafa bayanta idannuwansa sun mutu sosai a hankali ya idasa kwontawa da su yana kara shafata ya ce" Dama sai a hankali zaki saba Billy am"
'BA wayo ba?, wayo na shiga ukuna' shine abinda take fada a kasan zuciyarta kafin ta cira da sauri ta mike tana shada gaban goshinta ta ce" Kayana zan saka"
Bata tsaya ta ji amsarsa ba da sauri ta dauki kayan da ta ciro ta yi bayi har tana neman hardewa
Tana rufewa ta sauke nanauyar ajiyar zuciya tana lumshe idannuwanta a bayane cen cikin makoshinta ta ce" Wayo zai kashe ni, na shiga uku zai kashe min du wani kokarina, wayo zai saka na manta sunana"
Da sauri ta cire kayanta Allah ya taimaketa ta saka pant ta saka rigarta a sama da kyar dan ba wani garas take jin kanta ba, kawai dai bata son ta zabge ta kasa katabus ne
Da kyar ta iya fitowa sanye da hijabinta ta ja ta tsaya sakamakon ganninsa ya cenza kayan jikinsa ya saka sasauka na barci
Jikinta a mace ta idasa inda yake tsaye yana kallonta bayan ya miko mata hannayensa
Ba karfin jiki take kallonsa shi kuwa ba wata damuwa da nauyin baki yake bata kulawa ya jata saman bed sin ya cire hijabin ya sakata a jikinsa sosai ya rungumeta yana shafa gashin kanta har barci ya fara fuzgarsu baki daya
Tsuwar da wayarsa ke yi ba kakautawa ta tashesu wajen karfe goma na safe
A tare suka farka du suka kai dubansu wajen wayar
Hannunsa ya mika ya dauko wayar , yana dubawa ya ga sunnan Tati
A hankali ya daga ya kara a kunnensa bayan ya yi salama kasa kasa
Ido ya zarro a hankali ya ce" Kuma a nan nan yanzu Tati? "
Amsar da ta bashi ne ya saka shi kallon Billy dake zaune tana kallonsa
Murmushi ya sakar mata ya ce" Inarki ce ke falo "
Ido ta zarro da sauri ta ce" Ina kuma? "
Girarsa ya daga mata yana sauke kafafuwansa a saman bed ya dan dafe habarsa ya ce" Inaga tataraki zan yi mu yi nesa da gari, dan kuwa a garin nan da inarki, da Kadiri ba zasu barni na huta ba "
Tsuru tsuru Bilkisu ta yi a zaune ta ce" To yanzun yaya zan yi? "
Dakatawa ya yi yana kallonsa sai ya saki murmushi ya ce" Ban gane ba? "
Bilkisu ta sada kanta tana murza hannayenta ta ce" Idan, idanfa ta gane halin da nake ciki? "
Hisham ya dan rankwafo yana kallonta cike da sha'awar yannayinta ya ce" Kina nufin idan ta gane kin girma? "
Da sauri ta dago tana kallonsa, a shagwabe ta ce" Hamma "
Shima da yannayin da ta fada ya ce" Baby "
Da wata irin kunya ta sada kanta a jikin fillow tana labewa cike da kunyarsa
Mikewa ya yi tsaye yana murmushi ya ce" Bara na dawo ina zuwa "
Bai tsaya jin amsarta ba ya fice a dakin
Tato dake zaune ce suka yi ido hudu da shi, da sauri ta cire dubanta a kansa tana mamakin yadda ta ji matsananciyar kunyarsa
Hisham kan kwanonin dake jere ya bi da kallo kafin ya taka ya karasa wajen da take zaune ya zauna yana kallonta a sanyaye ya ce" Barka da safia Tati "
Tati ta cije sosai ta juyo tana dan murza gaban goshinta tamkar tana gaban ainahin sirikinta ba dan cikinta ba cike da jin kunyarsa ta ce" Dama abinci ne ne na kawo , kuma ina son ganninta"
Murmushin da ya jima bai yi ba a gabanta ne ya subuce masa, zamansa ya guara tsakaninsa da Allah yake jin a ransa yana son tsokanarta dan haka a sanyaye ya ce" Wace din ?"
Dagowa ta yi ta dan saci kallonsa ta kara sada kanta tana hadiyar yawun da kyar ta ce" Babyna "
Sai kuma ta mike zurbat ta yi hanyar dakin hakan ya saka shi yin yar karamar daria yana girgiza kansa ya mike ya nufi dakinsa dan yin wanka ya leka Aisha
Tati na shiga ta tarda ita yadda ya barta, murmushi ta yi a hankali ta karasa aman sai ta kasa hawa gadon ta tsaya daga gefe tana kallonta ta ce" Babyna "
Da sauri Bilkisu ta kara nitsa kanta a matashin tana zazaro ido, sai kawai take jin wani kuka na son kubce mata, me zata ce da ita ? Jiya jiyan nan ake neman kamota tana furta bata sonsa kuma kawai sai a ga har ta bashi kanta?
Wayar tati ce ta dauki kuka, murmushi dauke a fuskarta ta daga a sanyaye ta ce" Barka Gimbiya, gani yanzun na sameta gatanan kwonce ta ki kallona ko dan missing dina ina ga bata yi ba, aman gatanan bara na same shi kan maganar zuwa gyaran sai na shiryata mu taho in sha Allah, bara na baki ita "
β€οΈ
[7/24, 10:20 AM] BAK'A CE: πΎπΎπΎπΎπΎπΎπΎπΎπΎπΎ
*DUK NISAN JIFA*
_(K'asa zai dawo)_
πΎπΎπΎπΎπΎπΎπΎπΎπΎπΎ
_RUBUTAWA_
*SAJIDA*
*SADAUKARWA*
*GA*
*MASOYA NA*
π«β¨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*π
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_π€
β *[ T.M.N.A]* β πποΈ
https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/
_Bismillahir rahamanir rahim_
60
Bilkisu na amsar wayar ta kara cen kasa ta yi salama
Najeeba ta saki murmushi ta ce" Lalema, sannunki Mairama, sannu fa "
Kunya ta saka Bilkisu kuma labe fuskarta kamar sunna gabanta tana ayana' Ni kam na shiga ukuna da mutanen nan'
A sanyaye ta ce" Barka da safia Gimbiya "
Najeeba ta kuma yin murmushi ta ce" Za'a kawo ki yau na kashe saloon dan gyaranki na samu amincewar mai martaba zan wuni a cen tare da ku "
Dan murmushi ta saki a sanyaye ta ce" Allah ya kara girma aunty, na gode na gode "
Najeeba ta ce" Ba godiya, mu kin san irin karamcin da mijinki ya mana, ya mana karamci sosai "
Murmushi ta yi tana kara sine kanta cike da jin kunya
Tati na zaune a falo tana duba lokaci, a kadan ya dauki minti arba'in shigarsa dakin sai yanzu ya fito
Kamshin turaren da ya fara isowa ne ya sakata dagowa tana kallonsa
Allah yana gani sai ta ji kamar ta taka tsale dan farin ciki da mamakin yaron nata, wai wai wai Allah, Allah ya yi mata baiwa har haka tana cen tana shan rana kan dan abinda bai taka kara ya karya ba, wani lalausan farin yadi ne ya saka irin mai dabara dabaran nan mai shegen kyau, ba wani mahaukacin dinki akaiwa yadin ba, dinki ne simple riga daidai gwuiwa irin na zamani da wando daidai da shi , sai manchest masu shegen kyau na karfe bakake kirin sai bakar riga da ya saka a ciki sngil, sai bakin takalmi kafa ciki da bakar hula, aman ba karamin kyau ya yi ba haka kuma ba kananun kudi bane a jikinsa tun daga kayan har hular, takalmin da kuma agogon, Manchest din kansu zasu yi jarina (π), ya hadu ya hade irin yadda hannayen rigar suka masa tim tim abin ba'a cewa komai
Ajiyar zuciya tati ta sauke cike da wani tsadaden farin cikin gannin irin yadda yanzun yake sakewa da ita hankali kwonce ya yi hira da ita ba wata damuwa , ko yanzun yana dosata ya ringa sakar mata murmushi wanda sai ta tsargu, kai yaron nan hala ji yake ita kakarsa ce?
Zama ya yi yana kallon abincin a hankali ya ce" Tati mamana zuba min take yi, ki zuba min nawa da na Billy am"
Tati ta hadiyi yawu ta juyo wajen abincin ta bude, a nutse ta zuba masa ta ajiye masa ta tura masa jus din da ruwa tana kallonsa ta ce" Ita ba shi ba zata ci, ka ci ka gama ka tafi"
Cokali ya saka ya fara dan tsakura yana yi yana kallon Tati ya ce" Wane zata ci? Bata ci wani abin kirki ba fa Tati "
Murmushi ta yi ta ce" Zata ck yanzun, mamanku ce ta ce na zo na dauketa mu