Showing 51001 words to 54000 words out of 180809 words

Chapter 18 - DUK NISAN JIFA COMPLETE HAUSA NOVEL

sajida   

02 Feb 2025

12969

kuma ina sane da take takensa, ba komai zai yi ya gama ne! "

Ita kam Aisha bata da ta cewa sai mikewa da ta yi ya nufi dakin da take kwana ta kwonta tana mai kashe wayarta baki daya dan bata son damuwa, so take ta fuskanci magangannun mahaifiyarta da kuma irin yanda mamanta ke nuna mata ba laifi bane dan ta auri Hisham, irin yanda take nuna mata ba kanta farau ba, irin yanda take lwadaita mata rayuwa da wannan bawan Allahn da maganar fatar baki bata taba hadasu da junna ba

Sai da ya budi bakinsa da dan karfi ya ce" BILKISU mun karaso fa " sannan ta yi firgigit daga lumshe idan da ta yi ta bude tana zuba idannuwan nata a bangaren da kofar gidan mahaifinta yake

Mahaifinta ne tsaye cikin shiga ta doguwar rigar jalabiya kansa dauke da hula saman lalausan gashinsa yana kallon bangaren motar yana murmushi

A hankali ta ringa jin sanyi a cikim zuciyarta tana kallon fuskarsa daga nesa

Cikin nutsuwa ta bude ta fita a motar zuwa lokacin Kader ya fita ya ciro mata jakarta ya nufi wajen Abanta

Da fara'arsa ya fadada yana fadin" Oyoyo Mai gado, ki ce zaki kwanar min wannan karron? "

Kanta ta sada ta nemi zubewa kasa dan gaishe shi tana murmushin itama, sai dai bai bata damar hakan ba ya rikota ya dagota yana kallonta ya ce" Tashi tashi Mai gado "

Muryarta a sanyaye ta shiga gaishe shi , su ba sakewa sosai domin bata taba zuwa da niyar kwana a gidansa ba

Get din kofar aka bude aka fito
Wata budurwa ce ta fito cikin shiga ta dogon hijab

Wata irin fara'a ce a bayane a fuskarta ta nufo su da sauri tana fadin" Lalle marhababuki kanwata "

Itama murmushin ta sakar mata tana kama hannunta kamar yanda ta miko mata ta ce" *MAMI* na same ku lafia? "

Mami ta janyota jikinta ta ce" Ke meye kike wani dari dari, zo mu je ciki mana"

Har sun juya zasu shige ciki mahaifinta ya kirayi mami hakan ya sa suka dakata ta juyo tana kallonsa ta ce" Na'am Aba? "

Da yaren filatanci ya ce" Dan Allah bana so ko da wasa mamanku ta nunawa Bilkisu wani abin, kin ga Bilkisu y"ata ce ta cikina, ku biyu kawai na malaka kuma ina son abina"

Kanta ta gyada ta ce" In sha Allahu Aba, ai na gyara mata dakina ta yada zata walala da ranta, in sha Allahu ba abinda zai faru"

Bilkisu dake kallon kasa baki daya tana jin su, basu san cewa ta iya filatanci ba hakan ya saka mahaifinta yin yaren a kusa da ita, dan basu taba yin filatanci da shi ba
A kasan zuciyarta sai take jin wani dardar na tsoron shiga cikin gidan, shin matar gidan bata maraba da ita ne ko me? To me ta yi mata ita kuwa da ko ta zo gidansu bata taba yin zaman sama da awa daya ba bale ta ce ta mata wani laifi?

Sukuku ta bi bayan Mami har suka shige cikin gidan

Kofar dakin mahaifiyar su Mami din suka tsaya suka ringa salama sama sama

Da kyar aka amsa masu, cikin sanyin Murya Bilkisu ta ce" Mama nice Bilkisu ina yini "

Maman nasu ta dan yi jimm kafin ta amsa a dakile ba tare da ta kuma tambayarta gida ko mamanta ba ta ci gaba da ninkin kayanta

Janta Mami ta yi suka nufi dakin mamin

Abinci ta gabatar mata da su ruwan sha , baki daya a ciki farin cikin ganninta zaune yau itama tare da yar uwarta mace jinni guda, tun dazun da mahaifinta ya shaida mata maman Bilkisun ta yi kira cewar gatanan zuwa zata kwana biyu ta kasa zaune ta kasa tsaye sai da ta tabatar ta gyara mata waje ta mata girki sannan ta kimtsa tana gadin zuwanta

Bilkisu ta kalli hannunta dake cikin na mami ta saki murmushi a hankali ta ce" Lah, jibi tsagun hannayenmu sun kusa zuwa iri daya bayan bama kama Mami"

Mami ta fadada fara'ar fuskarta ta ce" Bilkisu, ima farin cikin kasancewarki a tare da ni, dan Allah ki yi zamanki a nan mana, kin ga Aba burinsa kennan ya hade mu a waje daya duda an kusan yi mani aure aman ina mai gabatar maki ko an min zan ringa zuwa kulun ina ganninki kanwata "

Bilkisu ta ringa jin wata irin kauna irin ta dan uwantaka na ratsa dukan gabai na jikinta,

A nan suka shiririce sunna ta labari, har mutumen da zai auri yayarta ya zo, watau UMARU
Ba wani zance sukai ba, Mami sai lalabewa take hakan ya ringa saka Bilkisu kilkilar daria har tana rike cikinta

Bai wani jima ba ya tafi, Bilkisu dama tana cikin hakin wanki, wanka kawai ta yi ta nemi waje ta ajiye hakarkarinta dan samun baci duda bata tunanin in har zata iya rintsawa

Haka kuwa ta kasance, domin kwana ta yi tana juyi sam bacin ya kasa zuwar mata, ga cenjin yannayi, ga rashin sabo, ga damuwa, zata iya cewa Alhamdulilah bata ga baci ba

Da sanyin safia ta farka ta fita tsakiyar gidansu

Tsintsiya ta dauko ta shiga share balbalin gidan mahaifinta mai girman gaske cike da kuzari domin ta dauri aniyar aikata nasihar mahaifiyarta ko dan ta samu zaman lafia da matar mahaifinta




. ............. *Walahi Jama'ar gidan DUK NISAN JIFA baki na yi , shi yasa kuka ji ni shiru ba labari, aman ina biye da comment din ku sau da kafa, na gode Allah ya saka da mafificin alkhairi, ina ji da ku fiye da tunaninku, Allah ya baku ikon ci gaba da bani zafafan comment*


BA EDDITING

Sajida ce
🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾
*DUK NISAN JIFA*
_(K'asa zai dawo)_
🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾

_RUBUTAWA_

*SAJIDA*

*SADAUKARWA*

*GA*

*MASOYA NA*


πŸ’«βœ¨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🀝

β˜† *[ T.M.N.A]* β˜† πŸ“–πŸ–ŠοΈ

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_


19




Shara ta yi ta mamaki, domin baki daya balbalin gidan nan sai da ta share shi tas tas sannan ta nufi wajen kwanonin da ta ga a ajiye duda basu da yawa haka ta wanke su tas sannan ta koma dakin ta dauko kayan wankanta da hijab dinta ta nufi bayi

Bayin tsakar gida ne da su har kwaya uku, na wankan ta shiga mai dauke da pampon sama da na kasa
Bata yi wankan ba sai da ta wanke shi tas tas, ta fito ta shiga sauran bayin suma du ta wanke domin a kowani bayi akoy clean da hypo da tsintsiya da buta ta wanke bayi, sai da ta gama tas sannan ta yi wankanta ta fito

Tana fitowa sukai ido hudu da matar gidan sanye da hijab a jikinta da alamu ta fito ne dan fara aikace aikacen cikin gidanta

Har kasa ta duka ta gaisheta cike da ladabi da biyaya hakan ya saka matar yin sokoko tana kallonta kafin ta amsa mata sai kuma ta bita da kallo har ta shige dakin Mami

Ajiyar zuciya ta sauke ta koma dakinta har gari ya hantse sai ta fito ta dora girki dama ta fito ne ta tsaftace gidan sai ta ga yarinyar da ta kasa cire kishin mahaifiyarta da tsoron kar a je wata mai baudadan hali ce rana tsaka za'a ce zata wani zo ta zauna da su ta share gidan ta tsaftace kwanoni harda bayi

A kasan zuciyarta ta ayanna 'Ba dai zan sakar maki fuska ba domin ba'a yabon dan kuturu sai ya shekara goma da yatsa, ban san me ya kawo ki gidana ba, kar a je mamanki ta turo ki ki kulan wata fitina ina zamana lafia da mijina, ta rabu da shi shekara da shekaru ta kasa aure kar a je yanzun ta waiwayo min abina ne dan ta hadasa min rashin kwonciyar hankali kamar yanda shekarun da ya aureta na kasa samun kansa har sai da ya rabu da ita!'

Wankan da Bilkisu ta yi sai ta samu jin dadin yannayin, hakan ya sa tana kwonciya sai baci ya dauketa

Ba ita ta farka ba sai kusan sha daya, a rikice ta mike tana salati tana kallon agogon dakin mami

Da sauri ta shuri brosh dinta ta fito tsakar gida

Mami na zaune tana daka a turmi sannan tana yiwa mamansu hira sunna yar daria ta dago da kanta ta ce" Hala har bacin ya isheki haka? Ko zafi ya tashe ki ne? Mama sam bata yi baci ba tsakiyar dare ban san ko me ya hanna mata rintsawa ba"

Mamanta ta ce" Eyah " daga haka ta yi shiru bata kuma tofa wani abin ba

Ita dai sai da ta wanke bakinta da fuskarta sosai sannan ta mayar da shi ta cenza audugarta ta kule wada ta cire din a leda baka da ta zuba a jakarta dan irin haka sannan ta fito ta nufi bayi mai dauke da masai

Tana shiga ta saka cikin masai din sannan ta rufe ta kunna pampo ta kara tsaftace jikinta sannan ta fito

Tana fitowa ta ga maman Mami tsaye kikam, ido cikin ido ta ce" Meye kika shiga da shi a leda ? "

Bilkisu ta dan tsura mata ido sai kuma ta sada kanta muryarta a sanyaye ta ce" Auduga ce na saka a masai Mama "

" LAFIA kuke tsaye haka a bakin bayi? " muryar mahaifinta ya karade wajen yana karasa shigowa da kafafuwansa

Matarsa ce ta dan daburce sai kuma ta ce" Ba komai baban Mami "

Murmushi ya yi yana kallonsu, Bilkisu ta duka ta gaishe shi

Irin yanda yake amsa mata cike da kulawa sai take jin wani irin yannayi na daban a zuciyarta a kansa, kauna ce irin ta mahaifi tsaftataciya mai kima, kauna ce tataciya mai daraja ke ahiga zuciyarta ko tace ke yin tsiro a cikin zuciyarta

"Ta karya ne?" Ya tambayi Mami dake tsayen itama jikinta du a mace sakamakon abinda mamarta ta yi na rashin yarda da nunawa da take kamar Bilkisun ta zo ne ta yi mata wani abin dan ta bata zamanta da mijinta ko ta saka ya maida mamanta dakinta ta dan girgiza kai ta ce" Yanzu ai ta farka Aba "

Abansu ya ce" To maza ku zo ku dauki abincin cen na dakina ku ci, bana son wasa da yinwa "

Mami ce ta fi kazar kazar, ita Bilkisu matsala ta rashin saurin sabo da mutane na damunta hakan ya sa sai dai ta bi Mamin da kallo har ta dauke wata kyakuawar kula shake da lafiyayan abinci ta ajiye masu saman tabarma kasan shukar mangwaron da ya yi diya sosai ga sanyi

Ruwan sanyi ta dauko masu da cokali sannan ta yiwa Bilkisu Bisimillah cike da kulawa

Zasu fara cin abincin kennan saurayin Mami ya yi salama

Da sauri Mami ta kafe Bilkisu da kallo a hankali ta ce" Na shiga uku me ya zo yi daidai lokacin da zan ci abinci? "

Bilkisu ta saki murmushin da ya fito mata tun daga cikin zuciyarta , domin irin yanda ta tsatsare Bilkisun da manyan idannuwanta sai abin ya mugun kasheta da daria, kunya, asalin kunya irin ta filani ce Mami ke nunawa a dukan motsinta, shi da kansa sai ya zauna ya maida gabansa gabas yana gaishe da su Mama

Abinda ya kara birgeta ya kasheta ya bata daria irin yanda maman ta tikice sai wani murza goshi take ta rasa inda zata tsoma ranta, ba irin sirikan zamani ba dake shagalinsu gaban sirikan nasu ba abinda ya dame su wai wayewa

Aba ne ya fito ya dan toge ya ce" Yauwa ka kawo? "

Kansa sade ya gyada kansa ya mika masa sako a leda sanann ya mike da sauri ya fice

Sai da ya fita, Aba ya bar wajen , sannan ta sauke ajiyar zuciya harma ta iya yin numfashi mai dadi

Waigawa Bilkisu ta yi ta ga Maman bata nan, hakan ya sakata yin daria a bayane ta ce" Ina Mama? "

Mami ta ce " Uhum, ai bata san zai shigo yanzun ba, da bai tardota ba, yanzu wannan gannin nata da ya yi da ranar nan gata ga shi ai ba zamu kuma ganninta ba sai gobe"


Cike da Mamaki Bilkisu ta ce" Aman meye anfanin hakan? Ina ce aurenku bai fi saura wata ba?"

Mami ta zarro ido ta ce" Ke Balki, mamanki ba bafilatana bace ina? Yanzu mutumen da aka saka mana rana saura yan kwanaki sai kawai mahaifiyata ta yi ido hudu da shi? Ai ko ni nan ana cewa wai bani da kunya ina sauraronsa idan ya zo min zance bayan basu san ba ni ba abinda muke cewa junna da wannan mutumen"

Bilkisu na rike dariyarta ta ce" Sunnansa UMARU ai"

Kanta ta dafe ta ce" ke kam idan aka saka maki rana ban san yaya zan yi da bakinki ba, birni ta lalata ki, yanzun sunnan wannan mutumen kike kamawa haka? Uhum"

Bilkisu kam a yau sai take jin kanta a wata duniya ta daban, a hankali ta ce" Sai nake gannun kunyar nan ta yi yawa, kin ce aurenki ya kusa ban ga an shiga yi maki shirye shiryen nan da ake yiwa amare ba, ban ga ana baki abubuwan sha ba, ban ga kema kina nemawa kanki wasu abubuwan ba bayan yanzun zaki ga yan mata da kansu suke nema gyara ne"

Mami ta gyada kanta ta ce " Haka ne, gyara ne, aman kin ga mu wancen tulun da kika gani dauke yake da maganin zafi, irin mai cire datin nan mai kashe sanyin nan, iya shi ake mana, ba'a yi mana wani gyare gyaren fata, idan mun je dakinmu sai mu yi abinmu a dakanmu, Bilkisu mu idan budurwa ta tsiri irin haka ai ta janyowa kanta da iyayenta abin magana, sai kace ba budurwa ba? , kuma maganar kunya ai Bilkisu kunya ado ce ga y'a mace, bari ki ji ko a zuciyarki bakya jin kunyar nan arota ki yafawa kanki, ba'a so mace ta zamana ita bata nuna halaya irin na jin kunya a gaban namiji, ko mijinta ne ko abokanan zama ne na yau da kulun, kunyar nan baban makami ne da muke takama da shi a duniyarmu"

BILKISU ta ringa gyada kanta tana kallonta, tabas ko da wa ka zauna zaka karu da sanni da dabi'u irin nasa, zaka anfana da ilimi na yau da gobe, tana da kunya mai girman gaske fa, aman a yau ta ga ahalinta da suka dameta suka shanye a kunya

Mami ta janye hannunta daga saman cokalin ta dibo abincin ta nufo wajen bakin Bilkisun hakan ya sakata dan zarro ido ta girgiza kanta

Mami ta yi murmushi ta ce" Baki isa ba, ina sane da tunda muka fara baki ci da yawa ba bayan Mama ta iya girki sosai, ci ko na dane ki na maki dura bari gannin kin dan fi ni gwabi "

Daria ce ta kama Bilkisu, kwarai ta fita gwabin sosai ma kuwa, Mami na fama da rashin lafia irin cutar kashi, mai karfin nan, cutar tata ke karar da ita lokaci zuwa lokaci, wani sa'in idan ta tashi har sai an cire rai da ita sai kuma Allah ya tashi kafadunta, tun tana jaririya mahaifiyarta ke fama da dawainiya da rashin lafiyarta, idan aka ce sanyi ya matso ko lokacin damana, kai wani lokacin ko zamanin zafi ciwon yakan tashi , sai ta kare kaf ta dawo sai kashi sannan ta samu lafia kuma sai ta dan farfado ta dan maro

Sai da suka gama cin abincin sannan suka nufi madafar, a cen suka gama dafa abincin da Mamansu ta fara suka zuzuba suka kilacewa kowa nasa

Sai bayan sallar la'asar yayansu ya dawo, nan Mami ta sakata daukan litafi suka je kasan innuwar nan bayan ya gama cin abinci suka shiga karatun alkur'ani mai girma

Irin yanda Bilkisu ke karatu ya saka shi jinta har cikin ransa, da farin ciki dankam a kasan zuciyarsa yake tambayarta a wace makaranta ta yi karatu ne?
Nan take shaida masa a makarantar Malan Hafizu (Allah ya jikan ka malamina, dan Allah ku mu yiwa Malan hafizu kulhuwalahu kafa uku uku Allah ya jadada rahama a kabarinsa da kuluhin musulmi, Allah ya sa kwonciya hutawa ce, domin kuwa shi din malami ne kuma uba a wajenmu Allah ya saka da alkhairi ) "

Tabas ya san mutumen, malamin akoy hakuri da jajircewa hakan ya saka su yin karatu mai tsayi yau domin tilawa suka yi ta bakara har sai da suka kai karshenta...................

A gidan mahaifinta yau kwananta hudu, sau biyu sunna waya da mamanta ta wayar Abanta domin a gidan yayansu da Aba kadai ke anfani da waya, Mami bata da ita, hakama maman mami

A zamanta a cikin gidan nan ta shaku da yan uwanta har take jin tsayin lokacin da ta dauka ba tare da su ba ta yi asarar rashinsu a cikin rayuwarta

Sosai suke fahimtar junna da Mami, takan kiya mata wasu al'adun nasu na filani da ita bata sansu ba domin mahaifinta da mahaifin mami asalin filanin jeji ne masu al'adu da dama haka kuma sunna rike da al'adunsu kai da fata

Takan sha daria idan Umaru ya zo zance, Umaru dan kasuwa ne yana harkar waya da yadika, yana da kokari sosai domin irin yanda yake iya yinsa dan gannin amaryar tasa na cikin walwala sai Hamdallah

Umaru d'a ne a wajen kanwar maman su Mami, bata taba gannin matar ba, aman shi Umaru yana da kirki daidai gwargwado

Irin yanda Mami ke sakata a tsakiyarsu idan ana zancen abin ke sakata tikar daria da nishadi, wani sa'in idan labe laben ya isheta sai ta shamaceta ta gudu daki, hakan ke saka Mami fit itama ta tsero dakin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login