Showing 87001 words to 90000 words out of 180809 words

Chapter 30 - DUK NISAN JIFA COMPLETE HAUSA NOVEL

sajida   

02 Feb 2025

12986

a haka

A hankali ya buda idannuwansa yana mai dafe bangon kofar tata suka hada ido da Aisha wace ta zo itama tana fadin "Bara na taya ka fitar da ita Hamanta ka ga tun safe Tati ta je na je aman ta ki fitowa mama ta ce wai mu kyaleta haka take idan yan rashin maganar suka motsa"

Shiru ta yi sanadiyar yannayin da ta ga ya shiga na lokaci daya da kuma irin yanda idannuwansa ke neman shanyewa karfi da yaji

A hankali ta sada kanta sakamakon abinda ya tsirga mata na tsoro da tarin kishi a kasan zuciyarta na yannayinsa
Zara iya rantsewa rabonsa da ya yi mata kallo irin wannan tun na daren da ta je masa a lokacin da bai san zata iya shigo masa ba har ya mata damkar da ba ita ta tada fitinarsa ba domin idan bata manta ba a tsaye kikam ta tarda soldier dinsa ba wai sakamakon ganninta ta motsa haka ba, to wai anya yana jin sha'awarta? Yau kwana na uku kennan da ya wayi gari ya mayar da ita cikakiyar mace a lokacin da basu shiryawa zuwan hakan ba, ita, ita zata bada shaidar cewa namiji ne harda kari a kan namijin domin sumewa ta yi tsabar azabar sabuwar rayuwar da ya kutsa da ita da abin da ya nemi waje ya cusa mata a lokacin da idannuwansa ke rufe bilhaki har sai da ta rasa numfashinta baki daya
Da ba dan haka ba sai tace ko motsin mace baya motsa shi? Sai dai kash, a yanzu yanzu da ya shigo gaban wandonsa bashi da wannan tudun duda tudun ba baban tudun da za'a iya ganewa farat daya bane dan kuwa da wandunna irin kananu da kuma matsatsen dake iya tare fitinar namiji kar a falasa shi zama daya, sai dai kash ya makaro domin dai koda shedan ne ya kai dubanta wajen ko kuwa motsin da wajen ya yi ne? Ita dai ta gani kuma ta ji wani irin abu ya sokar mata kahon zuciya a irin wannan lokacin

Da sauri ya juya yana beman hanyar da zata fitar da shi daga falon da gidanma baki daya
Sai dai a lokacin da ya kusan fita a falon ya juyo baya ko iya gannin gabansa da kyau ya dawo wajen da ya barta tsaye ya kama hannunta ba tare da ya yi mata kyakuawan bayani ba ya ja hannun nata ya fita da ita daga falon wanda hakan ya yi daidai da fitowar mahaifiyarta daga dakin dake kusa da na Tati tana amsa wayar mijinta da alamun hankalinta a dan tashe

Da ido ta bi su, ta so ta bi bayansu sai ta fasa ta nemi waje ta zauna da wayar a hannunta ta ce" Kuma yau yau zasu yi conseil din? Ya zama dole ka koma da wuri ni sai na koma asibitin aban Aisha "

Mijinta ya ce" Ko na koma a yanzu ba zan samu gannin Ministan nan ba, ina tsoron wajena ya koma hannun yan adawa, aman dole zan zo na ga mijin Aisha domin shi yana iya yin waya direct da president ya masa maganata "

A kan dole a haka suka ajiye maganar domin wannan shiga tari da za'a yi komai na iya faruwa ciki harda tsige shi a kan kujerar da yake takama da ita wace har yake da fadawan da suke masa fadanci dan suma su tsira sa nasu aikin ko su samu ci gaba, wanda idan yau aka ce an tsige shi shikenan zasu zubar da shi ne su kuma yayami sabo domin dama kujerar tasa suke yima hakan ya saka su kwanan zulumi

Wani dare ne mai cike da abubuwa , a wannan dare shine darenta na biyu da wannan bawan Allah
Dare na biyu wanda ta kara karda waye shi a fannin jarumtarsa da kuma adalcinsa, domin a yau dai bata kuma sumewar ba aman ta shide ya fi a kirga hakan ya sa ya taimaka mata har sai da ta shaida masa cewar zata iya idasa gasa kanta sannan ya fita a bayin

A lokacin da ta fito daga bayinsa ta tarar da shi kansa a kasa ya kai sujada wace har sai da ta gama shirya kanta ta nemi waje ta zauna tana duban agogo gannin har karfe daya ce ta kusan yi bai dago kansa ba

A kadan a wajen nan ta kwashi minti ashirin sannan ya dago da fuskarsa wace sai da ta saka gabanta ya tsinke ya fadi tsabar damuwa da yanda har jijiyar gaban goshinsa ta yi wani irin rado rado da ida, sannan idannuwansa tamkar ba nasa ba sun yi jajajir da su hakama fuskar tasa kanta bayan zufa da ta hada ta yi jajajir alamun yana cikin muguwar damuwa

Gaba daya ta ringa jin kanta a yannayi na damuwa, bawan Allahn nan dake cikin wannan yannayi shin ita din nan ita ce damuwar ko ba ita bace?
Tabas adalcinsa a gareta ta shaida sai dai har yau da ya sauke fitinar da ba ita ta tayar ba bata ga ko digon soyaya ba a tatare da shi

Bata gama tunaninta ba ta ji muryarsa mai dauke da amon murya irin ta kakarfan namiji jarumi aman a cikin yannayi na sanyi da dabe bacin rai ya ce" Tashi na raka ki "
Sai kawai ta ji wani irin tashin hankali wanda bata taba jin irinsa ba, kamar an kawo mace waje an gama anfani da ita za'a yi mata rakiya bakin kofa? Kamar wata marar gata? Kamar wata wace ta zo aka yi aka biyata? Subahannalah, bata taba tunanin zata fara jin wani abu mai kama da tsoron auren cushe ba irin na yau, wai duka duka har ta fara jin tsoron yaya zasu kasance gobe? Har ta ji ta fara shayin yaya zasu wanye gobe?

Jiki ba karfi ta mike daga zaunen da take a bakin gadon mijinta, ta kama hanya daga ita sai kalabinta dake saman kanta domin ko hijab babu ya mata cirar higa tana gaba yana biye da ita har sai da ya raka ta har tsakiyar falo sannan ya yi mata sai da safe ya juya ya nufi bangarensa

Wani kuka ne ya zo mata daidai wuyanta hakan ya saka da sauri ta fada dakinsu ita da mahaifiyarta da niyar kufa kanta ta koka ko zata ji tsoron ya fita a ranta

Tana shiga ta sauke idannuwanta a kan mamanta daje zaune kuri tsakiyar gadon tana dan karkada kafarta ta dama ta hagu din na tankwashe hakan ya nuna mata cewar mamanta na cikin tashin hankali dan haka da sauri ta nufeta ta hau saman gadon duda zogin da kasanta ke yi mata aman haka ta jure ta kamo hannun maman nata ta ce" Kin gani ko? Har yanzu ban tare a gidan da akai min jere ba, wace take takamar ta isa ta saka shin ta saka shi aurena a lokacin da bai shiryawa hakan ba aman ta kasa saka shi ya kilace ni ya ririta ni irin na amare, mama kwata kwata baya so na walahi ba wani digon so na a tatare da bawon Allahn nan"

Mahaifiyarta ta kama hannunta da kyau ta ce" Ke Aishatou ki nutsu ki saurare ni, ba maganar shirme nake yi ba yanzu, mahaifinki na cikin damuwar da ake iya tsige shi daga saman kujerarsa a kowani lokaci, wanda mijinki na iya yi masa maganin damuwar nan, ke nake dakon jira da koda safia zaki kai a cen sai kin shigo zan iya rintsawa idan na sanar maki abinda yake damuna, abinda nake so da ke shine ki yi masa bayani ta yada zai yi kiran President ya fada masa kar a sauke mahaifinki daga kujerarsa"

Ya Allah, lalle sai a yau ta gane cewar auren jari akai mata, sai a yau ta fahimci cewar jin dadin zama da miji ko akasinsa ba shine a gaban mahaifanta ba, muryarta a raunane ta ce" Mama , kin kuwa ji damuwata?, mama to yaushema aka yi auren namu da har zan billo masa da irin wannan maganar? Mutumen da ban ishe shi kallo ba har zai min wata alfarma ce irin wannan? Mama waima waye shi a kasar nan da har kike tunanin wannan lamari mai girma shi yana zaune a dakinsa zai iya magance maku shi? Mama ni abinda ya fi daga min hankali abinda nake fuskanta, duda yana bakin kokarinsa a matsayinsa na wanda akaiwa laifi yana kawar da kansa yana nuna min kulawa gwargwadon iyawarsa aman ni ban hangi rayuwata da mijina a haka ba"

Mahaifiyarta bata san lokacin da ta buga mata tsawa ba tana nunata da yar yatsa ta ce" Ki rufawa kanki asiri ki kamawa mahaifinki, domin cikin alatun da kike ciki dan yana rike da mukamin kawata maki rayuwa ne! Kin kuwa ga dakin ki? Kin ga gidanki? Ki ajiye min maganar wata soyaya ta banza da wofi mu fuskanci damuwarmu! So so so, to wai komai a so din zai kare ne ko shirme? Idan baki ishe shi kallo ba ya mayar da ke mace? Yanzun me kika fito yi a dakinsa ko baya taba hannunki yake kusantar ki? Bana son shashanci da yarinta dake dawainiya da ke , maganar waye shi shine kuwa wani, in ba dan kulafucin uwar rikonsa da ya saka a ransa ba kina tunanin ganninsa ba sai kin kusa wata kina cike takardu ba? Ki farka baban mutun kike aure ki kama mu fitar da mahaifinki kin ji dai abinda na fada maki dan haka yanzu yanzu zaki tashi ki koma masa da maganar dan ya san mai mahinmanci ce!"


Aisha tana hawaye ta ce" Mama yanzu kuma? Dan Allah ki bari safia ta yi kar ya ga azarbabinmu da kwadayinmu a bayane?"

Mahaifiyarta ta ce" Wasa kike, na san da cewa kina sonsa, to ina mai tabatar maki ko soyayar tasa sai dai ta kashe ki idan mahaifinki ya rasa wajen nan, dan a yanda na lura da uwarsa ta yi hadin nan ne dan ta samu a wajen aikinta ba dan komai ba, domin karara soyayar yar yar uwarta bata iya boyewa idan ke baki lura ba bara na sanar maki a yanzu yakin da take na yada zata saka yar yayarta ne dan kuwa koda ta boye sonta a bayane yake koda Allah ne ya kamata ta hanyar saka mata soyayar Bilkisun nan to fa ta kamu, ki motsa da jiki tun kafin damarki ta kubuce maki, kin ga dai kin rigaya kin rasa abinda kike takamar da shi ya amshe ya kwamushe ko tarewa baki yi ba! "


Jiki a sanyaye Aisha ta sauka daga saman gadon ta juya ta kama hanyar bangarensa duda uban daren da ya tsala wanda a fitowarsu ta dazu Kader na tsaye yana kai kawo a cikin aikinsa haka a yanzunma ta fice ya rakata da kallo ya cire dubansa ya ci gaba da aikinsa yana kai kawonsa

Tsayuwa ta yi gabanta na dokawa kamar zai yi tsale ya fado daga kirjinta ta shiga dan kwonkwasawa tana adu'ar Allah ya sa ta kwana a nan tsaye ba tare da ya bude ba...............









*Asakamu alaikum, sorry people wollah ni jiya da yau sai a slow, aman gashi in sha Allah idan baku ji ni ba ku tabata abu ne mai mahinmanci na gode*
[7/24, 10:19 AM] BAK'A CE: 🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾
*DUK NISAN JIFA*
_(K'asa zai dawo)_
🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾

_RUBUTAWA_

*SAJIDA*

*SADAUKARWA*

*GA*

*MASOYA NA*


πŸ’«βœ¨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🀝

β˜† *[ T.M.N.A]* β˜† πŸ“–πŸ–ŠοΈ

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_


34



Ba edditing



Ta daga hannunta zata kuma bugawa ya bude kofar,
Ido hudu suka yi yannayin da ta barshi fuskarsa ba annuri haka ta kuma samunsa yana tsaye kikam a bakin kofar shi bai bara hanya ta shige ba, shi bai rufe kofar ba

Baki daya sai ta daburce ta shiga inda inda karshe ta samu kanta da fashewa da kuka marar sauti sai hawaye dake zirara daga gurbin idannuwanta tana kara sada kanta tamkar an kawota gaban sarkin da ta yiwa karya

Idannuwansa ya lumshe, sam bashi da lokacin da zai iya karawa ransa damuwa, ya rufe ne ya ci gaba da ibadarsa ko zai samu mafita? Take taken mutanen dake zagate da shi ya fara bashi tsoro da tunanin sunna son su kasara tunaninsa ne

Hannayenta biyu ta dago ta hade waje daya tama rasa daga ina zata fara, me kuma zata ce da shi, yau koda auren soyaya ne yana mutuwar sonta ne ta yi wayewar da ta san cewar idan ka nunawa namiji zalamarka a fili komai tsakaninka da shi ana iya samun matsala irin ta raini, wulakanci a ciki, bale ita matar cushe

Muryarsa a dake ya ce" Sun rufe dakunnansu ne? "

Dubansa ta kuma yi a karro na hudu run tsayuwarta a gabansa ta kasa bashi amsa hakan ya saka shi komawa gefe ya ce" Shiga "

Jiki ba kwari ta raba gefensa ta shige dakin tana sauri ta je wajen kujera ta zauna kanta a kasa

Tsayawa ya yi yana kara kallonta, yaya aka yi ta kasance mai sanyin hali haka? Allah yana ganni irin sanyin halinta ya saka shi kasa yi mata rashin mutunci ko wulakantata, tabas da farko ya so ta kori kanta dan kanta saboda irin abinda ya mata tanadi na wulakanci , sai dai daga bakin ranar da ya sameta a budurwa sai kuma irin kalaman da ta furta masa a kan BILLY sai ya ajiye makaman yakarta da ya yi niyar yi, saima ya sakawa ransa zai bata darajarta a matsayinta na matarsa zai yi iya yinsa kar ya tauye hakinta

Sai da ya yi gyaran murya dan baya so kwata kwata kowama ya gansa a yannayi na bacin rai sannan ya ce" Tashi ki shiga cen dakin ki kwonta "

Dakin da ya nuna mata na kusa da dakinsa na baci ne, hakan ya saka ta mike jiki ba karfi ta nufi dakin tana yi tana tsayawa tamkar wace ake dannawa stop sai kuma ta daga kafarta har ta karasa ta bude ta shiga da bismillah

Sai da ta rufe sannan ta duke a wajen ta dora kanta saman gwuiwarta, rashin lafiar kakanta ya saka ta fuskanci su waye iyayen da suka haifeta, ta kasance tana zaune ne da kakanta, mutun mai daraja, mutun mai mutunci, mutumen da dukan tarbiyarta shine ya dorata sama, du irin sangarta ta kakani da suke yiwa jikokinsu tana samu a wajen kakanta aman kuma du wata tarbiya da ya dace ka yiwa yaro ya jajirce ya yi mata , a wajensa ta ji kalmar nan watau shi mutunci madara ne, daga bakin lokacin da ya zube shikenan kwasuwarsa zai zamo wahala, haka budurcin y'a mace yake, idan ta yarda ta zubar da shi ta hanyar shashanci ko wani iri ne ta cuci kanta, ta cuci iyalinta gyara kuma na Allah ne, tun daga nan ta dauri aniyar kilace kanta, samarin kansu sai take baya baya da su

Tabas zata nemi alfarmar komawa kusa da kakanta, tana kallonsa tana gannin warkewarsa idan ya samu lafia ta labarta masa abinda ya sameta, a yanzun babar damuwarta wannan umarni na mahaifiyarta wace ke cen zaune tana jiranta

Kusan a nan kasa ta kwana, sai da asuba ta samu ta dauro alwallah ta rasa ina zata samu abin sallah domin dai bata ga hijab ba, tayayama zata ga hijab bayan bangaren namiji ne ba mace ta taba tarewa a bangarensa ba bale

Tana nan zaune ta ji kwonkwasa dakin hakan ya saka ta tashi a dan tsorace tana kallon kofar kafin ta karasa ta bude ba tare da ta tambayi ko waye ba

Dan tsai ya yi, a kasan zuciyarsa yana ayanna 'bata tambayi ko waye ba ta bude idan wani mugu ne fa?'

Abinda ke hannunsa ya mika mata bai tsaya jin komai ba ya juya ya fice a dakin kwata kwata ya nufi masalaci

Itama komawa ta yi ta warware hijab ne ruwan hoda, sai kamshi yake, kamshin turaran da ta ji shi a dakin Bilkisu, du inda ya fito hijabin Bilkisu ne wannan

Haka ta saka ta tayar da sallah
Tana gamawa ta bingire a wajen ta kama barci, sai kusan karfe bakwai ta farka da sauri tana kallon tagar dakin ta ga da hasken rana har rana ta fito hakan ya sakata mikewa ta koma ta wanke fuskarta sannan ta bude dakin ta fito cikin sanda tana tunanin makomarta

Ido hudu suka yi yana tsaye cikin shigar sweeeeet aman bai dora rigar ta sama ba yana balla agogo a hannunsa

Farar ciga ce ta cikin, haka kuma bai bala botiran saman kwaya uku da suka rage ba

Irin tsayuwar da ya yi irin ta a tsaya din nan kafa a dan ware kafarsa sanye cikin bakar safa sidik wace bata da kwaliyar komai sai necktie dinsa dake ajiye itama kusa da rigar saman da zai dora

Muryarta na rawa ta ce" Barka da safia , an tashi lafia? "

Jin shiru bai amsata ba ya saka ta dago da kanta dan gannin ko tafiarsa ya yi?
Sai ta ga sun yi ido hudu again hakan ya sakata sada kanta gabanta na dokawa

Muryarsa a dan shake ya ce" Me ya saka ki kuka jiya ko na ji maki ciwo ne? "

Allah yana ganni sai da ta ji gabanta ya kara faduwa, wayo Allah son maso wani, wayo duniya iya muryarsa na neman zautar da ita, iya yan kalaman nan da ya yi ya sakata kamar ta taka rawa tamkar wanda ya wani ce da ita Aisha ina kaunarki ina son ki,, damuwar kennan, matsalar kennan, watau idan kana son mutun ko amsa gaisuwarka ya yi kai ka gode an wuce wajen sai casu, kai sallah ce a wajenka, abin farin ciki

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login