Showing 114001 words to 117000 words out of 180809 words

Chapter 39 - DUK NISAN JIFA COMPLETE HAUSA NOVEL

sajida   

02 Feb 2025

12995

kanta a tsayen da take tana ta rike kukan da take ji na son fitowa, ita daya ta shiga fadin" Dama kin san hakan na iya faruwa Asma'u, ki yi hakuri, ki yi hakuri ki jure domin idan kika karaya tun yanzu za'a tashi ba uwar ba ribar"

Yana fitowa tati ta mike da sauri tana kallonsa ta tarbi gabansa sannan ta saka hannunta ta tare kirjinsa duda irin yanda ya kereta a tsayi sosai tana kallon yannayinsa

Gabanta bai daina faduwa ba, haka kuma bata tunanin zata iya tsayar da maganarta tana kallonsa ta ce" HISHAM, SHIN MAHAIFINKA NA RAYE? "

Sai da ya lumshe idannuwansa yana kallonta, a hankali ya dago karfafan hannayensa ya dora a kan fuskarta ya talabo fuskar tata sosai yana kallonta kafin ya sauke ajiyar zuciya a sanyaye ya ce" YANA RAYE, YANA ZAUNE DA IYALINSA A YANZU HAKA A NAN CIKIN DAMAGARAM!"

Yana gama fada ya saketa ya fice a dakin inda wani irin abu ya shiga buga mata a kanta kamar ana doka mata guduma

Kafarta ta daga ya kai sau uku ta yi hanyar dakin mama sai ta dawo ta yi wajen kofa

Karshe dai da sauri ta fada dakinta ta dauko jakarta tare da wayarta ta fita dan amsar ky din mota daya ta fice a gidan kamar wace zata tashi sama ta nufi ainahin tsohon gidan da suka rayu da mijinta!


Kamar minti talatin tsakani Kader ne ya shigo falon gidan ya nufi mama dake zaune a kan kujera carbi a hannunta ta kasa katabus

Yana zuwa ya duka a gabanta gaba daya hankalinsa a tashe ya shiga fadin" Haba mama, haba mama, me kuke son yi ne tsakani da Allah? Mama menene haka dan Allah? Haba mamanmu me yake faruwa ne dan Allah?"

Ba zato ba tsamanin furucin mama, Kader ya ji ta shiga fadin kalamai kamar haka tana mai karra tsatsare shi da idannuwanta masu kima ta ce" Shin zaka auri BILKISU? "

tsittt ya yi da maganar da yake yi a hankali ya wawaiga ko zai ga da ainahin wanda mama take bayani da shi

Gannin bai ga kowa ba sai ya kara kallonta da niya ci gaba da maganar da ya shigo da ita sai dai kash, tun bai furta komai ba ya ji ta kara fadin kalaman nan wannan karron harda rike dan hannunsa dan ta samu amsa

A zabure ya mike tsaye yana kallon mama galala kafin ya ce" Takwarankwatsa ko wani shege ya nemi hakan sai mun halaka shi " wannan shine alwashin da muke yi ni da shi, yanzu mama tsakani da Allah kennan ni kike so a halaka din? Mama ni kadiri dan zuwaira nine zan tarbi wannan kasadar? Mama bari ki ji abinda yake faruwa ......"
Kader ya fada yana mai zama dangalgal yana tankwashe kafafuwansa tsabar kaduwa ya dago yan yatsunsa ya shiga irge da magana hankalinsa a tashe ya shiga fadin
........






I'm sorry biki muke wollah lv u all mutanena
[7/24, 10:19 AM] BAK'A CE: ๐ŸŽพ๐ŸŽพ๐ŸŽพ๐ŸŽพ๐ŸŽพ๐ŸŽพ๐ŸŽพ๐ŸŽพ๐ŸŽพ๐ŸŽพ
*DUK NISAN JIFA*
_(K'asa zai dawo)_
๐ŸŽพ๐ŸŽพ๐ŸŽพ๐ŸŽพ๐ŸŽพ๐ŸŽพ๐ŸŽพ๐ŸŽพ๐ŸŽพ๐ŸŽพ

_RUBUTAWA_

*SAJIDA*

*SADAUKARWA*

*GA*

*MASOYA NA*


๐Ÿ’ซโœจ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*๐ŸŒŸ
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_๐Ÿค

โ˜† *[ T.M.N.A]* โ˜† ๐Ÿ“–๐Ÿ–Š๏ธ

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_


41


Assalamu Alaikum
Masoyanmu da fatan kuna lafiya.

Muna miko maku godia da fatan alkhairi masu matukar yawa a yadda kuka nuna mana kara da kauna wajen siyan littafinmu na kudi.
Alal hakika munji dadi kuma mun gode sosai Allah ya saka da alkhairi ya kara budi.

Ina kuma kara kira ga masoyana wadanda basu siya ba dasu garzayo su siya domin muhimman darussa rayuwa, ilmantarwa da nishadantarwa dake cikin littafin. Dukkan wanda yaji taken littafin na *AURE YAKIN MATA* yasan littafi ne mai cike da ilmantarwa da bude ido akan irin rayuwar zaman auren da muke a zamanin yanzu don haka babu danasani a siyan littafin.

Yadda kuke siyan littafin yana kara mun kwarin guiwa wajen yi maku typing din littafina na *KOMIN NISAN JIFA* ina fatan zaku cigaba da siye don in samu kwarin guiwar yi maku typing din littafina na kyauta akan kari ba tare da bata lokaci ba.

Na yadda daku na aminta da irin kaunar da kuke mun, nasan kuma zaku siya littafinmu mai take *AURE YAKIN MATA*

*INA SONKU SOSAI INA ALFAHARI DA KASANCEWA A CIKIN DUNIYARKU.*

Ga mai bukatar wannan littafi *Farashin mai sauki ne* naira dari uku (300) kacal ga yan Nigeria, yan Niger kuma dala dari ne (500)๐Ÿ‘Œ zaka samu wannan littafi mai dubbin darussa a cikinsa.

_Domin tura kudin siyan littafin ga yan Nigeria sai a tura ta wannan account number din *2377403479* Khadija Umar Abubakar. Zenith Bank. Kuma akwai damar tura kati ta wannan lambar *081-686-594-14* IDAN KA YI TRANSFERT SAI KA TURA SHAIDA TA WANNAN NUMBER +227 93 81 16 18._

_'Yan Niger kuma sai ku tura katin MOOV ko Airtel ta dala dari watau 500 francs ta wannan lambar *+277- 94-98-56-52*_

Na yadda daku, na aminta da irin kaunar da kuke mun don hakan ina da yakinin cewa zaku siya don nuna mun kalar soyayya da kaunar da kuke mun da littafaina๐Ÿฅฐ


Kader ya ce"Mama idan baki sani bama ki sani walahil azim yaronki a kan Bilkisu dan ta'ada ne,a kanta ya iya irin maganar nan ta yan jagaliya sai ya murje uba da babarsa, mama walahi kin ga idan na ga Hisham na laso laso a kan abu nakan tare masa gaba na yi kundubala da abinda yake yiwa jinkirin na tarbi aradun ni, sai gashi mama sai ya fito da karfin gwuiwa sai ya dawo ya ce tausayinta yake ji, idan ya fada mata haka bata kai wajen gane me yake nufi ba, duka wannan rainon nata da ya yi ne yake nuna masa cewa yar yarinya ce bata kai daukan maganar samari ba balle kuma daga shi, mama kin ganni nan nine shaidar irin yanda yake daga kafa a kan izgili irin na Bilkisu, baya hukuntata sai dai mai rabon shan dukan wanda ya nuna mata soyayar, mama bana son na ganshi ya saki abu ya ja ya tsaya ya ce ba komai Allah na nan, mama a bakinsa yake furta haka a zuciyarsa ba hakan bace, mama wai shine da sakani ajiye shi wajen da baban bilkisu yake ya tafi ya fada masa a fara nema mata mijin aure yau yau yau , wai Hisham din yana fita a motar fa idannuwansa na son rufewa dan wahalar da zuciyarsa take ciki aman ina ganninsa na ce Haba Hisham wai me kake son yi, wa kake son birgewa? Sai ce min ya yi abin ya fi karfin birgewa umarnjn wace ta isa da shi zai bi, to mama shi kuwa tsabar ya raina kowa ke kadai yake bin umarninki ko wani iri ne , shi yasa na zo nan ki duba lamarin nan ba fa wasa ciki"

Mama kawai kallon kader take, shi tsakaninsa da Allah magana ce yake yi dan ya sakata ta yarda da maganar auren Bilkisu da shi Hisham din aman kuma bai san da ace zuwa ne suka yi lalabar iyayen yarinya aka ringa cewa wannen dan ta'ada ne, ko baya jin maganar kowa sai a hankali ba zasu samu ba

Murmushin da tun jiya bata yi ba kawai ta samu ta yi masa tana kallonsa ta ce" To na ji, ita Bilkisun ce ai tace bata son sa, ita a abanta ta dauke shi"

Gaba daya Kader ya shiga tafa hannu kai ka rantse a shirga masa karyan nan ne a cikin abokai zai karyata ya wani dafe habarsa ya ce" To ko giya ta sha? "

Mama ta yi masa zurru tana kallon ikon Allah

Kader ya dan juyar da kansa gefe ya ce" Kai ina, akoy abinda ya faru, ko yake faruwa tare da ita aman mama ita Bilkisun ce har ta ce wai Hisham abanta ne?............." sai ya samu kansa da yin yar dariya har yana hango Hishamu aban Billy ya ce" Kai inama zan iya hakura na ga baban Bilkisu da babar riga? "

Sai kuma ya girgiza kansa ya ci gaba da fadin" Mama, to a je din a haka, a kyale uwar kinibibin a aura mata baban nata baya komai, ke dai kawai saka a daura masu aure ki ga labari "

Mama ta juyar da kanta gefe ta ce" Kader tashi ka tafi "

Kader ya mata tsuru yana kallonta, gaba daya wadinnan mutanen sun rikita masu uwarsu walahi, kai shi fa idan iskancin ya yi yawa zai bugar da kowa a gidan nan ya ringa sace su daya bayan daya tun daga kawar uwar da uwar da amaryar ya bar masu gidansu iya su yanda suka fi morewa haba da Allah

Mama ce ta dan yi gyaram murya hakan ya saka shi gyarawa ya mike tsaye ya dan rankwasa ya dafe gwuiwoyinsa ya ce"kin samu mai biyaya mamanmu, walahi yana maki biyaya sosai, yau ko dan auren dolen da kika masa sai ki bashi wace yake so, mama kar ki biyewa magauta a kashe maki da a maki asara dan ke kadai kike da asara fa wollahi sai ko ni da zan yi ta ihu sai magulmaciyar mai tashen fitsarar dayar da zata kume kwana biyu ta bi shi, mama basu taba samun yar matsalai irin ta an mata magana saurayi a waje bai sha karin ruwa ba, nan da nan ruwan nasa yake yin kasa komai ya sauka sai an je an rufu a kansa, ko ciwon zuciyarsa baya tashi sai sun samu matsala dan walahi kwoncin nan da ya yi sau biyu a asibiti harda likitan zuciya tun daga Niamey Mr president ya turo aka duba shi yana ta fadan idan ba sauki a tafi maroko su bude kirjin su gani kiri kiri ya ce aa da sauki yo shi mahaukaci ne zai yarda yanzun ya yi tafiar kusan shekara Bilkisu na garari a anguwa? Aa idan dai ya daga sun daga ne ko a kaishi kabari ina dalili wannan kwalafa rai da abu?"

Mama da tunda ya fara maganar zuciya kirji ta yi tsai tana kallonsa ta ce" Lader waye yake da ciwon zuciyar? "

Kader ya yi gummm yana kallonta , innalilahi ya saki baki yana fasa eriya kala daban daban ashe harda wace ya masa kashedin idan aka jita shi da shi ne?

Idasa mike tsayinsa ya yi ya juya yana fadin" Ba komai, kuma walahi iya zuwaira ta min mata hudu a daina sakani a rigimar nan, kuma Allah dai"


Sako zuwa gareku yan uwa da abokanan arziki, biki muke๐Ÿ˜


๐ŸŽพ๐ŸŽพ๐ŸŽพ๐ŸŽพ๐ŸŽพ๐ŸŽพ๐ŸŽพ๐ŸŽพ๐ŸŽพ๐ŸŽพ
*DUK NISAN JIFA*
_(K'asa zai dawo)_
๐ŸŽพ๐ŸŽพ๐ŸŽพ๐ŸŽพ๐ŸŽพ๐ŸŽพ๐ŸŽพ๐ŸŽพ๐ŸŽพ๐ŸŽพ

_RUBUTAWA_

*SAJIDA*

*SADAUKARWA*

*GA*

*MASOYA NA*


๐Ÿ’ซโœจ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*๐ŸŒŸ
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_๐Ÿค

โ˜† *[ T.M.N.A]* โ˜† ๐Ÿ“–๐Ÿ–Š๏ธ

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_


42


Ba edditing fa


Mama ta raka shi da kallo tana jin gabanta na faduwa da sauri ta dauki wayarta dake ajiye gefe ta shiga latsawa ta danna kan sunnan yaronta wanda ta dora yarona a sama ta shiga kira tana jin hankalinta na neman kara tashi kan na da

Ringin take tana karawa ana kashewa ita kuwa ta ki daina kiran sai cen aka daga muryar cen ciki ya ce" MAMANA "

Gaba daya sai da mama ta ji hankalinta ya idasa tashi, jikinta ya gama mutuwa, a sanyaye ta ce" Kana ina ne? "

Hisham ya dan yi tari kadan ya kara iya yinsa dan fitar da muryarsa ya ce" Mamana lafia? Akoy abinda zan yi ne? "

Wasu zafafan hawaye suka shiga biyowa ta gefe da gefen idannuwan mama a kan yaron, a hankali itama muryarta bata fita da kyau din ta kuma fadin" Nace kana ina ne? "

Hisham ya daga kansa kadan ya ce" Mama na je wajen Aba ne , daga cen na zo office ina kan aiki ne "

Mama ta fashe da kuka ciki ciki ta kashe wayar a bayane ta ce" Makaryaci, wai yana cikin aiki makaryaci! Wayo Allahna ka dafa min Allah ka kama min, yarona bashi da lafia kuma? "

Mikewa ta yi hankalinta ba a jikinta ba ta yi dakin Bilkisu

Rana zuwa ta tarar da ita a kan salaya watau ta farka ta yi sallar azahar tana jan carbi kanta a sade

Jin budewar kofar ya sakata dago kanta da sauri
Gannin mama ya sakata jin wani karfi karfi ya shigeta da dan sauri ta kara gyara zamanta a samyaye ta shiga fadin" Mama, ban je ba dan kaina ke min ciwo banza banza ya kama min ciwo, ina ta so na zo na gaishe ki, mamana ina kwana, an tashi lafia? Yaya gajia, mama dan Allah ki yafe min, walahi koma da wa kika nuna min zan je na zauna na yi biyaya, aman na rantse maki da Allah na hakura da maganat Hamana, daga yau ba ni ba maganar hamana na ajiye shi bana sonsa ko tak a raina, bana sonsa mamana ko kadan na daina kar ki yi fushi da ni, son nasa bai isa ya sakani saka uwata zubar da hawaye ba, mama na san meye hukuncin wanda ya yi sanadiyar bacin ran iyayensa a kan abinda ba wani ba, na hakura har a gaban Allah"

Mama ta lumshe idannuwanta zuciyarta tai mata nauyi, ta kasa furta komai ta juya da sauri ta fita a dakin ta rasa ina zata nufa ga hijab a jikinta ta fara jiyo salama

Muryar da ta ringa jiyowa ta sakata jin kamar ta samu salama, da wani irin saurin da ita kanta bata san cewar a shekarunta zata iya hakan ba ta juya ta fita a dakin

Hannunsa ta damka wanda hakan sai da ya saka gabansa faduwa ta yi baya da shi bata ce da shi komai ba ta nuna masa wajen zama

Aba ya bi hannun nasa da kallo a zuciyarsa ya ce 'To fah' a bayane kuwa sai ya ringa binta da kallo bai ce komai ba har sai da ta kara nuna masa wajen zaman sannan ya ce" ASMA'U hannun mijin mutane kika kama haka kawai? Ko dai soyayar ta motsa ne kin yarda a maida auren yanzu na je na samu man liman a taru a daura mana? "

Mama dake tsaye tana kallonsa kanta na mata ciwo sai kawai ta sada kanta ta fashe da kuka

Shiru Aba ya yi gaba daya yannayin da ya zo mata da shi na su yita ta kare ya ji ya nema ya rasa, du wani tashin hankali da ya shigo mata da shi kwata kwata ya nema ya rasa, a yanzun a tsayen da yake idan bata yi da wasa ba zata saka tsohon gashinsa ya jika shi da kasa, da ta san yanda zaman mutunci da mutuntawa ya saka shi kasa mantawa da ita da irin yadda koda yanzu aka ce su koma zai iya maida igiyar aurensa da ita ta bine shi ko ya bineta cikin daraja da amincewar ubangiji
A hankali ya zauna a wajen da ta nuna masan domin da farko kin zaman ya yi ya so ya sauke mata vishiyar dake tsakiyar kanta wace ta zuba mata aljannun yi masa fitsara

Yana zama jikinsa a sanyaye yana kallonta ya ce" Asma'u zauna mana ki bar kukan nan haka ya isa "

Mama ta saka hijabinta tana ta goge hawayenta da hannunta mai dauke da zobunnan azurfar da Hisham ya yi mata masu kyau ta zauna a kasa maimakun ta hau dayar kujerar muryarta na rawa ta ce" Ka min fada, dan Allah ka min fada, na shiga uku, na rikice na rasa ina zan kama, yaron nan ashe bashi da lafia nake faman na rike shi na ganar da mamansa cewa abinda ta yi bai bashi da kyau itama ta ji idan da dadi? Ka ga sai ya min biyaya, gana ganni yarona bai taba bijirewa umarnina ba, sai ya min biyaya ya tafiarsa koda kuwa hakan zai cutar da shi, itama kanta mai gadon a wannan abin da na san muna iya fito na fito da ita idan na yi wasa ya saka ni yi mata magana da tsaurin da ya sakata yi min biyaya harma ta shiga tsorona? Ka ga zan kashe y'ayana da kaina wa'inda basu taba guje min ba du kangin talauci da rashin lafia da bacin rai, kaga gannin kamar wace na haukace na hada kan yaren na zauna abina ina kallonsu, na cika son zuciya ko? Na cika son zuciya jauro? "

Aba ya sauke ajiyar zuciya a sanyaye ya ce" Menene ya samu zumuncin naku da har haka take faruwa a tsakaninku baku yi gagawar zama kun fuskanci junna ba bayan kun san kun haihu y'ayan da koda babu maganar soyaya ya dace su rayu tsintsiya madaurinki daya ko so kuke su dawo kowa na jin haushin kowa sanadiyar haushin abinda ke tsakanin iyayensu? "

Mama ta ringa dan girgiza kanta , kanta a kasa tana kara share hawayenta

Aba ya ce" To Asma'u ina hakurin naki ya tafi? Kin san yada alkhairi yake kwuikuyo hakama shari, bana yiwa yar uwarki fatan ta ga rashin adalcinta a kwaryarta aman ai wasa ta yi da zumunci, yaron nan yana kuka da idannuwansa du juriyarsa wace ban taba gannin hakan ba har na rayu da ku na fita a rayuwarku har na

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login