Showing 159001 words to 162000 words out of 180809 words
jin abin ya fice a ransa,
Murmushi yake yana jin kansa wani iri, a hankali ya zauna yana jiran kiran Kader , wayar tasa ya shiga wajen mesage ya dano number Aisha ya rubuta mata mesage kamar haka "Kin yi baci? "
Yana turawa kiran na shigowa ya daga, sanar mata dukan abinda yake bukata ya yi sannan ta mikawa Kader ya ce" Ka kawo min "
Kader ya ce" Yanzu kuma? Dare fa ya yi "
Hisham ya ce" Minti ashirin na baka ma"
Kashe wayar ya yi gannin mesage din Aisha watau idannuwanta biyu?
Gyara zamansa ya yi ya danna mata kira
A sanyaye ta dauka da muryarta da ta shake ta yi masa salama
A nutse ya ce" Me ya hanna ki barci ne? "
Aisha ta gyara kwonciyarta rike da fillow ta ce" Ba komai "
Kansa ya dan shafa a hankali ya ce" Aisha kin ga ban dawo ba ko? "
Aisha ta gyara kwonciyarta a karro na ba adadi ta ce" Eh, aman ba komai ai na san kana tare da kanwata ne"
Murmushi ya yi ya ce" Kin san rigima take ji shine na yo gidanta da ita, in sha Allahu da sasafe zan zo"
A kasan zuciyarta ta shiga furta 'Gidanta kuma? Dama raba mana gida za'a yi?'
A bayane kuwa sai ta ce" Allah ya bamu alkhairi likita"
A hankali ya ce" Aisha? "
Amsawa ta yi tana jin yadda zuciyarta ke dokawa da wani irin karfi cike da tunani kala daban daban
Hisham ya ce" Ki yi adu'a kafin ki yi baci "
Ajiyar zuciya ta sauke a hankali ta ce" Ka kula da kanka Likitah"
Idannuwansa kawai ya iya lumshewa zuwa lokacin yana jin kiran Kader na shigowa ya mike ya nufi hanyar fita
A hankali Aisha ta ajiye wayar ta dauki fillo din ta dora saman kanta ta fashe da kuka
Kuka ne take mai zafi wanda ya tokare mata kirjinta, kuka ne take na tsananin kishin mijinta, tunani ya kasa barin kwakwaluwarta kan yana cen ya yi abinda yake yi da ita, baban tashin hankalinta a yanzun koda tana shan wahakar saduwa da shi aman ta fi jin dadin hakan fiye da wahalar, wani irin kishin kamshinsa, laushin jikinsa, yannayin da yake tafiar da ita ne suka hadu suka hadasa mata wani curaren dutse a kirji wanda bata iya samun saukinsa ba sai da ta fashe da wannan matsanancin kukan
Ko jin daurin aurensa bai tada mata hankali irin haka ba, a nan ne ta gyada kanta tana jinjina lalema idan Bilkisu ta ji su a dazun tana da hakuri, lale tana da hakuri, da ita ce ai sumewa zata yi ko ta afko masu, bata san abin haka yake da ciwo ba sai yanzu, abin ba na ka taba yi ko baka taba yi bane, abin zafi ne da shi koda baka san ana yinsa ba, abu ne da yake da ciwo, lale ta jinjinawa mata, ta jinjinawa kuma Bilkisu domin a irin yadda suke da shakuwa ta tausaya mata jin ihunta da ta yi
Luuuu ta yi da idannuwanta tana mikewa zaune dan bata tunanin idan har zata iya rintsa idannuwanta a yau, kishi ba karya bane, kuma du matar da ta iya sarafa kishinta ta hanyar kisa da kawar da kai lalle jaruma ce, a sanyaye ta sauko ta nufi bayi ta dauro alwallah ta dawo
Saman salayarta ta hau ta shiga gabatar da ibadarta ko zata samu sanyi a zuciyarta, kiran da ya yi mata ta ji dadinsa dimin ko ba komai ta tabata bai mantata ba, maganar raba masu gida kuwa bata ji dadinsa ba dan ita ta so ta kama kafar Billyn ta samu shiga, sai dai ba komai ta tabata idan da rabon zamansu ya dore ba zai wulakanta ta ba
Hisham na bude Dakin Kader ya kawo hannunsa zai kuma bugawa da sauri ya tsayar da hannun nasa yana fadin" Au ashe kana kusa, wai menene yake faruwa ne yau aikena kake ta yi tsakiyar dare bayan ka san bana son fitar dare , tsakani da Allah hala dukan yar nan ka yi? Kai yanzu Hisham baka da hakuri daga ce maka ka mata jan ido ko meye ne na ga du idannuwanka kamar mashayi bayan daga shayi baka shan komai?"
Hisham ya amsa yana kallonsa ya ce" Kana ta surutu tsakiyar dare baka ko jin kunya "
Kader ya dan saka hannunsa ya tare kofar yana kallon jalabiyar dake jikin Hisham wace yanzun mai ruwan ash color ce
Yar yatsarsa ya nuno ya ce" Ni kam kamar ba da wannan jalabiyar muka zo gidan nan ba, ina wancen din take ne? "
Hisham ya dakata da mamaki yana kallonsa
Kader ya karra ruko idannuwansa ya dafe tsatsonsa da hannunsa yana kallonsa ya ce" Aman idan ka aikata abinda muka yi da kai ba yanzu ba Hisham ka ji kunya! Yanzun Hisham kai din ne ka zo a haka dinka mikowar ingozoma gaban yar da ka raina?, Hisma kai kam akoy jarababe kuma abin nan ya bani kunya sosai da sosai, ban san haka zaka min ba na zauna na baka shawara dan kar a raina min kai to ko dai da karfi ta maka? Irin yadda kawarta ke min fada na tabata zasu aika, to yanzun kuma hala da gaske wancen din da ya saketa namiji ne ko dai dan ta bata maka rai ne? "
HISHAM ya zarro ido cike da mamaki da sauri ya juya ya ajiye ledar ya juyo yana fadin" Ni zaka yiwa iskancin da talatainin dare dan ina daga maka kafa? To nauyin kirjina ya sakeni ni da kai shege ka fasa !"
Da sauri Kader ya juya yana ayatul kursiyu dan dare ne baya iya doguwar tafia da dadare sam baya son fitar dare, a bayane yake karantawa wai kar Allah ya hada shi da mutanen, har fadi yake ka zo sun zo aka hade lokacinsu ne ko me suka yi maka kai ka ja
Hisham yana tsaye yana kallonsa har ya shige dakin da aka tanadar masa idan sunna gidan Bilkisun kafin ya juya ya koma ciki yana gyada kansa da yima kansa Alkawarin da safe zasu raba raini, duka kaf abinda ya dura masa zai amayar masa da abinsa
Mahalo
[7/12, 8:16 PM] BAK'A CE: 🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾
*DUK NISAN JIFA*
_(K'asa zai dawo)_
🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾
_RUBUTAWA_
*SAJIDA*
*SADAUKARWA*
*GA*
*MASOYA NA*
💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝
☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️
https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/
_Bismillahir rahamanir rahim_
58
Komawa falon ya yi ya zauna ya bude ledar da aka zo masa da ita
Cikin nutsuwa ya hada alurar zazabin da ya saka a zo masa da ita, sannan ya bali maganin zafin ciwon ya hade sauran ya kule harda su abin dinki wanda bai tabata ba sai ya je idan ta kama ya yi mata shi ta karfin balaki
Yana shiga a hankali ya karasa bayan ya kunna wutar dakin saman bed sin
Cikin nutsuwa ya hau saman gadon yana mai daukan goran madarar nan ya baleta
Bilkisu dake rawar sanyi da jin zafin zazabinta na hawa jikinta ta kara hade jikinta sosai cike da dana sani mai yawan gaske
Dana sani take yi a kan borin da ta masa dan kawai ta ji shi da matarsa, dana sani take yi na irin yadda ta nuna masa itama fa mace ce yake neman wulakantata, gaba daya bata taba jin azaba a tsayin rayuwarta irin ta yau ba, tabas ashe da take yiwa allura kuka nafila ce a kan wata azabar? Dama ta samu ? Sangarta ce? A yau da ta ji uwar allura sai bakin ya kasa daguwa, tun firgitacen ihun da ta saki a lokacin da ta ji ana neman tura mata icen maina sai komai nata ya tsaya ta kasa tantance halin da take ciki na azaba ne ko na barim duniyar ne
A hankali ya kwonto kusa da ita, cikin nutsuwa ya kara sakata cikin jikinsa ya kara matseta da kyau sakamakon mutsu mustu din da ta fara cike da tsoron me kuma ya dawo da shi jikinta bayan neman halakatan da ya yi?, a hankali ya ce" Ki daina kokowa kar ki ji ciwo Nuriyah"
Bilkisu ta zo hadiye wani yawun jin sunnaye kala daban daban bayan Billy am din da ake ce mata wanda shi ya dasa mata shi ,daidai zata hadiye yawun ta ji shigar allurar cikin gefen buraburanta (Duwawu) daga sama kadan
Da karfi ta rike shi ta dago rinanun idannuwanta ta sauke saman fuskarsa bayan ta kasa kallonsa tun dazun
A hankali ta ji ya sauke lalausan lebunnansa a saman nata leben ya ringa lasa yana kallon yadda ta yi gagawar rufe idannuwan nata ta maste su da karfi
Kasancewar ba rufe mata bakin ne ya yi ba a sanyaye ta ce" So kake ka kashe ni? "
Yana lasar leben nata ya dan girgiza kansa
Bilkisu ta kara rintse idannuwanta duda ba kallonsa take yi ba aman tana ji yannayin amsarsa ta kuma fadin" Baka jin kunyata? Nice fa?"
A hankali ya saki sansanyan murmushi yana kallon yadda idannuwanta suka dan kumbura, a sanyaye ya ce" Allah ya yi maki albarka da kika rufa min asiri, kika kilace min kanki har yau na malaki abina, Billy am bana jin kunyarki ina tsananin son ki"
Wani iri take ji, ta rasa gane wane zata kama, lalle du idan ya fada sai ta ji abin har kasan makoshinta
A hankali ya kara shafa bayanta ya ce" Kuma idan kika ringa jin kunyata zaki wahalar da ni, a yadda na tsara mana rayuwa zaki rayu sa ni cikin tunanin anya akoy marar kunya irina?, da sannu sai kin gane kazantar da kike tunanin kazanta ce a jikinki zan iya sidewa...."
A hankali take son bude idannuwanta dan gaskata shin shi din ne?
Muryarsa dai a sanyaye ya ce" Ki kale ni, just oje second ki dube ni, ki min murmushi ko baki yafe min ba? "
Bilkisu ta kara hadiye yawun bakinta tana jin kamar zazabinta na raguwa
A hankali ya ce" Zan kama ki ki tashi dan na baki maganin zafin da nan yake maki...." ya fada yana nunawa sannan ya dora da fadin" Sai kuma na kaiki bayi ki yi wanka dan yanzun zazabin zai barki kin ji? "
Bata iya bashi amsa ba har ya mike zaune , abin rufar da yake son janyewa ta rike da sauri ya saka shi kallon hannayenta dake kusan mamanta, a ransa yake furta' dole ki rufe yan matana domin sun cika sun batse sai bulbulbul suke sunna kiran Hisham.......'
Maganin ya bata yana jiran gannin ta kiya, aman sai ya ga ta saka a bakinta da sauri ta kora da madarar nan ta hadiye tana rintse idannuwanta dan zafin da take ji
A sanyaye yake kara binta da kallo har ta gama sha sannan ya mike ya yi bayi
Yana shiga ta cicina dan tashi, zafi sosai ta ji yana ratsata hakan ya sa ta rike abin gadon tana cije lebenta a bayane ta ce" Ya tsaga ni wayo ya rabani biyu, wayo ya halakani allura a kasana!"
Murmushi ne ya subuce masa kafin ya yi gagawar gimtsewa ya karaso inda take tsaye
A hankali ya kamata yana kallonta ya ce" Can i? "
Tana kallonsa bata iya bashi amsa ba ta ga ya hadeta da abin rufar ya dauketa a hankali ya nufi bayi da ita
Ririke shi ta yi da kyau dan kar ya makata da kas har sai da ta ji ya zaunar da ita saman kujerar dake bayin ta silba wace ke gine ta zama ce a hankali ya kama abin rufar
Da sauri ta rike tana dan girgiza kanta hakan ya saka shi rage tsayinsa sosai ya dora hannayensa saman cinyarta a sanyaye ya ce" Billyna, ta yiwu kin karu ne, kin ga ke din sirina ce, idan ba nesa na yi da gida ba ko mutuwa na yi ba zan bari wata ta gyara min ke ba, ki yi hakuri na duba idan har kin karu tun da wuri mu gyara kin ji?"
Ido ta tsurawa fuskarsa, su duba me a takaice?
Bata idasa tunanin ba ya saka hannunsa a hankali ya yaye zannin rufar
Da sauri ta hade santala santalan cinyoyinta masu haske da santsi tana zazaro idannuwanta , bata san lokacin da ta ce" Me zaka gani Hamma am? "
Daria ce ta so kama shi irin yadda ta yin, aman sai ya hanna kansa cikin sauki ya dan kara gyara tsuguninsa ya saka hannayensa ya rike nata hannayen , da dayan hannun kuwa ya saka ya wara kafafuwanta da karfin da bata tsamace shi da shi ba, sannan ya kara gyara tsuguninsa a hankali ya saka hannun nasa yana kara kallon wajen
Wani yawu ya hadiye da sauri ya sakete ya mike ya kamata a hankali ya karasa da ita cikin ruwan mai dan sasaukan zafi sannan ya juya da sauri da abin rufar ya rataya mata shi ya fice a bayin
Da ido ta bishi kafin ta girgiza kanta ta hada hannayenta duka biyu ta rafka wani uban tagumi cike da mamakin D'a namiji, lale bashi da kunya, lale namiji baya shayin abu sai dai idan ya saka kansa kawai
A hankali ta ringa gasa kanta, sarai ta san gasa kai ake domin ta karanta , sannan a makaranta an koyar da su, hakama ta ji a wajen yan mata da masu auren ajinsu
Ruwan nema ta ji bai mata zafi yadda ake fadi ba dan haka a hankali ta janyo igiyar ruwan zafin ta kunna ta ringa kara zafinsa idannuwanta rufe cike da dauriya har ta ji ya yi zafi sosai sannan ta kara gyara zamanta cikinsa yana ratsata a hankali a hankali
Tun a nan ta ringa jin wannan zafin uwa barkono na raguwa har ta ringa jin sa'ida
Ajiyar zuciya take saukewa a hankali ta girgiza kanta, to aman mata sunna da aiki a gabansu walahi, su rashin sannin ciwon kai ne suke kishin abin nan ko me? Ko dai kowa da irin nasa ne? Ita dai in dai a kan wannan ne a kai kasuwa!
Cikin nutsuwa ta bude jakuzi din ruwan ya tsiyaye ta kuma kunna wanni sannan ta dauki sabulun wankan mai kanshi ta ringa wankawa a hankali tana lumshe idannuwanta har ta gama ta darwaye jikinta ruwan ya tafi sannan ta mike ta dauki butar robar dake jere da na karfe ta yi wankan janaba cike da jin wani abu bako a rayuwarta, yau itace da wannan wanka? "ALHAMDULILAH " ta fada a sanyaye kafin ta dauki tawul ta daura ta kuma rufa abin rufar ta fita
Kasa take kallo, shi kuwa yana zaune bakin gadon da ya cenzawa shinfida sai kanshin turaran ruwan da ta ji wanda ga dukan alamu a yanzu ya fesa
A hankali ya nufeta rike da rigar barcin da ya ciro mata fara marar nauyi
Cikin nutsuwa ya ringa jan abin rufar, hakan ya sa ta kankame tawul din cike da tsoron lamarinsa tana kallon dukan motsinsa har ya saka mata rigar bacin sannan ya janye tawul din
Wajen gadon ya nufa da ita ya zaunar da ita
Madarar nan dai bridel ya kuma bude mata yana harhade rai ya ce" Oya shanye hajia "
Ajiyar zuciya ta sauke dan walahi ita kanta ta san tana jin yinwa, har mamaki take domin ta tataba naman cen fa
A hankali take dan sha dan bata saba kafa kai a gabansa ba har ta shanye gaba daya domin bata da yawa sannan ta mika masa
Murmushi ya yi harda sauke ajiyar zuciya a hankali ya rufe ya ajiye ya haura saman gadon
Janyota ya yi jikinsa suka kwonta saman bed din, a sanyaye ya shiga shafa gashin kanta dake jike wanda akai mata manyan kitson da har yanzu ba'a kunce shi ba, ba kunshi a hannunta ba kitso irin na amaren zamani da ake yayaba masu kitso da kunshi a maka masu mak'up kamar zasu je zaban sarauniyar kyau
Haka kawai sai yake gannin komai nata special, ko dan ita din ce special a duniyarsa?
A hankali ya ce" Na kasa hango me zan malaka maki a rayuwa dan na nuna maki farin cikina? BILKISU INA SON KI shin zaki yarda kuwa? "
A hankali ta saki boyayiyar ajiyar zuciya, tsake zuciyarta take, baban amsarta itace'Nima ina son ka, ban san wani so din bayan naka, da shi na tashi, shi ya min ila, shi ya gama kashe min tunanina da komai nawa'
Aman sai ta kasa fda a bayane kawai ta kara kutsa kanta a kirjinsa domin kanshin kirjin nasa akoy kanshi sansanya mai shiga zuciya
Idannuwansa ya kuma rintsawa cike da son jin kalaman soyaya daga bakinta, Aisha kafin ya tambaya take fada masa, aman wace ya fi muradin ji din batama yarda da nasa furucin ba
A cikin zuciyarsa ya ringa ayana ' Ya Allah, ka sanyaya mata zuciyarta, idan laifi take gannin na yi mata dan ja amshi watanta a lokacin da abin ya zo a gareni cikin ikonka, ka sanyayar min da zuciyarta domin ita din itace nutsuwata'
Kara riketa ya yi a jikinsa yana son enjoy din moment din nan, ya jima yana mafarkinsa, a yau da ya tanatar masa sai yake jin du duniya ya gama dace kennan shi ko yanzu ya tafi burikansa sun cika Alhamdulilah
Adu'ar barci ya totofa mata yana kara shafa gashin kanta har ya ringa jin numfashinta na sauya sauka a kirjinsa, hakan ya tabatar masa da ta yi barci ne
Fuskar tata ya ci gaba da kallo , eyelashes dinta yake ta kallo, lebenta zuwa karan hancinta
Murmushi yake yana karrawa a bayane cen kasan makoshi ya ce" Sonta kawai nake, my rigimamiya baby"
A haka shima barcin ya dauke