Showing 126001 words to 129000 words out of 180809 words

Chapter 43 - DUK NISAN JIFA COMPLETE HAUSA NOVEL

sajida   

02 Feb 2025

12966

sun dawo daga asibiti da Tati ne wace ta tsurawa waje daya ido ta kasa magana sai kallo

Yannaciki lon yadda mama ke rungumota a jikinta har suka shige kafin ya sauke ajiyar zuciya yana kallon wayar da ta kashe masa
A hankali ya danna dan maida kiran aman sai ya sameta online
Gurum ya yi da wayar a hannunsa yana ta tunani, gidan su Fareeda da wannan daren bayan ya fada ta dawo gida? Kuma ta katse masa kira yanzun take online da wa?

Kader ya gyara zamansa ya ce" To fita mana "

HISHAM ya juyo yana kallonsa yadda yake jira ya fita a motar shi kuwa ya gyara mata tsayuwa ya ce" ka san gidan su Fareeda kawar Billy ne? "

Kader ya girgiza kansa da sauri ya ce" ni ai mun jima da batawa da ita, sam na kula ba kaunata take ba tunda har ta ce sai ta yi exam zata aureni!"

Hisham ya tabe baki, domin haka suke bini bini zai kwashi fada shi sun rabu da farreda ba zai kuma kulata ba, kuma ana dan jimawa sai ya maido zancenta ka ga yana koda soyayarsu da abubuwa daban daban, ko yanzun ya tabata karya yake masa aman sai ya share yana kallon wajen redion motar Kader ya ce" Yauwa, ina fatan ka yi tunanin ta yadda zaka sanar da uwar gida zaka yi mata amarya ko? "

HISHAM ya zuba masa ido, ta yadda zai sanar mata? Har ta wani yannayi zai sanar mata da abinda ta rigaya ta sani kamar wani mawaki zai kama maimaita abubuwa? Ai ta sani, itama ta fada cewar bata kishi da Billynsa, dan haka baya gannin dalilin da zai saka shi zama da ita ya wani maimaita zancen

Irin yadda ya tabe baki ya cire kansa a maganar ya saka Kader gane ba wannan ne a gabansa ba, dan haka sai ya gyara zamansa yana kallonsa ya ce" Ka ga, kar ka zamo cikin mazan da so zai saka su shiga wuta, Hisham kai dai ba jahili bane a mayar da maganar auren hadi tsakaninka da Aisha tunda har ka iya amsar bakuntarta ka mayar da ita sirrinka ina gannin idan abu na cutarwa ya shiga ba dadi, me zai hanna ka kwatanta adalci? Ka yi kokari ka bata nata matsayi na matarka, to ka ga fa ko wata bata cire ba za'a yi mata kishiya, na tabata koda bata darza maka rashin mutunci irin nasu na mata ba sai ta sha kuka ko ta ce a saketa bayan ba wanda ya isa ya sa a saketa ko idasa more sadakinmu bamu yi ba! Ah tam million biyu? Idan ka saketa ni ko a hanya na ganka ba zan kuma kulaka ba!"

Hisham a dake yana jin gaba daya hayaniyar da tsarabe tsaraben matsalolin yau da kulun sun fara saka shi juwa ya ce" Ka rage murya mana kana min ihu a ka!"

Kader maimakun ya rage muryar sai ya yi gum da bakinsa yana kallonsa

HISHAM ya ajiye wayarsa nan ya kwonce belt din jikinsa ya fita ba tare da ya kuma ce masa komai ba

Kader ya gyara zamansa yana dan turo baki domin ya tabata fita zasu yi, shi kuwa a yau ba zai kaishi gidan su Fareeda ba dan ya san yana zuwa zasu shirya bayan ya kamata da wani saurayin daban sun yi fada basa magana salon gobe ta ce ai shi ya dawo ko?

Yana shiga fallon ya tarda tarron yadda ya saba, kowa na nan banda Billy

Mama dake waya ya kalla bayan ya amsar gaisuwar su Aisha yana sauraron abinda take fada
Mama ta ce" Bilkisu gani na yo ba sallah ba, ba wani biki ake ba, idan ba wadinnan ba ai bakya zuwa ki kwana gidansu, itama idan ana wani sabga take kwana a nan shikenan kamar tautau sai ki kama yawo harda su son kwana"

Hannunsa ya dora gaban goshinsa yanna kallon yadda fuskar mama ke nuna alamun amincewarta da maganar har sai da ta furta" To ki tabatar kin kula, ki kama mutuncin kanki safia na yi kuma ki dawo min gida kin ji ko? Bani maman tasu mu gaisa na fada mata safia na yi ki dawo kin ga bana son rigima ni!"

"AN gama", ya fada a kasan zuciyarsa kafin ya karasa ya nemi waje ya zauna yana fuskantar Tati dake zaune da mahaifiyar Aisha a kusa da ita tana wani yi mata magana kasa kasa, ga Aishar gefe tana zaune cikin shiga ta lesh tana danna wayarta domin au kansu basu jima da dawowa daga asibiti ba, yau kakanta har murmushi ya mata shi yasa gaba daya take cikin farin ciki.

Jiki a sab'ule ya mik'e ya bar falon ba tare daya tanka kowa ba sabida alhinin kwanciyar Billy a wani gidan da ba na su ba kuma bana Abba ba, gidan kawarta!



Da sassafe Abba ya doko musu sammako yazo, Tati da maman Aisha na gefe zaune tana ta tausarta da kalamai, sai Aisho da shigowar kenan falon tana mik'awa Tati tea mai zafi da Mama ta bado daga kicin, sallamarshi ce tasa Mama fitowa tana gyara zaman hijab d'inta tana kallonshi da mamaki, gaisawa sukayi sosai har yana tambayar jikin Tati, cikin son sanin abinda ya kawoshi Mama ta nuna mishi wuri tace "Bismillah ka zauna."

Da fara'a ya zauna yana d'an waigawa dan son ganin Bilkissu, kallon Mama yayi zaiyi magana sai kuma Hisham ya shogo da siriryar sallama a bakinshi cikin shirin fita, kamar kullum dai k'ananan kaya ne da suka dace da likitoci, da girmamawa ya isa kusa da Abba suka gaisa. Dan satar kallon Tati yayi data zuba mishi ido take ganinshi kamar ubanshi yace "Ya jikin?"

Mamar Aisha ce tace "Da sauk'i, saidai bata ma kowa magana har yanzu, ina tsoron damuwa ta mata yawa."

D'auke idonshi yayi kamar abun bai dameshi ba, saidai ciwon daga zuciya yake, haihuwa tafi k'arfin wasa kam, Aisha dake tsaye har yanzu ta kalleshi ita ma tace "Ina kwana."

Kallonta yayi fuskarshi bรข yabo ba fallasa yace "Lafiya lau."

Ganin kamar suna gaishe gaishensu yasa Abba kallon Mama yace "Ina Bilkissu ne?"

D'an sosai goshinta tayi tace "Tana gidan k'awarta, amma yanzu zata dawo."

Da mamaki yace "K'awarta kuma? Me ta tafi yi da sassafe haka?"

Galala mama ta kalleshi tace "Ai a can ma ta kwana."

Zarro ido yayi yace "A can ta kwana? Akan me? Dare tayi ne jiya?"

Shiru maama tayi kanta k'asa saboda yanda ya tsareta da ido yana tambayar kamar zai daketa, jinjina kai yayi ya muskuta ya gyara zamanshi yace "Yayi kyau, dama ba wani abu bane ya kawoni maganar aurensu ne."

K'uri duk mutanen d'akin suka mishi da ido suna kallo harda Tati, ba tare daya kula da yanayin kowa ba yace "Bayan mun tattauna da Bilkissu jiya nayi istihara a game da lamarin nan, ba abinda na gani sai alkairi, dan haka ku shirya *ranar juma'a* za'a d'aura musu aure."

Mik'ewa yayi alamar tafiya zaiyi, ga dukkan alama ya fahimci akwai Wanda zasu kawo masa wargi shiyasa, da sauri Mama data bishi da kallo tace "Abban Bilkissu."

Juyowa yayi yana kallonta sai kuma ta kasa magana, cikin taushin murya yace "Kina da magana ne?"

Rufe bakinta tayi sosai tana dan had'a yawu, murmushi ya sakar mata yace "Da namu auren za'a d'aura ai."

Sake wangale baki tayi kunya kawai ta ryfeta, tana kallo ya fice a gidan ya barta da kunya da al'ajab, yanda ta kasa motsawa haka Hisham ya daskare a wuri d'aya, juma'a kawai yake maimaitawa a ranshi, abu d'aya kawai ya sani indai juma'a za'a d'aura aurenshi da Billy to tabbas wannan juma'ar ta misamman ce a ganiyar na musamman d'in, yana tsaka da tunane tunane yaji muryar Maman Aisha tace "Tabb'! Lallai ma."

Kallonta duk sukayi ita kyma ta mik'e tsaye tana kallon Hisham kamar yanda yake kallonta tace " Maganar aurenka ake bayan aurenka na fari yarinyata ko tarewa batayi ba a gidanta? Wannan wace irin rayuwa haka? Ko gusar da ita bamuyi ba daga gabanmu za'a mata wata kishiya, to gaskiya da sake, wannan ba ma abu bane da zai yiwu ehe!"

Saida ta dasa aya Hisham ya saki wani lallausan murmushi ya mik'e daga rank'wafawar da yayi juya ya kalli Mama, takawa yayi har saida ya tsaya gabaanta ya rik'o hannayenta yana mata murmushi yace "Mama na, karki damu kanki dan Allah, karki bari damuwa ko tunanin wani zai d'aga miki hankali yayi tasiri a walwalarki, kinsan dai farin cikinki shi ne nawa ko?"

Yanda yake magana kawai yasa ta d'aga mishi kai alamun eh, jinjina kai yayi tare da sakin hannayenta ya juya zai fita, takon sassarfar Aisha yasa shi tsayawa ya juya ta b'angaren da take, ita ce ta bar wurin da sauri da alama kuma kuka ne take son b'oyewa.

Tab'e baki yayi ya juya zai tafi, cak kuma ya k'ara tsayawa saboda tuna maganganun Kader na daren jiya, a hankali a sanyaye yaji tausayin yarinyar na samun mafaka a zuciyarshi yana zama, d'an k'aramin tsaki yayi na rashin jin dad'i tare da juyawa da sauri ya nufi inda Aisha ta shiga...... mahaifiyarta kuwa buuuu ta mike ta yi ciki da waya a hannunta tana lalubar number mijinta, tati kam kanta na kallon kasa gaba daya ji take idan ta budi baki wani irin kuka ne zata yi wanda zai saka ta kuma wata sumar har jinnin nata ya kara hawa sosai

Yana shiga ya ja ya tsaya jikin garun yana kallonta
Kwonce ta yi tana rusa kuka duda irin yadda take kokarin hanna kanta yin mai karfin nan

Tausayinta sosai ya kara ji a kasan zuciyarsa hakan ya saka shi a hankali ya karasa bakin gadon ya dan zauna kafin ya dan yi guaran murya

Kittt ta yi da kukan sannan ta dago da sauri tana kallonsa

Ido ya tsura mata, Aisha bata da muni ko kadan sai dai da ake cewa shan koko bukatar rai kuma sam baya jinta yadda yake jin soyayar wace ya raina shekara da shekaru, aman kuma zai yi iya yinsa dan kamanta adalci a tsakaninsu, sam ba zai bari ta kara gaskata cewar dan ba itace zabinsa ba kuma ba zata ji dadin zama da shi ba

A sanyaye ya ce" Kuka kuma Aisha? "

Aisha ta zauna sosai tana dan girgiza kanta tana share hawayenta

A hankali ya kamo tafin hannunta yana kallonta ya ce" Da kika ce min zaki fi kowa taya ni son abinda nake so, ba zaki yi kishi da ita ba domin kanwarki ce shin kin fada ne dan kin ji a lokacin ta min nisa ko har cikin ranki da gaske kike? "

Aisha ta sada kanta tana sauke ajigar zuciya ta rasa me zata ce masa

A hankali ya ce" Ko dai dan bamu jima da auren bane kema yake maki ciwo? "

Aisha ta dago tana kallonsa ta ce" Tun kafin a sako maganana na san da so a zukatanku na junnanku har na so na takafa ku furtawa junna, na san cewa koda ta auri wani da kyar na iya samun kasonta, aman zuciya bata da kashi docter, na kasa hakuri har na kama kuka bayan ba rashin adalci akai min ba hasalima halaci akai min tunda ni din kutse ne na yi"

Hisham ya sakar mata dan murmushi yana kallonta ya ce" Ba'ai maki adalci ba, ki yi hakuri Aisha, domin ya dace na kilace ki na sanar da ke, haka na tsara to Aba bai san baki san da zancen ba, baki yi kutse ba dan kuwa kina da kima da daraja a idannuwana, Aisha kin zama sirrina ki kasance bargona ke din suturata ce, ba maganar kutse a matar aurena koda ban je shinfidarta ba bale jar hakan ya faru, Aisha i'm so sorry da irin abubuwan dake faruwa domin kin fi karfin haka, ki taso mu tafi gidanmu, ki saka a ranki Billyna kanwa ce zata zo ku zauna ku hade kawunnanku ba abokiyar gaba ba, ina rokarki da ki kwontar min da hankali domin da gaske *Damuwarki* na iya damuna"

Kalamai ne da basu taka kara sun karya ba, kalaman da bai dauki lokaci mai tsayi yana furta su ba, haka kuma bai tsara karya dan ya faranta mata ba sai tsantsar gaskiya da kula da dan lokacin da ya bata dan ya nuna mata cewa itama mutun ce kuma dan an masu auren hadi ba yana nufin ita din makiyiyarsa bane, haka kuma auren da zai kara ba dan ya tsaneta bane sannan zai kwatanta adalci a tsakaninsu sai ta ji wani sanyi ya ziyarci zuciyarta, a hankali ta dora kanta a tafin hannunsa muryarta a sanyaye ta ce" ni dai fatana kar ka guje ni, kar ka tsane ni, kar ka wulakanta ni"

Murmushi ya yi yana dan murza damtsen hannunta ta kuma dan yin murmushi ta ce" Saura kwana uku, kwana uku kawai ya rage , ina tsoron rigimarta "

Idannuwansa ya lumshe a kasan zuciyarsa yake ayana' Nima ina jin shayin sabuwar Billyna, shin yaya zamu fuskanci junna? Ya Allah ka san ta amsa ba sai na maganta ba, ta sada kai ba sai mun yi gumurzu ba, ta dube ni ba tare da ta kireni abanta ba' ๐Ÿ˜ซ


๐Ÿ˜๐Ÿ˜๐Ÿ˜
[7/4, 7:43 PM] +234 803 885 6944: ๐ŸŽพ๐ŸŽพ๐ŸŽพ๐ŸŽพ๐ŸŽพ๐ŸŽพ๐ŸŽพ๐ŸŽพ๐ŸŽพ๐ŸŽพ
*DUK NISAN JIFA*
_(K'asa zai dawo)_
๐ŸŽพ๐ŸŽพ๐ŸŽพ๐ŸŽพ๐ŸŽพ๐ŸŽพ๐ŸŽพ๐ŸŽพ๐ŸŽพ๐ŸŽพ

_RUBUTAWA_

*SAJIDA*

*SADAUKARWA*

*GA*

*MASOYA NA*


๐Ÿ’ซโœจ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*๐ŸŒŸ
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_๐Ÿค

โ˜† *[ T.M.N.A]* โ˜† ๐Ÿ“–๐Ÿ–Š๏ธ

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_



45



A fili kuwa sai ya mike a hankali da ita ya nufi wajen da akwatinta take ajiye
Hijab din dake sama ya dauka ya saka mata kafin ya kama hannunta ya juya da ita a hannunsa

Cikin nutsuwa suka fito daga dakin suka zo wucewa da wajen su mama dake zaune wannan karron daga ita sai tati tati ta dora kanta a gefen kafadarta tana ta shahsekar kuka maman na share mata tana mata magana kasa kasa

Sosai ya ji ba dadi a kasan zuciyarsa, har ya so ya duka a gabanta ya rarasheta, sai dai ya tabata Allah ya fito mata da wannan lamari a yanzu ne dan ya nuna mata cewar komai yadda ta kai da tsara rayuwarta da son kanta shi ke juya mata rayuwar a lokacin da ita kanta bata sani ba, hakan ya saka a sanyaye ya ce" Mun tafi mama "

Mama kai kawai ta iya gyada masa sam batama san ina suka tafin ba har ya fice Aisha na biye a bayansa

Sunna fita mama ta kuma rike hannunta ta ce" Dan Allah ki kwontar da hankalinki Zainab, ke kin san cewa namiji na abinda ya ga dama a lokacin da ya ga dama, ban san irin tsakaninki da mutumen nan ba, ban san irin yardar da kika bashi ba, abinda na sani shine a yanzu ke ba yarinyar goye bace, ban san irin rayuwar da kika yi bayan rabonmu ba, abinda na sani shine ko wace irin rayuwa ce kin yi wace ta nuna maki cewa mafi yawancin mutane na aikata aiyukansu na yau da kulun bisa son zuciyarsu da abinda zai gyara su, wasu kan dalilin da ya dace a dube su, wasun kuwa sunna yi ne dan jin dadinsu, bana so kan wannan ki sakawa kanki rashin lafia, bana so ki saka abin a cikin zuciyarki har ya jaza maki rashin lafiar da zata damemu baki daya Zannub"


Zainab ta lumshe idannuwanta hawaye masu zafi suka shiga biyowa kuncinta tana kallonta ta ce" Aunty, ina bashi da buri da ya fi HISHAM a duniya? A ranar da na haihu kuka da hawayensa ya yi haka yake jijiga sannan ya furta min cewa a duniya bayan mahaifiyarsa bashi da wani farin cikin da ya kai Hisham da ni wace na kawo masa Hisham duniya, Aunty, dama akoy abinda ya fi mu? Ta yaya ya iya tsara mutuwarsa ya bacewa duniya? Ta yaya ya dawo cikin kasar nan ya zauna ban taba sani ba? Ta ina ya samu duka wannan? "

Mama ta sauke ajiyar zuciya jin tati ta bude bakinta a sanyaye ta ce" Kamar yadda na fada maki wani lamarin kan zuwa aya hadasa tashin hankali mai girma haka ne, tabas mahaifin Hisham bai barshi dan wani abin ba sai dan girman umarni da soyayar uwa a kan yaronta, Mohamad kharibullah ya tafi wajen wannan yaki, hasalima da shi aka yi, su su uku suka rayu sannan cikin ikon Allah yana cikin hayacinsa, shi ya yarda galarsa da sunnansa a wajen matatun da kuma wa'inda aka koma sannan ya bar wajen, ko gwamnati bata san da yana raye ba haka aka salace shi da iyayensa wa'inda su kansu basu san da hakan ba, Zainab umarni ya bi na mahaifiyarsa a lokacin da ya kai mata labarinku, ranta ya bace, kololuwar bacewar da ta masa kwakwaran kashedi da rantsuwar mugun baki idan bai bi umarninta ba cewar ya sake ki, ya fita a harkar yaron domin duka duka aurensa bai yi jimawar da har zai wani fara hangen wasu ba, ita kuwa idan ba balarabiya ba ba zata taba yarda da wani jinsi ya zama tsatsonta ba!, wannan dalili ya saka shi bata na watani, har sai da kika bar gari ya dawo ga iyayensa , a nan suka daga suka bar kasa dan kar a gane cewar Balarabe na raye, sun jima a kasarsu ta larabawa kafin su dawo, domin a nan komai nasu yake, sun rigaya sun gina rayuwarsu a nan, uwa uba irin da suka bari wanda ya zame masu daya kwalin kwal domin bayan matar tasa an kuma aura masa wasu biyu shiru ba haihuwa bayan su dukansu lafiarsu kalau"

Da sauri Tati ta kara roke hannun mama a dan firgice ta ce" A ina kika sani, yaushe kika sani?

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login