Showing 48001 words to 51000 words out of 180809 words

Chapter 17 - DUK NISAN JIFA COMPLETE HAUSA NOVEL

sajida   

02 Feb 2025

12978

kasa, zan kara gaba ne dan fadan nan idan na ja sunnana marar nasara, furucin mahaifiyata na cikin lamarin, da ba dan haka ba Aisha na iya daura zani na iya saka gefto a kasan sket haka kuma na iya tuka tuwo!, zan je ne na samu nutsuwar zuciyata ne na dawo na buga kalangun auren ubana, ke miji aka baki, D'ansu suka baki, ni kuwa ubana ne, Aminina ne, HISHAM RAYUWATA NE! ba zan iya daga kai daga umarnin wace ta sakoni duniya ba, domin haihuwata aka yi"

Tana gama fada ta mike ta ja akwatin dan ba zata iya daukanta ba ta fito falo
Aisha kuwa tamkar mutun mutumi haka magangannun Bilkisu sukai mata kuwa kafin ta tashi a hankali ta bi bayanta

Gabanta bai taba tsintsinkewa ya fadi irin na yau ba

Sanye yake cikin bakin yadi mai sasaukan kwaliya, irin zaman da ya yi kafarsa daya ya dan tankwasata saman kujerar hakan ya sa ake iya gannin tafin kafar dayar kuwa a ajiye a saman cafet
Gefe da gefensa su Mama ne da Bakuwa, sai Tati zaune

Akwatin hannunta yake kallo hakama du wanda ke fallon ya bi akwatin da kallo

Bakuwar ce ta fara fadin" Aa, ya da kaya haka ina zuwa y'ata?"

Murmushi Bilkisu ta kakaro kafin ta yi magana Mama ta ce" Zata je ne ta yiwa Mahaifinta kwana biyu Hajia kin san a nan yake"

Mama ya tsurawa ido da dan mamakin abinda ta fada, yaushe Bilkisun ta fara zuwa har ta kwana a gidansu? Sai dai bai ce komai ba ya mayar da dubansa kanta, wanda hakan ke sakata jin tamkar zata fadi

Tati ta mika mata hannu ta ce" Zo "

Ajiye katuwar akwatin ta yi ta karasa gaban Tati tana shirin rage tsayinta

Tati ta kamota tana kallonta, muryarta a matukar sanyaye ta ce " Baki da lafia fa, maganar auren yayanki kuma ake fa, ba zai dauki lokaci ba, bakya nan waye zai yi bukukuwan? "

Idannuwanta dake lumshe ta bude a hankali tana kallon Tati

Muryarsa kasa kasa ya ce" Ba gaki ba Tati, ko ba komai ai ke ce kirjin bikin domin ke kika haifa? "

Du dubansa aka yi hakan ya saka shi yin murmushi ya kalli Mama a hankali ya ce" Ai zata yi komai ko *rayuwata tunda kin bata dama*? "

Sai kuma ya kai dubansa wajen su Tati,
Kunyar furucinsa ya saka Tati sai sasada kai take, ita ta haifa? Dama bakinsa na iya fadin ba dadi haka?
ya kara duban tati da kyau ya ce" Mama? "

Shiru wajen ya dauka
A hankali ya kuma cewa " MAMA? "

MAMA ta hadiyi yawu a makogwaronta cike da mamakin sabon Hisham din dake zaune dangalgal yana aniyar yayaba magana cikin ruwan sanyi ba da hayaniya ba, tun da ya zo ya zauna daidai da gaisuwar da ya yiwa mahaifiyar Aisha sai da ta ji kamar ba Hisham dinta ba domin cewa ya yi yaya dai sarakuwar? Ido cikin ido kuma yake fadin magana ya aiko da murmushi kamar wanda ya shanyo masu giyarsu ta kansu, sai take ji dama bata tirsasa masa zuwan ba a irin wannan lokacin
Jiki a mace, murya a sanyaye yannayin motsinta a hankali ta ce" Na'am? "

Dubanta ya kara yi ya sada kansa, sosai ya rage muryarsa ya ce" Ke mamana sunnanki, ita kuwa *Mama* dan cewa ta yi na ringa kiranta da Mama"

Mama ta ringa jifansa da kakausan kallo dan ya kama kansa ya daina wannan abin aman sai sun yi ido hudu sai ya sakar mata murmushi hakan ya matukar kayar mata da gaba, ya tayar mata da hankali , kallonsa kawai take ta kasa wani kwakwaran motsi, wannan tsaurin idon da tsayayar ba yaronta bane, wannan kafe mutun din da ido bata san danta da shi ba , so take ta dan mike ta ja hannunsa ta yi dakin cen da shi ta tuna masa cewar ita ce fa? Aman kuma tana gudun kar a ga zakewarta da yawa a kan lamarinsa bayan zainab ta gama shekar cewa ita ta haifi abinta

Rasa abin cewa ya saka tati mikewa ta nufi ciki dan daukowa Bilkisu sako, Bakuwar gidan kuwa sam bata gane abinda yake faruwa ba dan ita a ganninta normal dan ya kira mahaifiyarsa da sunna Mama

Da ido Aisha ke kallonsa, tamkar zata dauke shi da idannuwanta haka kuma sai ta juya dubanta wajen Bilkisu

Sai da ta duka har kasa ta gaishe shi, aman abin mamaki kallo irin kallon da ake kira na kasa kasa a bayane ne yake jifanta da shi, wanda du wanda ke wajen in dai zai kale shi to fa dole ya ga irin kallon nan ya zarce misali kuma mirsisi ya ki amsa gaisuwar tata har ta kai wani dan lokaci a tsugunen nan

A hankali ta dan dago da dubanta daidai lokacin da Tati ta dawo dauke da leda a hannunta tana jira Bilkisu ta mike ta bata

Bai amsa mata ba, sai ido hudu da suka yi
Kakausan kallon da ya watsa mata ya sakata kara sada dubanta sannan ta mike tsaye da dan sauri tana wani soshe soshen gaban goshinta

A hankali ta raba gefen Mama ta dan rungumeta a jikinta muryarta a shagwabe ta ce" i'll miss u mum"

Mama da turancinta ba wani nesa ya yi ba sai dan abinda ba za'a rasa ba ta sakar mata murmushi tana dan dadaba bayanta, muryarta ciki ciki ta ce" ki kula da kanki, ki kare mutuncin kanki, zan kirayi maman naku in sha Allah "

Bilkisu ta gyada kanta sannan ta juya a hankali ta koma wajen jakarta

Tati dake tsaye du baki daya yannayin ba dadi yake mata ba, tana ta tunani kala daban daban a cikin zuciyarta, shin zata dawo ta ce da shi basu sha nono daya ba? A me zai kaleta? Yaya alkawarin da ta yiwa mahaifin Aisha?
Yaya zata yi da kunyar abin kunya a ma'aikatarta? Ba zata iya jure wannan ba, dole ta yi hakuri da yannayin nan ta tabata na dan lokaci ne, idan Bilkisun ta matsa dinma zata fi sakewa a kan maganar auren nan

Hannu biyu Bilkisu ta saka ta amshi ledar hannunta , fuskarta dauke da dan murmushi ta ce" Na gode Tati, Allah ya kara arziki "

Bata iya bata amsa ba sai lumshe idannuwanta da ta yi

Shi kam ya mayar d ita TV, take takenta kawai yake kallo, to waima da izinin wa zata wani je gidansu?

Har sai da ta kai wajen kofar fita daga falon ya sauke kafarsa daya dake tankwashe cike da kasaita da isa ya budi bakinsa ya ce"

πŸ’ƒπŸ»
🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾
*DUK NISAN JIFA*
_(K'asa zai dawo)_
🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾

_RUBUTAWA_

*SAJIDA*

*SADAUKARWA*

*GA*

*MASOYA NA*


πŸ’«βœ¨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🀝

β˜† *[ T.M.N.A]* β˜† πŸ“–πŸ–ŠοΈ

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_


18






Cike da kasaita kamar za'a ciro maganar daga bakinsa ya ce" Yaya baki saka hijab ba zaki fita BILLKISU? "

Ja ta yi ta tsaya tana jin wani haushi haushin kin amsa gaisuwarta da bai yi ba
Akwatin hannunta ta duka ta zuge hakan ya saka shi rage girman idannuwansa yana binta da kallo

Ciro hijab ta yi fari kal mai tsayi ta saka a jikinta ta rufe akwatin
Tana kokarin kinkima ta ji ya kuma fadin" Wa kika tambaya zaki tafi gidan Aba? "

Gabanta ne yanzu ya fadi hakan ya sa ta juyo da dan sauri tana kallonsa

Idannuwanta ta yiwa rauraurau da kyar ta budi bakinta da yaren filatanci wanda ta tabata Mama da tati kawai suka iya yaren nata a wajen sai shi ta ce" Miyecci Dada kanko on hokkiyam lawol hamma am (Na fadawa mama, itace ta bani dama Yayana ) "

Bakinsa ya dan tabe yana kallonta tsai cikin ido ya ce" Yaushe Mama ta fara baki damar zuwa wajen da zaki kwana? "

Sai kuma ya rage amon muryarsa sosai da yaren hausa ya ce" Yaya kike so na iya rintsa idona bayan kina nesa da ni? "

Gaba daya wata irin kunya ce ta gama kama mama hakan ya saka ta mike ta shiga gyare gyaren zanin jikinta fit ta shige cikin kicin

Tati kuwa harta da bakinta daidai yake da budewar da ta yiwa idannuwanta tana kallon ikon Allah cike da mamakinsa

Aisha kam har ga Allah sai da gabanta ya yanke ya fadi , wanda bata san ko na meye ba

Mahaifiyarta kuwa ta kara kura masa ido tana kallonsa itama da mamakin furucinsa, me yake son nunawa? Ko dai da Aisha ta ce ba zai taba sonta ba Bilkisu yake so din yake son tabatar masu?

Bilkisu kam gaba daya sai ta rasa a yannayin da take ciki, a sama take ko a kasa take, a wani irin yannayi take jin kanta? Gaba daya lakar jikinta sai ta zare, ta nemi kuzari ta rasa sai na kyafta ido da bin fuskarsa da kallo, ...........inama zai gane cewar yana ilatata? Inama zai gane tatausan lafazi ko nuni da an damu da mutun a yanzu idan yana yi mata yana sakata a hakin ha'ula'in rayuwa? Inama zai zabureta, ya hankadeta, ya turata zuwa wajen da zata ji ta tsani ganninsa ko jin labarinsa? Inama zai kasance mai adalci a yar marainiyar zuciyarta da ta rayu da begensa?

Da yaren filatanci wannan karron ya ce"Mijabi do dum jarrabore on do bo dum salan to de donma de dillai mihosi banni dau hoddirore am on hamma am (ki kula da kanki, ki kula da ibadarki, ki kare mutuncin kanki, Allah ya tsare Bilkisuna....) "


Sai da ta hadiye yawu mai kauri tana dubansa a hankali ta dago hannunta ta duba agogon hannun nata, muryarta a sanyaye cikin ta kara lumshe idannuwanta ta ce" Na yarda da cewa jarabawace wannan kuma zata kauce, idanma tana nan bata kauce ba na dauki hakan a matsayin kadarata Yayana "

Gabansa na faduwa ya mike tsaye daga zaunen da yake, a hankali ya ringa nufota, su kuwa kamar wa'inda aka dasa su ukun nan ba wanda ya matsa daga wajen da yake, hasalima Tati kadai ke fahimtar abinda suke fada da yaren filatanci, su biyun kuwa kowace da abinda take son ganni a bayane

Sai da ya zo daf da ita ya kura mata ido a sanyaye cikin yaren filatancin ya ce" don jarrabore fere je jodanima der berde na ko don ko ayidi yeccugo am do dama berdema laram hado miko am yeccam minbo mihaban ko be moi hader duniyaru do gam miyi,a mihokkimamo (Akoy wata jarabawa da ta tsaye maki a rai ne? Ko akoy abinda kike son sanar mani dake damun zuciyarki?, kaleni nan kanwata ki fade shi ni kuwa zan yi kokowa da ko wanene a duniya dan gannin na baki shi!)"

Da mamakinsa take kallon fuskarsa, yaya aka yi ya yi tunanin dan ya girmeta a haife yana mai sakata a hanya har yake tunanin yana iya sakata a cikin hali na mugun matsuwar da zata budi baki ta kale shi shi ta furta masa kalmar dake da matukar girma da nauyi a bakinta? Ko ya manta ita, itace fa bafilatanar domin mahaifinta filo ne? Ko ya manta cewar shi ke iya furta rashin lafiarta tsabar yanda take fama da nauyin baki? Lalle ya dauki lamarinta da wasa.
....

Murmushi ta yi masa ta langwabe kanta, yan lebunnanta ta hade ta kuma bude a sanyaye ta ce" Bana tunanin haka, ban yi furucina dan wata manufa ba, sababin halayan yayana nake yiwa inkaya da jarabawa, kuma na san zasu kauce, zan je na kwana biyu na dawo ko dan na ciro anko in sha Allah "

Tsatsareta da manyan idannuwansa ya yi, hakan ya sa ta ringa dan wasa da yan yatsunta tana kallonsa

Bata taba tunanin abinda zai fada kennan ba, bata kawowa ranta cewa HISHAM zai iya wannan tataciyar maganar ba, sai ji ta yi ya furta "NA RUNGUME KI? "

Dan zabura ta yi ta matsa baya kadan tana kallonsa hakan ya saka shi sakin dan murmushi ya juya wajen Tati dake binsu kuri da kallo ya dan girgiza kai yana hangen yanda Mama ke son fitowa aman ya gagara dan sai ta leko kanta idan ta ha sunna nan sai ta koma da sauri

Dan daga muryarsa ya yi ya ce" TATI, yarinyar nan yar kauye ce, koda yake filatancin ne ko meye wama ya sani, aman in ba filatancin ba ni ai Yayanki ne dan kawai na ce zan rungumeta kin ga wata zabura da ta yi kuwa? "

Yanzun kam Tatin ce ta juya takim takim ta gudu da kafafuwanta, kusan a tare suka aikata hakan ita da Bilkisun domin kuwa a da tana gannin jakarta da nauyi ba zata iya dauka ba sai gata ta kinkimi jakar ta yi wata kwana ta fice a fallon

Sai da ya sauke ajiyar zuciya ya dantse lebensa na kasa har ta bacewa ganninsa sannan ya juyo ya kuma kallon Aisha da mamansa

Kallon tsaf, kallo irin na gaku zaune, ku ne kuka shigo min rayuwa a yannayin da kuka ga dama kuke son yi min wasa da rayuwa ko?
Sai kuma ya juya ya fice yana daidaita agogon hannunsa cikin takunsa na kasaitacen namijin da ya san kansa ya kuma gane cewar yana birge mai kallonsa

Jikinta a mace ta karasa gaban mahaifiyarta ta duka kusa da kaffafuwanta tana kallonta, kukanta da take rikewa ya kasa rikuwa hakan ya sakata yin magana cikin muryar kuka tana son rage sautin muryarta da karfi da yaji ta ce" Cikin wannan yannayi da suke ciki ake son raba su? Tsakanin wannan soyayar biyu ake son saka ni? Idan ya wulakanta maku ni shin kuna da damar nuna kun ji ciwo kuwa? Idan na fuskanci rayuwar rashin y'anci a tare da shi ba zan taba gannin laifinsa ba mama, ya furta , ya bayana, ya nuna ga wada yake so mama, me yasa kuke son saka ni a tsakaninsu? "

Mamanta ta dora hannunta a gefen kuncinta a sanyaye ta ce" Ba zaki gane ba Aisha, ina son tabatar maki cewa ko wani mahaifi burinsa yaronsa ya samu wajen da zai huta, wajen da hankalinsa zai kwonta, Aishatu a tunaninki soyayar da suke danewa suka kasa furtawa junnansu har soyaya ce? Ke a ce a cikin soyaya tsamo tsamo muka tarar da su irin wace basa iya second daya basu ga junna ba kina tunanin bayan auren itace zata ci gaba da wakana a tsakaninsu? A gabanki aka tambayeta shin da wani abu tsakaninsu? Ta bada amsar *aa*, shima a gabanki aka yi masa tambayar shin wani abu ke tsakaninsu? Ya nuna aa kanwarsa ce! Mahaifiyarsa sai da ta kara tambayar marikiyarsa itama ta nuna AA ba hakan bane, idan mamansa ta masa zabin abokiyar rayuwa mu sai mu kiya? Babu fa wanda ya zalince su, ba wanda ya shiga hakkin soyayarsu, idanma tunaninki ke nuna maki an zalince su zan fada maki cewar su fara tuhumar kansu kafin su tuhumi wani! "

Tsayar da maganar ta yi gannin mama ta fito dauke da abinci a hannunta ta kawo masu tana murmushi ta ajiye tana duban yannayin Aisha ta ce" Lafia take kuka? "

Mamanta ta ce" Kin san bata iya sabo ba hajia, wai Bilkisu ta tafi "

Mama ta ce" Ayyah, ai zata dawo nan ba da jimawa ba, abinda bikin ba da jimawa za'a yi ba, dolema ta dawo a yi bikin nan da ita ki daina kuka kin ji Y'ata?"


Aisha ta sada kanta tana sauke ajiyar zuciya , sai da Mama ta tafi sannan Aisha ta dagi tana duban mamanta ta ce" Sai nake jin tsoron mahaifiyarsa, sai nake gannin matar da bata yiwa wada ta rike mata yaro da gaskiya adalci ba, anya idan ta gama samun abinda take nema ba zata juyo da gabarta a kaina ba? Ko tace zata juya min da ragamar nawa gidan ba? , Mama sai nake gannin matar nan kamar irin matan nan ce masu zama da mutun idan yana da shi, idan ba wata alfarma zaka iya yi mata ta rayuwa ba sai nake gannin kamar ba zata iya zama da kai ba Mama sai nake jin tsoro da tsoron shiga hakki na kama zuciyata "

Mamanta ta yi mata murmushi ta ce" Sai kike gannin kamar ita din kaska rabu mai jinni jika ce?"

Da sauri Aisha ta sada kanta tana tsoron kar mamanta ta rufeta da mugun fada

Mamanta ta ce" Haka ne, bari ki ji wani abu, sannin cewar da na yi mulki zamani ne, a yanzu ana iya cirw mahaifinki daga saman kujerarsa a dora wani mai yiwuwa ya samu wajen da ya fi wanda aka cire shi, mai yiwuwa kuma a kara yin kasa da shi sha'ani na siyasa ya saka ni zagewa na hau na zauna kan maganar aurenki da PROFESSOR HISHAM, ita, ita ke rike da ATTAJIRI, ita ke rike da dama a hannunta, ba'a yiwa likita kutse ko a yaki ba'a yakar likitoci da yan jarida, Bale nata, watau mai gidan likitoci, Hisham din yanzu ya fara girma a haka, yanzu ya fara gidan Aisha, kar ki ga laifina dan na nemawa y'ata wajen da zata huta, ko a musulunci ba laifi na aikata ba, idan kuwa tunaninki zata samu abinda take so ta dawo ta wulakanta min y'a ai nima ba mahaukaciya bace da zan zauna na zaune, kin kuwa san ita ke mararin zama kawata ni kuwa ni ke tunkahon a san ina tare da uwar wannan wata sha kallon? Kar ki damu da shariyarsa, da yannayinsa, na san me yake nufi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login