Showing 45001 words to 48000 words out of 180809 words

Chapter 16 - DUK NISAN JIFA COMPLETE HAUSA NOVEL

sajida   

02 Feb 2025

12970

hankali kwonce dan kuwa an hana kama su hakan ya saka suke yawaita su sha rawarsu ba mai hanna su

Yan duwatsun da yake dan jefawa yana kallon ruwan ne suka kare a hannunsa hakan ya saka shi juyawa dan daukan wasu

Ido hudu suka yi da Kader dake tsaye yana kallonsa

A hankali Kader ya karaso hannunsa cike da yan sumbulilikon duwatsun da ya tsintsintar masa ya mika masa

Amsa ya yi ya juya a hankali ya ringa dan jefawa kamar wanda yake son samun kan wani abu

A hankali Kader ya ce" Me ka dauka mataki a kan damuwarka ?"

Bai bashi amsa ba har kusan minti daya kafin ya dan sabule farar kafarsa daga cikin takalminsa kafa ciki ua zauna a kasa nan wajen farar kasar dake zagaye da katon tafkin

Shima Kader din zama ya yi yana kallonsa

HISHAM ya yi murmushi a hankali ya ce" Jarabawata ce wannan "

Kader ya kale shi da sauri ya ce" kana nufin matar da ta zo maka rana tsaka zata kashe maka mafarkinka na shekara da shekaru? A kan me zaka kirayi haka matsayin jarabawarka bayan kana da damar bijire mata!"

HISHAM ya kale shi ya yi masa murmushi ya ce" Ta isa da ni fa Kader, haihuwata ta yi, sannan wace ta sha fama da ni din ta giya mata baya, Kader tun da na tashi ni na dan sarki ba, ba sarki na, ba wani dan kusan da ya tsaya min a duniyata ba , mahaifina MUHAMMAD KARIBULLAH na raye, ya gudu dan ya bi umarnin mahaifiyarsa shima, Kader sai Allah ya talafe ni, na ringa tafia bisa kariyarsa da ikonsa da saka albarkarsa, a hankali duniya ta san da ni, ya zamana Kader ni ba sarki ba, ba shugaban kasa ba aman sarki da shugaban kasar ke neman alfarma a wajena! Ba fadar shugaban kasar garina ba, ko ta wata kasa na je takardata na iya bani damar shiga kai tsaye kuma a mutuntani"

Sauke ajiyar zuciya ya yi ya kuma kalle shi a hankali ya ce" Maganar mata ba sai na fada maka ba, a zamanin nan na tsaya na kara fada maka yanda mata ke wawata na zuba shirme, Kader ita nake mafarki, baka sani ba kamar sakarai bana sannin ni namiji ne sai ta min irin rungumar nan ta ba zata, sai gashi sun ce sun Ki"

Kader ya ce" Dan Allah kar ka kashe walwalarka a kan umarnin Tati "

HISHAM ya kuma kallonsa ua juyar da kansa ya ce" walwalata, nutsuwata, farin cikina, burina duka Tati zata kashe su idan har ta yarda ta yi haka......babar damuwar shi ne, zan fitar da fuskar da yan gidanmu basu sanni da ita ba, hakama mutanen gari, ........"
Murmushi ya yi mai ciwon gaske ya ce" Domin ba zata rayu da wani kato ba, ba zan iya buda idannuwana na ji cewar wai an na yi aure itama haka? KADER Uktina ce"

Kader ya sada kansa yana jin kansa na sara masa, a kan me wai zai wani yiwa matar da bai wani sani ba biyaya? A kan me zai yiwa Tatin nan biyaya?

Mikewar da ya yi ya saka Kader mikewa ya bi bayansa da dan sauri

Maimakun ya shiga bayan motar gaba ya shiga ya zauna a sanyaye ya ce" Ka kaini gidana dake Jeune cadre "

Da to kader ya amsa ya tuka shi ya nufi cen da shi

Jikinsa ya gama yin zafin da har huci yake fitarwa, sai dai karfin hali da tunani sun hanna masa fahimtar cewa bashi da lafia

Nacin kader ya saka shi balar magani ya taune ya hadiye ba ko ruwa sannan ya koma ya zauna yana nazarin rayuwa.


Kamar da wasa kwana biyu cir Hisham ya dauka su mama da kowa basu san inda yake ba, sai kader kadai dake jinyarsa da faman ya ci abinci

Haka kuma Bilkisu kwonce take jirgat ba lafia, ba wanda ke iya gane ganta, Mama kawai ta san cutarta kuma ta yi biris danma kar ta samu kwarin gwuiwar da zata kara langwabe mata

Yau kam Mama ta shirya dan zuwa inda yake, ta kasa hakura, hankalinta ya kasa kwonci, gashi har mahaifin Aisha ya zo sun zauna sun yi magana, duda Aishar kallonsu kawai take sai ta yi murmushi ta dan girgiza kanta har zuwa yanzu ba abinda ta iya ce masu amsa,

Da kyar ta shawo kan Kader ya zo gidan, ba tare da ta ce da shi komai ba ta shiga cikin motar da ya da ita ta bashi umarnin ya kaita wajen da yaronta yake

Ba yanda ya iya haka ya ja motar suka tafi

Jikinta a mace ta karasa inda yake tsaye tun shigowarta, sai da ta dan yi dadage ta shafa gefen fuskarsa tana kallonsa da kauna irin ta d'a da uwa , da yaren filatanci ta ce"Wakkati doggugo am wadina bingel am? Hande baldema didi Hisham adoggiyam dume aibe am? (Lokacin guduna ya yi ne Yarona?, yau kwananka biyu Hisham ka min gudun hijira meye laifina? )

Jikinsa a mace shima ya kakaro murmushi ya rike hannun nata yana kallonta a sanyaye ya ce"Doggugo mon jemiwadi kanju on aibe manga jemiwadi daga wakkati miwadi hakkilo Amman dada am noi miwatta miwarta bawo misaldiri watango hore am muyal (yin nesa da ku shine horo mafi tsanani da na yiwa kaina tun da malaki hankalin kaina, aman Mamana yaya zan yi na dawo bayan na kasa sakawa zuciyata hakuri? ) "


A hankali ta kuma dubansa ta ce" Aviya to wodi mo awaddino miholli owadanai am awawata tokkugo hala am Hashim mivi miyida miheban na ko mihebata (ka ce da wata ka kawo na nuna batai min ba ba zaka min biyaya ba? HISHAM na ce maka hakan bai min ba, shin ba zan samu ba? )


Idannuwansa cikin nata, yana jin a duniya anya akoy masu irin halayanta ko dai ita kadai ta rage ya rike hannunta da kyau cikin yaran filatancin ya ce" Ayidi miwadana mikoma doutarena dada am? Gam banni awokata? (So kike na yiwa kanwarki biyaya mamana?, saboda shi ne kike hawaye? ) "

Mama ta share hawayenta tana kallonsa a hankali take gyada kanta hakan ya saka shi sakar mata murmushi ya ce" To accuwokugo mimetata dada am wartuhado be jonde hakonbi am hankobo ojoda hato har otimmina bangal sai owailita ko ojoda be debbo je osubi man (Tohm ki daina kuka, ba zan kuma ba, ama mamana ku dawo nan da zama kusa da ni, ita ta zauna a cen har ta gama bikin auren sai ta juya ko ta zauna tare da matar da ta zaba din )


Hade fuska Mama ta ringa yi ta janye hannunta daga barin fuskarsa ta juya masa baya ta kaisasa muryarta ta ce" Kai bingel am mendayima on na an on dayi amin ba he ima banni Hisham to milaraima hasare to hande mi accinte sarema midillan bo mihuni ni ma be bilkisu midillidinta men majjinte hader duniya gam na kanya men yahata balle ahefta amen (Kai yarona, haihuwarka muka yi ba kai ka haife mu ba! Ya isheka haka, Hisham idan ban ganka yau a gidan cen ba zan bara maka gidanka na yi tafiata, kuma na rantse da Bilkisun zam tafi zamu bace maka bat a duniya domin ba Kanya zamu je ba bale ka samo mu!) "



Tana gama fada ta yi tafiyarta da sauri tana danne zuciyarta

Kader dake tsaye a kofa ya bi bayanta yana jin zuciyarsa na tsintsinke masa, ya san idanma ya tsaya suka hadu sai ya yi masa ba dadi domin shi ya kawo Mama inda yake






๐Ÿ˜Œnot edditing๐Ÿ˜
[7/24, 10:18 AM] BAK'A CE: ๐ŸŽพ๐ŸŽพ๐ŸŽพ๐ŸŽพ๐ŸŽพ๐ŸŽพ๐ŸŽพ๐ŸŽพ๐ŸŽพ๐ŸŽพ
*DUK NISAN JIFA*
_(K'asa zai dawo)_
๐ŸŽพ๐ŸŽพ๐ŸŽพ๐ŸŽพ๐ŸŽพ๐ŸŽพ๐ŸŽพ๐ŸŽพ๐ŸŽพ๐ŸŽพ

_RUBUTAWA_

*SAJIDA*

*SADAUKARWA*

*GA*

*MASOYA NA*


๐Ÿ’ซโœจ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*๐ŸŒŸ
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_๐Ÿค

โ˜† *[ T.M.N.A]* โ˜† ๐Ÿ“–๐Ÿ–Š๏ธ

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_


17



Tana dawowa ta tarar da Tati na tsaye kan Bilkisu , tana ta lalabata kan ta yi hakuri ta tashi ta ci abinci aman fir ta ce bata jin yunwa


Aisha dake zaune gefe tana kallonta ta lumshe idannuwanta tana jin ba dadi a kasan zuciyarta, ita ta kasa gane kan su biyun nan, wai a kan me ba zasu iya bijire wannan lamari ba bayan sunna da damar yin hakan?

Mama ta girgiza kanta ta ce" to in ba zaki ci ba ki tashi ki ba mutane waje kafin na tsintsinkawa fuskarki mari mai gado, ka ga marar kunyar kawai shine har kike wani lalamata kamar yarinyar goye?! "

Tati ta kaleta ta ce" Haba aunty, yarinyar ba lafia maimakun a lalabata sai a ringa kirta mata fada me ya yi zafi, ni dai ta tashi ta sha magani ko zafin jikin ya barta? "

Bakuwar Tati ta ce" A yi hakuri maman Y'ata, wannan fada haka ? Ni sai na dauke y'ata mu yi gaba su Elhaji sa isko mu"

Yar daria Mama ta yi ta cire hijab dinta ta ajiye saman kujera ta ce" Ai sai ku yi, bara na yi sallar la'asar ni "

Du da ido suka rakata kafin Bilkisu ta mayar da idannuwanta a hankali ta lumshe, bata san da wani ido zata buda ta kalli Tati na, bata san ta yaya zata fahimci kaunar da take nuna tanai mata ba, a yanzun burinta ta yi nesa da wannan mumunan mafarkin, yau kwana biyu kawai du ta rasa tunanin me zata yi, cin abinci na gagararta , walwala ta kaurace mata, da gaske suke maganar auren yayanta da gaske ake magana ta kankama domin har baba na Kanya ya zo da kansa sakamakon kiran da mama ta yi masa (Mahaifin tsohon mijin Mama), sai ta ji kamar zazabi zai rufeta , sai ta ji kamar ta yi ta rusa kuka.....lalle ta lazumci adu'a dan samun saukin yannayin aman cikin ikon Allah sai ta ji ita dai bata jin saukin nan

Ta dauki dan lokaci sannan ta tashi daga wajen ta nufi dakin mahaifiyarta, hakan ya saka Tati rakata da kallo sai kuma ta sada kanta, Aisha kam ta zubawa tati ido tana karantarta, haka kawai take ji a zuciyarta wannan mata anya zata yiwa d'an adam alfarma? Ta kasa fuskantar y'ayanta d'an wa zata fuskanta?

Bilkisu na shiga ta nemi waje ta tsugunna gaban Mama da ta gama sallah tana jan carbi

A hankali Mama ta kura mata ido ta kasa ce mata komai

Bilkisu ta sauke ajiyar zuciya ta ce" Mama, ina son na je gidan Abana na yi sati daya dan Allah "

Mama lumshe idannuwanta tana jin wani irin abu mai ciwo a ranta, wai Bilkisun da bata iya motsawa nan da nan yau itace ke son zuwa har ta yi kwanaki gidan mahaifinta, yarinyar da mahaifin nata shi yake so ta zo masu ta yi masu koda kwana daya ne sai ta kiya ta nuna aa mamanta ba zata iya baci ba idan bata nan yau gashi da kanta zata tafiarta
A sanyaye mama ta ce" Yaushe ? "

Bilkisu ta kara sada kanta ta ce" ko yauma Mamana "

Mama ta yi dan murmushi ta ce" Zaki iya har sati guda? "

Gyada kai Bilkisu ta ringa yi hakan ya saka Mama cewa" to tashi ki je ki ci abinci, ki sha magani sai ki kimtsa kayanki idan rana ta kara yin sanyi sai na saka Kader ya kai ki "

Kanta ta kuma gyadawa a hankali ta ce" Na gode Mamana "

Har ta kusa fita Mama ta yi kiran sunnanta hakan ya sa ta dawo ta kara dukawa a kusa da Mama

Mama ta ce" Zaki guje ni ne? Zaki kaura wajensa da zama ne tun kafin aure ya raba mu? "

Bilkisu ta ji zuciyarta ta karye, a hankali ta matsa sosai jikin Mama ta dora kanta a gefen kafadar mama ta sanyaya muryarta ta ce" So nake na bi umarnin mace mai daraja a cikin mata, so nake na taya mutun mai daraja a rayuwata samun aljannah, shi yasa zan yi nesa da nan na dan lokaci, Mamana ko aure ba zai rabani da uwata ba sai dai mutuwa in sha Allah"

Mama ta sauke ajiyar zuciya a hankali ta ce" Allah ya yi maki albarka, ya baki miji na gari "

Bata amsa a bayane ba sai a cen kasan zuciyarta hakan ya saka mama furta mata furuci kamar haka" Yin nesa da abinda ke saka maka damuwa ba laifi bane Bilkisu, tashi ki tafi, ki dauki adadin kwanakin da kike so har ki ji sanyi sanyi a kasan zuciyarki, aman ina mai tunatar da ke Matar mahaifinki mamanki ce, tsakaninki da ita kar na ji kar na gani maganar raini ko wulakanci, ki yi mata biyaya , ki yi aikin gidanku da dukan karfinki, ki zauna lafia da kowa ki yiwa yayunki biyaya hakan zai sa kowa ya kaunaceki idan kin tafi tafia a yi kewarki, kar ki yarda ki je bakunta waje kina zaune ana aiki a gama a baki ki ci hakan na sakawa ki gunduri mutanen gidan koda kuwa gidan mahaidinki ne"

Bilkisu ta ringa gyada kanta alamun amsawa sannan mama ta ce" Tashi ki tafi, Allah ya yi maki albarka"

Tashi ta fice a dakin, hakan ya saka mama daga hannunta ta shiga kora adu'o'i zuwa ga mahalincinta, shi take kaiwa kukanta, shi take fadawa damuwarta, shi take fadawa ya shiga lamarin iyalinta

Sai da ta sha madara mai sanyi sannan ta hadiyi maganin zazabin dake taso mata

Tana cikin hada kayanta Aisha ta shigo dakin ta jingina da jikin garun dakin
Aisha yarinya ce mai matukar sanyin hali, tana da wayewa da kuma hakuri, uwa uba ita din ba mai naci a kan komai bace, du abinda ta ga ya zama na jayaya ko na naci takan saki, Aisha bata son a duniyarta ta kwonta da sannin ta cutawa wani, hakan ya saka take bin iyayenta da kallon abinda suke zumudin hadawa, su ko bari basa yi kakanta ya warke sumul? Dan sun san idan ta shaida masa ga irin auren da suke shirin hadawa ba zai lamunce masu hakan ba, shi yasa mahaifinta yake ta rawar jiki shine harda cewa ba sai an kai sadakinta da kayan aurenta garin Niamey ba tunda ga shi a nan ga mahaifiyarta kawai a bada komai a nan gidan su mijin da za'a aura mata, a haka bata gannin an siyan mata mutunci, gani take kamar abin hannunsa ke saka su rawar jikin nan, hakan ya sakata cikin zulumi

Da bakinta ta shaidawa mahaifinta cewa bata cikin maganar hadin nan, domin akoy wace ta fita son sa kuma shi din kansa ita yake so, sai cewa ya yi ita bata son sa? A gaskiya karya ne ta budi baki ta ce wai bata son Docter Hisham, aman kuma bata son rigima, bata so ta rayu da namiji tamkar ba mace ba, ta yi rayuwar nan irin ta dole, rayuwar nan bata da ma'ana domin rayuwa ce marar yanci

A cikin akwatinta take saka kayanta a nitse, tana jejera su har ta saka kala goma, manyan suturu na mutunci da hijabai da su pant da bra da clean sai turare da mai da sabulu

Rufeta ta yi ruf sannan ta mike ta nufi bayi

Ta dauki lokaci mai tsayin gaske a ciki, domin sai da ta ci kuka harda na mamaki sannan ta kimtsa kanta ta fito

Sasaukan shiri ta yi, sai turare da ta wanke jikinta da shi

Agogo ta saka a hannunta sannan ta daure gashinta a tsakiya ta yafa dan mayafi a saman kanta bata daura dan kwalin lesh din ba

Ido hudu suka kuma yi da Aisha a hankali ta taka gabanta ta tsaya tana kara binta da kallo
Murmushi ta sakar mata, murya ciki ciki ta ce" ALLAH YA SADA MU DA ALKHAIRI AISHATU"

AISHA ta kara wara idannuwanta da mamaki a kan yarinyar, what? Shine abinda take fada a kasan zuciyarta

Juyawa ta yi ta duka ta dauki katuwar jakar hakan ya saka Aisha shan gabanta da sauri ta ce" Meye wannan? Me kike nufi da wannan? Kin kuwa ji cewar ni ake shirin aurawa muradin zuciyarki? Ina zaki je? Ba zaki tsaya ki nuna masu cewar kin fi kowa cencenta kasancewa mai dakinsa? "

BILKISU da zuciyarta ta kyekyashe da wani koke koke ta kaleta tar cikin ido ta ce" Mun taba yi da ke cewar ni din nan shine muradin zuciyata? Me ya ke ba zaki dubi iyayenki ki nuna masu cewar bakya so a shafa maki lafia ba? Me ya sa ba zaki daina hashashe a kan lamarina?, Abinda ya hanna ki kallon idannuwan iyayenki ki bijire masu nima shi yake dawainiya da ni! AISHA ni bafilatana ce ciki da bai na ga damar na saka ki shakun sunnana bale wai har ke ki san abinda yake cikin zuciyata, zan tafi wajen mahaifina ne domin yana garin nan ba wai dan wani abin ba!"


Aisha ta saka hannunta ta riko damtsen hannun Bilkisu ta juyo da ita sosai ta ce" Ama baki san ciwon kanki ba ko? Wasa zaki yi da damar ki a kan wani dalili? Har zaki tafi ki bara mana gidan sai kace dole? "

Wajen hannun ta bi da kallo ta kuma kallon fuskar Aisha da wata irin daure fuska hakan ya sa ta cika mata hannunta

Hannunta ta kama ta nufi wajen kujera da ita ta zaunar da ita, hannayenta ta dora a saman hannayen kujerar tana kallonta ta ce" Ki kular min da shi domin shi din ba burina bane, Aisha DOCTER HISHAM *RAYUWATA* ne, ba tafia ce zan yi na bara maki gida dan na

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login