Showing 144001 words to 147000 words out of 180809 words
akan gadon tare da d'aukar wata lafiyayyar salayya ya shinfid'a, tana ji tana gani ya kabbara sallah ba tare da yace ga abin da zatayi ba, kuka kawai ta sake fashewa da shi sakamakon wani katutun bak'in ciki daya taso ya tokare mata zuciya, gaskiya yau Hamman nan ya ci ta wasan, ita zai kawo gidanshi a wannan sigar? Ai kam ko gobe ne sai ta bar gidan saidai ya sakΓ© d'aukota ta karfi
Yana gama sallar ko nace yana salamewa ya dan dafe gaban goshinsa
Dan tsaki ya yi ya mike tsaye ya kama rigar dake jikinsa ya yi sama da ita gaba daya ya cireta
BILKISU dake kukan tabara sama sama sai ji kake dif kamar irin an kashe redion nan ta kwalalo idannuwanta tana kallonsa kafin ta yi gagawar juyawa gaba dayanta gefen da kayansa suke hannayenta suka kwashi bari
Bakinsa ya tabe ya nufi wajen kayansa ya tsaya ya bata baya ya bude sif din ya shiga dan kallon kayan
Tawul ya fara janyowa ya rataya a kafadarsa sannan ya dauko dan karamin wandonsa na ciki da farar riga ya juyo
Karaf idannuwansu suka sarke cikin na junna hakan ya saka da sauri ta sada kanta ta hade hannayenta ta jimke waje guda a bayane take sauke ajiyar zuciya tana jara rintse idannuwanta
Karar rufe kofar bayin ya sakata dagowa a matukar razane ta diro kasa
Kai kawo ta shiga yi da wani irin sauri hankali tashe cike da mamakin yannayinsa da irin yadda yanzun ya cire rigarsa a gabanta bayan a da ko baya cikin hayacinsa baya tsayawa gabanta a haka, hannayenta ta dora saman bakinta a hankali ta ce" Na shiga uku, shikenan nima zan shigo layin gannin kato ba riga? Katonma Hamma? " (π)
Budewar da aka yi ya sakata juyowa , a hallin yanzu ta fara kokonton idan tana da hankali, a yadda ya kuma fitowa sai ta ji wani fitsari na matsota
Da sauri ta tinga matse kafarta ta rabe jikin garu tana son matse kwallah
Tawul din dake kugunsa ya cire hankali kwonce ya shanya a abin shanyawar sannan ya kuma dauko farar jalabiya ya zura a jikinsa kafin ya dauki turaransa sosai ya feshe jikinsa da shi
Wajen da take tsaye ya nufo cikin nutsuwa ya saka hannunsa ya janyota kusa da shi sosai
A hankali ya dora hannunsa jikinta dan ya ji yaya yannayin zafin jikin nata yake yanzu?
Sosai zafin ya ragu, aman kanta da zafi hakan na nufin kan nata na yi mata ciwo,
A hankali ya nufi wajen bayi da ita, hannunsa ya saka ya bude muryarsa cen ciki ya ce" Shiga "
Bilkisu da jikinta ke rawa ta yi gagawar fadin" Na yi me? "
Juyota ya yi yana kallonta a hankali ya ce" Na zata fitsari kike ji na ga sai matse kafa kike Billy am"
Idannuwanta ta lumshe sakamakon wata mashahuriyar kunyar da maganarsa ta bata, yau itace Hammanta ke fadin fitsari take ji?, ya subahannalahi,
A hankali ta ringa girgiza kanta domin koda fitsarin take ji ba zata taba iya bari ya sani ba, ina dalili wai wannan abin kunyar
A hankali ya juyota ta yadda take facing dinsa, cikin nutsuwa yake dan matsawa da ita kusan garun jikin bayin, sai da ya danganata a hankali ya dan daga hannunsa ya mata runfa, yar yatsarsa ta kusa fa babar yatsa ya dora saman lebunnan nata yana dan zagawa yana kallon yadda take fiki fiki da idannuwanta
A sanyaye ya kuma rage tsayinsa sosai ta yadda ya kara matse mata waje
Cikin nutsuwa ya dora lalausan lebensa saman nata, ta yadda tsoron da ya sakata zabura ta dago dubanta tare da bude bakinta ya bashi damar cafkar harshenta da ta yi niyar yin maganar da shi
A hankali ya lumshe idannuwansa ya shiga tsotar harshenta harda kuma rufe ido sannan ya saka dayan hannunsa ya kara kusantota da shi sosai
Sai da ya tsotsa, ya tsotsa iya tsotsarsa sannan ya cire bakinsa
Barkewar da ta fara yi da kuka ya saka shi da kyar ya dora dan yatsansa saman lebenta cen ciki ya furta" SHUIIIIIIIIIIIIIIIIT "
Shirun ta yi gaba daya jikinta na rawa tana jin kamar zata kifa
Da kyar ya daga luhu luhun idannuwansa yana kallonta ya ce" Harshenki, ya ringa tauna magana yana tacewa, yana gwadawa yana kara gwadawa kafin ya furta min ita Billy, a yanzu ina da damar da dukan abinda na aikata da ke lada ne, bana son gagawa a tafiata da ke aman idan kika min garaje zan maki garaje!, kin fahimta?"
Bilkisu dake hawaye kanta take gyada masa cike da mamakinsa, wai dama namiji haka yake? Sha nawa zata dora hannunta saman nasa ya wurga mata hararar da sai ta ji kamar zata saki fitsari na tsoro? Yau kuma itace ya yiwa haka?
"KUKAN da kika so yi da karfi dazun na menene? " ya fada yana karra kallon bakinta, baban burinsa ya kara talafota ya mata rikon da zai cinye bakin nan kowama ya huta, gaba daya jikinsa ya amsa ya kuma yarda cewa ba wai dan kawia yana sonta bane idan ta taba shi yake jinsa a namiji, aa, ita dinma mace ce harda kari, dumin harshenta ya kasa barin bakinsa....................
Da muryar kuka ta ce" FISTARIN NE ZAN JE NA YI inagama na fara "
a hankali ya sauke dubansa kan kugunta , da sauri ya lumshe nasa gannin ya kauce yana mai nuna mata hanya
Da wani gudu ta kwasa ta fada bayin ta maida ta rufe
Da gudu ta haye saman WC bayan ta cire pant dinta ta lumshe ido tana sakin fitsarin da take jin ta fara a wandonta, tana gamawa ta dauki butar dake ajiye ta wara kafafuwanta dan kama ruwa, sai dai me wani yauki yauki ta ji a jikinta hakan ya sa ta ciro hannun nata tana kallo
Wani abu ne fari kar mai yauki yauki shi ba fitsari ba, shi ba jinni ba, wanda a matsayinta na likita sannan wace ta yi islamiya sarai ta gane ko menene aman sai ta ture, ta hankade, ta ingije tana mai ayannawa kanta cewa ita ba yar iska bace bale har daga namiji ya tabata ta fitar da abin nan!
Lebenta na kasa ta cije a lokacin da ta hango abin a idannuwanta, sajensa na gugar habarta, damshi damshin fuskarsa na kai mata salama cikin salama sai ta samu kanta ta dan langwabar da kanta tana sakin wata irin ajiyar zuciya, a yau itace bakinta da na hammanta suka?????????
Ido ta zarro da sauri ta idasa wankewa ta mike tsaye tana gyara hular dake kanta , dan kai kawo ta yi a bayin nan tana dan wana yar yatsarta guda a hankali take tunaninta da jadadawa kanta kamar haka'Hamma am, ka samu in sha Allah ba zaka kuma samu ba, Hamma am kana da kyau, lale kana da karfi, kana da aji kana da kamshi......sai dai nima da nawa lamarin, Hamma am sai na nuna maka bana ji, Hamma am garajen naka nake son gani!, sannan sai na nunawa matarka ita take iya bayanawa ba dai ni ba!, sai na tayar maku da hankaki ku dukanku, kuma gida ko ka maida ni ko kar ka maida ni sai na koma domin na san hanya, walahi sai an rako ni irin na kowace amarya, sai an min jere a gidana ba gidanta ba!, Hamma am sai na daga maka hankali fiye da tunaninka wannan alkawarina ne!'
[7/8, 5:15 PM] +234 816 920 1901: πΎπΎπΎπΎπΎπΎπΎπΎπΎπΎ
*DUK NISAN JIFA*
_(K'asa zai dawo)_
πΎπΎπΎπΎπΎπΎπΎπΎπΎπΎ
_RUBUTAWA_
*SAJIDA*
*SADAUKARWA*
*GA*
*MASOYA NA*
π«β¨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*π
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_π€
β *[ T.M.N.A]* β πποΈ
https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/
_Bismillahir rahamanir rahim_
52
Tana gamawa ta wanke fuskarta da kyau tana jin yanzun zafin jikinta ya sauka hakama dandatsarta da yake yi
Fitowa ta yi cikin sanda tana dudubawa, gannin baya nan ta dauki lafayarta ta nada a jikinta ta zauna ta tankwashe kafafuwanta sosai ta gyara zamanta a hankalo ta fashe da kuka
Hisham na fita daga dakin jikinsa a mace ya karasa kusan Aisha dake zaune saman kujera
Zama ya yi kusa da ita sosai har jikinsa na gugan nata ya zuba mata ido yana kallonta
Murmushi ta sakar masa duka a kokarinta na son sai ta dane kishinta da abinda ke damun zuciyarta
A hankali ya lumshe idannuwansa ya saka hannayensa ya kamo nata yana kallonta, a sanyaye ya ce" Aish "
Aisha ta dago idannuwanta ta sauke a kan kyakyawar fuskarsa
Murmushi ta kuma sakar masa ta ce" Yau baka samu halartar sallar juma'a ba, kuma baka ci abinci ba har yanzu "
Hisham ya ja numfashi muryarsa a sanyaye ya ce" A lokacin da na fito da alwallah ina duba agogo na ga lokaci har ya zarta, Aish cikina kuwa bana jin yinwa "
Murmushin ta kuma yi masa ta gyada kanta ta ce" Ina kanwata ? "
Idannuwansa ya lumshe yana kara rike hannunta a hankali ya janyota jikinsa sosai ya rungumeta muryarsa cen ciki ya ce" Tana cen tana rigima "
Aisha ta yi yar daria domin a yadda ya fadan yana nunawa kamar wanda yake tsoronta ta dan dago tana kallonsa ta ce" To wani abin ka yi mata ne? "
Kansa ya girgiza a hankali ya ce" Wai cewa take an mata auren dole da hammanta ina hammanta ina ita? "
Murmushi ne ya subucema Aisha a hankali ta dago dubanta ta dora saman fuskarsa, hannunta ta saka a hankali tana shafa fuskar tasa ta ce" Ranta ne a bace "
"WANI abin akai mata da ranta zai baci? " ya fada yana rike hannunta a hankali ya kai wajen lebensa ya sumbuta, yana matukar jin yarinyar nan a ransa daga bakin lokacin da take taya shi kaunar Billy, walahi yana girmama irin yadda take dane damuwarta a gabansa, sarai ya san tana cikin damuwar shi yasa shima yake iya yinsa dan gannin bai tauyeta ba
Aisha ta sauke ajiyar zuciya ta ce" Laifi aka yi mata mana, laifi mai girma ma kuwa, ranta a bace yake sosai, kuma ban ga laifinta ba domin mijinta miskili ne ya kasa furta mata kalmar so dan ta girma a gabansa, bai san da nesa da shi ta girma da sai ya ji tsoron ganninta a gabansa, Billynsa mace ce"
Murmushi ya yi, a kasan zuciyarsa yana furta 'Fadin ina sonta ne damuwarta? Bafa shine damuwarta ba, kai anyama ita ta wani damu da ace ana son nata? Gashi dai tana faman tsorata shi domin a da ya gama sakankancewa cewa tana jin an daura masu aure zata kama tsalen murna da farin ciki har sai ya tsawatar mata, aman yanzun sai wani zilewa take tana neman kwonce masa arzuzumi a kasuwa '
Tabararen kukan da Bilkisu ta saki ne ya saka su da sauri kallon kofar, sai kuma suka kalli junna
Da sauri ya nemi mikewa yana jin zuciyarsa na dokawa, ya kamo hannun Aisha a sanyaye ya ce" Dan Allah mu je ki yi mata magana "
Aisha ta shiga raraba ido tana son ce masa kai itafa Allah tsoron fitinar matarsa take aman kuma ina tuni ya jata ya yi gaba da ita hakan ya saka ta sauke ajiyar zuciya tana biye da shi
Dakin ya bude ya shiga tare da Aisha, turus suka yi sunna kallonta, irin zaman da ta yi da irin yadda take rusa kukan abin sai wanda ya gani
Karasawa Aisha ta yi tana fadin" Subahannalah Bilkisu yaya haka? "
Billy ta dago kanta tana kukan ta ce" Aunty Aisha gida nake so, a kaini gida aunty Aisha, walahi ba zan iya rintsawa a wajen nan ba, haba bana baku tausayi ne? Ku duba fa ku gani bani da lafia wa zai kula da ni? Bana iya yin shiru idan ina kukan rashin lafia , Aunty Aisha "
Aisha ta kara sasauta muryarta sosai ta ce" To aman Bilkisu ba gani ba kuma ga mijinki hammanki? "
Bilkisu ta kaleta, a hankali kuma ta saci kallonsa, ya wani hadu da garu ya jingina yana lumshe ido, ita walahi kwata kwata kwana biyun nan sai yake mata kama da wasu yan duniya, da sauri ta cire dubanta gannin kamarfa ita yake kallo ta dan turo bakinta ta rage muryarta sosai ta ce" Ba zaki daina hadani da mijinki a matsayin nawa ba ko?, ki fada masa ya maida ni gidanmu kusa da iyayena ban tashi tarewa da kaina ba gaskiya!"
Sai Aisha ta samu kanta da tunanin to meye a ciki? Dan ka tare d akanka me a ciki? Wannan zamani na warce warcen mazan mutane ba tarewa da kai ba da gata tare da mijinka ko kira ya yi ya ce zo ita bata ga wani damuwa a ciki ba, abinda ba adini ne ya ce a rufeki a kawoki ba? Idanma mijinki ya dauko ki ai a ganninta abin gadara ne, ita fa koda duka kaf jikinta kune ne Bilkisu ba zata samu nasarar saka mata tunanin bata son Hisham ba, ta riga da ta yi sake tun farko ta karanci sonsa da kishinsa a tatare da ita, shi yasa take baya baya tana kafa kafa da dukan wani motsinta a kusa da su, tabas mahaifiyarta ta fada mata cewar koma meye ta riga da ta sha gaban Bilkisu tunda har ta fara amsa kiran matarsa, kuma ta lura yana da adalcin da ba zai wulakantata ba dan tana matarsa ta hadi, aman ita sauraronta kawai take, ba abinda so baya saka namiji ko mace aikatawa, shi yasa take a supporting dinsa, walahi kokarinsa da kamanta adalcin da yake son yi a gareta na matukar kara daukaka girmansa a idannuwanta, ita ta san ba maganar so bace ta hada su, mutuntuka ce mai girma da daraja wace ta fi wani son anfani ainun
Zamansa a gefen Aisha ya sakata kallonsa tana kayse tunaninta
Muryarsa a sanyaye yana kallon Aisha ya ce" Ki ce mata ba adini bane sai an rakota, ki fada mata ta daina daga min hankali bana so dan Allah"
Aisha ta yi murmushi tana jin yadda zuciyarta ke dokawa da sauri sauri wani irin abu ne ke son dunkulewa ya tsaye mata a kahon zuciya mai kama da nauyi da daci mai kama da mangari da fata, a hankali ya ci gaba da maimaita adu'o'in da takan lazumta dan samun saukin zogi irin na kishi ta dubeta ta ce" Kin ji abinda ogan ya fada? "
Bilkisu ta lumshe idannuwanta ta kuma gyara zama sai kawai suka ji kamar daga sama ta kuma rushewa da kuka harda dora hannayenta saman kanta tana fadin" Na shiga uku na lalace"
Abinda yake danewa ne yake son fin karfinsa, da sauri ya kamo hannunta yana kallinta ya ce" bandirawo, duka wannan din na kina ne?, Billy am duka wannan kukan na tsanata ne?, duka wannan din na rashin kaunata ne ? "
A tare suka dube shi ita da Aisha da sauri, gabanta ne ya buga ita din kanta dan a yannayin da yake tambayar kamar wani dan maraya sannan fuskarsa na nuna matsanancin tashin hankali
Bata kai ga bashi amsa ba ya mike da sauri ya juya ya yi waje, hakan ya saka su dukansu binsa da kallo mai kama da tsorata da yannayinsa
Da sauri Bilkisu ta mike tsaye ta yi taku biyu dan bin bayansa sai kuma ta ja ta tsaya cike da jin kunyar Aisha wace bata taba jinta ba sai yau, da kuma tausayinta
A hankali ta dawo ta zauna a gefenta ta sada kanta tana sauke ajiyar zuciya
Aisha ta kamo hannunta tana kallonta ta ce" A karro na barkatai zan kuma rokarki abinda na san kin san ba laifina bane Bilkisu, ki yafe min kin ji? Ina dora abin nan a kan kaina ne sai na ji da nice yaya zan dube ki?, walahi ba zan boye maki ba da wuya na iya dubanki , sai dai ina so ki ringa duba abu guda Bilkisu, kadarata da kasantuwata daya daga cikin matansa ya kawoni gidanku har haka ta kasance da mu baki daya, sannan na san cewa ko babu ke idan da rabon wasu su shigo zasu shigo, Bilkisu a duniya idan kina son hankalinki ya ki kwonciya ki auri mai kyau, ko me kike hankalinki na kansa , nutsiwarki na tare da shi, ke koda Allah ya yi shi ba mai kale kalen matan bane su zasu kale shi, balantana yawancin mazanmu sunna anfani da damar da Allah ya basu ta kyau ko kudi dan su tagayara yan mata masu karamin kwakwaluwa, Bilkisu idan bayanmuma akoy rabon wasu ina mai neman alfarmar da mu kwontar da hankalinmu mu hada kanmu, kin ganni nan alfarma rayuwa ta min, kuma zan iya rantse maki ina farin ciki da buda ido na ganni a wannan matsayin, ba dan kudinsa ba, ba dan kyansa ba, ko matsayinsa ba, aa Bilkisu dan nagartarsa, dan nasabarsa, dan iliminsa, da kyawawan halayensa, kin ga fa du irin yadda akai masa kutse bai dagani ya makani da kas ba, ni na san ya kuma san ba maganar so bace face mutuntawa da biyaya ga iyaye, Alfarmar mamanki nake ci wada ba zan taba mantawa da ita ba, na sha na duka ina kuka nace da ita ku ke son junnanku kar ta tirsasashi aikata wannan aiki duda tunda na ganshi na kamu da sonsa, aman sai ta min fada irin na uwar arziki wace zata yiwa y'ayanta, ta min kashedi da fadin cewa na fadawa Allah, iean har ni din nan matarsa ce Allah ya tabatar mana da alkhairi, Bilkisu ban san gidan boka ko malan ba hasalima ni din nan ban yarda da cewa wani na iya min abinda Allah bai min ba, Bilkisu ban tara kawaye ba