Showing 33001 words to 36000 words out of 180809 words
ta gama sannan ta bude sabon abin kilace broch da soso ta saka mata su ta rufe ruf
Wankanta ta yi cikin nutsuwa, ta darje jikinta sosai da sosai sannan ta daura tawul din nan ta fito
A lokacin da ta fito Aisha na zaune wajen kujera, ta cenza kayan jikinta ta fesa turare tana zaune tana dadanna wayarta
Bata ce da ita komai ba ta nufi wajen kayanta
Wata doguwar riga irin ta nilon din nan ta ciro mai ruwan baki
Rigar irin mai kama jikin nan ce sosai domin kuwa koda ta yiwa mutun yawa takan bi jikinsa bale wa nan batai mata yawa ba daidai da jikinta ce , yannayin yanda take yiwa mutun rawa a jiki koda bashi da abin motsawar a bayansa abin birgewa ne, irin yanda kalarta ke haska fata koda bak'ar fata ce kuwa sirri ne
Dinkin irin mai baban wuya ne hakan ya sa dole ana iya gannin saman kafadunta kadan harda wajen kirjinta kadan
Wajen turaranta na fesawa ta je ta dauka
Irin fesawar da ta yi masa sai da ya baiwa Aisha mamaki
Pant dinta ta dauka kalar fari ta yi cikin bayi ta saka ta kuma fitowa
A hankali ta je wajen kayan kwaliyarta ta ja ta tsaya tana bin su da kallo
Murmushi kawai ta yi ta ciro kwali baki ta sakawa idannuwanta
Ta caje gashin kanta ta daure da ribom sannan ta dauki wata yar siririyar sarkar da bata da komai jikinta sai dan igiyar sarkar ta karfe ce ba azurfa ba ba komai ba , tsarin kyanta ne ya saka ta siyeta
A iya wuyanta ta saka ta rufe komai ta juyo da niyar komawa bayi dauko kayan shanyarta
Ido hudun da suka yi da Aisha ya sakata dan kura mata ido itama sannan ta juya ta nufi bayin
Aisha kam a yau ta ga abin mamaki, ashe yan gayu ne mutanen garin nan? Kuma sun iya kwaliya da tsafta da anfani da turare? gannin tankamemen gidansu bai saka ta yarda cewar sun kai haka ta yiwu kudin ne aman ba'a iya gayun ba, bata tashi binta da kallo ba sai da ta fito da tawul, daga dan rabin cinyarta kadan da sauran kwabrinta har zuwa kafafuwanta da tafin kafafuwan nata sai ta kara sara mata, uwa uba irin kayan fake dakinta, komai da komai nata mai tsada ne mai aji ne, na manyan babys ne, sai da ta saka suturarta ta ga yarinyar mai tsada ce, uwa uba turarenta , irin shirya kanta da ta yi ta hanyar anfani da abu karamin da ya fito da ita kamar zinari a cikin kasa watau tana kyali abinta
Tana nan zaune Bilkisu ta fito rike da bokicin kayan makarantarta
Da sauri Aisha ta mike ta tsaya a gabanta tana kallonta muryarta sanyaye ta ce" Dan Allah ki yi hakuri, ban san ko bakwa so a rabi inda kuke bane, ko ni din ce ban yi maku ba? Aman ina neman alfarmar da ki sasauta min daure fuskar nan domin ba da gangan na zo gidanku ba, ba kuma da gangan na shigo rayuwarku ba, mun kawo papy dina ne ba lafia, yayanki zai yi masa aiki shine aka ce mu zo nan, idan zaki amince da na mun yi kawance duda na san na girme ki aman ni kin min zan iya kawance da ke "
Bilkisu dake kallonta har ta kai ayar maganarta ta yi mata dan murmushi ta ce" A kan me zaki bani hakuri bayan ba abinda kikai min? Juste ni ina da wahalar sabo ne a duniyata, ama tunda Allah ya hada mu, ki kwashe kayanki daga kasa ki saka cikin drawer, bakunta bata saka ni banzatar sa suturata "
Tana gama fada ta juya da bokitin ta yi gaba
Sai da Aisha ta sauke ajiyar zuciya ta dauki kayan nata ta buda bangaren tufafin Bilkisu
Hangam ta yi da baki tana bin suturun da kallo, to ita wannan yarinyar ko amarya ai sai haka , amaryarma yar gata bafa an min aure ba!
A yau sai ta tsinci kanta da raina kanta du kuwa da irin yanda take da nata gatan da saka mahaukatan kaya , du irin yanda mahaifinta ya daure mata mahaifiyarta kuwa ke kashe mata kudi
Da sauri ta kilace kayan ta rufe ta juya ta bi bayan Bilkisu
Ja ta yi ta tsaya sakamakon abinda take hange
Bilkisu ta bada baya tana shanyar kayan da basu fi hudu ba, sket da riga da hijab da dan kwali
Abinda ya sakata kurawa wani lamari ido ba komai bane sai wannan gayen, wannan ingarman namijin, a yanzun jikinsa sanye yake da wando gahere irin wanda ya wuce gwuiwar nan na maza baki sai riga ruwan ja wace botiran saman ke dan bude haka kuma ta ainahin kama jikinsa ta bi lafiar jikinsa
Abokanansa ne har mutun biyar, abokanan aikinsa sun fito tare, sai dai bai kai ga idasa fitowa ba ya ja ya tsaya tare da zarro ido cike da mamaki sai kuma nan da nana kyakyawar farar fuskarsa ta fara rikida tana yin ja da yannayi na bacin rai na neman samun matsuguni a tare da shi
A hankali ta bi wajen da ya kurawa ido
Daidai lokacin da Bilkisu ta duka ta ciro farin hijab dinta ta kama shi da kyau dan matse shi da kyau, a irin wannan yannayi ne yannayin halitar da Allah ya yi mata ta bayana a idannuwan dukan wani wanda ya kura mata ido a irin wannan lokaci, haka kawai Aisha ta juyar da dubanta kan sa
Idannuwanta ta kura masa, lokaci daya ta ga ya shiga gaban mazan nan, kakarfan hannunsa ta ga ya daga ya shiga yi masu nuni da su kalli wani wajen da ta tabata ba abinda yake nuna masu
Ita dai ta kasa gane komai a kan lamarin nan, ta shiga rudu mai girma
Sai da ta gama shanyarta ta saci kallon bangaren yayanta ta ga sunna hira da abokanansa sunna kallon wani wajen ta tabe bakinta ta dauki bokicinta
Sai da ta darwaye shi ciki da bai sannan ta raba gefen Aisha bayan ta sakar mata murmushi ta shige ciki dan maida shi
Bayan ta gama kimtsa kanta Tati ta kuma yi mata maganar cin abinci
Mama ta yi murmushi ta ce" Zainab, ki ba kanki wahala tunda kin yi niyar damun kanki, wannan fa haka take, yanzun da cak ne ko ice cream ko wani jus mai kyau da kin ganta tsaye a layin masu amsar nasu da farko farko, aman idan abinci ne haka zaki gaji tana sakar maki murmushi tanai maki kwalkwal da ido masha Allah idan kika takurata kuwa ta sakar maki kukan iya shege"
Tati ta dauki plat ta zuba mata soyayan dankalin turawa ta zuba mata vinaigrette ta ce" shi ya sa cikin nan baya tasowa, dan Allah kalli cikin ki Babyna yanzun idan kika auri mijin da baya so ya ga mace ciki a shafen nan yaya zamu yi kennan? Ki rufa min asiri wannan kugu naki kar ya karye rike da kayan nan bakya gannin sun masa yawa?"
Matar DG me zata yi banda dariya ta ce" na raba ki, a yanzun daidaikun maza ke son macen da ta ajiye tumbi, kuma ni wannan kira ta Bilkisu haka ita ce daidai, irinta ke haukata bayin Allah "
Ita dai du sai abin ya sakata jin kunya, ita mamanta bata taba irin wannan maganar haka a gabanta ba, sam mama bata sakin bakinta ta yi wata maganar da bai dace ba a gabanta, ita ganni take wannan ai sam bai dace ba, ba zancen da iyaye ya dace su ringa sakin baki sunna yi a gaban y'ayansu ba, dan gudun sakawa yaro wani abin a cikin kansa domin kuwa yara sunna anfani da fadar iyayensu, sunnan msaurin daukan abinda ke fita da dabi'un iyayensu
Mama ce ta dubeta dan sam bata son tana zaune haka ana magangannu irin haka a gabanta, duda ta san yanzu adu'a ita kadai ce zata iya kare maka yaronka domin kuwa kana iya kwasar shekaru kana kafa kafa da abinka rana tsaka idan Allah ya kadarta yaron zai iya haduwa da wata muguwar kawa, ko mugun saurayi, ko jarabar wayoyin zamani da abubuwan dake cikinsu ya lalace maka, kwarai ta san ba abinda Bilkisu bata sani ba na irin magangannun da akai, sai dai bata so ta tanka a haka ko ta bari a ci gaba da kodanta abin, hakan ya saka ta dubeta zata yi mata magana dan umartarta ta koma daki
Tana shirin yin maganar wayarta ta dau tsuwa
Tana dagawa iya abinda yake so ya fada ya kashe kiran domin kuwa ransa a bace yake a irin wannan lokacin
Dubanta ta yi ta ce" Tashi ki je yayanki na kiran ki "
Mikewa ta yi ta kama hanyar fita,
Mama ta ce" Hijab din fa ?"
Tati ta yi gagawar fadin" Hijab kuma? Ana zaman kalau sai kace ba yayanta? "
Da dan mamaki a fuskar mama ta kalli Tati da kyau, yau ko muharamarsa ce ai ta lulube jikinta a gabansa bale ba ciki daya ba suka fito, shi din shine zai yi kwalo da ita idan ta je masa a haka ita kanta ta sha'afa da hakan ne
Mama ta yi murmushi ta ce" Ai ya hannata yawo hakan ne, idan ta tarda shi haka ita da shi ne ba ruwana "
Bilkisu dai zuwa ta yi ta dauko dogon hijab dinta mai hannu ta saka sannan ta fito ta nufi bangarensa
Duda gabanta na faduwa, aman bata hanna kanta amsa kiransa ba
Da siririyar muryarta ta yi salama har sau uku kafin ta tsinkayo muryarsa kasa kasa ya amsa yana bude mata da kys din da ya saka bayan dawowarsa
A hankali ta tura ta shiga da salama tana kallonsa
Gabanta ne ya fadi gannin yannayinsa, yannayin fuskarsa da hucin da yake saukewa a hankali a hankali
"Yaya gani" ta fada tana dan rage tsayinta irin zata yi ladabin nan
Saman kujera ya hau ya zauna ya talabe habarsa yana kallonta , kakausan kallo mai tafe da sakwani kala daban daban, irin ana jin haushin nan naka hakan ya saka ta yi tsomomo ta zauna saman kujerar ta tankwashe kafafuwanta ta rike babar yatsar kafarta tana dan wasa da ita a ranta kuma tana ayana 'dama na san a rina'
" *IDAN RUWAN SAMA NADA LOKACI, TO NUMFASHIMA YANA DA IYAKA BILKISU* " Ya fada cen kasan makoshinsa yana dan dafe gaban goshinsa
BILKISU ta dago da dubanta ta kura masa ido tana kallonsa , daidai lokacin ya dago da nasa duban shima yana kallonta ,
Sai da ya kara nutsar da dubansa cikin nata sannan ya dora da fadin" *IDAN KIKAI HAKURI ZAN MUTU NA BAR MAKI DUNIAR BA SAI KIN KASHE NI BA BILKISU* "
Gabanta ne ya tsinke ya fadi, a hankali ta rarafa ta karasa kusa da kafafuwansa tana kallonsa ta ce" Yayana, na yi wani laifi ne? "
Hannun nata da ta dora a saman kafarsa ta dama ya kurawa ido, zara zaran yatsutsan hannun nata yake kallo, sai akaifunta dogaye masu kyau da tsari,
A hankali ya lumshe idannuwansa ya yi mata nuni kan ta tafi
Rintse idannuwanta ta yi tana jin yanda zuciyarta ke dokawa, anya kuwa zata iya ci gaba da neman fitina a duniyarsa? Domin a yanzu ta samu amsar maganar duniya, ba wai iya duniyarsa bace ta shi kadai, duniyar ta su biyu ce, wace tana da yakinin idan ta shiga da garaje tana iya ture ginin bulo da bulo din dake rike da katangun duniyarsu
A hankali ta so dora kanta saman kafarsa, sai dai ta yi gagawar hanna kanta haka dan ta tabata yanzu zai janye kafafuwansa su yi baran baran
A sanyaye ta ce" ka yi hakuri da rashin ji na yayana ba zan................
Bai barta ta idasa maganar ba ya yi gagawar fadin" Karya kike, zaki kuma, idan kin tashi kumawar sai kin min abinda zai gigita ni, shin baki san cewa dan ina yayanki dan uwanki wanda yake matsayin uba a wajenki .....dan kuwa ai baban wa uba ne ko? Ya sa nake damuwa da tarbiyarki ba? "
A hankali ta dago rinanun idannuwanta tana kallonsa, bata san lokacin da ta ce " Iya shi ya sa ka damu da shigata ? "
Shima kureta ya yi da kallo, a hankali ya hade fuskarsa tamau yana kallonta ya ce" bayan shi, bayan tarbiyarki kina tunanin akoy dalilin da zai saka ni Hisham na damu da shigarki ne Bilkisu? "
Wani irin haushi, takaici, da dana sannin fara jin tausayinsa ne suka turniketa, a hankali ta janye hannunta daga saman kafarsa tana son hanna idannuwanta lumshewa domin bata son yin kuka ko kadan a gabansa duda irin yanda kukan ke cin ranta
Sai da ta yi iya yinta ta cije ta dube shi ta ce" Zan kiyaye in sha Allah "
Tana gama fada ta mike tsaye hakan ya saka shi cire dubansa a kan fuskarta
Juyawa ta yi a hankali da niyar tafia sai kuma ta tsaya ta duka ta ce" Na tafi ne yaya? "
Ji yake kamar ya ce da ita aa kar ki tafi, ki dawo ki zauna na fada maki abubuwan dake faruwa da ni, ki dawo na fada maki irin haukan da na zubawa kartin da suka fito zasu bi layin da kike tsaye kina shanya, ki dawo na fada maki cewar maganar shanya ta kare a waje, ki dawo na fada maki Bilkisu ki daina neman halaka ni na tuba
..........sai dai ina, da yannayi irin na bada umarnin nan ya kara hade fuska ya guada mata kai
A hankali ta juya ta fice a katon falonsa
Direct wuce iyayenta ta yi ta nufi dakinta
Tana shiga kamar yanda ta saba kus ta saka da sauri ta zube nan jikin kofar ta fashe da kuka tana hade kanta da gwuiwarta
Kukan nan mai zafi mai ciwo take bilhaki
A hankali ta kai hannunta jikin hijab dinta tana kallonta ta ce" Bilkisu lafia? Kukan me kike? Wani ya dake ki? Me akai maki? Ko dukan ki yayanki ya yi ne? "
A firgice ta dago dubanta ta dora saman fuskarta, gabanta ne ya tsinke ya fadi a lokacin da bata shirya ba, bata san cewa tana dakin ba, yaya aka yi ta shigo ta shiga kuka bata duba ko da wani a dakin ba? Ko dan ba mai shigo mata daki ya zauna mata sai yanzu?
Da sauri ta mike ta nufi bayi da dan gudu gudu ta ja ta rufe kofar
Wajen madubi ta nufa ta kunna ruwa ta shiga wanke fuskarya da sauri da sauri tana jin wani abin da ya tsaya mata a wuya ya fada
Ajiyar zuciya ta ringa saukewa tana kallon fuskarta a cikin madubin
Me ta tuna sai kuma ta juya da dan sauri ta bude bayin ta fito
Ganninta tsaye a kusan bayin ya sakata sauke ajiyar zuciya
"DUKAN KI YA YI NE?"
Aisha ta kuma tambayarta tana kallonta
Bilkisu ta dube ta a hankali ta ce" Aa, bai dake ni ba "
"To me ya maki kike kuka haka? Wani laifi kikai masa ne?" Aisha ta kuma tambayarta
Bilkisu ta dan kura mata ido, bata bata amsa ba ta zagayeta ta karasa wajen bed tana cire hijab din jikinta
Nan ta ajiye shi ta haye ta kwonta tana lumshe idannuwanta
Jiki a sanyaye AISHA ta karasa saman bed din, muryarta sanyaye ta ce" Sai na ji an ce yayanki ne, kuma sai na ga bacin rai a tare da shi dan ya ga maza na kallon ki, shin yayanki ne ciki daya ko ba ciki daya ba? Shin meye musababin bacin ransa? Ko irin yayun nan ne masu matukar kare mutuncin kannen su? "
Sai kuma ta juyo baki daya wajen Bilkisu ta ce" Ko ba ciki daya kuka fito da shi ba? Shin saurayinki ne? "
Da sauri Bilkisu ta mike zaune tana kallonta, sai da ta gama sauke ajiyar zuciyarta ta ce" Ba ciki daya muka fito da shi ba, yayana ne, kuma ba saurayina bane......"
Kanta ta dafe sannan ta cire ta ce" Dan Allah ki rufa min asiri ki daina yi min tambayoyi a kan rayuwata, ban saba da fayace rayuwata ba ko bada amsa a kan abinda ya shafe ni ba"
" *SON SHI KIKE NE?* " Ta fada tun kafin Bilkisu ta ajiye maganar ta daina yi mata tambayoyi
A harzuke Bilkisu ta juyo da dubanta wajenta ta ce"
Sorry people, jiya ba post gashi yau na fanshi kaina walahi na yi wasu uzurriika neππππ
[7/24, 10:18 AM] BAK'A CE: πΎπΎπΎπΎπΎπΎπΎπΎπΎπΎ
*DUK NISAN JIFA*
_(K'asa zai dawo)_
πΎπΎπΎπΎπΎπΎπΎπΎπΎπΎ
_RUBUTAWA_
*SAJIDA*
*SADAUKARWA*
*GA*
*MASOYA NA*
π«β¨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*π
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_π€
β *[ T.M.N.A]* β πποΈ
https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/
_Bismillahir rahamanir rahim_
13
A harzuk'e, yannayin maganarta zai nuna maka a bakin wuya take ta mik'e zaune da kyau ta nuno Aisha da hannunta baki daya ba da yatsarta ba ta ce" Me kike nufi da maganar ina son sa? Kin san ni ne? Kin san wacece ni ne? Meye had'inki da rayuwata da zaki ringa neman yi mini titsiye da tambayoyi barkatai? Me zai kai ni son sa? A kan me zaki yi tunanin ni ina son sa? Baki san yayana yake ba? Wanda ya raine ni tamkar ubana ya sha wahakar ciyar da ni da shayar sa ni ba? Fad'a ya yi min dan na daina fita gaban gardawa da k'aramar sutura, ke a gidanku babu baban namijin dake maki fad'a dan ya isa da ke ko so kike ki ce min ba'a taba yi maki bane? Shikenan sai a ce so ne? Ki barni na yi nazarin rayuwata haka, ki barni na huta...!" Ta karashe tana mai kara yin kici kicin da fuskarta tana dane damuwarta tana iya yinta dan gannin ta nunawa Aisha cewar itace damuwarta a yanzun.
Aisha ta sauke wata nanauyar ajiyar zuciya, ta sanyayar da muryarta sosai ta