Showing 39001 words to 42000 words out of 180809 words

Chapter 14 - DUK NISAN JIFA COMPLETE HAUSA NOVEL

sajida   

02 Feb 2025

12952

, muryarta kasa kasa sosai ta ce" baki ji yanda DG ke murnar wannan maganar ba, Aisha ta nuna farin cikinta da amanar wannan magana, sai dai tsorona shi ogan, ahin anyama yana da wannan ra'ayin? "

Tati ta lumshe idannuwanta a hankali ta ce" Ina zuwa "

Sai da likitocin du suka fito daga office dinsa sannan ya buga ta shiga

Ido hudu suka yi da kader, wanda yake tsaye yana saka turare a office din dan Hisham din ne ya ce hancinsa na jin wani wari wari

Karasawa ta yi saman kujera ta zauna tana kallon sa hakan ya saka Kader ajiye komai ya fice a office din

Ajiye kofin Lipton din da yake surba ya yi yana kallonta, a sanyaye ya furta" TATI"

Murmushi ta yi tana kallonsa ta ce" kwana biyu na yi ina nakudarka, na sha wahala jina ashe jarumi ne ke hanya "

Dan murmushi ya yi shima yana kallonta

Tati ta ci gaba da fadin" Mahaifinka bai rintsa ba, ko na second daya yana tsaye a kan kafafuwansa yana kai kawo domin kai ne dansa na farko kuma kwansa daya a duniya"

Ajiye dubansa ya yi a kan fuskarta, hankali ya saki lalausan murmushi ya ce" talk m about hm "

Tati ta ajiye wayarta kirar samsung saman table tana kallonsa ta ce" Bai min ba, bai cuta min ba, bai wulakanta ni ba, ya kasance mai min adalci daidai da bukatata, ban nemi nesa ba, ya bani bukatata"

"Ina yan uwansa? Ko bashi da kowa? Wani irin aure kuka yi da shi? Domin mamana ta ki ta fayace min komai a kanki da kansa, ta ce min ku din adalai ne kuma iyayena ne, ko zaki karan haske a kan wanene ni?" Ya fada stil cikin sanyin muryarsa yana kallonta

Tati ta sauke ajiyar zuciya, me zaka ce masa? Ta ina zata fara? Wanene shi? Su waye ahalinsa? Du bata dauki cewar wannan din zai masa wani anfani a rayuwarsa ba, me yake nema? Me yake so bayan ya tara? Bata san ko sun san da shi a duniya ba ko har ya mutun bai fada masu cewar ya auri wata bafilatana har ta haihu da shi ba, abinda ta sani kakarsa bata so wani ya fito daga tsatson wata da ba balaraba ba kar a jaza mata abin kunya, bata sanma tana raye ita dinma ko bata raye ba

Wayarta ta dauka ta shiga amail dinta, tsohon ajiyar vidion da ta yi a TV a lokacin da aka hasko family din mahaifinsa wajen jana'iazarsa sanye da nikaf ta fitar ta ajiye masa a gabansa tana kallon yanda ya tsurawa vidion ido da kuma kalaman dake fita a cikin vidio din duda ba wani sosai daukan ya dauku ba, sai gurshekan kukan macen dake tashi wanda da dukan alamu ba a cikin TV din bane

Dubanta ya yi da duba irin na son karrin bayani hakan ya saka ta sanar masa baki daya rayuwar da ta yi da mijinta, da abinda ya faru na alkawarin da ya yi mata idan ya dawo zai gabatar da su wa familly dinsa, sai dai bai dawo ba sai dawo da shi aka yi a cikin sanduki

Ajiye wayar ya yi ya talabe gefen fuskarsa sai kuma ya saki dan murmushi mai ciwo ya ce" Kina nufin basu san da dansu ya yi aure ba, kika amince rayuwa da shi a nesa da gari daga ke sai shi? Baki ga fuskarsa a lokacin da aka ce ya rasu ba? Sai a TV da kika ga irin haka shikenan? Shin Tati kin tabata cewar mijinki ne a cikin nan? Duba da sai da ya malaka maki gidaje biyu, ya gama yi maki komai harkar kudi da takardar dake iya baki damar cire kudi a banki ya tafi, idan fa ba shine a cikin wannan akwatin mai lulube da zanin shaidar dan kasa ba? "

Tsurawa fuskarsa ido ta yi gabanta na faduwa tana kallonsa ido cikin ido, da dan sauri saurin magana ta ce" me kake nufi HISHAM? "

Hisham ya d'an dage k'afadunsa ya koma da kyau saman kujerar ya zauna yana kallonta ya ce" Kin san dogon karatu, ba abinda baya haifarwa dan kuwa karfi da yaji so suka yi sai sun haukata mana kwakwaluwa ta hanyar dora ayar tambaya a kan mu kan kanmu, sun saka mana shaku a kanmu bale a kan wani, sai kawai na yi tunanin to yanzu idanfa karfin ikon mahaifiyarsa ya yi tasiri a zuciyarsa ne? A matsayinsa na baban mutun kamarsa me ya kaishi jeji wajen yaki bayan basa zuwa zamansu suke a office kasan AC kafarsu daya kan daya?"


"Kana nufin mahaifinka na raye ko me? " ta fad'a a gargitse tana kara kafe shi da idanuwanta.

Zamansa ya gyara ya ce" AA, ban ce ba, juste na yi tambaya ne dan ina son kartin haske ko na ce ina jin curiosity na son bincika labarin nan! Labari ne, rayuwata labari ce, an zayano min ita shine nake son yin tambayoyi a wajen da ban fahimta ba, idanfa bai mutu ba, aman ya yiwa duniya karyar ya mutu ciki kuwa harda familly dinsa da yan uwansa duba da baki daya Familly Muhammad Karibullah sun koma Lybia da zama wata biyu bayan rasuwarsa?"

" *HISHAM!* " TA FADA DA KAKAUSAR MURYA.

Idannuwansa da suka fara rikida ya dora saman fuskarta ya ce" TATI idan ubanama ya guje ni dan gudun bacin ran mahaifiyarsa bayan uwata ta gujeni dan neman na kanta? "

A hankali ta sada kanta tana jin wani iri a kasan zuciyarta, muryarta sanyaye ta ce" Ban guje ka ba "

Kura mata ido ya yi bai ce komai ba

Tati ta d'ora da fadin" Ban guje ka ba, na kaika hannun da na san ba zai cutar da kai ba, zai kula da kai mudin ransa, na barka a hannun da zai tarbiyantar da kai, zai iya sadaukar da komai nasa dominka, Hisham dan na kasance mai son ci gaban rayuwa laifi ne? Ilimi na je nema, ilimi na zurfafa ilimi na nema, yaya kake tunanin uwa zata manta da yaron da ta dauki cikinsa na tsayin wata tara da satika, ta yi kwana biyu tana nakudarsa ya tsaga jikinta ya fito duniya, ta shayar da shi tsayin shekara daya da eata takwas? HISHAM na san ban zauna inda kake ba, ban ci kashinka da fitsarinka ba, ban sha wahalar rainonka ba, ban raba fadanka ko na saurari kukanka ba, aman yanzu gani na dawo, na dawo da dukan k'arfina fa lokacina, Hisham gani na dawo da kokon barata, na zo maka da alkhairina, domin burina a daura aurenka da *AISHA* na zauna tare da ku, na kula da dukan bukatunku, na raini yarenku da hannuna, Hisham koda aikina ka ce na ajiye zan ajiye ne na kula da ku ka fuskance ni."

Kansa ne ya ringa sarawa a hankali ya sakar mata murmushi yana kallonta , muryarsa ya sanyaya ya ce" Da na fi kowa farin cikin ki kasance a tare da mu, Aman tati ba da wata halitar sabanin jinsina sama da *BILKISU* ba, Tati kin san *INA SON TA* kamar yanda nake son aljannah, Tati ina son na rayu da ita kamar yanda nake son na rayu komai kankanin lokaci, idan kika zauna tare da mu, watau Babynki da ni da mamana Tati ina mai tabatar maki farin cikin duniya, umarninki sai inda k'arfina ya kare ba zaki yi hawaye ba."


Gabanta ban da fad'uwa ba abinda yake, irin yanda yake nuna mata k'arfinsa duka ya k'are a soyayar Bilkisu sai shaku da tsoron abinda ta gama shiryawa rayuwar yaronta da ita kanta suka shigeta, anya zata aikata kuwa? Idan ta aikatan zai kasance kuwa? Kauna irin ta d'a da mahaifi na ratsa dukan gaban jikinta.

Hannayensa ta kamo cikin nata tana kallonsa ta ce" Ka kire ni da mama koda sau d'aya ne HISHAM."

Hisham ya lumshe idannuwansa ya bud'e a sanyaye ya ce" Ina son ta kamar yanda nake son yin numfashi Tatina."

Zainab ta lumshe idanuwanta hawayen da suke kusa da zuciyarta suka shiga zuba a saman fuskarta, yaya aka yi ta kasance mace mai son jima yaronta ciwo, a yanzun dole ta yi hawaye idan hasashen yaronta gaskiya ne cewar mijinta na raye, dole ta yi tir da alawadai da irin aurenta, sai dai kuma dole ta sanar masa burinta , buk'atarta , niyyarta a kansa.

Tana kallinta muryarta na son amayar da amon kuka ta ce" *Ai ba aure tsakaninka da Babyna HISHAM, domin mamanta ta shayar da kai*."

Da farko zai iya cewa bai fahimci abinda take fada ba, sai da ya k'ara sauraron amon a kunnayensa sannan ya ringa janye hannunsa daga cikin nata.

A hankali ya kai hannunsa wajen gashin kansa yana shafa kansa sai kuma ya yi murmushi ya dora hannunsa saman table din da take zaune ya ce" shekara daya da wata takwas kika kaini kika yarda ni, bayan na kai shekarun yayan ne zaki fito min da maganar mama ta shayar da ni, ita da bata taba haihuwa ba ta yaya ruwan nono zai zo mata a haka ko kin manta sai bayan na shekara kusan goma sha hudu ta haihu?"

Da sauri ta ce "A lokacin da na kaika wajenta kana cikin wani mugun sabo na son madara, madara kake sha ba dare ba rana da kuma nono, a kauye ina ta ga noni ko madarar da zata baka bayan ko akuya bata kiwatawa bale a yi tunanin zata iya samun nononta? Ka je ka tambaya akoy maganin da ake badawa na hausa mace ta wanke nononta ruwa ya sauko, shi aka kawo mata ta wanke nononta ta saka ka HISHAM."

"DAN GIRMAN ALLAH KI YI SHIRU! Dan Allah ki yi shiru da maganganun nan naki!" Ya fad'a da k'arfi yana kaiwa table d'in dake wajen duka.

Itama mik'ewa ta yi tana tsayawa kan kafafuwanta ta ce" ka tambayeta mana idan karya nake maka! Ka tambayeta mana!"

Cike da mamaki hannunsa na dama na rawa rawa ya ce" Yanzun har zaki ce na tambayeta? Har zaki iya wannan gangancin? Idan akasin haka ya fito a bakinta me kike so da ni? Kin san da kin rasa ni har karshen rayuwa ko?"

Tati ta yi shiru tana kallonsa hakan ya saka shi juyawa da wani irin sauri ya fita.

Yana fita ta zube kasa ta fashe da kuka a fili ta furta" Na shiga uku, shikenan na rasa yarona? "

Tuk'i yake na garari yana gannin mutane na tare masa hanya hakan ya saka shi dane odo biiiiiiiiiiiiiiiii har mutane na raka shi da kallo.

A tsiyace ya danna kan motar cikin gidan a lokacin da mai gadi ya bud'ewa Bilkisu ta shigo da babur d'inta daga makaranta.

Bai kula da ita a wajen ba ya bud'e motar ya barta bude da gudu ya nufi b'angaren mama.

Gabanta ne ya fad'i, da sauri ta diro a babur d'in tana cire hijab dinta tana kallon irin yanda yake taka yar matakalar nufar b'angaren mama.

Da d'an sauri ta nufi bayansa dan ta tsorata ainun kar a je wanda akaiwa aikin ne ya mutu?

A lokacin da ta d'ora hannunta dan bude kofar ta ji magangannun da suka so tarwatsa mata zuciya kamar haka" *MAMA, KI CE DA NI AA, KI CE BA HAKA BANE, MAMA KI CE DA NI ABINDA ZAINAB TA FADA TA FADA NE DAN SON ZUCIYARTA DA KUDIRINTA A KAINA, MAMA SAI DA NA CE DA KE TA YI TAFIYARTA KIKA NUNA MIN AA TA ZAUNA TARE DA MU, BA YANDA BAN YI DA KE CEWAR INA TSORON MUTUN MAI SON KANSA BA KIKA FATATAKI KALAMAINA HAR KIKA ZUBAR DA HAWAYE A KAN HAKA, MAMA KI FADA MIN CEWAR TA FAD'A NE DAN SON RANTA!*"

MAMA dake zaune rik'e da hannayensa gaba d'aya jikinta b'ari yake, innalilahi wa'ina ilaihi raj'une, hasbunnalahu wani'imal waki, me hakan ke nufi? Me ya faru? Me yasa Zainab aikata haka?

"*MAMA*" ya fad'a yana dan girgiza hannayen mama.

Mama ta lumshe idanuwanta hawaye suka shiga zuba, a sanyaye ta ce" Ita zainab d'in , ita ce ta fad'a maka cewar na shayar da kai?"

HISHAM ya ringa gyad'a kansa dan ko maganar a yanzun ya kasa amsar mama yake jira.

Mama ta sauke ajiyar zuciya ta ce" *HAKA NE* "

HISHAM ya k'ura mata ido gabansa na fad'uwa.

A hankali mama ta d'ora da fad'in " *Haka ne Hisham, na shayar da kai*."

" *HABA mamana, haba uwata, kema zaki yarda da wannan tatsuniyar? Wani irin kin shayar da ni bayan ban taba jin haka ba? Kin shayar da nine kike mana wa'azin mu ringa kiyaye kadaice kanmu da ita? Mama aman ai ni Ina son ta, mamana ina son BILKISU."* "Ya k'arashe baki d'aya kamar wanda zai saka ihu ya fashe da kuka, haka kuma zufa na keto masa ta ko ina, gaba da'ya jikinsa nema yake ya saka, numfashinsa nema yake ya yi masa wasa.

Mama ta ringa rik'e kukanta aman ina sai da ta sake shi, ta janye hannunta d'aya ta kai wajen kanta tana kallonsa ta ce" Innalilahi wa'ina ilaihi raj'une, Hisham ba shi yasa koda yaushe nake maku tambaya ba? Ba shi yasa nake tsatsare ku da tambayar shin menene tsakaninku ba? Da ace na fuskanci magana makamanciyar wannan da na tsayar da ku, da na dakatar da hanzarinku Hisham!"
[7/24, 10:18 AM] BAK'A CE: 🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾
*DUK NISAN JIFA*
_(K'asa zai dawo)_
🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾

_RUBUTAWA_

*SAJIDA*

*SADAUKARWA*

*GA*

*MASOYA NA*


πŸ’«βœ¨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🀝

β˜† *[ T.M.N.A]* β˜† πŸ“–πŸ–ŠοΈ

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_


15



Da sauri ya mik'e tsaye, kai kawon da ya ringa yi ya fi a kirga sannan ya dawo ya tsaya gaban Mama yana kallonta ya ce" Ba zan iya hak'ura da Biliisu ba mamana, na rayu ne da k'aunarta, ina matsanancin kishinta, na yi shiru ne dan kar na fallasa wannan abu a k'ananun shekarunta, na yi shiru ne dan ina so sai na kai wajen da zan iya biyan dukan buk'atocinta, sarauniyata ce ta ni kad'ai, jin cewar wani ya furta mata kalmar so na saka min zazab'i, mamana ai maganar shayarwa ta kasu ta rabu, malamai sun yi sab'anin hujoji, wasun sun nuna haramtar hakan wasun sun nuna halastar shi, mamana ko da kin shayar da ni din tunda shayarwar ne ai Bilkisuna tawa ce."

Mama ta kamo hannunsa tana kallonsa ta ce" ka nutsu Hisham, idan akai irin wannan sabanin barinsa ya fi zama alkahiri."

"Mama ba zan iya ba" ua fada wannan karon muryarsa na cracking.

Hannunta ta kai wajen fuskarsa a hankali ta dan mari fuskar tasa ta ce" Kai bana son rashin kunya, yaya ina nuna maka abu kana ce min ba zaka iya ba? Ba zaka iya me ba? A kan mace zaka yiwa mahaifiyarka gardama ko ka ki bin umarninta? A kan mace zaka saka kanka a halaka? To bari ka ji wani abu, idan ka yarda ka dauki bangaren malaman da suka halasta maka Bilkisu ka ce aurenta zaka yi aura maka ita zamu yi, aman ka sani tun a nan gidan duniya sai kun dawo kun tsani junna kai da Bilkisu domin kuwa Allah zai rikita zaman namu ta hanyar sakawa mahaifiyarka take umarninta da ka yi, uwa wasa ce? Umarnin uwa wasa ne? Uwa fa Allah cewa ya yi idan kana cikin sallah mahaifiyarka ta tsananta kiranka ka katse ka amsa mata! Kai kuwa ka san girman darajar matar da Allah ya saka aljanarka a karkashin kafafuwanta? Kai zaka yi gigin daga kanka a kan umarninta? Wasu iyayen zaune suke a anguwar da bata dace ba, sunna aikata masha'arsu aman idan Allah ya albarkace su da y'aya masu albarka haka zasu ringa bin su sunna masu biyaya sunna masu wa'azi, da yawa sun mayar da rayuwar y'ayan nasu tamkar ukuba tsabar muzguna masu da suke aman haka suke yi masu biyaya sunna like da su! Da yawa ana haihuwar tasu kaisu aka yi aka siyar, daga baya suka nemo iyayen nasu suka runguma, kai ita da aure ta same ka, da yawa a haka aka same su kuma idan Allah ya yi masu kimtsi ne sunna nan tare da iyayen nasu! Meye laifinta, dan ta kawo min kai? Na wulakantaka ne? Ko ka yi dana sannin kasancewa a tare da ni ne? Tsayin rayuwar da muka yi da kai ka taba jin an ce da ita karuwa? Ta kama mutuncin kanta, nema da karrin ilimi kuma ba haramun bane, HISHAM ka yiwa mahaifiyarka biyaya ga dukan umarninta idan ba haka ba zaka hadasa min kuka ba dare ba rana HISHAM."

Hannunta ya kuma rikowa yana kallonta, a hankali ya kai hannun nata wajen fuskarsa ya dora ya rage muryarsa sosai da sosai ya ce" Mamana, da ace kin san girman juyani da abinda nake ji a zuciyata games da kanwata da kin tari koma waye kin yi fada da shi kan kar ya kuskura ya shiga wannan lamari, ina zaune a Niger ne dominta dan bana son na gusa wani ya shigar min wajena, mamana dan Allah kar ki min haka."

Mama ta kara rike fuskarsa a tafin hannunta tana kallonsa ta ce" ina iya fada da kowa a kan yarona, sai dai bani da karfin gannin yarona kai kansa ga halaka, a irin wannan lokacin kuma zan iya fada da yarona, domin bijirewa mahaifiya yarona na iya kona kansa, abinda ya yi dominsa bai ji dadinsa ba haka kuma ya je lahira ya tashi a babu!"

Sakin hannunta ya yi a hankali ya ringa ja da baya yana kallonta.

Dago hannun nata ta yi muryarta sanyaye ta ce" HISHAM"

da sauri ya juya ya kama kofar ya bud'e.

Tsaye take sunna kallon junna ido cikin ido, gabanta bai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login