Showing 18001 words to 21000 words out of 180809 words

Chapter 7 - DUK NISAN JIFA COMPLETE HAUSA NOVEL

sajida   

02 Feb 2025

12962

takan yiwa yar uwarta adu'ar shiriya, sai kuma ta bige da zanen adu'o'in yaronta sannan ta yiwa yarinyarta
Wannan gudunmuwa da ta ringa tura masa ta adu'o'i su suka kara taimaka masa ya yi fice

Tun kafin ya gama karatunsa ya ringa sauya rayuwar Mama da ta kanwarsa

Du idan ya ga sutura ta masu daidai shekarunta zai saka kudi ya siya ya tura ta jirgi, takalma ne, Riguna ne, harta da pant siya yake abinsa ya tura

A kadan sai da ya dauki shekara takwas yana karatu , sannan ya kara shekara uku yana karantar fannin mata dan wani kudiri dake cikin zuciyarsa
A cikin shekarun nan sau goma sha daya cif ya koma gida shima karshen shekara yake samu ya je ya yiwa mamansa sati daya cif sunna tare da kanwarsa da mamansa sunna gannin gari sunna raba lokacinsu tare cike da kaunar junna

Tun a shekararsa ta bakwai ya biyawa mama makkah tare da Bilkissu suka hade suka tafi tare, a dawowa suka biya ta wajen da yake karatunsa nan suka ga tamkar wani dan sarki irin yanda yake cikin alfarma, karatunsa ya janyo masa alkhairi

Tun daga lokacin mama ke hankalce da su, hakan ya sa take taka tsantsan a tsakaninsu dan kuwa su din sun san cewa su ba muharaman junna bane, babar shakuwar dake tsakaninsu, irin yanda HISHAM ke kafa kafa da lamuran Bilkissu , yanda ya mayar da ita tamkar princsss sai abinda take so, yakan kashe kudi masu yawa ya kawata mata jin dadinta, duda daga bakin lokacin da ta kai shekaru goma sha hudu sai ya zame mata wani tsadade , hirar na hada su aman ba irin ta da ba, domin bata hayewa kansa ta yi ta murginarsa, bata gagawar taba jikinsa du ya yi mata iyaka da hakan

Bai tashi dawowa garin Damagaram kwata kwata ba sai da aka sha rigima da shi, domin kuwa karara gwamnati ta nuna ya zauna a baban Birnin Niger ya yi aiki, sai dai ya nuna masu aikinsa zai yi shi a Damagaram, zai koma ne ya kula da jama'ar Damagaram, aman du inda yake idan ana da bukatar aikinsa za'a iya tarda shi

Gagarumin biki aka yi masa na dawowa wanda mama ba yanda bata yi ba dan ta samu gannin Zeinab ta fada mata irin alkhairin da yaronta ya zama sai abin ya gagara, wayarta dake shiga da sai ta daina shiga, hakan ya sa ta ajiye cewar Zeinab dai ba mahaukaciya bace ko ba dade ko ba jima zata waiwayi gida ko dan yaronta, sannan ta san a irin shaharar yaronta tabas labari zai kai mata, idan kuwa ya kai mata zata fito ta neme shi ne! Hakan ya sa ta cire komai a ranta ta ci gaba da rayuwarta

Ba shi ya baro garin niamey ba sai da tsarabobi

Yana zamewa a damagaram a baban offishin sojojin garin, a nan aka sha rigimar yan tsaro domin shugaban kasa ya bada umarnin a hada shi da mutun hudu

Sai da kyar ya shawo kansu kan kwaya daya ya ishe shi, kuma shima shi ya zabi abinsa watau dan uwansa abokinsa *COLONEL KADER*

Sati biyu suka kara a gidan mama na asali, wanda ke daukan baki ta ko'ina ana ta kawo gaisuwa da barka

Satitikan na cikawa ya kwashe su ya nufi sabon gidan da ya kyakyara masu bayan mama ta bar sanarwar cewa a ko wani lokaci ana iya yin bakuwa kanwarta ce mai sunna Zeinab sai a kaita sabon gidan


Daga wannan rana suka ci gaba da shinfida rayuwa mai tsafta a cikin gidan nan

Wani irin lamari ke faruwa a tsakanin bayin Allahn nan biyu

Irin yanda HISHAM yake kafa kafa da du abinda ya shafi kanwarsa, daidai da zuwa anguwa shi ke tuka ta, makaranta haka, mota ce da ita mama ta hanna ta tuka, suturunta mama na kyautarwa kowani lokaci domin bashi da lokacin siyan mata kaya, daidai da bra da pant yakan siya duda pant din da yake siyo mata sun jima da yi mata kadan aman bata taba fada masa ba sai dai ta ringa kwashewa tana baiwa kawarta Laila
Kudin makarantarta, kudin gyaran gashinta, sabulanta, turarukanta kai komai na gidan duniya kafin mama ta ce zata kai dubanta ya siya ya ajiye har tanadawa yake a dakinsa
Kalar turaranta na ruwa da na hamata princss ne mai gida pink, computernta aple pink, wayarta Iphine X Max du ta saka mata abin barbie jiki, du kashe kudinta ba shine damuwarsa ba domin a duniya damuwarsa yau a wayi gari wani saurayi ya yi tunanin zai iya yiwa kanwarsa wani abu bayan yana raye!

Bangaren Bilkissu kuwa, ta kasance a kan lamarin da ya shafi yayanta jiki na bari take komai, bata wasa, bata son a yi mata wasa da maganar da ta shafi yayanta, kama daga wankin bayi, gyaran daki, kilace kayansa takalmansa, takardunsa , amsa kiransa, komai tana yi ne kamar irin aikin da zaka yi a biyaka
Bata saka munafurci a abinda ya shafe shi, dalilinsa ta kasance mai kutse kutsen koyon girki dan kuwa burinta ya ci sabo mai dadi ya yaba duda ba yabawar yake ba aman idan ya cinye ta tabatar dan ya yi masa dadi ne
A kulun so take ta yi sabon girkin da zai birge shi a bakinsa, takan jirga dakinsa ta gyara ta yadda a kulun zai kara jin sha'awar kwonciya a cikinsa, tana kiyaye harkar samari du rashin jinta, dan kuwa Bilkissu bata jin magana ko kadan saima idan ta fito daga gida, aman fa ba ruwanta da harkar maza tana kiyayewa

Mama kuwa na taka tsantsan a kan kusancinsu a gida ko a waje, tana jan hankalinsu tana yi masu nasiha sannan tana adu'ar Allah ya kori shedan a tsakaninsu

Har zuwa wannan rana rayuwar ke tafe cikin salama


*Labari*

A yau ranar litinin ta kama ranar da ya tashi da tiyata har kwaya biyu, hakan ya sa tun da duhu duhu ya shigar da dayan marar lafian Namiji ne mahaifin Hajia Aisata

A kadan sun kwashe awa hudu a ciki dan tiyatar ba mai zafi bace aka fitar da shi cike da farin cikin hangen nasara a aikin

Sai babarbarar matar da zai saka zuwa karfe goman safe

Ba wani abinci mai nauyi ya jimga ba dan salak ne akai masa sasauka sai lipton da dan jus na Xmen dan ya kara samun karfin jikinsa da nutsuwar aiwatar da aikinsa

Yana gama sha ya zauna ya ci gaba da bincikar takardunta daya bayan daya yana kinkimtsa komai

Karfe tara doctors din da zasu yi aikin tare suka bayana a office dinsa

Nan ya kara bude masu takardun ya yi masu bayanin komai dala dala ta yanda zasu fahimta da kuma irin aikin dake jiransu wanda a kadan ya tabata zasu kwashe awanni shida domin wani karri ne za'a cire mata a kanta daga gaban goshinta

Secretariarsa ce ta shigo a karro na uku ta shaida masa ya yi baki, matar ta ce a ce masa *ZEINAB CE MAHAIFIYARSA*

Da mamaki ya kalli matar ya maimaita 'ZEINAB mahaifiyata?' A kasan zuciyarsa sai kuma ya basar ,
da hannunsa ya nuna mata yana zuwa

Bai kuma bi ta kanta ba sai Kader da ya yi kira cike da miskilanci ya ce" Karfe goma sha daya da rabi Bilkissu ke sauka , sha daya ta maka a cen Kader"

Kader ya amsa shi sannan suka kashe wayoyinsu baki daya goma na cika suka shige dakin tiyatar da Nurse suka gama shiryata da komai sai fatan nasara


Du ta daburce a wajen a tsaye cikin rantsatsen lesh dinta, ga wace bata da lafiar tana cikin watsetsiyar motar DG dinsu tare da matarsa da yarsu daya mai sunna *AISHATU*

Gannin abin na neman jan daga sai kawai ta ce da su tana zuwa

Tsohon gidan ta je, nan aka samu yaro ya kaita gidan HISHAM

Tun daga kofa take sakin baki da hanci, harda masu tsaro da mai gadi , irin tsarin gidan ya sakata a fili ta furta" Yaushe ka zama mai kudi haka? nake cen duniya ina faduwa a kasa ina shan wahala HISHAM? , *YAYA AKA YI AUNTY BATA FADA MIN BA?*

Tsaye take tana faman son masu tsaron kofar su barta ta shiga sai dai sun tatare hanya da komai sun ki bata wannan dama

Motar dake dauke da BILKISSU ce ta danno kai, watsetsiyar yellow din Hamer sai nishi take ta ja ta tsaya a kusa da Zeinab

Zeinab na gannin hakan ta kara bin motar da kallo

Kader da mamaki ya bude motar yana kallon matar dake kama da Mama sai dai ta fi mama yarinta da sa kaya kananu domin lesh din dinkin sket ne jikinta tamkar bata kai shekara arba'in da takwas ba

"Sannu fa?" Ya fada yana kallonta da yannayin mamaki

Itama su take kallo, da budurwar dake lekowa tana kallonta
Kyan Bilkissu, da yannayin fuskarsu da ta dauko ya saka Zeinab zagayawa tana son bude motar

Da sauri Kader ya fito ya zagaya ya dakatar da ita yana fadin" Malama lafia dai? "

Zeinab ta yi murmushi ta kara nuno Bilkissu da yar yatsarta ta ce" Babyna? Baki gane Tati ta waya ba? Ni ce fa tati ZEINAB ko ba Bilkissu bace?"

Ido Bilkissu ta zarro cike da mamaki sai kuma ta tuntsere da daria tana cire hijab din kanta ta bude motar ta ce" Lah, yaya kader maman Hama ne fa, wallahi Tati Zeinab ce a gidanmu yau bara na kirawo mama...."

Da gudu gudu ta shige tana ihun kiran mama da murna da farin cikin yau ga tatinta, yau ga mahaifiyar Yayanta, yau ga kanwar mamanta da kulun take cewa har yanzu shiru Zeinab bata neme mu ba? Ko tana raye? Ko lafia? """"""""








😁
[7/24, 10:18 AM] BAK'A CE: 🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾
*DUK NISAN JIFA*
_(K'asa zai dawo)_
🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾

_RUBUTAWA_

*SAJIDA*

*SADAUKARWA*

*GA*

*MASOYA NA*


πŸ’«βœ¨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🀝

β˜† *[ T.M.N.A]* β˜† πŸ“–πŸ–ŠοΈ

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_


8



Bata san wani irin farin ciki ta samu kanta a ciki ba a lokacin da ta fito daga dakinta rai bace dan dauke fuskar Bilkiss da mari sakamakon ihun da ta hannata yi haka kawai kasancewarta mace , sai dai abinda take fada ne ya sakata ja ta tsaya, sannan ta wara idannuwanta tana mai jin wani irin farin ciki da zumudi da son gannin ta inda zata billo

KADER ne a gaba , tana biye da shi a baya har suka shigo

Baki daya hankalinta ya fi tafia kan kallon tanfatsetsen fallon dake dauke da kalar ruwan zeba da fari gini tamkar na gidan saraki, gini kamar na wani kusa a gwamnati ga uban sanyi da kanshin turaran wutar da ya mamaye dakin kamar wata duniya daban ba cikin niger ba


*ZEINAB* Mama ta ambaci sunnanta a sanyaye cike da kaunar yar kanwarta kwalin kwal wace suka fito ciki daya

Da sauri ta juya wajen da take jin sunnan nata

Wannan karron kam mamaki ya gama dameta ya shanye tassss

Shekara da shekaru basu saka junna a ido ba, zata iya rantsewa a lokacin da ta barta ta fi yanzu tsufa, domin a yanzun Mama ta zama wata kamilaliyar yar gayu wace ta san kanta, bata da wani mugun jiki, jikinta madaidaici ne gata da tsafta ga hutu, kai idan aka barta zata iya cewa a yanzun Asma'u ta fita zama gangariyar mace mai aji da tsari

Sai da ta hadiyi wani abu a makogwaronta sannan ta lumshe idannuwanta dan ta samu damar controling din du wani abin dake taso mata

A sanyaye ta karasa ta mika hannunta kamar yanda ta saba ta kamo na Mama tana kallonta idannuwanta cike da hawaye aman ta kasa magana

Da sauri mama ta janyota jikinta ta rungumeta sosai sai kuma ta fashe da kuka mai dan sauti tana kara riketa a jikinta

Da a da ne, ba zata taba yarda ta shiga jikin Asma'u ba ko dan rashin kanshin turaren jiki da kuma wadatacen wankan da zai cire dati da kayan da suka sha rana, sai dai a yanzun wani irin kanshi ta ringa shaka a jikin yar uwar tata wanda idan dai ba mantawa ta yi ba, ko rudewa ta yi ba kamshin turaran ruwan sandal roz ne mai tsadar nan

"INA kika shiga? Ina kika je kika manta da ni? Kika manta da amanarki? Shin kin san girman hakkinmu dake kanki kuwa? Kin san girman darajar zumunci kuwa? Kina raye dama? Kina Niger ko zuwa kika yi? Aure kika yi kika manta da mu?

Sai kuma mama ta kara dago da habar Zainab ya kasance wannan maganar da zata yi daga cen kasan zuciyarta zata fitar da ita ta raunana muryarta sosai ta ce "Koda kin san zan rike shi tamkar dan da na haifa kin manta uwa uwa ce? Kin manta ke Allah ya sakawa kwan haihuwarsa ke zai tambaya amanar da ya baki? Zeinab shekara nawa rabona da ke tun HISHAM na tatata ga shi har kaina ya fara cika da furfura? Ina kika yarda layin naki har nake kira bana samu? "

Zainab ta ce" Aunty"

Mama ta katseta da sauri tana fadin " A ranar kin ce na barki ki ji da kanki zaki tabo ni kin san cewar karya na yi masa dan na kare ki kar ya gane abinda kika fada min? Sai dai kash ina fada ya tsatsare ni da kallon da bana iya tanka masa sai sada kai na ringa yi a gaban yarona? ? Haba Zeinaba , haba kanwata" .......Mama ta karashe tana mai fashewa da kukan da bashida sauti

Itama muryarta na rawa ta raba rukunkumar da mama ta yi ma hannayenta a hankali ta kai kasa saman lalausan cafet din fallon ta zauna tana mai cire mayafin jikinta da dan kwalin baki daya, sai a lokacin ta kula babu Kader da Bilkissu watau sun basu waje su gana da junna

Muryarta a sanyaye ta ce" Haba Asma'u ashe har yanzun baki daina saurin kuka ba? Ke da zaki yi ta farin cikin na dawo sai kuma ki yi ta kuka? Dan Allah ki daina haka ya isa kar kanki ya zo yana ciwo, Asma'u yanzun gani na dawo gare ku, kuma ba inda zan koma"

Mama ta zauna kusa da ita tana daria hakan ya baiwa hakoran makkar dake bakinta kwaya biyu damar bayana a kan idannuwan Zeinab wanda ke shaida mata cewar Mamar har makkah ta je, Mama ta ce" Ba zaki gane bane, ban san yaya aka yi kika kasance mai karfin zuciya da kokarin rayuwa cikin duban jama'ar dake baki a gare ki, ni na sha wahala, Zeinab iyayenmu sun fadi sun rasu haka mijina da naki, bayan iyayen marigayi da ke wa na sani? Dole na ji wuyar rayuwa ni kadai kin sanni da sarkafa"

Zeinab ta yi murmushi tana kamo hannunta cikin nata biyu ta ce" Yanzun ba ganni a kusa da ke ba, yanzun ba ganni na zo inda kike ba? Ba zan kuma barinki ba, ki fada min yaya bayan gamo? Me ya faru da ku? Yaya kuka yi kuke cikin wannan gidan? Gidan waye"

Mama ta yi murmushi ta kara rike hannunta da kyau ta ce" Zeinab abubuwa na alkhairi su muka yi ta haduwa da su, HISHAM da kike ganni shine mamalakin wannan daula, ke bama wannan ba maganar da nake maki HISHAM a yanzun ya zama wani kwaron da nake bi da adu'a dan Allah ya shiga tsakaninsa da magauta, Zeinaba a ranar da na yi kiranki dan na sanar maki dadadan labarin dacen da aka yi na samun fitarsa karatu, Zeinab bayansa na yi ta kiranki a ranar da ya fara yi min aike......na takaice maki sai dai na cire na anfanina na ajiye maki naki dan na kiyaye masa fita hakkin uwa, ina kika shiga kika bar yaronki har haka? Ina kika shiga ke? Me kike yi yanzun a rayuwarki? "

Murmushi mai ciwon gaske Zeinab ta yi, sai take gannin rayuwa batai mata adalci ba, tana cen tana wahala? Wahala mana karatun nan ita kadai ta san irin wahalar da ta sha a kansa, ta gama ta samu aikin a matsayinta na mai aikin sai gashi ta zo ta tardo wace ta bari cikin tsuma ta dameta ta shanye a gata? Yaron da ta dire a bayanta yana ihun kuka yana rarumar hannu yana neman nono shine yanzun ta je ganninsa ya gagara? Ashe su a nan din da take yiwa kallon kauye ta tafiyarta baban birni dan ta zama wata sai gashi su dake kauyen sun fita da komai ciki harda wayewa?
A hankali ta ce da Mama" karatu na yi mai Zurfi Asma'u, na sha wahalar rayuwa dan neman na kaina, wani tudu wani gangare a shekarun nan nakan iya wuni ban ci ba, da kyar na samu takardar da nake nema sannan na shiga fafutukar neman aiki, kin san garinmu, kin san me yake cikinsa, da kyar Allah ya tsaya min na samu, layina da wayar bacewa suka yi Asma'u a lokacin bani da halin tasowa na zo gareku dan amsar numberku kuma bani da wanda zan turo hakan ya sa na ci gaba da karatuna da ku a zuciyata, bayan na gama kuma na samu aikin nan sam oganmu baya bari mu matsa, adu'ata Allah ya nunan ranar da zan samu damar zuwa inda kuke, to a wajen aikin namu baban namu ne mahaifiyarsa ba lafia, idan kin ga irin wahalar da take sha gaskiya sai kin tausaya mata, tana fama ne da matsala a kanta, mayar zata summe na lokaci kafin ta farfado, jikinta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login