Showing 1 words to 3000 words out of 180809 words
ο»Ώ[7/24, 10:17 AM] BAK'A CE: πΎπΎπΎπΎπΎπΎπΎπΎπΎπΎ
*DUK NISAN JIFA*
_(K'asa zai dawo)_
πΎπΎπΎπΎπΎπΎπΎπΎπΎπΎ
_RUBATAWA_
*SAJIDA*
*SADAUKARWA*
*GA*
*MASOYA NA*
π«β¨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*π
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_π€
β *[ T.M.N.A]* β πποΈ
https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/
_Bismillahir rahamanir rahim_
1
ALHAMDULILAH
A hankali yake takawa cikin dogon coridor din dake sada shi da dakin tiyata
Jikinsa a mace yake dukan alamun gajiya da mutuwar jiki sun bayana a tatare da shi
Da sauri Nurse din dake bayansa rike da litafi ta kara saurinta ta bude masa office dinsa
Yana shiga wani sansanyan kanshi hadi da dadadan kamshin turaransa na ruwa mai sunna SAKEENAH ya bugo yana huda dukan gaban jiki da na hanci
Kayan ta ajiye masa sannan ta ja ta tsaya tana kallon abokinsa dake soja zaune ya dora kafa daya kan daya yana binsa da kallo
Necktie din wuyansa ya sasautawa daurin sosai sannan ya cire Lab coat dinsa
Da sauri ta amsa ta kai wajen da ake rataya ta rataya haka kuma ta dawo ta amshi Hand gloves din da yanzun ya saka su da zai fito ta kai wajen abin zuba shara ta zuba sai kuma ta dawo ta ja ta tsaya
Ya yi kai kawo sau biyu yana dafe da gaban goshinsa sannan ya dan duka ya yi rubutu a takardar ordonance ya mika mata ya yi mata nuni da ta je
Da sauri ta fita har kamar zata kifa dan kai sakonsa, domin kuwa ba wanda ke gangancin yin sake da wasa da aiki idan har aiki ya hadoka da shi
Zama ya yi saman kujerar ya dauki ruwa ya kafa kansa ya sha mai sanyi sannan ya buda idannuwansa masu launin ja ya sauke a fuskar abokinsa
Murmushi abokin nasa ya yi masa a hankali ya ce" SANNU "
shima murmushin ya mayar masa da shi ya dauki wayar dake saman table din ya danna kira
A ringin na biyu aka daga da salama
Sai da ya amsa salamar a cen kasan makoshinsa kafin ya buda zazakar muryarsa mai fita a sanyaye ya furta" Tsohon dake daki na goma sha daya ku je ku cire masa abin taimaka masa numfashin nan, y'arsa ta hakura a barshi ya huta Allah ya sa mutuwa hutu ce a gare shi"
Dan sauke ajiyar numfashi ya yi ya dora da fadin" wace muka fito aikinta yanzun kar ku saki ku bata abinda ya shafi siga, tana da ciwon siga, dan haka ki kula da kanki, kar ki yi saken da zan kama ki da laifi "
Daga haka ya kashe yana kara jin kaunar patients dinsa da tausayinsu a kasan zuciyarsa
Ajiyar zuciya ya kuma saukewa ya dan shiga shafa lalausan bakin gashin dake kansa, yana jin cikinsa na yi masa kugi kasa kasa
Yar daria abokin nasa ya saki yana kallonsa ya ce" Awa daidaidai ina jiranka a nan har awa hudu, kafin na shigo kuma an ce min awarka uku a ciki, ka shiga ka kwaso wannan uwar gajiyar ka zo ka saukewa kujera, abokina idan aljihun nan naka dake cike ne baka son tabawa ka bari na zuba na dauko maka zafafa hudu, wai ko dai baka da lafia ne? "
Murmushi yake yana kallonsa a hankali ya dan cije lebensa na kasa
Mikewa ya yi ya dauko bak'ar rigarsa ta sama irin ta sanyin nan ta fata mai tsarin kyan gaske ya dora sannan ya dauki abinsa na wuya mai kalar maroon ya laulaya a wuyansa
Takalminsa na aiki fari ya cire sannan ya zira maroon kafa ciki na fata a kafarsa
Hannunsa ya mika ya dauki jakar laptop dinsa sannan ya kai dubansa wajen Abokinsa da tuni ya mike tsaye shima yana harhada wayoyinsa dan ya san tafia zasu yi
Murmushi ya sakar masa a hankali ya ce" Bana tunanin matatun yan matanku zasu iya da lafiata,.........
Sai da ya ajiye maganar da yannayi na iya gaskiyarsa ya fada sannan ya rike abin bude kofar ya kara lumshe idannuwansa ya ce" Wace ta gama da rayuwata ta hada komai da hudun nan da zaka samo min na tabata basu hada ba, horona ce, tarbiyata ce, ita kadai zata iya da lafiata " irin yanda ya karashe maganar cike da miskilanci ya saka abokinsa mai sunna KADER yin daria yana girgiza kansa kawai sannan ya bi bayansa yana rike da laptop din har suka shige motarsa ya rufe masa ya zagaya ya ja shi
A takaice dai KAder Aboki ne, Amini ne, kuma bodyguard ne a wajen *PROFESSOR DOCTER HISHAM MUHAMMAD QARIBULLAH*
Mai gadi na wangale kofa ta yi wani irin dirkowa daga saman babur dinta kirar Honda ja wanda ta bi ta kwaliye shi da hotunan princess barbie ta ko'ina sai kyali yake uwa wata dangin fulani (ππ₯΄π€£)
Gilashin dake fuskarta mai kirar heart baki ta yi saurin cirewa daga fuskarta ta yi tsaye kikam tana jin zuciyarta na bugawa
Da yan yatsunta ta shiga kirga dukan abubuwan da ta san tana yi masa kafin dawowarsa irin su 'wankin bayi, gyaran kayansa, girka abincinsa, cenza zanin gadonsa da sauransu '
Kanshin turaransa ne ya fara yi mata salama a hankali ta sada kanta hakan ya baiwa lalausan gashinta dake gaban goshinta damar yin kasa ya kuma kara bayanar da bakinsa ya fitar da tsarin xagayayoyar fuskarta ta yi das da ita
Tsayawa ya yi a gabanta, tun daga kafarta mai dauke da jan dogon takalmi mai madauri faratunnan sanye da pentin farce ya bi da kallo , zuwa damamen wandon dake jikinta mai igiya wanda ya gama bayana asirin jikinsa sai rigar da ta saka mai dan tsayi sannan budadiya sai dai daga sama a dan bude take dan har ana gannin kalar ta cikin fara tas, sannan ya dire a kan fuskarta mai dauke da sasaukan mak'up da gashin kanta dake waje sai kys din babur dinta dake hannunta
Idannuwansa ya lumshe a hankali ya dora hannunsa a wajen habarta, hakan ya sa ta dago da dubanta da sauri tana kallon kyakyawar fuskarsa
Ta fi raja'a dubanta a kan lebunansa, a duniyarta ta zana zanen lebensa da hannunta ya fi a kirga a cikin litatafan makarantarta
Kalar leben wata kala ce mai dauke da pink da kuma orange color, leben na kasa ya fi fadi na sama kuwa bashi da wani girma sosai, leben shi kadai ke nuna irin laushinsa a ido, a yanzu haka burinta ta dora yan yatsunta ta shafa laushinsu a yatsarta, so take ta shafa laushinsu da hannunta ta ji yaya suke ne a zahirance??
"Ki je dakin ki, ki tube, ki yi wanka, ki saka abaya sannan ki yi karatu "
Kamar wata gaula ta juya jiki na bari dan ta aiwata umarnin da ya bata
A hankali ya raka bayanta da kallo kasa kasa kafin ya sauke wawuyar ajiyar zuciya ya juya da sauri dan sai a lokacin ya tina bafa shi kadai bane
Murmushi ya saki dan gannin Kader ya sada kansa yana dadana waya, wato dai ya ji gargadin da ya masa kan ya daina kallon matan nan biyu dake gidansu, matan nan biyu da ya kasa tantance irin matsayinsu a rayuwarsa
Ita dai babar ya sani cewar mahaifiya ce kuma mahaifi a gareshi duda ba ita ta kawo shi duniya ba, ba zai iya lamuncewa kowa yi mata kallon kurullah ba dan kuwa darajarta da girmanta da kimarta ta kai wajen da ba kowani shashasha bane zai samu damar jin muryarta bale har ya hada ido da ita wato mamansa,
Sai wannan yar ficiciyar yarinyar dake fama da wutar balaga, wannan yarinya da ya goya ya wankewa pampos, wannan yarinya da ya yiwa wanka ya kuma rakata makaranta da ya kasa gane wace irin girman daraja ne ta samu a rayuwarsa, lalle *kanwarsa* abin kilacewarsa ce
Juyawa ya yi ya shige falonsa da dan sauri sauri
Sai a lokacin Kader ya dago kansa yana murmushi yana dan girgiza kansa
Tana shiga da sauri ta shige bayi
Sai da ta cire kayan nata ta yi wanka ta fito ta cenza doguwar rigar bak'a sai kuma ta yi turus cike da mamakin kanta
A hankali ta jinginar da bayanta jikin garun dakin ta lumshe idannuwanta tana murmushi, ta daina mamakin irin yanda zuciyarta ke yi masa biyaya a dukan umarninsa koda kuwa ranta baya so, ta daina mamakin irin yanda jikinta ke bari a kan lamarin da ya shafe shi
A yanzu ta fi ajiye lamarinsa a wani mataki na rayuwarta, ta san cewa shi din baban mutun ne wanda yake da daraja a wajen manyan mutane, suke girmama shi suke bashi girma koda kuwa sun girme shi
Shi din shine cin su, shan su, suturarsu, yana tsaye kan kafafuwansa a kan karatunta, baya barin ko wace irin kofa ce da zata iya gurbata tarbiyarta
Juyawa ta yi ta dauki litafinta na adini ta fada saman gadonta mai daukan mutun daya wanda shima yake dauke da kwaliya kayataciya du hoton barbie ne zagaye a ko'ina
Budawa ta yi a bayane ta shiga karanta Jouz-ou Ammah domin shi ta zago a cikin alkur'anninta mai dauke da izuf bibiyu har zuwa izuf sittin
Message din dake ta shigowa ya sakata mika hannu ta kashe wayar kwata kwata tana tunanin irin masifar da zasu yi da kawayenta na rashin halatar wannan taro na birthday din haduwarsu, sun shirya taron ne zasu yi shi a school bayan sun kwana da sannin headmaster dinsu zai iya korar su a kan wannan gagarumin taron, sai dai kamar yanda ya saba korar su ko ya rufe ajinsu har sai sun gabatar da iyayensu kafin ya bude masu aji sun darmi aniyar saka shi dogon bacin da sai an sada shi da asibiti ko zai farko dan su rakashe abinsu, sai gashi ita dake daya daga cikin manyan mararsa jin maganar ajin ta fasa tafia tun ba'a je ko'ina ba dan kawai yayanta ya bata umarni.............m
Cike da nutsuwa ya gama dukan abubuwan da ya zame masa jiki
Sanye da jalabiya har kasa ya karasa saman table dinsa
Cikin nutsuwa ya shiga buda kulolin abincin yana mai lumshe idannuwansa
Zumudi yake ji, sauri hannayensa suke, hadiyar yawu yake dan ya taba girkinta, girkinta na daya daga cikin abinda yake baiwa time dinsa, yakan taba test din kalolin abincicikanta da take bashi mamaki da su a kulun, ya san mahaifiyarta ba baya ba wajen koyar da girki sai dai ya tabata irin na zamanin nan garin kutse kurtsenta take koyo abinta, sai dai abin birgewar na kulun kara dadi yake, haka kuma kara shiga ransa yake
Cikin nutsuwa ya cinye tas kafin ya goge bakinsa da tishu yana hamdallah a kasan zuciyarsa
Sansanyan kunnun ayyar da ta ajiye ya juye a kofin tangaran ya lumshe idannuwansa ya kora yana tunanin wannan abin shi ke rikita yannayinsa, ama ba zai iya kin sha ba
Nan da nan wata nutsuwa ta ringa sauko masa harma ya ji kawatacen lalausan kafet din da ta gama sharewa ta goge na masa gwalo
A nitse ya karasa yana jin jikinsa na kara dadaure masa domin akoy gajiya a tatare da shi duda bai ji shigowar mamansu ba ya tabata da ba bacin zai iya yi ba har sai ta dawo ama haka ya mike ya kara gudun AC ya shiga lumshe idannuwansa yana tunanin rayuwa da abubuwan dake cikinta
Abinka da gajiya, wani irin nanauyan baci ne ya fuzge shi ko sallar isha'i bai yi ba
Kukan da wayarsa ke yi sama sama ta saka shi zabura a firgice har yana kaiwa kujera duka da kafarsa
Ganninsa ya yi lulube da abin rufa sannan an rage gudun AC din, hakan ya tabatar masa mamansu ta dawo
A gajiye ya daga wayar yana kallon Agogo,
Lokacin da ya gani da irin abinda aka fada a rikice ya saka shi ajiye wayar da wani irin sauri ya dauro alwallah
Sallar ya gabatar dan ya san tana gaba da komai, kafin ya saka dogon wandonsa ya shiga wartar kayan aikinsa ya fito da gudu gudu
Goren da suka yi da kawunnansu hannunta dauke da tea, da ihun da ta kwala ya saka shi janyota da karfi jikinsa ya matseta idannuwansa rintse yana jin yanda kansa ke sarawa
A cen kasan Makoshinsa ya furta " *BILKISSU* "
cike da sangarta ta kara yarfe yan yatsunta da suka shiga cikin tea din ta ce" Wayo Allahna hannuna yaya "
Da sauri ya cireta a jikinsa domin sai a lokacin ya gane dare dare a jikinsa take a kwonce abinta
Hannun nata ya kamo yana kallo, tabas yatsotsun sun yi jajir sun duro ruwa, sai dai aikin dake gabansa a yanzu baiwar Allahn da ya gama yiwa aiki ne ta farfado tun yanzu bayan ba lokacin da ya dace ta farfado kennan ba, hakan na nufin tana cikin daya biyu, ko aikin ne ya yi kyau sosai har haka ko kuwa tana gab da barin duniyar nan ne
Gefe ya mayar da ita ya fara takawa da sauri sauri
Sai dai kash wani irin lamari ne ya dake gaban kirjinsa hakan ya sa ya ja ya tsaya ya kasa gaba ya kasa baya
Muryarsa cen ciki ya kuma furta " *BILKISSU, ZO MU JE* "
sai da ta yi dan juyin murna ta juyo da gudu gudunta ta rigaye shi karasawa wajen motar, ta san tafia da shi akoy riba, yau zata more iya morewa abinta dan kuwa kama daga dangin chocolate da su ice cream sai ta kwasa iya cinta
Da kallo ya bi rigar jikinta dake kadawa kamar wata tarwada, irin yanda jikinta ke yi idan tana gudu abin har mamaki yake bashi
Da sauri ya cire idannuwansa yana sauke ajiyar zuciya a karro na ba adadi kafin ya karasa ya bude motar ya shiga
Yana zama wajen direba motar ta kwashi kuka hakan ya sa sukai tsam daga shi har ita
Da gudu Kader ya fito yana kallonsa dan ya tabata shi ne,
Kallon junna suka yi Kader ya karaso yana kara tamke fuskarshi dan kuwa Allah ya taimake shi ya samu hanyar da zai ringa kama shi ya daina guduwa yana barinsa a gida idan ya samu kiran gagawa daga wajen aiki
Shima fuskar ya tamke tamkar bai taba yin daria ba yana kallonsa ya ce" Kashe min kukan nan kar ka tayar min da uwata a baci"
Da sauri Kader ya kashe , yana shirin ce masa ya koma baya duda ya san abu ne mai matukar wahala ya bari a tuka kanwarsa aman sai ya so ya kwatanta
Tun kafin ya idasa maganar ya ga ya kunna motar ya tayar dan haka sai ya matsa yana kallonsa har ya fice a gidan
Murmushi ya yi a karro na biyu a kasan zuciyarsa yana ayana .......... 'kashi baya zama a ciki'..............
Asalamu alaikumπ
[7/24, 10:18 AM] BAK'A CE: πΎπΎπΎπΎπΎπΎπΎπΎπΎπΎ
*DUK NISAN JIFA*
_(K'asa zai dawo)_
πΎπΎπΎπΎπΎπΎπΎπΎπΎπΎ
_RUBATAWA_
*SAJIDA*
*SADAUKARWA*
*GA*
*MASOYA NA*
π«β¨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*π
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_π€
β *[ T.M.N.A]* β πποΈ
https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/
_Bismillahir rahamanir rahim_
2
Cikin nutsuwa yake tuka su har suka karasa
Mutun hudu ya tarar sunna jiransa tun daga kofar da zata sada shi da dogon corridor din dake sada shi da office dinsa da kuma dakin tiyata da dakin hutun mararsa lafia
Bai iya tsayawa ya kula kowa ba sai jan hannun BILKISSU da ya yi har cikin office din ya nuna mata wajen zama
Tana nan zaune tana bin du wani motsinsa da kallo har ya gama saka safar hannu ya dauki abin jin numfashi ya dora a wuyansa ya juya da sauri ya fice
Tana shirin mikewa tsaye ya dawo da wani saurin ya kamo hannunta da ta tsoma a cikin shayi ya kara bin yan yatsun da kallo
Murmushi ya yi harda sauke ajiyar zuciya ya saki ya juya ba tare da ya ce da ita komai ba
Jikinta ta kankame a fili ta furta" Wayo Allahna yayana, wollah hannunsa kamar na yan dambe, kan balaki! "
Karar shigowar message wayarsa ta ankarar da ita wayar na wajen
Ai kau da sauri ta dauko ta koma saman kujerar ta kwonta ta bude wayar
Kirar iphone 11 pro ce, kalar blue ce, wayar sabuwa ce dal
Sai da ta fara saka number kawarta ta yi serving sannan ta mike ta dauki hoto a office din kusa da hoton HISHAM ta koma ta kwonta ta shiga whatsupp
Searching din sunnan ta yi ta shiga ta tura mata hoton da gwalo
Voice ta turo mata mai dan tsayi , sai ta ki budewa ta gyara zamanta ta danna voice cikin sansanyar muryarta ta ce" Ki yi hakuri, na san na bata maku yau, aman kun sani bana hada umarnin yayana da na kowa, har na fito muka hade da shi ya mayar da ni na koma na yi tilawa "
Kan uba, shine abinda kawar tata ta fada a bayane ta tashi ta zauna ta danna mata voice ta ce" yanzu a ina ne kike? Me kike? Aman Kiss kin san da komai a hannunki yake shine kika ki daga kiranmu bale ki bamu ko? Wai komai ki ce Docter, komai Docter, kai da Doctern nan ba yayanki bane da kin saka na maki wani irin zato a kansa "
Murmushi kawai Bilkiss take ta kyaleta ta ki bata amsa dan kuwa ta san ta rufe wancen babin kuma sai sabon fada, domin ta rarashi uwar dabar (wannan ne rarashin)
Tana gamawa da kawarta maimakun ta ajiye wayar sai