Showing 153001 words to 156000 words out of 180809 words

Chapter 52 - DUK NISAN JIFA COMPLETE HAUSA NOVEL

sajida   

02 Feb 2025

12964

kasa a yadda ka yarda ta gane kana son nan nata, ka ga abokina isaka da yake da aure ya sha fada min, mace ba'a zama kalau da ita sai an kirta wulakanci, idan ka yarda ta san ana kara maka ruwa dan kun yi fada akoy matsala Elhaj dan kuwa zata ringa jan matsalar ne ana ta huraka uwa tanti!"

Hisham ya kara lumshe idannuwansa a sanyaye ya ce" Ta sani fa, na fada mata duka komai, na fada mata ina sonta walahi sai kawai ta karyata ni"

Kader ya shiga tafa hannu ya ce" Muhamadu rasululahi salalahu alaihu wa salam, wa ya fada maka duka ake fadi? Ko fadin kalmar so din abinda kadan ake fada a gimtse sauran shine tsakani da Allah zaka sakata a gaba ka bata komai kuma ka yi jiran me?, to ko nine ai sai na yarfaka kafin na yarda, yanzun dole a samu wanda zai kuma tsawatar mata, ka ga mama duka take da kokara , tati kuwa babyna take kiranta, abanta kuwa autana yake kiranta, ni din nan ni kadai ne zan iya magance maka matsalarka"

Hisham har ga Allah mafita yake nema hakan ya sa yake ta kallon Kader , kader ya gyara zama ya ce" Yanzun ni zan yi gaba da gudu na afka falon sai ka biyo ni ka ringa rikeni ina kubcewa ka ce da ita allurar sojojinmu ta tashi, ni kuwa in ringa ihun ka sakeni na bugata da kasa rashin jinta na tayar min da allurata, nake fada maka Elhaj hakuri zata baka koma me ka mata a wuce wajen"

A hankali Hisham ya girgiza kansa

Kader ya ce" Bai yi ba kennan? "

Hisham ya gyada kansa yana kallonsa

Kader ya dan yi shiru sai kuma ya ce" To ko ka yi mata irin na isyaku da amaryarsa?, ka ja ka toge ka kirta mata rashin mutunci na wahalar da kai da ta yi, sannan ka zarro mata ido ka daka mata tsawa ka bata umarni, Bilkisu fa kanwarka ce, wace kake yiwa jan ido ta zabura jiki na bari ta yi abinda ka sakata, a kan me zaka yarda yanzun ta rainaka? "

Hisham kifta ido yake yana kallonsa sai ya mike tsaye

Kaderma ya mike tsayen yana fadin" Yauwa mutumina , shin bata san su waye mu ba?, ko yanzun sai da na yiwa kawarta kaca kaca na tafiata mu za'a wulakanta? Yo Allah na tuba in ba dan so mai kawo raini ba ai da sai an lakada mata duka kuma ta ce ta gode kuma ya dora kalamai, yanzun mu je na raka ka kofar sakin ko sai mun je an dubaka? "

A hankali Hisham ya girgiza kai da jalabiyarsa a jikinsa ya fara yin gaba , tsakani da Allah ya ji dan kwarin gwuiwa na fuskantarta, hakan ya sa yana gaba Kader na biye da shi hat suka zo kofar falon sannan suka ja suka tsaya

Hisham ya juyo a sanyaye ya ce" Ka tabata idan na yi hakan zata nutsu irin na da? "

Kader ya gyada kai yana kifta ido uwa kadangare ya ce" da guduma "

Hisham ya gyada kansa ya kuma dan kamo hannun Kader ya ce" To kuma kazar fa? "

Kader ya zarro ido ya ce" Inace cewa ka yi ba yanzu ba zamu siyi kaza? "

Hisham ya dan kauda kansa ya ce" Kai ni ba wace kake tunani ba, dan na rarasheta na bata ta ci bata ci komai ba fa take yawo tun da safe"

Kader ya gyada kai ya ce" To yanzun shiga , karfa ka shiga da sakin fuska daureta da kyau, a yi sama a yi kasa kar ka sasauta ka ji? Bari in je in siyo mata kazar dama akoy cenjina a nan, shiga ina kallo"

Kamar wani dan yaro, yadda damuwa ta saka shi bin umarnin Kader sam shi a yanzun kader din kamar wani majinginarsa, sosai ya yarda da maganarsa a hankali ya shiga cikin dakin yana salama muryarsa cen kasan makoshinsa

Idannuwansa ya sauke saman kanta, ta yaye lafayar tata ta yi kwonce saman kujerar irin kwoncin nan ta mike kafafuwanta a sama hannayenta saman cikinta idannuwanta kumshe

A hankali ya karasa kusa da ita, cikin nutsuwa ua zauna gefenta a hankali ya kamo hannun nata muryarsa a sanyaye ainun ya ce" I'm sorry "

Kai zafa mu daku da kuπŸ™„
🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾
*DUK NISAN JIFA*
_(K'asa zai dawo)_
🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾

_RUBUTAWA_

*SAJIDA*

*SADAUKARWA*

*GA*

*MASOYA NA*


πŸ’«βœ¨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🀝

β˜† *[ T.M.N.A]* β˜† πŸ“–πŸ–ŠοΈ

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_



55




A hankali ta bude idannuwanta da suke da ja dan irin tsabar cin kukan da ta sha kama daga jiya zuwa yau tana kallonsa,

Idannuwansa ya kuma lumshewa a hankali ya ce" Ki yi hakuri, kin ji? "

Bilkisu ta yinkura a hankali ta tashi zaune tana kallonsa, a sanyaye ta ce" Na hakura "

A bayane ya sauke ajiyar zuciya yana kallonta

Bilkisu ta ce" Ina ne dakina? Ina ky? "

Hisham dake kallonta a sanyaye ya ce" Babu dakin ki, babu dakina sai dakin mu, a kowani daki shirin na mutun biyu aka yi a wane kike so mu kwana? "

Sai da gabanta ya buga , tana matukar girmama wannan rana sai dai irin yadda aka nuna mata bata da wata daraja sai abin ya mata sanyi, du take daukan komai a baibai irin kamar karya

Mikewa ta yi da kyar tana kallonsa ta ce" A wane kayana suke? "

Shima dake gannin yannayinta kamar bata huce ba ya saka shi mikewar yana kara kallonta ya ce" Sai nake gannin kamar baki huce ba Billy am"

Bilkisu ta kakaro murmushin yake ta yaba masa ta ce" Na huce Hamma am "

Ajiyar zuciya ya kuma saukewa ya ce" A kowani daki akoy kayanki, a wancen ne kawai aka saka iya na barcinki kadai ky din kuma sune jikin yar lokar cen "

Kanta ta gyada , sannan ta juya a nitse ta je ta dauki kys din

A hankali ta gwada a dakin dake kusa da ita, tana murdawa ta ga ya bude, sai ta shiga gwada sauran dakunan da ky din nan kadai dan gannin idan ky daya na iya bude dula dakunnan, nan ta ga kowani daki da ky dinsa hakan ya sa cikin nutsuwa ta dawo ta bude ta shige sannan ta maido kofar ta kule da ky din hannunta ta barshi a jiki

HISHAM dake tsaye ya ji karan rufe kofar bai kawo komai a ransa ba har ya dauki kusan minti goma shiru ba motsi hakan ya saka shi mikewa ya karasa kusan kofar ya shiga kwonkwasawa

Bilkisu dake zaune kasa jikin gadon ta kurawa kofar ido, bata iya amsa shi ba har ya kara bugawa ya ce" Wai me kike haka ne? "

Bilkisu ta taso ta zo kusa da kofar ta jingina a hankali ta ce" Dakina na shigo, barci zan yi Allah ya bamu alkhairi"

Ido ya tsurawa fuskar a sanyaye ya ce" Haka kike son gina mana rayuwa? Mata na wawa sunna kama mazajensu sunna rikewa da karfinsu ko a yi sama ko a yi kasa ke so kike ki fara mana da haka?, koma me na maki ai na baki hakuri ko? Wai menene a ciki dan na jewa matata? Inace halalina ce Aisha ba haramun dina na jewa ba?, kuma abin nan kece kika kunna shi kamar yadda kika saba , kuma shikenan sai abin ya zama fitina? "

Bilkisu ta hadiyi dadacen abinda ya tsaya mata, kennan dai ba zai yarda cewa rana ce special a gareta, abu ne da yake sabo a gareta, kai koda an rakota ne idanma ba ranarta bace ta ji irin haka ai sabon shiga ce ita bata san dawan garin ba bale har a ce za'a ga laifinta a kan hakan ko?, shine yake fada yana kara jadada mata matarsa ya jewa

A sanyaye ta ce" Haka ne, matarka ce, halalinka ce, kana da damar zuwar mata, kamar yadda nima nawa tsohon mijin ya zo min a lokacin da ya yi niya kafin ya dankara min saki!"

Kamar wata wawuya ta saka hannu ta bude kofar ya kasance sun yi ido hudu da shi bayan ta gama fadar maganar da bata san cewa yana iya halakata a kanta ba

Jan kallon daya wurga mata ya kai hannu zai kamota kamar ta sani ta zille ta maido k'ofar ta rufe da k'arfi, kys tasa gabanta na fad'uwa HISHAM kuma saiya shiga jijjiga k'ofar da k'arfin tsiya, idonshi sun rufe sun kad'a sunyi jajir, jijiyoyin jikinshi duk sun bayyana rad'o rad'o, cikin tsananin bacin rai da tashin hankali na masifa ya ke fad'in "Billy ki bud'e kofar nan, ki BudΓ© na gaya miki, yau saina banbance miki aya da tsakuwa, ba dai ni kika..."

Wani tafasa da zuciyarshi ke yi yasa kawai yake girgizz kofar dakin yana mai nadamar me yasa yayi kofar nan mai karko ne.

Kader na dawowa ya ji wannan tashin hankali, sai ya rud'e yayi tunanin ko dai shawarar daya bashi ce ta harzukoshi haka ta taso musu da iskokanshi, ai da gudu gudu ya shigo yana duba wayar dan ya kira d'aya daga cikin abokan aikinshi dan su zo su taimaka mishi ko allurar bacci su mishi dan yana tsoron masifar Hisham, saidai bai kai ga kiran lambar ba ya k'araso da gudu yana fad'in "Kai kai! Subhanallah!"

Rik'eshi yayi gam da iya k'arfinshi yana cewa "Me ya faru? Me ta maka? Billyn ce kake neman halakawa haka?"

Cikin k'arajin murya mai amon b'acin rai ya finciki jikinshi yana fadin "Sakeni Kader! Sakeni na nunawa Billy na fi karfinta, ni zata mayar dan iska da baisan me yake ba? Ni zata kalli idona ta ce wai wani ya je mata? Me take ji dashi? Akan me zata dinga cizgani? Dan ina son ta?"

Sake rike shi yayi gam yana sakin ledar kazar daya siyo yace "Ka yi hakuri, yi hakuri Hisham yarinya ce, muje dan Allah ka ji wani abu."

Fizgewa yayi a hassale yace "Kader fita a nan, babu inda zanje, ka ce mata ta bude kofar nan, ka ce ta budeeee!!!"

Yanda yayi maganar duk gidan na amsawa yasa Bilkisu sulalewa kasa ta fashe da kuka tana mai dora hannunta saman kanta, sakinshi Kader yayi yace "Shikenan na sakeka, ka balla kofar dan Allah ka kakkarya Bilkinsun ka kaji, kaga da safe sai Mama ta zo ta kaita asibiti tayi jinyarta, ai haka ya Maka ko?"

Ficewa yayi ya barshi tsaye sai yaji ya rasa kuzarin yin komai kuma, a hankali ya matsa jikin kofar yana taushe bacin ranshi ya kai hannu ya kwankwasa kofar, shiru yaji sai sautin kukanta da take rerawa, a nutse ya saita muryarshi yace "Billy am, ki yi hakuri kinji Ki bude kofar, ki fito ki ci abinci dan Allah kar yunwa ta kamaki." Irin yadda yake maganar dole ne ka ji gaba daya hankalinka ya tashi, tabas so so? So tashin hankali ne

Ita kanta da rarafe ta nufo kofar cikin yin watsi da dukan wani tsoro ta kama ta mike tsaye ta bude gaba daya jikinta na bari

Ido cikin ido suka kalli junna da shi a lokacin da ta ga danshin abin da ya biyo ta kumatunsa sai jan da idannuwansa suka yi

Zuciyarta ce kw tsintsinkewa a hankali ya duka ya dauko ledar ya miko mata yana kallonta

Hannunta na rawa ta amsa tana nan tsaye ta ga ya yi wajen kys din ya dauki guda ya juya da sauri ya yi daya daga cikin sauran dakunan ya bude sannan ya maido ya rufe da wani irin karfin da sai fa ta zabura

Gaba daya kafafuwanta na rawa har ta daga dan nufar wajen sai kuma ta ja da sauri ta tsaya cike da tsoro da fargaba , wani abin ke tunasar da ita hammanta ne fa? Sai kuma wanin ya ce da ita ai shima ya san ke dinsa ce aman ya jewa wata a ranar da take taku kuma har yana ikirarin matarsa ce

Kai kawo yake a dakin da wayarsa a hannunsa, gaba daya a birkice yake yana jin zuciyarsa na suka, a yau sai yake jin mema ya hada shi fadawa soyaya? Wai haka zai kare? Haka zai kare? A yanzu abinda ya dakatar da shi da wancen yarinyar ta ci abinci, tabas rainin hankalin d atake masa kwana biyu tsakanin daya biyun sakin da shashashashan cen ya yi mata bayan kadararen aurensa da ya hau kanta zai je ya bambancewa kansa, tunda har ta san ta yi fushi kan wannan abin zai bata isashen da sai ta ringa sakin fitsarin dake mararta!


Gyaran murya malan ya kuma yi ya ce" A tunaninku an sauke maku aure a kanku ne NANA da ZAINABa? "

A tare suka kali junnansu suka kuma kalli malan

Jauro ya ce" Ko baku da ainahin wanda zai fada maku gaskiya ko ya maku nasiha kai harma ya tirsasaku ne?, shekarunku nawa tsakaninku da maza na aure? Shin baku da lafiar raya sunnar ma'aiki ne ko bakwa kwadayin rayuwa irin ta aure? "

Mama ta dafe habarta tana sada kai ciki da jin kunya ta ce" To kuma Malan me ya kawo wannan? "

Jauro ya dube ta ya gyara zamansa ya ce" Kya ce haka, dole ki dubeni ki ce haka mana, aman ina so ki sani Asma'u idan ke kin murje idannuwanki kina zamanki haka ba ruwanki da maganar duniya bale ta kiyama sai ki tsawatarwa kanwarki, yanzun me take nufi? Jira take a gama biki ta juya ta koma? shekaru fa tafia suke, kowa faman da yake shine ya samu wajen da zai saka ransa ya ji sanyi, ku yau ko kunyar y'ayanku bakwa ji? Danma Allah ya wanke ya baku tsararu wa'inda suke girmama ku, suke kiyaye du wani tashin hankalinku ba zaku iya shiga dakin aure ba? Ko kun yi tsufan da ba zaku iya zaman aure ba? "

Mama ta kara sada kanta cike da jin kunyar kalamansa duda tsagwaron gaskiya ce yake fada mata

Jauro ya ce" to zancen gaskiya fa zan fada maku baki daya shine, ku gyara, ku gyara domin nan kusa zaku fara tara yan jikoki ana kada maku zawarawa, kin ga Zainabu mahaifin Hisham ya min bayanin komai, kuma na gamsu, nima a shirye nake da irin muradinsa, na ce ku shigo nan ne dan na jadada maku, da wannan salar du zaku kara daraja a kan taku, Allah ya rufa maku asiri kun samu kar ku yarda wani shashancin ya shiga kwakwaluwarku fa!"

Tati ta dago tana kallonsa, muryarta a sanyaye ta ce" Yaya, auren dole ne za'a min da tsufana? Aman yaya me zan yi da mutumen da tsabar tsanar zama da ni ya min karyar ya mutu? Ni kam ko duniya ya tara ya kara gaba, in dai aure ne zan yi aman ba dai uban Hisham ba!"

Jauro ya gyada kansa ya ce" Kafin ki yanke hukunci ina so ki yi tunani a kai, sannan ki barawa Allah zabi, idan kin kula saura wata uku biyu sallar, idan lokacin ya zo sai mu ga Abinda Allah ya yi"

Dubansa ya maida kan Mama, wace ke kallon matarsa wace kanta ke sade itama ya ce" Ke fa? "

Sai da ta zabura wollah, kasa fadin komai ta yi ta mike da sauri tana fadin" Allah dai ya bamu alkhairi, Zainaba mu je "

Sorry nah? Bukukuwa
🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾
*DUK NISAN JIFA*
_(K'asa zai dawo)_
🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾

_RUBUTAWA_

*SAJIDA*

*SADAUKARWA*

*GA*

*MASOYA NA*


πŸ’«βœ¨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🀝

β˜† *[ T.M.N.A]* β˜† πŸ“–πŸ–ŠοΈ

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_



56



Da ido malan ya rakata har suka fita a gidan ya yi dan murmushi yana kallon mahaifiyar Mami a sanyaye ya ce" Kin ga abinda na fada maki da kika ce dan me ba'a daura mana auren ba?, bata bani amana bane"

Ajiyar zuciya ta sauke, kwarai ita ta masa nuni da a yi abinnan , ba dan komai ba sai dan ta gyara kuskurenta na farko kan tubure masa, tayar masa da hankalin da ta yi har ta nisanta shi da matarsa, ita mutuwar Mami gaba daya ta saka ta yi sanyi da rayuwar, tana kallonsa ta ce" Ai ba ta haka zaka saka a yi dole dole ba Malan, da rarashi ake yi ko dan ka tsufa ne ka manta yaya ake samun amincewar mata ne? "
Ta karashe tana daria

Malan Jauro ya gyada kansa yana murmushi ya ce" Watau ninema na tsufan ko ? Na ji, in dai Asma'u ce barta inda kika ganta wai itama ta girma shine har take kora y'a dakin miji bayan ita tana gudun mijin"

Nan dai suka ci gaba da hirarsu cikin raha da sakin fuska wa junna da fahimtar junnansu

..................................


Karfe daya kennan na dare, a irin wannan lokacin da zuciyarta cikin nutsuwa take da ta jima da kamo tashar baci
Sai dai kasancewar bata cikin nutsuwa ya saka tana saman salaya bayan ta yi wanka ta dauro alwallah ta saka wata doguwar riga mai hade da hijab din nan ta dubi gabas

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login