Showing 69001 words to 72000 words out of 180809 words
ta yi, ta ringa kuka kamar zata hadiyi zuciya.
Mama hankalinta ya tashi sosai, dama tana cikin tashin hankalin wai daga daura auren yarinya an saketa duda an kawo mata dalili kakarfa mai zaman kansa wanda tabas idan akai mata haka an tauye hakinta , aman irin kukan da Bilkisu take sai ya bata tsoro.
Tana kallonta ta ce" Bilkisu dama ko kina son Umar din ne?"
Bilkisu na rizgar kuka ta ce" Mama, ya sakeni fa, ya sake ni fa? Mama ni tarewa zan yi, tafia zan yi ya fada min me na masa ya sake ni a kan wani dalili ya sake ni?"
Sai su dawo kallon kallo, sun kasa budar baki su ce da ita wai ga dalilin da ya sa ya saketa, wanda koda bai saketa ba tabas sai an raba aurensu.
Hankalin mahaifinta ya tashi ainun, hakan ya saka shi tafia da gagawa ransa jagule da yanayin Bilkisu.
Kukan balaki ta sha kafin ta yi baci a nan falon a takure saman kujera, inda suka kasa tashinta dan tsoron kar ta d'ora daga inda ta tsaya.
Sai a lokacin mama abubuwa suka shiga kanta harma ta gane dalilin yanayin Hisham.
Mik'ewa ta fara yi tana kallonsu tace "Mu tafi."
Irin yanda take kakawar da dubanta ya saka su du mik'ewa suka bi umarninta.
Har sun fita ta dakata tace "Ina zuwa."
Dawowa ta yi d'akin a lokacin Hisham ya mik'e tsayen shima.
A hankali ta k'arasa kusa da shi ta tsaya a gabansa tace "Cikar darajar namiji, kamilalan namiji, namiji mai kima da ya san kansa shine ya san darajar iyalinsa, ya tatali iyalinsa, ya basu nasu matsayi ko yayane, bana so ka kasance a layin mazan da ake iya jin kunyarsu dan munanan halayansu ba dan cikar nagartarsu ba." Tana gama fad'a ta juya ta fice a d'akin.
Ajiyar zuciya ya sauke ya yi murmushin da bai san daga inda ya fito masa ba, ya yi murmushin da rabonsa da ya yi irinsa har ya manta a hankali ya taka ya shiga dakin.
Hangota ya yi sai jan abin shinfid'ar take tana rinrintse idanuwanta hankalinta a tashe tana waige waige ta kasa tashi a hankali ya nufeta yana k'ara kallon yanayinta.
Tana ganinsa jikinta ya kara d'aukan rawa ta rintse idanuwanta ruf ta fashe da wani kukan ta ce "Dan Allah na tuba, dan Allah kar ka kashe ni, ba zan kuma shiga harkarka ba, ba zan kuma matse maka waje ba, dan Allah ka rufa min asiri kar ka kashe ni."
Murmushi ya yi ya zauna a gefen gadon yana kallonta, tabas wannan yarinya dake kwonce a gabansa a dazu kadan babu wace ya tsana irinta, ba dan komai ba sai dan ta masa karan tsaye a cikin lamuransa, ta masa shigar sauri, duda shi din namiji ne yana da damar auren mace na bin mace har hudu, sannan a wannan zamanin kalilan ne dake rik'e da irin damarsa a hannu kuma suka kilace kansu daga aikata zina, sunna aikata zinarsu ne a bayane ba wani a boye ba, sunna yin kayansu ba tare da jin kunyar Allah ba bare mutun
Aman shi, Alhamdulilah, bai taba aikata zina ba ta kwonciya da mace ko ta shafe shafe ko ta rike riken hannayen mata duda zamansa a garin turawa da cudanya da su
A gaskiya ya yi waje ya ajiye daraja da girman budurcin y'a mace kasancewar irin yanda ya gama gane cewar a yanzu mata kalilan suka san darajar kame kansu daga aikata alfasha
Da yawa kan je su aikata ne dan son ransu, wasun mugwayen kawaye ke yi masu jagora, wasun kangin rayuwa ke saka su kasa hakura da tawakali da Allah, wasun dogon buri da hangen nesa da rashin godiya da Allah ke sakasu aikaya zina dan kawai a basu dan datin dake cikinta su kashewa cikinsu da jikinsu, wasu kuwa makauniyar soyaya ke rufe idannuwansu ta yadda suke zuwa su mika ragamar jikinsu ido rufe har su yi ikirarin basu da regret bayan abinda basu sani ba shine, sun rigaya sun ginawa kansu zurfafen ramin da zasu rufta da kansu ba tare da sun shiryawa hakan ba, aun zubar da kimarsu sun ciyar da kansu da kud'ad'en haramun wanda ke zagwaye naman bawa a cikin kabari, sun yiwa y'ayansu illa sun gurbata zuri'arsu domin zina bashi ce ....... *AMAN TSAKANIN BAWA DA UBANHIJINSA AKWAI YAFIYA, ALLAH KAN YAFE ZUNUBAN BAWANSA IDAN YA TUBA YA TSARKAKE KANSA YA K'I KOMAWA, ALLAH GAFURUN RAHIM NE* ..."
Da yawan lokuta matan duniya sai sun tashi yin aure zasu fantsama asibiti kofa kofa wajen likitocin mata sunna neman taimako, taimakon ba na wani abu ba sai na a rubuta masu ko a yi masu aikin da zai mayar da su ya rufe su dawo tamkar budurwa, shin dama dan adam ya isa ya maida yanar budurcin da Allah ya yi da kansa aka watsar? Lalle suna cutar kansu da yan kud'ad'ensu da gaulayen mazan da basa ganewa.
Ya karanci mace zahirinta da badininta, zamansa a garin Niamey sai da ya dawo ya daina bashi mamaki irin yanda Budurci ya bace bat a cikin gari sai wani gagarimin ikon Allah
Da ya dawo damagaram sai abin yake zaburar da zuciyarsa, hakan ya saka shi kasawa ya tsare du budurwar da ta yi gigin tako baban asibitin da gwamnati ta kafa ta tsare ta dora sunnansa ta dire takardu ba dan komai ba sai dan zurfin karatunsa da k'wazonsa wajen aikinsa ya kasance yarinya ta gama banzatar da kanta a titi ta shigo dan neman taimakonsu a kan zata biya su makudan kud'ad'e dan su d'inketa ko su rubuta mata abinda zai had'eta sosai yakan nemi baban matakin da yake d'auka a kanta ciki kuwa idan ta yi wasa ta tsaya har na had'uwarsa da iyayenta ko mijin da zata aura, ba dan komai ba sai dan ya tsoratar da su ko zasu daina halayensu duda ya san abi ne mai matuk'ar wahala, k'arshen zamani kenan.
A yau da ya afkawa yar garin Niamey da k'arfi da yanayi na b'acin rai ya yi mata shigar da ba rarashi ko dan aike duda fiyayen halita ya mana nuni cewar a fara tura dan aike aman shi ya afka mata haka kai tsaye du a tunaninsa Allah yana gani irin yanda take bajen nan ta gama sanin kan harkar wace shi shine bak'o a cikin garin.
Sai dai a yanzu zai iya rantsewa cewar ta ciri tuta kuma ya ga darajarta da kimarta fiye da tunanin bawa harma yana iya kiranta da babar murya da *MAI D'AKINA* ba dan komai ba sai dan wannan gagarumar kyauta da babar darajar da ya kwata, wace yana iya yin alfahari koda a wannan saduwar ta d'auki cikinsa bashi da dar dan an ce alhamis din kirki daga larabarta ake ganeta, idan har bata garwaya masa y'aya ba, du wani mumunan hali in sha Allahu da sauki Allah na iya tseratar da y'ayansa bale idan yana tsaye a kan k'afafuwansa, kuma duka wannan kima da ta cira a yanzu ba komai ya saka ba sai dan ta rike mutuncin kanta ta kawo masa kyautar *BUDURCINTA*.
Murmushi yake ya kawo hannunsa a hankali ya rik'e nata da ta jimk'e abin shinfida ta rintse ido gam, muryarsa a sanyaye yace "Kar ki raba min gadona gida biyu *Aysha*, kin kuwa san irin nauyinsa? Ki rufa min asiri ba zan iya siyan wani ba."
Shiru ta yi daga magiyar da take, da sauri ta nemi bud'e idanuwanta duda tsoron hakan da take, aman irin yanda muryar dodonta ta shiga kunnayenta sai da ta ji idanuwanta sun d'agu sun shiga cikin nasa.
Ido d'aya ya kanne mata yana d'an murmushi a hankali ya furta "Na k'ara ne?"
Da sauri ta rintse idanuwanta tana jin gabanta na fad'uwa "Wayo Allahna ni Aisha na shiga uku na lalace, wannan mutumen shine ko wani ya turo min? Meye hakan kuma? Me yake yi haka kuma? Dama ya san sunana? Harda wani fad'in Aysha." Take ayyanawa a cen k'asan zuciyarta.
"ki yi hak'uri kin ji? Ba zan kuma ba in sha Allah, na zo maki da ganganci bayan ke d'in baki saba ba, ba zan kuma turmusarki da k'arfi ba har sai kin ji kina iya d'aukata, shin zaki iya sakin jikin ki na duba ki?" Ya fad'a yana d'an shafa gefen hannunta.
Kan uban cen kayyasa, alkur'an ta gama mutuwa ta mace a kan gayen nan, wato ita duniya ta damketa irin damk'ar nan mai saka bawa cikin garari, to alkur'an ji take a kan mijinta rana iya yin komai, ba wai ta buda masa ya gani ba kai koda komawa ruwa za'a yi a yi kawai ba komai koda ya kasheta ta san ta mutu da k'aunar mai hankali, mai ilimin islamiya, wanda ya san darajar mace.
Idanuwanta lumshe tana jin yanda yake binta a hankali har ya bud'a k'afafuwanta ya haska yar k'aramar fitilar da ya ciro daga cikin kayan aikinsa.
Sosai ya hahaska wajen baya ko jin k'yank'yamin datin da ya d'an bushe a jikin fatar wajen sannan ya rufe.
Ajiye komai ya yi ya shige bayi.
Ruwa ya tara masu dumi sosai, bai zuba masu komai ba ya fito ya kamata ya taimaka mata ainun ya nufi bayi da ita.
A gaskiya sai da Hisham ya tsaya ya bata kulawa iyakar iyawarsa, fuskarsa a sake iyakar sakewar da zuciyarsa ta samu, sai da ya gasata sosai da sosai ya barta ta dan huce dannan ya yi mata allurar kashe zafi mai tsadar gaske sannan ya d'inke wajen cikin nutsuwa domin ta k'aru, k'aruwa mai d'an yawa ma kuwa.
Yana gamawa magani ya bata wanda ya tabata nan da yan mintuna zata iya samun babci sannan ya d'an yi gyaran murya yace "Zaki kwana a nan ko na raka ki?"
Idanuwanta da take lumshewa ta gyad'a masa hakan ya saka shi mik'ewa ya kamata ta mik'e.
A hankali take takawa yana biye da ita har suka k'arasa kusa da falon mama.
Ja ya yi ya tsaya gabansa na fad'uwa ya kasa shiga, mamaki tsoron had'uwa yake da ita duda yanayin da yake ciki wanda bai san takamaiman yaya zai kwatanta mutuwar auren k'anwarsa a k'asan zuciyarsa ba.
Kallonta yayi ya tallabo fuskarta yace "Je ki kwanta, ki yi bacci sosai kin ji, ki kula da kanki."
Abinda shi kan shi baiyi tsammanin zai iya bane, sumbatar goshinta yayi tare da lumshe ido, ita ma haka wani dad'i ne ya ziyarceta, ko ba komai tayi farin cikin kulawar daya nuna mata a daren nan mai tarihi. Saida ya ga shigarta ciki kad'ai a hankaki ya juya ya koma b'angarensa ya samu waje saman kujera ya zauna ya d'aga kansa kadan ya lumshe idanuwansa.
Mutun na tsara rayuwarsa ne bayan ba shi yake da ikon wanzar da ita yanda yake so ba, tausayin k'anwarsa, muguwar k'aunarta uwa uba magangannunta na tsaye a k'asan zuciyarsa, *NA TSANE KA HISHAM*
Leb'ensa na kasa ya cije yana dan shafa wajen zuciyarsa a hankali ya ce "Shin b'acin rai da firgici ne ya saka ki furtan kalmar tsana a irin wannan lokacin? BILKISU HAR SUNA NA AKA KAMA KAI TSAYE FA."
Ya jima nan zaune sai da ya ga dare na kara tsalawa sannan ya mike ya nufi dakinsa na baci
Cenza abin shinfida ya yi ya idasa tatare kayansa ya rama salolinsa sannan ya nemi waje ya kwonta yana jin tar nutsuwa na ratsa shi
Yakan hangota a idannuwansa ne a hankali ya gyara kwonciyarsa a kasan zuciyarsa yana bitar sunnanta kamar haka "BILKIS, BILLYNA, BALKI, NANANA"
tun da ya tunkaro dakin yake jin sautin kukanta, da sauri ya idasa shiga har yana buge hannunsa da necktie dinsa a hannunsa yana son idasa kwonceta ya daura
Turus ya yi gannin Bilkisu tsugune daga ita sai yar ficiciyar rigarta wace da kadan ta dara gwuiwarta kanta ba ko dan kwali har yanzun kuma kitson filanin ne a kanta sai na gaba da ta kunce tana rizgar kuka,
Tati na tsaye tsakaninsu da Mama, inda mama ke fadin" Ki bani ita Zainab, iskancin Bilkisu ya isheni yaushema ta san Umar din? Idan zafin rasuwar yar uwarta ke sukanta ai ba ta haka zata ringa nunawa ba? A ina ta san dadin auren da zafin sakin? Me ke damunta ta samu ta sha bacinta kamar yarinyar goye dan salon iya shege tana buda idannuwanta ta barke min da kukan sangartar sai na fada mata dalilin da mijinta ya saketa? Ita a kaita wajensa dan tana son sa to dan Allah Balki tashi ki je na gani ga hanya nan kin ji mai gado?"
Idannuwansa ya rintse yana jin gabansa ya kwonci kwonci ya tsinke ya fadi
Da sauri ya kara dora dubansa a kanta, gaba daya ta yi ja tsabar rigimar da take zubawa kan jiya zuwa yau, a hankali ya ringa fama da zance a kasan zuciyarsa kamar haka' dan Allah kar ki kwacen yannayin da nake ciki, kar ki ji haushina dan na tara da matar da take ta sunnata, kar ki dauko fitinar da zata saka hankalin kowa tashi'
Bilkisu na kuka Tati ta ce" Dan Allah aunty ya isa haka, ki barta haka, wai dan Allah bakya tausaya mata ne da wane ake so ta ji? Ko mahaukaci in dai ya san yana da aure kuma aka ce da shi bashi da shi ai zai ji ba dadi, aunty ba maganar so bace maganar nan ta daraja da girman igiyar aure ce, kamata ya yi mu zauna mu rarasheta har ta saurare mu, ta ce ko ba auren Umar sai ta auri wani a yau yau mu saurari yarinyar nan mu rarasheta domin tana cikin tashin hankali Aunty"
Mama ta dafe gaban goshinta ta juya zata shige ciki sukai ido hudu da Hisham dake tsaye kikam
Idannuwansa sun rikide sun yi jajajir kana ganninsa yannayin tashin hankali ya bayana a tare da shi, 'what? Kukan katon da ta hadu da shi jiya jiya ne take, shi fa sam bai gane ba'
A hankali ya ringa takawa ya karasa yama kasa yiwa kowa magana
Dukawa ya yi daf da ita ya kai hannunsa ya dora saman damtsen hannunta muryarsa a sanyaye ya ce" BILKI? "
Da sauri ta dago da kanta duda ta ji kanshin turarensa tun kafin ya karaso daf da itan aman yana tabata ta ji wani irin yar da bacin rai sun hade mata
Da dan sauri ta ja baya idannuwanta rufe ta ce" Tati dan Allah ki kai ni gidan Abana "
A hankali ya kuma fadin" Fushi kike da ni? "
Ido cikin ido ta kuma kallonsa , tabas basu taba furtawa juna gani da gani maganar soyaya ba, aman ya fada a lokacin da take lab'e, ta yi gudun gidan dan shi,
Sai da ta langwab'e kanta, bata tuna cewar Tati na tsaye ba, Mama na wajen ba, mahaifiyar aisha na wajen ba ta ce" Ba fushi nake da kai ba yayana, bana son zama a inda kake ne koda na second daya, yayana ja taimakeni ka tambayar min su me yasa mijina ya sakeni bayan ina son sa? Ya dawo gareni ka ji yayana?"
A hankali ya lumshe idanuwansa, da kunnayensa a gaban idannuwansa Aba ya fada cewa ya saketa ne dan baya iya yi mata komai, shin ko dai karya yake yi ya nuna mata wani abu? To ta yayama aka yi iyayensa zasu furta haka idan fa ya warke a saninsa da suka yi? Kardai a ce ya ya ya.
A gigice ya damk'i hannunta ya mik'ar da ita.
Janta ya yi dakinta ya turata ya shiga yana kallonta ido cikin ido
Duda gabanta na tsintsinkewa da tsoron yanayinsa aman haushinsa da take ji ya hana tsoron yin tasiri a tare da ita.
Yanda k'irjinsa ke yin sama yana yin kasa abin tsoro ne.
Gaba daya jikinsa rawa yake ya nunota da hannunsa ya ce "ABA ya ce mijin da ya d'aura maki ya sake ki ne dan bashi da lafiyar da zai iya gamsar da ke, ke kuwa kina kallon tsabar idona kina ce min na kaiki wajensa a kaiki wajen mijinki, d'aurin aurenki da shi a jiya ne bayan sallaar azahar, da yamma da d'auko ku ke da mama, baku samu kad'aicewar da wani abin zai iya faruwa a tsakaninku ba! BILKISU ki ce min Hamana babu abinda a taba shiga tsakanina da shi, ko shi ko wani namijin daban, dan Allah ki ce min Hamana babu wanda ya taba taba koda yar yatsata ne domin bana bari bana yarda, ki ce min hamana har yanzu babu wani namijin da ya tab'a rik'en hannuna in ba kai ba sai Abana."
Had'e hannayensa ya yi k'irjinsa na ci gaba da yin sama da k'asa yace "Dan Allah kar ki fadi abinda zan kasa d'auka, dan Allah kar ki min haka."
Bilkisu na kallonsa da yanayi irin na mamakin son kansa, watau ita sakarai ko? Ita da bata san ciwon kanta ba ko? Lalle ma.
Yanayinsa ya hana mata furta masa kalaman da ta tsara a zuciyarta, da sauri ta juya ta fad'a bayi ta rufo k'ofar ta nufi wajen wanka.
Takawa ya yi ya tsaya a hankali ya ce "So kike na kasa anfanuwa? Me zai hanna ki bani amsar wannan yar tambayar?"
Daga inda take tsaye kanta take cikin nutsuwa, idan ta tuna kalmar bazawara nan take jin wani katutu ya tsaya mata a k'irjinta, bashi da lafia? Rashin lafiyar ta fad'a masa ita abinda ya dameta kenan? Sai a irin lokacin nan da ta d'auri niyyar zama da shi shi kuwa ya hankad'ota gaban mak'iya? Ai ita yanzun mak'iyinta HISHAM ne! Alamu sun nuna so yake ya halakata!
Ta jima cikin bayin nan sosai dan sai da ta kunce kitsonta ta wanke kanta ta darji jikinta tas sannan ta saurara.
Jin shiru ya sakata fitowa daure da tawul a k'irjinta.
Turus ta yi ganin Mama zaune a gefen gado stil da bakar abayar dake jikinta tun ta jiya, watau ko wanka bata samu ta yi ba tsabar damuwa?
A hankali ta k'araso inda take zaune ta duk'a ta d'ora kanta saman cinyoyinta.
Mama ta ringa shafa gashin kan nata a sanyaye tace "Dan Allah kar ki tada min hankalina Mai gado, shin yaya kike so na yi ne, kin kuwa san irin ciwon da nake ji a zuciyata na sakar min yarinya da aka yi? Kin ga ba uwar dake son haka ta faru da ita, dan Allah idan rasuwar Mami ce ke