Showing 60001 words to 63000 words out of 180809 words
farin cikin auren nan, shirintama yau zata koma gidan mahaifinta har sai bayan auren
Tana ninke sauran kayanta ta kalli mamanta ta ce" Mama, a daina irin haka dai ba kyau, dan ita bata zo auren danki ba shine kema sai ki ce ba inda zaki je? Ai Abana ya zo, kuma Mami kwananta uku a gidan nan ko?"
Mama ta tura baki ta ce" Ke ni banma san shirmen me matar nan take ba, Allah na tuba da tsufana me zan tsaya yin shirmen kishi? To kishinma na me bayan na rabu da tsohon mijinta mai doro?"
Bilkisu ta zarro ido ta ce" Lalala mamana, walahi Abana bashi da doro, mama zankadin da shi? Uhum su mama ko dai ko dai? "
Tati ta bushe da daria ta ce" Kema kya fada wannan karfin hali da fada da wannan matar take, an ce ta koma dakinta ta ce aa bata san yaren ba kuma tana cakalkalar santalin habibinta "
Mama ta mike ta ce" Ban san ina bakinku ya koyi rashin kunya ba, aman ina ga zan kaura kusa da yarona ko zan daina jin zanceceku kamar an turo ku"
Daria suke mata har ta tafiarta dakinta
Sai da Bilkisu ta gama komai sannan ta shiga da dan sauri dan yiwa mamanta salama domin wannan tafiar a motarta zata yi
Mama ta dan kura mata ido ta ce" Walahi gabana ke cika faduwa mai gado ban san dalili ba, kuma kin ga yayanki ko? Ya ki ya zo ya dauki matarsa ko? Dan Allah yaushe ya taba yin kwana biyar yana aikin tiyata? Hum, kuma na rasa inda zan matse shi na kama shi"
Bilkisu ta ce" Aya mamana zai dawo da kansa ne, kin san fushi yake, idan ya saku zaki ganshi da kanshi ya dawo gareki, mamana ba zai iya nesa da ke ba bayan kina raye a duniya"
Mama ta yi murmushi ta ce" Gashi ke kina son ki koma wajen abanki? Bilkisu sai na ga kamar yanzun kin fi son sa a kaina ko? "
Bilkisu ta dora kanta a gefen kafadar Mama ta ce" dukanku ina son ku, ku din kune duniyata, lahirata, farin cikina Mamana"
Mama ta yi murmushi a hankali ta ce" Ki je, Allah ya kiyaye, kar a yi abinda za'a ce ba kunya kin san fa mutanenmu na gida, kuma in sha Allahu zan zo nima aman ranar daurin auren ba ana gobe ba"
Bilkisu cike da murna ta mana mata kis a kuncinta tana tureta tana komai ta fita tana daria
Yauma Tati sai da ta bata kudi sannan sukai salama ta shiga motarta ta tayar ta nufi gidan mahaifinta
Gidan cike yake da dangi, ana ta shagulgula tun yau kasancewar akoy fili da kuma dakunna masha Allah
Kowa sai sam barka yake da gannin Bilkisu, da yawa sun yi mamakin girmanta, da yawa na fadin Lalle jauro ashe yan matan biyu ne da shi
Ita dai sai da ta gaida mama sannan ta nufi dakin yar uwarta
A kwonce take idanjuwanta lumshe, kanta daure da dan farin kyalen da ta daure dan ya daina sasara mata, kafafuwanta du ta saka tsuma ta kukule dan ta ji dama damar dadatsa matan da suke yi
Da sauri Bilkisu ta karasa tana fadin" Subahannalah, Mami jikin ne ya motsa ko sakatar amarci ne? "
Mami ta kakaro murmushi ta ce" kin zo Balki am? "
Bilkisu ta zauna gefenta ta ce" Eh na zo, tashi na ji menene? Baki sha maganinki bane ko meye? Mama ta san baki da lafia kuwa? "
Mami ta kamo hannunta ta kai kusa da kirjinta a hankali ta lumshe idannuwanta ta ce" Balki am, kin san ina son ki kuwa? Ina son ki sosai yar uwata, na yi farin cikin samun kasancewa da ke na tsayin sati uku, ban taba fara'a irin haka ba yar uwata, ban taba jina da farin ciki madaukaki kamar irin yanda muke baci tare ba, kin san wani abu kuwa? Da na dawo na kwonta ni daya sai na kasa yim baci, sai kawai hankalina ya tashi sosai har na ji kamar zan sike, Balki Am sai na tuna kwoncin kabari, na tuna kadaicin kabari, ya Allah ka sa mu samu wadatace mu hadu da mataya zama na alkhairi, Balki Am Allah ya raba mu da duhun kabari"
Bilkisu ta tsaya da murmushin da take tana kallonta, gani ta yi idannuwanta ai a rufe suke take bayanin nan, ga kuma hawaye a gefen idannuwanta
Da sauri ta ce" Ke Mami? "
Mami ta dan daga idannuwanta
Bilkisu ta ce" Meye haka? Tashi tashi mu tafi asibiti ko na kira yaya ne ya zo ya duba ki? "
Mami ta bude idannuwanta tana sakin murmushi ta ce" Ke dan Allah kawai ke motsi kadan sai asibiti? Ni barni baci ne nake ji sosai walahi "
Bilkisu ta sauke ajiyar zuciya aman duda haka sai da ta kawo mata maganinta ta sha sannan ta tashi ta shiga shirya masu suturunsu tana labarin sai ta koya mata rawar filani
Washe gari haka aka wuni nanma ana shagulgula, ango ya zo ya gaishe da iyaye cikin shigarsa ta kamala, Umar yana da daraja mutane, ga biyaya ga kunya, a nan ne Laila ta ganshi take cewa" Kai wai da Umar mai waya ne angon? Kai masha Allah aunty ta yi dace domin Umar da kika gani kin ga yanda yan mata ke kai masa hari kuwa? Ko dan abin hannunsa ne? Ko dan kyansa ne? Aman ba ruwansa da sha'annin mata da fade faden nan, ke har shari aka so yi masa wai ko baya son mata sai maza, kin ga gashi zai yi aurensa shima "
Bilkisu dai sai murmushi take jira take ya fita ta bi shi ta tsokane shi
Yana fita har zai shiga motarsa madaidaiciya mai kyai ta ce" Ango ango, ango Umar na Mami bada kanka a sare ka je gida ka ce ya fadi"
Yana daria ya dan nuno mata yatsa ya ce" Allah ya shirya ki Bilkisu "
Bilkisu ta ce da shi" Sai goben ko ina fatan zaka zo da karfe shida na safe dan ka shinfida tabarmu"
Yar karamar wayarsa ya jefo mata ta cafe ya ce" Yarinya kyauta ce ki kaiwa amaryana mu zanta "
Ai kam ihun murna ta sa tana ta kilkila daria ta juya wajen yayanta da yake daria shima tana fada masa hakan ya sa da sauri Umar ya shige motarsa ya tsere
Nan suka shantake da yayanta sunna ta hira tana daria abinta cike da farin ciki
Ba su laila su bar gidan ba sai kusan karfe tara na dare, a lokacin ne ta raka su sannan ta tuna Mami
Da yannayin tsokanar ta nufi dakin da Mami take a labe tana fadin" Ke walahi fitowa zaki yi ki sha iska ina dalili sun saka baiwar Allah labewa a daka "
Yanzunma Mami na jingine da garun dakin idannuwanta lumshe
Bilkisu ta ce" Kin yi sallah kuwa? "
Mami ta gyada mata kai daga zaunen da take
Bilkisu ta yi alwallah ta gabatar da shafa'i da wuturi sannan ta haye saman gadon
A hankali ta jinginar da bayanta jikin garun ta kamo hannun Mami
Mami ta zame ta dora kanta saman cinyar Bilkisu tana rintse idannuwanta da take jin tamkar ba nata ba dan kuwa wani irin nauyi suke mata sosai, haka kuka jikinta ya yi zafi sosai
Bilkisu ta ce" Kin cin abincinki? Kin sha maganinki? "
Mami ta kara gyara kwonciyarta a hankali ta ce" ina jin dadin rabar jikin ki, barni na huta "
Bilkisu ta yi dan shiru hankalinta ba a kwonce ba da yannayin Mami na kin son yin magana , ga kuma irin yanda baki daya jikinta ya kaure da zafi
A hankali ta ce" Wai dama haka ake shiga idan za'ai yiwa mutun aure? Yana shiga haki na rashin lafia da rashin walwala? Yana zama kamar wani wanda zai haukace dan tsoro da fargaba? Kin fara bani tsoro auntyna, shin nima haka zan ji idan Allah ya nuna min ranar aurena? "
Mami ta dago kanta da kyar ta iya buda idannuwanta ta sauke a fuskar Bilkisu, a hankali ta sakar mata murmushi ta dago hannunta na dama ta shafa gefen fuskarta muryarta cen ciki ta ce" Ina son ki sosai, ki yi ta yin biyaya ga iyayenmu kin ji? Sannan ki rage kukan banza, yanzun kuma ki min shiru na samu na huta"
Bilkisu ta sakar mata murmushin itama dan a yanda ta yi maganar tana dan jan habarta sai kuma ta maida kanta ta kara kifawa
A hankali Bilkisu ke shafa gashin kanta da aka kwonce mata da niyar sai a gobe za'ai mata kitso
Itama wani irin nanauyan baci ne ya fizgeta mai matukar nauyin tsiya
Bata taba baci irin haka a zaune a takure waje daya kuma baci mai nauyin haka ba
Bacin cike yake da wasu irin mafarkai na abin al'ajabi, abin tsoro, ita kadai sai kakaba daria take tana neman Mami eai bata ganta ba bayan tana jin maganarta a daf da ita
Ji ta yi an shafa gefen fuskarta da wani abu mai danshi kamar ruwa hakan ya saka a hankali ta ringa buda nanauyan idannuwanta mai cike da baci
A fuskar mahaifiyar Mami ta sauke dubanta, lokaci daya ta ga Mahaifiyar Mami din ta sada kanta
Wasu mata biyu ne suka shigo a firgice sunna nufo su
Bilkisu bata gama wartsakewa da abin bacin da take ji wuyanta ya sangaye mata ta kasa motsa shi da kyau ta ga mamanta ta shigo itama a firgida sauro ta dora idannuwanta a kan hannun matar da aka ce ita ce mahaifiyar Umar ta saka hannayenta tana kokarin daga Mami dake saman cinyarta
Da sauri ta ce" Kai, menene? Kun ga baci ne mukai mai nauyi jikin Mamin ne ya tashi ko kitson ne za'ai mata? Sai kuma ta kai dubanta wajen Mamanta ta ga ta yi baya ta fadi kasa zaune tana toshe bakinta da hannayenta bibiyu, sai kuma ta kalli Mama ta ga mama ta jingina fa garu ta rintse idannuwanta kamar wace take shirin fashewa da kuka
Da wata irin murya matar ta ce" INNALILAHI WA'INA ILAIHI RAJ'UNE "
Da sauri Mama ta juya sakamakon shigowar da Aba ya yi da wani irin sauri bakinsa da kalmar shahada ya nufo wajenda suke
Hakan ya saka Bilkisu zabura tana son mikewa tsaye
Daidai yayanta ya shigo watau HISHAM wanda ya kawo Mama
Idannuwansa a kanta suka sauka, ya cire dubansa da sauro ya nufi wajen da Aba ke ce masa" Ka duba min ita Docter, innalilahi wa'ina ilaihi raj'une wai da gaske bata motsi bata numfashi? "
Tamat
πππππππ Dan Allah ku kara hakuri kun ji.....haka salon labarin ya zo, kuma ba ku kuka ce a baku na kuka ba?βΉοΈ
[7/24, 10:19 AM] BAK'A CE: πΎπΎπΎπΎπΎπΎπΎπΎπΎπΎ
*DUK NISAN JIFA*
_(K'asa zai dawo)_
πΎπΎπΎπΎπΎπΎπΎπΎπΎπΎ
_RUBUTAWA_
*SAJIDA*
*SADAUKARWA*
*GA*
*MASOYA NA*
π«β¨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*π
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_π€
β *[ T.M.N.A]* β πποΈ
https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/
_Bismillahir rahamanir rahim_
23
Dukawa ya yi a hankali ya lalubi jijiyar bayan wuyanta
Idannuwansa ya rintse kafin ya dago su ya sauke a kan fuskar Aba
Aba ya yi gagawar dukawa kusa da ita ya kamo hannunta na dama muryarsa a sanyaye ya kuma furta" Innalilahi wa'ina ilaihi raj'une, Mami rasuwa kika yi ranar aurenki kamar kina baci? Allah ya jikanki Mamina, Allah ya maki rahama "
Bilkisu ta idasa karasowa wajensu a firgice ko dan kwali babu a saman kanta tsabar kaduwa , bakinta ta buda tana kallon Aba, Hisham na kallonta zata yi magana aman ina, gaba daya sai ta shiga jan numfashi kafin a ankara ta tafi
Da sauri Hisham ya tareta ta fado a jikinsa ya rukunkumeta a kirjinsa yana jin numfashinsa na neman barin gangar jikinsa shi dinma, da sauri ya cireta a jikinsa yana shafa gefen fuskarta muryarsa cen ciki yana ambatar sunnanta, sai dai ina ta sume bata ko motsi hakan ya saka Aba idasa rikicewa
Mama na gannin haka ta fice a dakin ta shiga kai kawo a tsakar gidan duda mutane du sun nutsu sakamakon jin abinda yake faruwa, domin tun da sanyin safia kanwar ta Maman su Mami ta shigi dan tafia da Mami dakin da zasu shiryata, sai dai kash ta tarda su a wani irin yannayi Bilkisu kanta a langaye baci take kashirban Mami kuwa idannuwanta kakafe hanunta daya a jirge dayan kuwa cen gefe guda ba alamun numfashi a tatare da ita hakan ya tsoratata ta fice a guje neman taimako
A cikin dakin kuwa gaba daya Aba ya gama rikicewa, mahaifiyar Mami kuka take ta kasa tsayar da kukanta hakama yar uwarta
A haka Umar ya shigo a rikice ya tarda wannan kyauta ta Allah
Kasa ya kai ya jingina yana kuka a fili yana hasasota da irin yanda suke zance bata ko iya hada ido da shi
A wannan rana sun shiga tashin hankali na mamaki, dama haka ake ji? Dama haka ake gani? Sai dai gagarumin tashin hankalin da ya kuma gigita zukata ukun nan shine a lokacin da Mahaifin Mami da Bilkisu ya nuna cewa daurin aure ba fashi, za'a daura auren nan a yau yau bayan jana'izar Mami, adu'ar za'a hade da daurin auren kanwarta da ainahin shi Umaru
A wannan lokacin zukata suka gigice, sun shiga tashin hankalin da ba'a saka masa rana, sai dai gawar dake shinfide ta hanna kowa daga kai bale ya yi masa musu, haka aka shirya Mami aka fita da ita Bilkisu bata cikin hayacinta, mahaifiyar mamaciya na zaune kanta a kasa, Mama na zaune gefe ta rasa tunanin me zata yi a cikin zuciyarta, mahaifiyar Umaru kuwa ta yi kuka ido ya yi mata jajir waje daya kawai ta kurawa ido shine Bilkisu tana tunanin anya wannan bata fi karfin yaronta ba? Uwa uba irin lalurar yaron, wace daga ita sai yayarta suka san da wannan damuwa ta yaron, damuwar dake hanna masa biye biyen yan mata, damuwar da ta yi masa katutu take hanna masa dukan kirji ya kirayi kansa da sunna namiji, damuwar da suka so su aurawa Mami su je su hadu su rufawa junnansu asiri domin itama ta kasa samun miji a shekarunta domin dai kowa ya san y'ayan filani da aurar da yara da wuri
Tsoro, abin rasuwar Mami sun sakata ta zama wata iri sai kawai ta yi zugum jira take su dawo ta fadawa Aban su Mami cewar wannan magana ama barta bata da wani anfani a barta
An yiwa Mami rakiya, rakiya ta dumbin al'umar da suka halarci wannan daurin aure daga bangare daban daban
A lokacin da aka dawo ana gama adu'a aka jone da daurin auren Bilkisu bisa sadaki mai albarka
Duban mutane sun shaida daga nan aka dora da zaman makoki wanda Aba bai samu shiga cikin gidansa ba sai da yama ta yi sosai
Ido hudu suka yi da Mama, wace ta wuni zaune Bilkisu na jikinta, ta farfado aman kamar bata gane wani yaren da ya wuce na bin kowa da ido, uwa uba irin yanda maganar daurin aurenta ya shiga kunnayenta sai kawai ta daga kai ta kalli Mamanta sai ta maida ta kwontar bata kuma dagowa ba
Aba ya kasa karasawa, sai juyawa ya yi da sauri yana neman layin Hisham dan su yi maganar lokacin da ya dace ta tare, shi da son samu ya yi ta tare a yau yau dan baya son wani abin ya kunno kai
Tun da ya dauko shi a mota ya nufi asibiti da shi ya shigar da shi office dinsa ya kwonta a saman gadon marar lafia idannuwansa ke kallon waje daya, ashe ya yi hayaniya ma dama ta bashi? Ashe ya yi fadace fadacema dama ya samu? Idannuwansa sun kyekyashe baya jin komai a zuciyarsa tamkar ta daina aiki
Karin ruwan da aka saka masa sai da ya kare tas sannan doctern ya zo ya cire masa
Kujera ya ja ya zauna yana fuskantarsa a hankali ya ce" Docter, me yake damunka ne? Ka yi hakuri da tambayar da na maka aman ka san kaf niger kai kadai garemu Professor fannin kwakwaluwa, docter idan kana cikin halin damuwa baka aiki, ga al'uma na cikin ciwo, dan Allah idan wata damuwa ke damunka ka yi kokarin shawo kanta ko ka fada mana mu mu hadu mu magance maka ita dan ka dawo normal, idan kuwa baka da lafia ne ka fita waje ka je asibitinku na manya a gama cajeka, likita muna da bukatarka a tare da mu domin ni kaina yarinyata rashin lafiar nan nata na damuna, summa take a kai a kai gashi ka ce ba zaka fasa yanzu ba, dan Allah ka taimaka ka waiwayomu muna cikin halin rasuwa da rayuwa ne"
HISHAM ya juyo da dubansa yana kallonsa, a hankali ya mike zaune yana kai dubansa wajen agogo
Muryarsa a sanyaye ya ce" Ka kawota gobe in sha Allah, yanzun zan je na dauko mamana tana wajen rasuwa "
Godiya doctern ya ringa yi har Hisham ya fito
Da kyar Kader ya bashi ky din motar ya shiga ya tayar ya kama hanyar gidan Aba
Daga kan kwana ya tsaya ya dannawa mama kira
Tana dagawa ya shaida mata ya zo yana kwana
Mama ta mike ta cicibi Bilkisu ta mikar da ita ta saka mata hijab dinta ta juya wajen matar Aba a sanyaye ta ce" Allah ya kara mana hakurin rashin Mami, zan tafi da mai gado in sha Allah dab bata da lafia, daga baya sai a maido ta"
Amsa suka bata duda muryar maman Mami bata fita da kyau, da tausayi suka raka su da kallo har suka fita a gidan
Da ido Aba ya raka su, har sai da suka sha kwana ya mike ya tarda su da dan sauri ya ce" ASMA'U "
MAMA ta dakata ta juyo tana kallonsa
A hankali ya karasa yana kallonta ya ce" Asma'u kin ga yanda