Showing 75001 words to 78000 words out of 180809 words
jiyo sirrinsa domin abu ne mai girman gaske, kuma ta falasa shi haka bai dace ba
Tana zuwa ta tsaya jikin abin ta rage muryarta sosai ta ce" Akoy magani a duniya, na likita ko na hausa , ni likita ce ina so ka je a bincika lafiarka, idan da rabon ka samu lafia a baka magani ka samu lafia, Umaru baka san adadin shekarun da zaka yi a duniya ba, ba kowa zai fuskanci cewar dan baka da lafia ne ka ki yin aure, tuni an fara yi maka mugun zargi duda ba'a iyawa mutun. Aman tafia na tafia darajarka na raguwa, zaka dawo kunci ya yi maka yawa a ranka, ina anfanin ka kashe kanka da kanka? Dan Allah ka nemawa kanka magani ka yi aure, domin sunnar ma'aiki sallalahu alaihi wa salam ce , cikar mutun mutun shine aure "
Tana gama fada ta juya ta fita a shagon ta barshi tsaye jikinsa a sanyaye yana ta auna magangannunta a kan mizani, haka kawai sai ya ji wani kwarin gwuiwa, a kasan zuciyarsa ya ringa tunani to wai me ya sa ba'a nema masa magani ba? Yaya aka yi bai kawo neman magani cikin ransa ba har yake rayuwar kunci? Rayuwar kunci mana ba damar ya saka mace a ransa dan bashi da wannan sha'awar, ba damar ya zauna cikin maza a dauko maganar mata a ringa zuzuta abubuwan da shi bai sanma akoysu a duniyar matan ba, ga abokanansa du sun haihu sun masa sunnan mai ruwan ido tuzuru
Tabas ko an masa shari ba abin mamaki bane domin dai da sana'arsa yana samu sosai Alhamdulilah kidi sunna shigo masa, aman ya kasa yin aure sam baya kuka matan ai dole a yi tunanin maza yake kulawa
Daga nan ta wajen gidan sarki suka bi, daga nesa suka tsaya sunna kallon yanda dogarai ke shiga da fita, sannan suka zagaya ta zagayen baya, a nan suka ga wasu dakaran dogarai sunna gadin kofar sai watsa watsan motocin dake shiga wa'inda sai sun nuna katin dake shaida yau suke da appointment da wajen kwaliyar sannan a basu damar shiga
Ajiyar zuciya Bilkisu ta sauke tana bin tsayin ginin da kallo nan ta kuma goyon Laila suka ringa zagayawa a saman babur kasancewar gidan a tsakiya yake du girmansa sai da Bilkisu ta zagaye aman bata ga hanyar da zata iya dirawa ba, da takaicin wannan suka je wajen mai siyar da dambu ta kofar makarantarsu suka yi zamansu sunna hira Bilkisu na fadawa Laila ta fadawa people zata hau whatsup yau,
Ai kau murna suke , uwa uba da ta ce za'a bude mata Instagram da Facebook du sun yi mamakin yanda aka yi yayanta ya barta shiga Facebook da Instagram.
Kai tsaye ya shigo office din gannin cewar ya gama duba mararsa lafia ya zauna yana kallonsa yauma bai cire takalmin kafarsa ba hakan ya sa Hisham bin kafafuwan da kallo
A hankali ya ce" wai cewa ta yi ta tsane ni fa, to me ya yi zafi in ba rigimarta ba tsakani da Allah? Abinda ya kasa gushe min a raina shine sababin hakayan da take nuna min tun daga jiya har zuwa yau, ko dai dama fada ne da ita har haka? To wai meye laifina a nan? Ko dai itama tana jin abinda nake ji? Abinda ya tsaya min a raina kuma shine a kan me zata damu da wani? Ko dai ya nuna mata wata hanyar da ban dora abina a kai ba? Da kuwa na ci uwashi!"
Kader ya hadiye dariar da yake jin tana son kwace masa ya gyara zamansa ya ce" Wai Hisham da wa kake ? Wace kake zancenta? Ko amarsusunmu ce? " ya karashe yana dage masa gira hakan ya saka Hisham kafe shi da ido
Mikewa ya yi lokaci daya ya karasa wajen kofar ya datse kofar da ky ya juyo yana kallon Kader da ya mike tsaye yana tafa hannayensa yana kallonsa
Hisham ya ce" wani salon iskanci ne yake yawo a kwakwaluwarka da nake son ka zazago shi ko na saka kusa na kunce kan na zazago shi na gyara shi na maida Kader! Ni ka raina kake hawar min kafet da takalmi dan wulakanci? Ba dai amarsusu ba asusu!"
Kader ya yi sauri dukawa yana cire takalman kafafuwansa yana fadin" Allah dai ya baka hakuri, mugun sabo ne ba zan kuma ba"
Hisham ya karasa ya zauna ya ce" zaka bi dukan motsinta, zaka ringa bibiyarta, du wani gaulan da ya mata magana zaka sato min shu ka kawo min shi ka barni da shi, zaka ringa korar du wanda ya so rabarta, zaka ringa yi mata nasiha har sai ta cire wannan sabon hayakin dake kanta, Kader idan wani ya yi gigin yin abin dana sani zan aikata laifin dana sani a kanta na rantse maka"
Kader dai yana gyada kansa dan baya so ya rike shi a hannunsa gaskiya, gashi ya shamace shi ya rufe kofa
Kader ya ciro takarda mai dauke da tambarin gidan sarki ya ce" Hisham, ni ban gane ba, wai so kake sarki ya zo ya kawo maka yaronsa ko gimbiya? Ka san dai ba fitowa zasu yi da rana tsakiya ba dan kawo maka shi ba ko? Kai kuwa ka ce baka aikin dare, ka duba fa rubutu ne na hankali aka rubuto maka cewar idan Har Allah ya sa ka samu lokaci ka je dan duba yaronsu dake fama da rashin lafia, da ace da garage ne zai hauka sai ka ringa masa hanya hanya, ka san da yana da damar baka umarni kuma ka bi ko? Aman sai yake lalashinka dan shi din mai mutunci ne, dan Allah ka taimaka ka je ka ga yaronsun nan an ce yaronsa na farko da ya rasu irin ciwon ya yo, wai sai ya ringa summa ga zafin zazabi "
Hisham ua sauke ajiyar zuciya ya ce" ka gane Kader, ni ba zuwan bane nake ji irin idan na tashi tafia kayan aiki zan kwasa ? Ka ga fa dole sai an bincika duda ina tunanin rashin lafiar dake saka shi hakan aman sai an auna an gani za'a iya yanke hukunci, ta yaya zan iya yin wannan aiki ba tare da kayan aikina ba, ai ba dole sai sun zo ba sunna iya turo masu yi masu hidima da yarron sai a yi binciken a gama, idan rashin lafiar ce a kan magani ne zan dora shi idan abin bai yi tsanani ba, in kuwa ya yi tsanani sai dai a yanke, ban ga anfanin zuwana ba bayan ba aikin zan gabatar ba ni kuwa bani da abin gannin a idannuwana!"
Kader ya kara yin tsam yana kallonsa ya ajiye masa takardar a nan ya juya ya je ya bude office din
Sai da ya fitar da jikinsa da kansa sannan ya leko ya ce" idan kana so kar ka je, in dai sarki Shaheed ne zaka ganshi a wajen nan shima kansa hayakin yake ai!"
Da kallo ya bi shi sannan ya dauki takardar yans karantawa
Kuri ya yi mata yana jujuyawa sai kuma ya kai dubansa kan agogo sakamakon tunawa da ya yi da ita, ya rashi da niyar zuwa ya ganta kafin ya fita aman Billy ta rikita shi ta yada ya manta da ita kwata kwata Allah yana gani
Mikewa ya yi yana cire rigar aikinsa dan ya koma har gidan ya ga yaya saukin jikinta, sannan ya ga Bilkisu
(Shi mutumen da ya san darajar dan adam ba wai dan an maka auren hadi da mace ba zaka wulakantata, da yawa basu so ya je mata ba, da yawa basu so ya bata kukawa ba har ya tsaya ya dinketa ya taimaka mata, shin so kuke ya zama sakaran namiji wawan namijin da bashi da tausayi ko jin kai? Namijin dake take mace ya sa kai ya fice? Dan kawia haya son mace sai ya kasa bata kulawa bayan Allahn da ya halice shi ne ya bashi umarnin ya kula da ita a karkashinsa take, hakinta ne a kansa? π ku ji su, a dai linga jin tsoron Allah ah tomπ)
A lokacin da ya dawo ya tarar da Mama zaune a tsakar gida tana faman gyara miyarta wace take son yin murzajiyar miyar malifiya da kifi
Zama ya yi ya mike kafarsa yana tsince yan hakukunan da take tsincewa sunna hirarsu
Mama ta ce" Ka rafe fushi yarona ka ji? Kwana biyun nan abu kalilan sai ya saka ka daukan fushi"
Murmushi ya yi bai ce komai ba
Mama ta gyara zamanta ta ce" baka tambayeni jikin matarka ba, baka kuma shiga ka ga jikinta ba ka yi tafiarka"
Kansa ya sada yana jin kunyar maman, ita kuwa ta dora da fadin" Ko me zaka yi a duniya ka ringa kiyaye hakin mutanen da kake tare da su, bale hakin iyalinka, Hisham du wanda ya kasance yana muzantawa iyalinsa ina mai tabatar maka bashi da rabo duniya da kiyama domin Allah ba zai barshi ba"
................kumu ci gaba
[7/24, 10:19 AM] BAK'A CE: πΎπΎπΎπΎπΎπΎπΎπΎπΎπΎ
*DUK NISAN JIFA*
_(K'asa zai dawo)_
πΎπΎπΎπΎπΎπΎπΎπΎπΎπΎ
_RUBUTAWA_
*SAJIDA*
*SADAUKARWA*
*GA*
*MASOYA NA*
π«β¨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*π
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_π€
β *[ T.M.N.A]* β πποΈ
https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/
_Bismillahir rahamanir rahim_
29
Hisham ya sauke ajiyar zuciya ya dago a hankali ya ce" Mamana, wai me yasa yanzu ta koyi fada? Ko gigitar rasuwar yar uwarta ne? Wai mama wai a maidata wajen mijinta ji fa abinda take fada ko kunya bata ji"
Mama ta yi murmushi dan sarai ta gane da wa yake ta ce" Uhum dama bata da kunyar in dai mai gado ce, ai du kai ka sangartata, ta fita fa tun dazun"
Shiru ya yi daga yannayin murmushin da yake ya ce" ta fita Mama ? Ina ta je kuma?"
Mama ta ce" Hum, ta ce zata je wajen abanta, abin na mai gado kamar wace take neman fitina kamar wace take hin haushin kowa, ka ga wai rigimar? Ita ba zata ci gaba da karatun likita ba wai kwaliya zata je ta yi"
Mama na fadin abin shashakai ne , shi kuwa abin ya fara shigarsa, kwaliya? Zata bar karatunta ta koma kwaliya? To me hakan yake nufi?
Zai kuma yin magana ya hango mai gadi ya bude gidan
Tsai ya yi da dubansa yana kallo ta danno kan babur dinta, fuskarta dauke da bakin gilas
Duda hijab ne a jikinta aman gilas din ya mahaukacin haska fuskar nata ya wani gyara fuskar
Wajen ajiye babur din ta kai abinta ta ajiye ta sauka tana rike yar karamar jakar hannunta ta cirro wayar dake ciki ta yi niyar nufa falon mama ta hango su zaune saman tabarma tsakiyarsu miya ce ana tsintarta sai wayoyinsa dake ajiye gefe
Gabanta sai da ya fadi irin kyan da ya mata a idannuwanta
A hankali ta karasa ta sasauta daurin fuskarta ta cire gilas din ta duka muryarta na fita da sanyi ta ce" Barka da warhaka, na dawo"
Mama ce ta amsata shi kuwa ya zuba mata shanyayun idannuwansa yana kallonta, shagali watau ko tambayarsa ba'a yi ba, fitsararta take zubawa son ranta
A hankali ta mike ta juya tana cire hijab dinta
Kuri shi kuwa ya bita da kallo, kallo irin na kurulah wanda idannuwansa sun fi sauka a kan mazaunanta
Har ga Allah ba cen ya yi niyar bi da kallo ba , shi Allah yana gani ko a da yakan dan kalla aman baya taba kawowa ransa irin abinda ya shiga ransa a yanzu, tafiar tata a hankali take yi, mazaunanta ba wasu jibga jibga bane madaidaita ne masu tsari sai juyi suke tamkar wace aka zaunar aka koyawa
A hankali ya samu kansa da sauke ajiyar yana datse lebensa na kasa
Gaba daya sai da ta bacewa ganninsa sannan ya tuna a gaban wa yake a zaune, hakan ya saka shi juyo da dubansa a hankali
Ido hudu sukai da Mama, hakan ya saka shi kifta idonsa sai kuma ya dake ya ce" Mamana kina ji? "
Mama ta basar ta ce" ina jinka yarona"
Hisham ya rasa meye zai ce da ita din hakan ya saka shi yin shiru yana jin yanda zuciyarsa ke bugu, kai Allah ya yiwa musulunci albarka da ya zo da tsarin da mata zasu suturce jikinsu kafin su fita , koda a cikin gida ne, shi yanzu da ina zai saka ransa ya ji dadi? Sai kuma ya tuna dukawar da ta yi bata kama sunnan kowa ba , da da ne zata ce 'Hamana barka da gida na dawo, hamana ka ci abinci ko na kawo maka?' Aman rabonta da ta kula shi ko ta damu da bangarensa da share share da kula da cikinsa ba har ta manta, sai mamansa dake kulawa dan safia bata wayewa dare ya shigo bata gyara masa part dinsa ba domin tun da ta turo Aisha ya nuna baya so sai take yi, aman abincinsa Aishar ke kaiwa koda yaushe
Ya kara kamar minti talatin tare da Mama domin har sai da lokacin da zai koma wajen aiki ya kusan yi ya mike ya shiga fallon
Zaune Aisha take tana kallon Bilkisu dake gefe rana hada madara da zuma a cikin kofin kwalba
Tun da ta shigo gaisawa kawai suka yi , ta shige ta yi wanka ta dawo ta zauna ta hade fuska, sam bata bata damar yi mata magana bama bale har su yi hira hakan ya sa Aishar binta da kallo ta kasa yi mata magana duda irin son da take su yi hira
Tsayawa ya yi ya kasa karasawa
Bilkisu na gannin hakan ta mike da abin shanta zata basu guri dan ta tabata wajen matarsa ya shigo
A hankali ya juya yana gannin niyarta ta ratsa shi ta tafiarta?
Ji ya yi ya kasa, bai san lokacin da ya saka hannunsa ya riko tsintsiyar hannunta ya dawo da ita baya yana kallonta ido cikin ido ya ce" Meye? A kan me kike fushi da ni? Me na maki? Dan kawai kin ganni daure da tawul shine zaki ringa fada min mugayen magangannun da ba zan iya dauka ba? Dan Alkah yaushe kika zama haka Bilki am?"
Bilkisu ta yi dan murmushi ta ce" Yayana wani irin fushi zan yi da kai kuma ni a su wa? A kan me? Ko daya ni ba fushi nake da kai ba, idan ka kula a yanzu kai mai iyali ne, ni kuwa koda mun sha nono daya akoy dan bambancin dake iya saka matarka jin ba dadi idan kusancina da kai ya ci gaba da kasancewa a haka , bana son saka matsala komai kankantarta a gidan yayana"
Kalaman dake fitowa daga bakinta daban ne da abinda yake cikin zuciyarta karara yana iya karanta hakan, a bayane yake gane komai dake fitowa daga bakinta idan daga zuciyarta ne ko ta fada dan kawai kar a takurata ne
Dan murmushi ya yi ya saka hannun nasa ya matsota sosai kusa da shi har tana jin hucin numfashinsa, yar yatsarsa ya dora wajen lebanta na kasa
A hankali ya dan shafa shi yana kallon yanda yake pink
Dan murmushi ya yi ya rage muryarsa sosai ce" Ki daina kin ji Bilki am? Ba laifina fa a nan, kuma dan kin ganni da tawul idan kin gane me na aikata sai ki saka zuciyata ta girgiza, a ina kika san yannayin nan? Kin ga na san ranki ne a bace kike haka, na san hankalinki ne a tashe kike cikin wannan yannayin, ki yi hakuri kin ji, irin haka na daga min hankali baki sani bane, kin ga dazu har tafia na yi ban duba matata ba kar ki dauki hakinta mana"
Bilkisu ta lumshe idannuwansa domin maganar da yake wata iska mai dumi dumi ke sauka a kan fuskarta daga bakinsa mai tafe da kanshin fraiz na irin turaran bakin da yake anfani da shi, dumin jikinsa walahi take ji a nata irin rikon da ya yi mata, sai uwa uba ta shiga hakkin matarsa da ya fada
A hankali ta ce" Yaya am? "
Leben nata kawai yake kallo hakan ya sakata dago dubanta ta sauke a kan tsarariyar girarsa mai cika da shegen kyau irin girar fararan larabawan nan da dogon karan hancinsa ta ce" Yaya am, ina son Umar, ka ga ya sake ni ya mayar maka da ni karamar bazawara, ina so a hau kan maganar da malamai suka saba cewar saki uku kai tsaye a matsayin saki daya ake daukansa, ka ga a zamanin mazon Allah aka yi, daga baya ne da abin ya zama ana neman a mayar da lamarin wasa sai aka soke, aman ba wajen da ya nuna ba kyau sai dan kar batanci ya yi yawa, yaya am ina son sa sosai, ka yi magana a zauna ka mayar da auren nan ka ga kaine ubana kai kake iya tsawatawa kar a min illah" ta karashe tana mai cire dubanta daga wajen girarsa da ta ga ya hade tamkar zai hade su waje daya, sai rikon hannunta da take jin ya fara tsaurara, a hankali ta saci kallon wajen Aisha, gani ta yi bata nan hakan ya sa gabanta faduwa, watau daga ita sai shi ta zuba wannan magangannun? Tabdi
Gaba daya nema yake ya fita a hayacinsa idannuwansa kyam a kan lebunnanta, muryarsa yake son daidaitawa da kyar ya iya ciro maganarsa ya ce" .....................................................
Salamπ saura a ce karami ne
[7/24, 10:19 AM] BAK'A CE: πΎπΎπΎπΎπΎπΎπΎπΎπΎπΎ
*DUK NISAN JIFA*
_(K'asa zai dawo)_
πΎπΎπΎπΎπΎπΎπΎπΎπΎπΎ