Showing 138001 words to 141000 words out of 180809 words

Chapter 47 - DUK NISAN JIFA COMPLETE HAUSA NOVEL

sajida   

02 Feb 2025

12988

ikon Allah, dan karamin yaki ne ake zubawa a cikin falon tsakanin mutanen nan baki daya

Mamansa ya bi da kallon tausayi wace ke zaune ta yi gurum tana kallon yadda Larabawan nan ke larabci kowace na fadin nata ga Tati gefe tana kada kafa ta daure fuska tamkar bata taba daria ba, ga Muhammad Kharibullah na zaune yana bin matayen da iyayen da kallo hankali kwonce bai ce komai ba

Sai da kowace ta gama nata sannan Mama ta dan sauke ajiyar zuciya ta ce" A dai yi hakuri, duka abinda aka yi bai dace ba aman kuma hakurin shine ya fi cencenta"

Muhammad Kharibullah ya dubi mama ya ce" Bama wannan ba, wai ni Zannu ke yiwa rashin kunya? Ke zannu nine na mutun? Ai sai ki saurareni ki min uzuri ko? Da kike maganar idan na fito a mutun na fada maki gaskiyar lamari ke din nan ke ce zaki yarda ki rabu da ni bayan mutuwar da kika yi a sona? Kin ga mu yi maganar gaskiya ni bana son abinda zai daga min hankali, kin ga yaron nan ya kulanima na kasa samu yaya kike so na yi? Kin manta shi daya tak Allah ya bani ne? Ko mahaukaci dai ya kalli HISHAM ya kale ni zai gyada kai ya ce ni ubansa ne, kin ga ki daina abu kamar wata karamar yarinya mu fuskanci junna a yafewa junna dan nima kin min laifin kyaleki ne na yi, domin laifin da kika yi min kika yarda min yaro kika tafi idan da biyaki zan yi sai mun ga bakin junna a gidan nan!"


"TO mu gani mana Muhamadu?, ka ga ba ka gama abinda ya kawoka ba? Ka tashi ka kwashi nunanun ranarka da wace ta saka ka watsa mu ku yi tafiarku, da kake maganar na yarda yaronka ai ni ba cewa na yi na mutu ba, kuma wajen yayata na kaishi inda na san idan bai ci ba sai dai in bata ci ba! Kuma tarbiya irin nagartaciya ya samu, dan haka ka je ka kara gaba idan kana so daga nan ka wuce kudus!"

Mama ta ce" Toh fa "

HISHAM ya tabe baki a hankali ya idasa shiga ya ratsa su ya wuce ciki hakan ya sa du suka raka shi da ido kuma hayaniyar ta yi duf

Yana shiga cikin gagawa ya cire manyan kayan nab ya cenza wasu ya dauro alwalah ya fito ya dauki abubuwan bukatarsa ya fito daga dakin

Da mamaki ya kalle su gannin har yanzun da alamun shi suke jira ya kuma tabe bakinsa ya zo zai wuce ya ji muryar mahaifinsa na fadin" Kuma wucewa zaka yi ba zaka saurareni ba Nur?"

Bai yi niyar tsayawa ba har ya kusan fita a tsakaninsu ya ji muryar tsohuwar na gargada ta ce" Haba mijin, ka tsaya ka dube ni shin bana baka tausayi tsufa ya kama ni so kake har na mace baka yafe min ba?"

Bai kuma yi niyar tsayawa ba hakan ya saka mama fadin" HISHAM"

Turus ya yi daga tafiar da yake, mama kuwa a hankali take nazartar yannayinsa, muryarta a sanyaye ta ce" Baka ji ana yi maka magana ne Hisham?, me ke damunka nake gannin kamar hankalinka a tashe?"

A hankali ya juyo inda take zaune ya shiga takowa cikin nutsuwa har ya karaso kusa da ita , muryarsa ya rage sosai wanda hakan ya saka kowa kashe kunne da kuma zuba masa ido ya ce" Mama, bata da lafia sosai baki ji jikinta ba ya dauki zafi sai rawar sanyi take, kuma kin ga bata son ganina ban san yaya zan yi ba, walahi mama ina tsoron wannan sabuwar Billyn kin ga dai tawa bata fushi da ni, ita kuwa tun ranar nan da ta ganni na fito din nan shikenan sai nake fuskantar rashin yarda, rashin tausayina a tatare da ita"

Mamama ta rage muryarta sosai tana kallonsa ta ce" Kar ka biye mata, ka tsawatar mata idan kuma ta so kawo maka raini ka tatakata ta yadda zata gane kai din ba sa'anta bane yayanta ne kuma uba a gareta bale yanzu da ta dauki matsayi na matarka ta yi maka biyaya ko ta kona kanta ne!"

Dan girgiza kansa ya yi a hankali ya rike hannun mama ya ce" Na tatakata na shiga ina kuma? Ni dai ki koya min yadda zan bata hakuri ta daina fushin nan"

Mama ta ringa bin mutanen dakin da kallo domin cikinsu daya ce kawai bata jin hausa fa kyau itama tana tsintar wasu kalaman duka hausar ce bata ji sosai kowa ya kashe kunne ya zuba masu ido yana sauraronsu balema kakarsa wace har dan dukowa ta yi ta yi masu kuri da ido

Mama ta ce" Wannan itace shawarata idan ka yarda ka lalabata ka santa sarai kamar ka izata ne ba zata gane yarenka ba ni dai na fada maka"

Baki ya dan tabe a hankali ya ce" To na tafi"

Mama ta ce" Ina zaka je ne?, kana ganni zaman nan naka ne fa da Mamanka fa"

HISHAM ya ce" zuwa zan yi na dauketa mu tafi asibiti na smduba lafiarta daga nan na kaita gidan namu ta huta kin ga fa ta gaji sosai ga hayaniyar nan da mutane ke yi ni kam ban san me kuma suke jira ba"

"haka muka yi da mamanka daga ni sai ita muka tare abinmu, aman mu an yi mana nasiha ko zaku zo nan na maku nasiha?" Ya fada a dake abinsa hakan ya sa kuma kowa ya kale shi

Hisham ya yi dan murmushi yana girgiza kansa ya kalli mama ya ce" na tafi mamana "

Mahaifinsa ya mike tsaye wannan karron karara tashin hankalinsa ya kasa boyuwa yana kallonsa muryarsa a sanyaye yanzun ya ce" Kai baka yafiya ne?, dan Allah ina rokonka ka sasauta min haka Hisham, ka duba ka ga tun kana dan yaronka na bayana gareka, a tunanina zaka fada jikina da farin cikin bayanuwata a gareka tun da sauran numfashinka? Hisham da uba ake ado ba da riga ba, ka sani na aikata wannan abin ne dan na yiwa mahaifiyata biyaya, sannan kafin na aikata sai da na tabatar na barka a hannun uwa mahaifiya sannan na yi iya yina na bara mata dan abinda zata anfaneku da shi kafin na rarashi mamana, Hisham shin ka manta girman uwa a kan yayanta ne ko ka manta aljanata na karkashin digadigenta? So kake na yi wasa da aljanata ne ? HISHAM a yau ba ita ba ni kaina tsufa ya fara zuwar min domin a yanzu haka ina iya rantse maka ban san kan dukiyata ba, dukiyarka, Hisham dukiyar da take da ita ta ninka tawa kuma ta dora kaso mafi girma a kanka tun bata ganka ba, ka sani kowani bawa da irin tasa kadarar da irin nasa yannayin rayuwar, ka ga fa ita ta nemi a yi haka kuma daga baya ta kasa samun nutsuwa, ka duba mamana na hawaye dan kaunarka, ka dube ni ka dawo gareni na rungumeka a jikina ka fauki dukan dukiyata ka adana domin bani da wani da zai kula bayanka , kai daya na malaka, kai daya Allah ya bani yaya kake so na yi ne? "

Hisham na kallonsa shima muryarsa a sanyayen ya ce" Ni fa ban ga laifin wanda ya yiwa mahaifiyarsa biyaya ba, ban ga laifinka ba, abinda ka yi daya ne ya firgita ni shine ka kashe kanka!, ita kuwa tsohuwar nan sai ta fada min a ayar da aka haramtawa balarabe auren wani yaren bayan nasa!, ka ga ni fa zan zo da kaina har gidan mu zauna da ku duka aman dan Allah yanzun ka barni na je na duba lafiar Bilkisu ka ga rigima take bata son jin komai ni kuwa hankalina ya kasa kwonciya"


Murmushi ya masa ya rage muryarsa sosai ya ce" Kaima haka kake ji ko? To Allah ya kama mana domin mace idan ta gane ana sonta bata da kirki" ya karashe yana wani kai dubansa kan Tati wace take kada kafarta har yanzun kiri take jira ta maida magana

Tunda suka fara magana sai yanzu Hisham ya ji murmushi ya zo masa tun daga zuciyarsa, a hankali ya kada kansa ya yi gaba mama kuwa ta mike da sauri tana kallon tati ta ce" Zainab kin ji wai tafia zasu yi, kin ga mutane a cike baya jin kunyar kar a yi gaba da su? "

Tati ta kaleta ta mike tsaye tana fadin" Bara na raka su dan zan fi sakewa a cen"

Sunna kallonta ta fita hakan ya sa dole mama ta dawo ta kuma zama cikin nutsuwa ta shiga basu hakurin irin dan mirdiyar dan nata da kuma halayan kanwar tata, ta dora da fadin" zasu sake ne daga sun huce in sha Allah "

Murmushi ya yi yana gyara zamansa domin ya yi niya ba zai tafi ba sai sallar juma'a , mahaifiyarsa kuwa da farko niyarta sai ta kai amarya to yanzun abin ya lalace

Zaune yake a motar yana dan duba agogon hannunsa, Kader na gefensa zaune sai mutanen dake bashi kariya na waje tsaitsaye

Kader ya kara sakin murmushi ya kuma miko masa hannu ya ce" Kai barkarmu dai oh Allah mai iko yau Hishamu ya zama mijin Nana"

HISHAM ya bi hannun da kallo wani kayatacen murmushi ya kubuce masa a fuskarsa a hankali ya ce" Alhamdulilah "

Kader ya kara gyada kai ya ce" Kuma yanzun idan muka dauketa ina zamu tafi ko irama mun tare? "

Hisham ya kale shi, wannan barkar da ya masa fa a kadan ta kai ta goma da ya dan juya ya juyi sai ya wani ce oh Allah duniya barkarsu dai, kuma yanzun ya wani tsatsare shi da tambaya bai san abinda yake ciki bane ko meye? Bai taba yi mata biyaya kai tsaye ba sai yau da ta ce da shi ya tafi mota zata kawota aman shiru a kadan sun dauki minti talatin a zaunen nan

Hango su da ya yi ya saka shi rage murya ya ce" Ka nutsu dan Allah ka gansu fa"

Kader ya gyara zamansa yana fadin" Ban taba gannin fitsararen ango irinka ba, yanzun me zaka aikata? "

Hisham bai iya bashi amsa ba har zuwan Tati ta bude baya a hankali ta saka Bilkisu dake cikin abin rufa irin lafayar nan an luluba mata ita

Wani fitinanen kanshi ne ya yi masu salama, kanshi mai hade da na turaran wuta da na ruwa, irin sansanyan kanshin nan ne mai nutsar da zuciya , sai tsintsiyar hannunta fara kal da bata dauke da zanen kunshi ko digo daya da ta fitar a hankali muryarta cen ciki ta ce" Inata, idan mun je cen din ki ce ya dawo da ni da wuri dan Allah "

Tati ta kali Hisham da ya lumshe idannuwansa yana ta kokowa da zuciyarsa da numfashinsa ta ce" Yauwa Hisham idan kun je hayaniyar ta rage sai ka dawo da ita dan bata jin dadin jikinta na ce ta zo ka kaita cen wani wajen ta dan huta kafin taro ya watse "

Bai iya amsawa ba Allah yana gani bakinsa ya masa nauyi, sai kader ne ya amsa yana mai tayar da motar yana gumtse dariyarsa

A hankali ya dauki hanyar asibiti, cen kasa kasa Hisham ya ce" Ka tsaya pharmaci na sayi allura mu wuce gida ba zan iya zuwa a sibiti da ita ba"

Kader ya mulmula kansa ya ce" A kan wani dalili fa? "

Na yi jiran matar mutun😭😭😭😭😭
🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾
*DUK NISAN JIFA*
_(K'asa zai dawo)_
🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾

_RUBUTAWA_

*SAJIDA*

*SADAUKARWA*

*GA*

*MASOYA NA*


💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝

☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_



50


Hisham yi ya yi tamkar bai ji shi ba hakan ya sa ya tuka su har gaban katuwar pharmaci mai sunna NWALA

HISHAM din ne da kansa ya sauka cikin nutsuwa ya nufi wajen Pharmaci din
Bai jima ba ya fito ya dawo bangarensa ya bude ya shiga sannan ya amshi ledar da yaron wajen ya riko masa yana daga masa hannu

Ajiyewa ya yi yana sauraron shashekar kukanta a hankali ya lumshe idannuwansa yana sauraronta Kader kuwa na fafala gudu a saman kwontaciyar kwaltar suka nufi gidan

Sunna zuwa Hisham ya dubi kader muryarsa dai cen ciki ya ce" To koma gidan ka gama bikin ko? "

Kader ya kale shi da mamaki harda rike baki ya ce" Ai ba haka muka yi da kai ba na fada maka na tsara mana wuni da abokanai kuma harma fareeda ta cajeni kudin kitso yanzu in baka je ba laifina zata gani, kuma da kace na je na wuni da mutane yo nine angon hala? "

Hisham ya dan yatsina bakinsa a hankali ya ce" Ai dama ni bance maka ka yi wani wuni na rashin aikin yi ba, kuma farida ta ga laifinka mana ina ruwana, ka ga ka tafi ba zan fitar da ita kana tsaye kana irga min takuna ba dan bakar jaraba!"

Kader ya gyada kansa ya kankance ido ya ce" Ka yi da mutun Hishamu! Da ni kake zancen kuma sai na koma na sa an zo an dauki marainiyar Allah kar a shiga hakinta!"

Shi dai yana kallonsa ya gama bude buden cofre din motar sai kuma ya juyo yana kallonsa ya sasauta muryarsa ya ce" Dan Allah bani kudin kabou kaboun ka ji? "

Hisham ya yi dan murmushi ya karkata ya ciro gaba daya cenjin aljihunsa ya mikawa Kader

Kader ya dan zarro ido da sauri ya yi raf da kudin ya bude ya fita, sai da ya dan yi nisa ya ce" Ka kuwa ga kudin da ka jibga min? "

Hisham ya dan dafe gaban goshinsa kafin da yan yatsunsa ya masa nunin ya tafi

Daria Kader ya yi yana jinjina ya ce" Kai dama kulun ake daura aure ka yi ta bani wannan Allahma ko"

Kasancewar kasan katuwar runfar motocin ya ajiye su ya saka ba rana sai inuwa duda ba mai sanyi bace inuwar aman kuma bata da zafi

A hankali ya sauke ajiyar zuciyar tunanin da ya sha kansa a nitse ya bude ledar nan

Bai ce komai ba ya fitar da yar kwalbar garin allurar sannan ya fitar da ruwan da sering
A nitse ya zuki ruwan ya bale farin marfin dalmar garin allurar ya soka ta saka ya fesa ruwan ciki
Dan jijiga shi ya yi da kyau sannan ya kuma zuka a cikin seringer din sannan ya dora farin marfin allurar ya rufe ya saka a gaban aljihunsa a hankali

Cikin nutsuwa ya buda bangaren da yake zaune wanda hakan ya yi daidai da bugawar zuciyarta domin a jikin kujerar take a jingine idannuwanta lumshe ba wai barci ne take yi ba idannuwanta bude kuma dukan motsinsu tana ji hakama dukan motsinsa daidai da bugawar zuciyarta ne

Bata ji kamar numfashinta zai tsinke ba sai da ta ji ya bude bangaren da take , da sauri da sauri kuma numfashin nata ya shiga bugu, abin lafayar da ta saka ta rufe fuskarta sai ta ji tana neman hanna mata numfashi, gaba daya sai ta ji kofofin hancin nata sunna neman donewa

Da sauri ta saka hannunta ta janye abin tana mai bude manyan idannuwanta tana neman janyo numfashi daga bakinta dan ta daidaita kanta

Gaba daya fuskarta da yannayinta yake kallo daga irin rankwafawar da ya yi a jikin motar hakan ya sa itama ta dago dara daran idannuwanta ta saka cikin nasa

Idan ba gizo take ba gani take kamar gaba dayansa rufowa kanta yake neman yi, hakan ya sa nan da na ta tsayar da dan hakin da take ta kurawa kyakyawan sajen fuskarsa da jajayen lebunansa ido tana gannin yadda yake kara kure mata waje
Bata ankara ba ta ji kamar an mata wani wawan tsimko a cinyarta wajen da bata san a lokacin da har ya yaye mata shi ba har ya tara wajen nama ya soka tsinin allurarsa a hankali ya matsa ruwan ciki

Wani irin ihu ta saka hakan ya sa da sauri ya zare bayan ya gama zuba ruwan allurar ya rufe allurar da sauri ya duka wajen da ta rinrintse ido tana rawar jiki gaba daya tana murzawa da dukan karfinta ya dora hannunsa saman hannun nata a hankali ya dauke ragamar murzawar ya shiga murzawa a hankali tare da hannunta stil yanna kallon fuskarta da lebunnanta da take cijewa har sun kara ja a kan kalarsu ta pink color

A hankali ya lumshe idannuwansa muryarsa cen ciki a sanyaye ya ce" I'm sorry angel, i'm so sorry"

Kuma zubawa fuskarsa ido ta yi wadda ita kanta bata sannin da ta aikata hakan , a hankali yale cire idannuwansa daga cikin nata har ya kai kansa saman cinyoyinta da ya janye doguwar rigar dake jikinta mai santsi da laushi fara kal wace tati ta cenza mata bakar ta jiya

A hankali ya zubawa cinyoyin ido, fararen cinyoyin nata da basa dauke da gashi a jikinsu sai yan hudojin gashishikan wa'inda bata barin jikinta da gashi du kuwa da irin yadda take da saurin fitar da gashi da izgar gashi a jikinta baki daya
A hankali ya dora hannun nasa da kyau kafin ya shiga dan shafa wajen allurar maimakun murza matan da yake da farko

Zabura ta yi a bayane ta ce" HAMMA ya daina zafin zan tashi "

Ta fada tana saka hannunta cike da kunya da tsoro tana jan rigar tata da kyau dan rufewa

A hankali ya dago dubansa ya dora saman fuskarta wadda hakan ya saka mata faduwar gaba sakamakon gannin yadda idannuwansa suke lumshewa haka kuma sunna

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login