Showing 120001 words to 123000 words out of 180809 words
share hawayenta
Aba ya ce" To Asma'u ina hakurin naki ya tafi? Kin san yada alkhairi yake kwuikuyo hakama shari, bana yiwa yar uwarki fatan ta ga rashin adalcinta a kwaryarta aman ai wasa ta yi da zumunci, yaron nan yana kuka da idannuwansa du juriyarsa wace ban taba gannin hakan ba har na rayu da ku na fita a rayuwarku har na dawo kuna masa abubuwa sai yau yana labarta min bayan na matsa masa cewar ita tana yi batama san mijin nata na nan raye da ransa ashe a nan din dai cikin garin damagaram din da bata da wani wawan girma ko mutanen cikinta basu da yawan da balarabe zai bace cikinta, aman balaraben nan dai da na sani Elhaji balarabe shine ashe mahaifinsa? Ai sai ki katse maganar da ta kula tun farko ki nuna masu ba haka bane sannan ki tirsasa su yi mata biyaya domin ta isa da su ba wai ki hau kan zancen ki zauna dan kawai kina gudun ki saki jiki a kan maganar yaron nan, Asma'u idan ba abinku na mata ba har a maki kallon wace ta saki jiki a kan yaron da tun yana zanin goyo take amsa kiran mamansa? Ai ba sakin jiki zaki yi a ciki ba, karbe komai zaki tunda dama naki ne ki aura masa zabin mahaifiyarsa sannan ki aura masa zabinsa, kin ga maimakun hakan sai kika ce da shi shi din aban Bilkisu ne? Abanta fa? Baki ga yanda ya ringa maimaita wai shi abanta, kin yiwa kanki adalci ne ?"
Mama ta ringa sauke ajiyar zuciya tana kallonsa ta ce" To To ni ba zaka ce ba'a min adalci ba tsakani da Allah? Ka duba fa ka gani uwar yarinyar nan a nan take a tare da yarta, ba hakan na damuna bane sai dan irin yanda nake so ya yiwa yarinyar nan adalci domin baka ga yadda take yi masu biyaya ba har shi din, basa tsoron gori ko banzatarwa irin ta d'a namiji sanadiyar wannan abin da suke a kan yarinyar?, ai sai ta koma wani wajen daga bakin lokacin da yarta ta zama matar gidan, ni ba zan kuma zama a wajen da Bilkisu ta zama matar gidan ba ko na wuni ne bale kwana!"
Ta karashe tana cire dubanta a kansa
Aba ya ringa murmushi ya ce" Yar fari ce kike kama sunnanta anya filatanci bai yi maki kaura ba kuwa Asma'u? "
Mama sai a lokacin ta tuna, da sauri ta sada kanta tana jin bakinta ya mata abinda ba shi ba
Aba ya kara yin murmushi gannin ta fara saukowa ya ce" Ba'a yi maki adalci ba Asma'u, ai akoy karra, akoy kunya, akoy cire kai a kan abubuwa, yau koda ba kowa bane a matsayin kudi yaron nan ai bai dace a yi haka na, aman kuma ke din dama dole ki ringa shanye bugu sakamakon darajar da Allah ya baki ta zamowa baba, kina hakuri sosai Asmana ni shaida ne aman kuma haka zaki kara hakurin domin mai hakuri mawadaci ne, baya taba tabewa sai dai ya samu nasarar rayuwa ko yayane, mahakurci zai kai ga ci ne Asma'u"
Mama ta kara sada kanta tana jin sanyi sanyi na shiga zuciyarta
Aba ya ce" Yarinya kuwa mai biyaya, Allah zai dubeta, matarsa ce kuma dan mahaifiyarta na nan sai banzan namiji zai mata gorin hakan duda na san bamu da kirki aman bana tunanin yaron nan zai yi haka sam sam"
Mama ta dago tana kallonsa irin yadda yake bayanin a sanyaye sai ta ji tana samun nutsuwa a kan tashin hankalin da ya dirar mata dazun
Aba ya ce" Kira min Bilkisun kin ji? "
Mama ta gyada kanta a hankali ta mike daga zaunen da take ta je ciki ta yi kiran Bilkisu cewa mahaifinta na kiranta
Bilkisu tana zuwa bata zame ko'ina ba sai daf da kafarsa ta duka kanta a kasa ta raba kan nata da jikin kafarsa muryarta a ciki sosai ta shiga gaishe shi
Bai iya amsa gaisuwar ba sai harara da ya aikawa mama wace ta cire kanta tana tura bakinta gaba , ya girgiza kansa kadan ya ce"Mai gado, ina son na tambaye ki, shin kina son hamanki kuwa? Zaki iya aurensa? "
Bilkisu bata san lokacin da ta dago da dubanta ba, a tsorace ta kale shi, sai kuma ta kalli mama ta ga kanta a kasa yake ta kuma kallon Abanta
Nan da nan ta afka tunani 'Shin kin tabata shi din yana sonki ko kawai shirme baki tafasa bama bale ki kone har kike kokarin nuna shirme a gaban mutane a kan wata wai soyaya? To bari ki ji zamanin da da yanzu ba daya bane, idan kika yi sake sai hamanki ya ja gashin kanki a kasa ya kirta maki abinda baki taba tunani ba domin ya san ke kike sonsa ba inda zaki je ba abinda zaki masa!'
"BILKISU?" Aba ya fada yana taba gefen fuskarta hakan ya sakata dan zabura tana kuma kallonsa ya ce" Kin yi shiru ina magana"
Bilkisu a hankali ta ronga girgiza kanta tana kallon mahaifinta kafin ta buda sanyayar muryarta ta mayar da idannuwan nata kasa a hankali ta ce" Aba bana son sa, bana son Hammana ko kadan, ba so irin na soyaya nake yi masa ba, ina masa so na dan uwantaka, Abana ka duba ka zaba min koma wanene zan zauna da shi aman banda Hamana"
Mama ta ce" Karya kike, hamman ne bakya so kuma? "
Bilkisu ta dago dubanta tana kallon mamanta, a hankali ta gyada kanta ta ce" Mamana, ba zan taba zama da hamana ba, na rantse maki bana so kar a min!"
Tana gama fada ta mike da sauri ta fice hakan ya saka suka rakata da kallo a bayane mama ta ce" Ka ji wani sababin "
Aba ya ce" Kya ce haka mana, ta yaya kike so dama yar ta nuna tana so bayan kin gwagwabran min bakinta, Asma'u haka rikon amanar yake? Gaskiya a bani y'ata na tafi da abina domin a yanzun kin ganta nan mace daya kwal uwa rai ita me da ni kuma ina son abina, ina dalili ji yadda yarinya ke sauke ajiyar zuciya ko tausayinta bakya ji? An ji kunya a gidan nan za'a kashe min yarinya? "
Mama ta saki baki harda dan tare habarta tana kallonsa ya dage bilhaki fada yake an tarru za'a kashe masa yarinya
Aba ya ci gaba da fadin" Dama ta yaya kike so ta fito tana kallonki ta ce tana son wane ai tashin kunya ne, wannan sai ke idona idonki yanzun kin nuna min soyaya?, kin ga ba zata iya haka ba sai dai ta nuna bata so idan ya so ni sai na gane yarenta"
Mama ta ce" Kai aban Mai gado dan Allah ka girma fa kake irin haka"
Aba ya tabe bakinsa sannan ya sasauta muryarsa yana kallonta da yannayi irin na maganar bakinsa mai mahinmanci ce zata fito ya ce" kamar yadda kika ajiye maganar daurin auren yaronyata nan da kwana shida magana na nan, sai fai da yaronki, shin kina da ja da maganar nan har cikin zuciyarki ko kin barwa Allah komai? "
Mama ta sada kanta cike da jin kunyar irin yadda yake dadaureta da magangannu yana sako Allah ciki hankalinsa kwonce bata iya cewa komai ba
ABA ya yi murmushi sannan ya kara sasauta muryarsa yana ta yi mata nasiha ya kara dorawa da fadin" Zumunci? Daga sallah sai zumunci wanda ya yi wasa da shi shi da allahnsa"
Mama ta dan girgiza kanta a sanyaye ta ce" Ni kam na yafe mata, bana so Allah ya kamata, ko kadan, abinda nake so yar uwata ta gane rayuwa ta gane mahinmancin dan uwa da kuma meye datin duniya"
Aba ya ringa gyada kansa kafin ya mike da takalmansa a kafarsa yana fadin" Nima na yarda a maida auren namu rana daya kawai ba komai "
Mama ta mike da sauri tanaai jin matsananciyar kunya ta ce" Jauro aa ni ban ce ba.....
"
Katsewa maganarta ta yi sakamakon gannin motar da Tati ta fita da ita ta dawo ta ajiyeta ba ainahin wajen da ake ajiye motocin ba ta fito ko takalmin kafarta bata saka ba ta nufo su hijab dinta a hannunta
Tana zuwa ta kama hannayen mama dake tsaye turus ta fashe da kuka a rikice take fadin" Da gaske yana raye, da gaske yana raye? Tun yaushe kuka sani, yana kuma cikin garin nan baku fada min ba? Ashe namiji kanin ajali ne ban sani ba? Ashe namiji bashi da amana ban sani ba? Me na masa da zafi? Baro dangina da na yo na zo ma zauna da shi na haihun masa ne laifina ko me? Ko karya yake baya son haihuwar ne ya saka min sonsa ya tafi ya barni? Ashema a cikin garin nan yake? To ta yaya aka ce ya mutu har aka nuno shi da iyayensa sunna kuka? Shin gwomnatim sojoji ta san da wannan maganar cewa yana raye daure masa ta yi ko suna karyar ya masu? Ni ni ni ya wulakanta ya cuta yanzun yake zaune hamshaki da matarsa jinsinsa? Ta yayama aka yi har Aka hasko shi a TV a mace? "
Mama ta dan tsaida yadda take girgizata tana kallonta cike da tausaya mata ta ce" Zainab akwatin gawarsa kika gani a TV ko har shi din aka gwado a cikin akwatin da ake saka su? "
Tsai Tati ta yi da kukan nata tana tunano ainahin abinda ya faru
Gaba daya ta ringa jin iska na yiwa kofofin hancinta kadan
Wani irin jan numfashi ta yi ta so kara fashewa da kuka aman abin ya gagara domin gaba dayanta ta yi baya luuuuuuuuuuuuu
Nace ba yau juma'a ce ko? Dan haka sai atinin ni da ku in sha allahu watau kwana biyu na hutun weekend saura na ji wani ya ce min na yi gagaπππ»ββοΈ
Assalamu Alaikum
Masoyanmu da fatan kuna lafiya.
Muna miko maku godia da fatan alkhairi masu matukar yawa a yadda kuka nuna mana kara da kauna wajen siyan littafinmu na kudi.
Alal hakika munji dadi kuma mun gode sosai Allah ya saka da alkhairi ya kara budi.
Ina kuma kara kira ga masoyana wadanda basu siya ba dasu garzayo su siya domin muhimman darussa rayuwa, ilmantarwa da nishadantarwa dake cikin littafin. Dukkan wanda yaji taken littafin na *AURE YAKIN MATA* yasan littafi ne mai cike da ilmantarwa da bude ido akan irin rayuwar zaman auren da muke a zamanin yanzu don haka babu danasani a siyan littafin.
Yadda kuke siyan littafin yana kara mun kwarin guiwa wajen yi maku typing din littafina na *KOMIN NISAN JIFA* ina fatan zaku cigaba da siye don in samu kwarin guiwar yi maku typing din littafina na kyauta akan kari ba tare da bata lokaci ba.
Na yadda daku na aminta da irin kaunar da kuke mun, nasan kuma zaku siya littafinmu mai take *AURE YAKIN MATA*
*INA SONKU SOSAI INA ALFAHARI DA KASANCEWA A CIKIN DUNIYARKU.*
Ga mai bukatar wannan littafi *Farashin mai sauki ne* naira dari uku (300) kacal ga yan Nigeria, yan Niger kuma dala dari ne (500)π zaka samu wannan littafi mai dubbin darussa a cikinsa.
_Domin tura kudin siyan littafin ga yan Nigeria sai a tura ta wannan account number din *2377403479* Khadija Umar Abubakar. Zenith Bank. Kuma akwai damar tura kati ta wannan lambar *081-686-594-14* IDAN KA YI TRANSFERT SAI KA TURA SHAIDA TA WANNAN NUMBER +227 93 81 16 18._
_'Yan Niger kuma sai ku tura katin MOOV ko Airtel ta dala dari watau 500 francs ta wannan lambar *+277- 94-98-56-52*_
Na yadda daku, na aminta da irin kaunar da kuke mun don hakan ina da yakinin cewa zaku siya don nuna mun kalar soyayya da kaunar da kuke mun da littafainaπ₯°
[7/4, 7:43 PM] +234 803 885 6944: πΎπΎπΎπΎπΎπΎπΎπΎπΎπΎ
*DUK NISAN JIFA*
_(K'asa zai dawo)_
πΎπΎπΎπΎπΎπΎπΎπΎπΎπΎ
_RUBUTAWA_
*SAJIDA*
*SADAUKARWA*
*GA*
*MASOYA NA*
π«β¨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*π
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_π€
β *[ T.M.N.A]* β πποΈ
https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/
_Bismillahir rahamanir rahim
43
Tabas idan aka ce tashin hankalima an fadi kadan, domin gaba daya hankalin mama ya tashi ta taro tati a jikinta a firgice take fadin" Zainab, zainab meye haka? Ke zainab meye zaki sakawa ranki damuwa irin haka a kan namijin da ya watsar da ke? Zainab kar ki min haka, ku uku kawai nake da ku a rayuwata kar ki min haka!"
Dagowa ta yi a rikice ta ce" Malan ka yi wani abu mana "
Ajiyar zuciya ya sauke daga tsayen da yake ya juya ya nufi bangaren da ya tabata Bilkisu na cen
Tana zaune a fallo ta kurawa waje daya ido ya dan yi gyaran murya ya ce" Taso ki ja mota a kai mamanku asibiti na ga ke kadai ce shi kadirin baya nan"
Da sauri ta mike a tsorace ta ce" Aba mama? Mamana? "
Abanta ya kamo hannunta yana dan girgiza kansa ya ce" Eh dayar maman naki maman Hisham, ina makulin motar gidan naku? "
Da sauri ta juya dakinta ta shige da dan fudu duda jikinta ba wai ainahin karfinsa take ji ba ta dauko kys din motar ta fito
Tana zuwa ta tarar da mama rungume da tati tana ta hawaye tana kara kiran sunnnata
A raunane ta rage tsayinta muryarta bata fita da kyau ta ce" mu kamata mu sakata motar mama "
Kai kawai mama ke gyadawa sai a lokacin ta kamata da dukan karfinta Bilkisu ta kama mata suka cicibata suka nufi mota da kyar domin jikinta ya mugun saki dole ta kara nauyi a kan ido bude
Da kyar suka daidaita mata zama Aba na rike da kofar motar sannan mama ta shige ta talabeta a jikinta Aba kuwa ya zagaya dayan bangaren ya bude ya shiga ya zauna
BILKISU ta sauke ajiyar zuciya a sanyaye ta tayar da motar kafin ta dauki hanya
Kwata kwata sai ta rasa ina zata nufa da su, haka kawai ta juya ta nufi wata clinik da su hankali kwonce
Mama da yake hankalinta tashe bata kawo komai ranta ba, batama kula cewar tafiar ta yi wuri ba domin a clinik nandu ta kaisu haka ta talabo kanwar tata a lokacin da likitoci suka fito dab da motar domin ana bude clinik din ake shaidawa likitocin idan abin na urgence ne
Kama tati suka yi suka dorata kan gadon turawa suka gyarata da kyau sannan suka turata
Wani likita ne rike da safar hannu yana kokarin sakawa yake yiwa su mama tambayar me yake damunta, me ya sumar da ita? Shin dama tana suman haka? Da dai sauransu
Mama gaba daya a rikice take sai juyi take ga hawaye sam bata gane cewar ba ainahin wajen aikin Hisham bane a rikice ta ce" HISHAM, ku kira min yarona HISHAM muhamad karibullah, ku shaida masa gamu nan Zainab ba lafia dan Allah"
Mutumen ne ya kara kallonta da kyau, sai kuma ya juya da sauri ya bi bayan likitocin
Jim kadan ya fito ya yafito Aba dake tsaye da wayarsa ya gama kiran Hisham wanda da kyar ya same shi
Aba na zuwa cikin datakonsa ya masa salama
Likitan ya amsa shi da kulawa ya ce" Yauwa, muna bukatar cike dukan abinda ya dace, muna da bukatar samun dukan information na sunnanta, shekarunta da ainahin abinda yake damunta, yanzu an samu an farfado da ita aman gatacen tana kuka hasalima jinninta ke ta hauhawa ta ki yin shiru, ga kuma ita macen ta kasa daina kukan itama sai kuma na ji ta kirayi sunna complet na Professor HISHAM MUHAMMAD KARIBULLAH a matsayin yaronta bayan idan har mamansa ce yaya aka yi suka nufo nan su dake rike da baban asibitin kasar? Nan fa na kudi ne ko shi ya fi kusa ne? "
Mama dake gefe ne ta shiga bin wajen da kallo, har ga Allah ita sai yanzu ta gane ashe ba wajen aikim Hisham suka zo ba
Dubanta ta maida wajen Bilkisu dake tsaye cen gefe da kys din motarta a hannunta fuskarta hade ba alamun kuka ba wata karaya a tatare da ita, in ba dan jin cewa Zainab ta farfado tana kuka ga jinninta ya hau ba da ta je ta kama yar cen ta wanka mata mari ta yadda zata bata kyakyawan bayani a kan kawo su nan da ta yi
Sai dai ina, bata samu wannan damar ba ta ji Aba na mata magana a sanyaye ya ce" Asma'u, ki daina hawayen nan mana ya isa hakanan, ki jajirce ki shiga ki basu dukan bayanan da suka tambaya domin jin mahaifiyar yaron nan ce gaba daya na ga sun juya sunna maganar jininta dake hawa, kece fa baba idan baki daina kukan ba wa kike so ya tsawatar mata? "
Mama ta ringa sauke ajiyar zuciya a hankali ta ce" To, to "
Aba na kallonta ta juya a hankali tana cewa" A ina zan ga inda take?...."
Bai kai ga bata amsa ba wata daleliyar mota ta dano kai balbalin wajen sakamakpn budewar da mai gadin ya yi
Hasken motar da kyanta ya raja'a hankalin mutane da dama a kanta , uwa uba irin parking din da aka yi a tsakiyar wajen maimakun a kai motar cen layin motoci ya saka da yawa suke jira su ga mai tsaron nan ya zo ya kori mai motar a wajen, sai dai ba shi ba alamarshi
Kafarsa ta hagu ya fara fitarwa wace ke cikin takalmi baki sau ciki na fata mai shegen kyau wanda ya rufe yatsutsin kafar tasa da bayan kafar aman ya fitar da kadan daga jikin farar kafarsa kal kal kal da ita
A nitse ya idasa fitowa daga cikin motar sannan ya rufe yana tsaye kikam yana kallon wajen haka kuma idannuwansa na kan mama
Sanye yake da bakin dogon