Showing 72001 words to 75000 words out of 180809 words
shigarki haka ki yi hak'uri, Bilkisu muma jiran lokacinmu muke kin ji? Ki koma makarantarki ki gama karatunki Allah zai fitar maki da miji mai mutuncin ki aura, ni na godewa Allah da ba kowa ne ya san maganar wai."
A hankali tace " Mama, bana son ci gaba da karatun likita."
Mama ta yi tsam tace "Kamar yaya, harda burinki zaki watsar?"
D'ago kanta ta yi a hankali tace "Ba burina bane, burina na zama cikakiyar yar kwaliya, wace ta iya kwaliya da kitso da k'unshi, mama kin san shine burina."
Mama ta yi shiru tana kallonta , Bilkisu tace " Zan shirya ne na je wajen Aba mama na masu sannu da zama, sannan na samu na ga ko zan samu shiga gidan sarki? Mamana dan Allah kar ki hana ni mik'ewa a kan k'afafuwana, ina so na je na samu shiga saloon din gimbiya NAJEEBA, mama ina son na samu ganin Gimbiya ko ta yayane, Mamana ina so ta daukeni aiki, na koyi aiki a hannun matar nan, mamana ina so na yi aikin da nake sha'awa, zan kare mutuncin kaina, zan kiyaye mamana, bayan wannan adu'arki ba zata bari magauta su cin min ba mamana, Allah zan je na samu aiki na yi shi da zuciya daya mamana, ina so na jajircewa kaina, abinda yake tare ni na kawara da shi a shashena zan mik'e na nemi na kaina ta hanyar da ya dace mamana, dan Allah ki kama min na samu ganin gimbiya Najeeba."
Mama ta kamo hannunta tana kallonta tace "...
*Barkanmu da warhaka.*
[7/24, 10:19 AM] BAK'A CE: πΎπΎπΎπΎπΎπΎπΎπΎπΎπΎ
*DUK NISAN JIFA*
_(K'asa zai dawo)_
πΎπΎπΎπΎπΎπΎπΎπΎπΎπΎ
_RUBUTAWA_
*SAJIDA*
*SADAUKARWA*
*GA*
*MASOYA NA*
π«β¨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*π
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_π€
β *[ T.M.N.A]* β πποΈ
https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/
_Bismillahir rahamanir rahim_
27
A hankali Mama ta ce" Ki rufa min asiri Bilkisu, wani irin zaki bar karatun da ya dauki shekara da shekaru yana biya kina kai kawo, karatun da ya bata lokaci yana kashe kudinsa, lokacinsa, nutsuwarsa a kan ki maida hankali ki yi, haba Mai gado shin fushi kike da yayanki ko me? "
Bilkisu ta dago dubanta tana kallon Mama ta ce" Mama, idan kana son mutun ya yi abu ai dama kai ne da hidimarsa, Mamana inaga ba laifi bane dan na je na koyi abinda yake ra'ayina tun farko, kin ga fa shi yake son aikin likitanci har ya saka min a rai, sai na ji yanzun ba zan iya ba dan Allah kar ki ce min aa, kuma kin ga kwaliyar nan sana'a ce, yau idan Allah ya dafa min na tsaya kan kafafuwana zan dauki nauyinki, zan dauki nauyina, zan kula da ke da dukan karfina mama"
Mama ta fara hade fuska da magangannun Bilkisu ta ce" Me kike nufi da zaki kula da ni, zaki kula da kanki? Bilkisu kina tunanin kina karatu ne dan ina jiran ki kawo karfi ki dauki nauyina bayan ga yayanki raye da ransa da lafiarsa, bilkisu ko millionia kika zama kika tunanin zan tashi na yarda ni Asma'u ki dauki nauyina bayan ga yarona? Yau ko mutuwa ya yi na san bani da gadonsa aman ai ana kara ko? Kin ga idan fushi ne kike da shi cen ku karata dan shima a yanda ya fito daga dakinki ya fita fit ko waiwayomu bai yi ba ya tafiarsa na san kun yi fada ne, ki cire komai daje ranki bana so fa"
Bilkisu gannin idan da boren nan zata hau mamanta ba zata taba samun galaba a kanta ba har ta barta ta je ta yi abin nan duda ta so ce mata SHIN KIN TABATA YAR UWARKI ZATA YI MAKI KARAN? sai ta yi shiru kar ta ja su yi fada da mamanma
Sosai ta langwabe kanta ta zauna ta jinginar da bayanta ta ce" Shikenan, bani da Mami ta tafi, yau da tana raye zata saurareni, Zan je na samu Abana mu yi magana ko yayane na ji sanyi a raina domin shi cewa yake bashi da kamar ni, Mama idan karatun likitancin ya zama dole na yi ai sai a hada min da wanda nake so ko? Zan ci gaba da karatuna aman kuma dan Allah mama ki nema min hanyar da zan samu gannin gimbiya, ni ita nake son ta koya min ba wani ba, Mamana dan Allah ki taimaka ki je da kanki da shi ko za'a baku damar ganninta na roke ki"
Mama ta mike ta fita tana ta mitar Bilkisu tana son kaita bango ta yi mata dan banzan duka duka yi kicibus da Tati dauke da tea a hannunta zata kaima Bilkisu
Ido hudu suka yi Tati ta rakata da kallo a bayane ta ce" Wanda ba halinsa ba idan ya dauka shi da kansa gajiya yake, jibi yanda kike haki wai fada ne kike, Allah dai ya baki hakuri"
Mama ta juyo ta harareta ta yi kwafa ta yi dakin da Aisha take dan duba lafiarta da bata abinci
Tati na shiga ta tarda BILKISU tsaye tana shafa turare
Tea din ta ajiye mata ta zauna tana fadin" Ki saka blue din rigar nan zata maki kyau sosai Babyna
Bilkisu ta dauki blue din ta mikar da ita ta saka sannan ta dauko ribom ta zauna ta mikawa Tati
Tati ta shiga caje mata kanta zata saka mata Ribom Bilkisu ta ce" Innata, tun ina karama burina na zama mai kwaliya, sai yaya ya ce ba da shi ba kar na je a lalata min tarbiya, Innata na ga kwaliyar nan ba wani abin mugun abu bane, ba zancen lalalta tarbiya tunda sana'a ce, sai ya kaini makarantar likitoci, abin takaicin bana gane komai a abinda ake mana kulun ina karshe, shine yanzun nake cewa dan Allah a samu a ga Gimbiya Najeeba an ce tana girmama manya ko zata koya min da kanta? Innata ina son na san matar a irin yanda ake labarin yan matancinta an ce yanzu haihuwarta uku"
Tati ta daure mata da kyau ta kama hannayenta ta mikar da ita ta zaunar da ita saman gado tana kallonta ta ce" ke xe bakya gane karatun? Kin san fa sai da na leleka takardun jarabawarku ? , yanzu bama wannan ba kin san sarai gidan sarauta yanda yake yanzun mu samu zuwama sai dai mu kai gaisuwa mu bar wajen, me zai hanna na fitar da ke waje ki je ki koyo kwaliya mai sunnan kwaliya? Idanma bakya son yin nesa ga nigeria kwaliya dai mai sunnan kwaliya ba irin wace basu iya ba, idanma ni kike so na raka ki ko wata biyu ne sai mu tafi mu yi har ki gama mu dawo, aman da sharadin sai kin yi karatu domin bana wasa da karatu ni"
Bilkisu gannin kamar tati zata daure mata sai ta zauna sosai ta ce" Yauwa Innata, ina so walahi sosaima ina so , aman dan Allah ni na Najeebar na fi so dan kuwa ina son na ga na iya zane furkar mata da gyaran kai"
Dan shiru tati ta yi, sai kuma ta mike tsaye ta ce" Zan kwatanta in sha Allah, zan dubo mana hanyar da ta dace mu bi"
Da yannayin sakin fuska da fara'a Bikkisu ta rungumeta ta yi mata godiya hakan ya saka tati jin farin ciki a ranta harma ta fita da sauri tana ta tunane tunanen ta inda zasu bi su samu gannin Gimbiyar
Hijab ta dora sama dogo sosai har kasa sannan ta fita bayan ta dauki yan cenjinta
Ga motarta ajiye, aman sai ta je ta hau babur dinta ta kunna tana duba man dake ciki
Girgiza shi ta yi da kyau kafin ta tayar ta fice a gidan da wani irin gudu
Bata zame ko'ina ba sai gidan su Laila tana fatan Allah ya sa tana nan
Ai kau tana nan, da mamaii Laila ke kallonta ta ce" Ke daga ina haka kuma ina zaki? Ba da ke aka daura aure da Umar ba jiya?"
Bilkisu ta ce" Eh ya sake ni, zo mu je mu gaishe da su Aba daga nan mu je ki kaini wajen da kika san zamu same shi in ci uwashi a kan maida ni bazawara da ya yi!"
Ido Laila ta zarro tana kallonta ta ce" Bilkisu ki rufa mana asiri a garin nan dan Allah, wani irin ya sake ki a kan me yo ko dan ba ke ba yake so? "
Takaici ya kama Bilkisu ta ce" zaki zo mu tafi ko sai na maki abinda ba shi ba ? "
Laila ta juya da sauri fallonsu ta dauki hijab din mamanta wanda shi ya fi kusa ta tarda mamanta kicin ta fada mata Bilkisu ce wai ta fito wai ya saketa zasu je gidan makokin su yi gaisuwa
Mamanta ta masu fatan alkhairi da gargadin kar a jima sosai
Fafara gudu take ko cask babu a saman kanta , uwa uba ko takardu mashin din bashi da shi har suka je gidan Aba
Shi kam da mamaki yake kallonta irin yanda ta mike gar ta fito ko bata ji abinda Umar ya aikata ba?
Gaisawa suka yi sai kallonta yake hakan ya sakata yin murmushi ta ce" Abana bara na gaishe da su mama"
Kansa ya gyada mata ta shige ciki
A cen dinma sun gaisa sai dai sam su maman sun kasa dubanta cikin ido, kamar itace baba sune yaren sai suke sada kawunnansu hakan ya sakata kure mama da kallo, a kasan zuciyarta tana ayanna' ba zan taba jin haushinki ba, domin ke din ke kika haifi Mamina, kuma Mamina ta dauko kamanin fuskarki, ba zan taba daina kaunarki ba dan ke din abin kaunar Mamina ce'
Sun dan jima a gidan kafin su fito
A bakin baban layi suka tsaya sunna zanen wajen da yake zama
Babura babur din ta yi ta fara nufar bakin tasha, wajen matataran samarin yan kasuwan
Sun je cen basi same shi ba , an ce da su baima fito ba yau dan haka suka karkata suka dauki hanyar shagonsa
Sun tarar da shagon a rufe aman ba kwado a jiki, hasalima kamar da abin fanka duda ba motarsa a waje
Bilkisu ta yi tsai tana bin kofar da kallo sai ta sauka ta je ta tsaya tana kallon yanda aka rufe kofar
Dukan karfinta ta saka ta aniya tura kofar hakan ya sa kofar ke jijiga daga ciki
A tsorace Laila ta ce" Ke Bilkisu kar ki sa a yi zaton barayi ne mu a kama mu dubi fa ana kallon mu"
Bata bata amsa ba sai ci gaba da ta yi da jijigawa
A firgice ya ce" Wai waye? "
Bata bashi amsa ba ta ci gaba da jijigawa hakan ya saka shi mikewa da sauri ya dauki sandarsa ya karaso ya bude yana shirye da shirin ko ta kwana
Gabansa ne ya yanke ya fadi da sauri ya ja baya jikinsa na bari bari yana kallonta
[7/24, 10:19 AM] BAK'A CE: πΎπΎπΎπΎπΎπΎπΎπΎπΎπΎ
*DUK NISAN JIFA*
_(K'asa zai dawo)_
πΎπΎπΎπΎπΎπΎπΎπΎπΎπΎ
_RUBUTAWA_
*SAJIDA*
*SADAUKARWA*
*GA*
*MASOYA NA*
π«β¨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*π
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_π€
β *[ T.M.N.A]* β πποΈ
https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/
_Bismillahir rahamanir rahim_
28
Bilkisu ta bi shi da kallon sama da kasa kafin ta shiga bin shagon da kallo a bayane ta ce" Bakama san safia ta yi ba ko? "
Da sauri ya zauna dan daga shi sai dan gajeran wando a jikinsa yana ta mamatse kafa dan har fitsaro yake ji ga tsorata shin da ta yi, dan Walahi bai taba kawowa ransa ganninta ba a duniyar bale wai har a gabanshi da safiar nan
Bilkisu ta yi tsaye jikin dogon abin da wayoyi ke ciki ta rungume hannayenta a kirjinta ta ce" To yaya zaka yi da ni? "
Kuma dubanta ya yi sai ya sada kansa hakan ya sakata da karfi karfi ta ce" Ba da kai nake ba UMARU? "
da sauri ya dago da kuma mamaki yana kallonta, muryarsa a shake ya ce" Ban gane yaya zan yi da ke ba Bilkisu, hala Aba bai fada maki sakona ba?"
Bilkisu ta masa kallon uku dala ta ce" ashe vaka da kuzarin kawo min gwa da gwa sai dai ka aiko ubana ya kawo min? An fada maka nima dan ina sonka aka daura mina aure da kai? In ba dan mutuwa mai saba lamura ta dora su yanda take so ba Umar ina ni ina mijin da yayata zata aura? Mami ta so ka da zuciya daya , tana jin kunyarka tana kaunarka da a haka ka yi niyar aurenta? Ka ce da ita me? Ka halaka min ita dan bata magana? Allah daya da a lokacin zaku gane mahaukaciya ce ni baki dayanku! Ka godewa Allah da Allah bai baka damar cutar min da ita ba, da ba abinda zqi hanna ni nemanka lungu lungu ko ni ko kai!"
Kunya ce ta ringa kama shi da mamakin ashe haka ta iya masifa? Dama ta iya fada haka? Kuma ta san dalilin da ya saka shi sakinta to me ta zo yi shagonsa? Dan ta masa gargadi?
Bilkisu ta sasauta muryarta ta ce" An ce maka dan wannan abin nake iya zama da kai, ina iya zama da kai Umar ko dan soyayar da yayata ta yi maka a duniya, ni ban san komai ba bale ya dame ni! A kan me zaka watsa kin kasa a ido ka min saki irin na wulakanci har saki uku? Bama wannan ba kai kennan ba zaka rayu ba haka zaka zauna kana bakin rai da kumbiya kumbiya ba zaka nemarwa kanka magani ba ko dai da gaske ne sharin da aka ce ana maka a gari cewar da maza kake harka? "
A zabure ya kuma kallonta har wata zufa na sin keto masa ya ce" Ashe baki da kunya Nana? Kina bafilatana kina sakin magangannu haka daga bakinki me na maki to ni? Na ga dai ba soyaya muke ba bale ki ce na yaudare ki da soyaya, ko yayarki kin taba gannin mun yi kalaman soyaya da ita? Bari ki ji mahaifanmu ne zasu hada mu wai dan mu rufawa junna asiri a bar kallona a matsayin wanda ya kasa yin aure, itama a bar mata kallon ta tsufa bata samu miji ba! Ni babu yar wanda na je na yaudara na furta mata kalmar so ko na bata mata lokaci dan na san bani da lafiar da zan iya rayuwa da mace, Namiji kuwa bana cikin wa'inda Allah ya dorawa kula maza Alhamdulilah, Balki da yarintarki, da kyanki, da mutuncinki da gatanki kike fada dan na baki damad rayuwa mai kyau? Dan Allah ki yafe min idan nine na saka kika fara fada haka, idan kuwa dama mafadaciyar ce ki min hakuro kar ki yi fada da ni dan ba zan iya ba walahi"
Bilkisu ta sada kanta tana jin hawaye ya cika idannuwanta
Dago dubanta ta yi ta nuna masa wata watsetsiyar waya kirar samsung bata ce komai ba
Cirowa ya yi daga cikin madubinta ya miko mata yana kallonta, bai taba tsayawa ya yi mata kallon tsaf irin na yau ba, kai da ace zai samu lafia da ya ringa yiwa mata kallon tsaf har ya samu wace ta kwonta masa a zuciya, da ace bai saki Bilkisu ba da ya nemi lafia ko ta halin yayane ya zauna da yarinyar nan a matsayin mai dakinsa, ashe haka take da kyau?
Atm dinta ta miko masa bayan ta gama jujuya wayar bata ce komai ba
Amsa ya yi yana kall9n ATM din sai ya mata murmushi ya ce" Ashe hajiar mai kudi ce, to ni sai dai idan baki daya kudin ciki zan wawashe"
Dubanta ta tsaida a kansa ta kasa yin koda murmushi ne hakan ya saka jikinsa ya kara yin sanyi ya miko mata cart dinta yana kallonta
Bilkisu ta shanye kukanta ta ce" Baka anfani fa abin cirewa ne?"
Ajiyar zuciya ya sauke ya dan girgiza kansa ya ce" ina yi, aman na baki kyauta Balki, ba zan saida maki waya ba gaskiya"
Bilkisu ta kalli wayar, ta kuma kallonsa, a hankali ta kai hannunta ta ajiye wayar zata juya ya ce" Dan girman Allah ki dauki wayar nan ba dan na isa ba sai dan ina son wanke kaina, ki yafe min, ki yi min uzuri, ban yi haka dan na wulakantaki ba ko dan na lalata maki sunna ba, bama kowa ya san cewa igiyar wani ta hau kanki ba, na katse hanzarin nan ne dan karma sai kin tare duniya ta dauka kuma na dawo na rabu da ke ta yada duniya zata dauka, ke yar uwata ce , zan so mu yi zumunci mai karfi"
Bilkisu ta juyo tana kallonsa ta kuma sauke dubanta a kan wayar, bata taba amsar sako daga hannun wani namijin da ba yayanta ba, bata taba anfani da wayar da ba yayanta ya siyan mata ba
A hankali ta dora hannunta ta dauki wayar tana ji a ranta zata iya amsa ta fara anfani da abin hannun wani namijin da ba yayanta
Dubanta ta dago ta sauke a kansa ta matsa sosai dan tana wajen kofa ne bata so Laila ta