Showing 90001 words to 93000 words out of 180809 words

Chapter 31 - DUK NISAN JIFA COMPLETE HAUSA NOVEL

sajida   

02 Feb 2025

12984

ne a wajenka, kai ka samu abinda kake so ba batun karya ka samu ka more, saima ka ringa wani jin sanyi na wahala bayan ba cewa ya yi da kai ya yarda da muradinka ba!

A hankali ta kuma sauke ajiyar zuciya muryarta a sanyaye ta ce " Mama ce ta aiko ni "

Dan dakatawa ya yi daga kokarin daura necktie dinsa a hannunsa yana kallonta, aman bai ce da ita komai ba, mama? Wace mama? A tsakiyar daren nan ko wani ne ba lafia? Hakan da ya fadawa kansa sai ya ji hankalinsa na neman tashi

A hankali ya ce" Wani ne ba lafia? "

Da sauri ta girgiza kanta, sai ga hawaye wani na korar wani, ta hade hannayenta ta ce" Wai, wai Papana ne zai samu matsala da wajen aikinsa, shine ta ce na fada maka "

A yanzun ya kara tarkata mata hankalinsa gaba daya yana kallonta dan jira yake ta gama ga wani kuka da ta aura tamkar mai makokiya a ciki

Gannin shirun ya yi yawa sai kuka take masa ya saka shi cewa " Wace irin matsala? Ni kuwa mai zan iya yi a kan matsalar? "

Sai da ta sauke ajiyar zuciya ta yi zaman dirshan ta ce" Walahi ban sani ba, ta ce kana iya samun President a kan maganar kar a sauke shi, sai da nace da ita ba zaka iya ba sai ta koro ni....." ta karashe tana mai fashewa da kuka abinta dan har ga Allah ita ta rasa madafa, to ita tama san ta wani bayan layi zara biyo ra masa bayani ne? Ita fa burinta bai wuce ta ji ta samu sukuni a zuciyarta ba

Bai ce da ita komai ba sai ya juya mata baya ya daura necktie dinsa da kyau sannan ya dauki rigarsa ta sama ta saka ya bala mabali daya tak na tsakiya ya soka hannunsa na hagu cikin aljihun wandonsa ya kuma kallonta ya ce" na bara maki dakin a bude ne? "

Da sauri ta girgiza kanta domin kallonsa take itama sannan ta mike tana share hawayenta ta fara yin gaba

Takalmansa ya saka bai dauki komai na aikinsa ba ya bi bayanta a hankali tana tafe yana biye da ita har suka fito

Fitarta kawai ya hanga sai rufewar da mai gadi ya shiga yi na get din gidan, ya hangi da hijab dinta ta fita hakan ya saka shi dan sauke ajiyar zuciya ta babura babur dinta yau yar babur din ce
Murmushi ne ya ji ya subuce masa a kan lebensa sai ya fasa shiga bangaren nasu domin dama dan ya fitar da ita su tafi ne hakan ya saka shi kamo hijab din Aisha

Juyowa ta yi tana kallonsa shima ita din yake kallo ya ce" Ki daina kukan kin ji? Ki share hawayenki sannan ki yi adu'a Allah ya sanyaya maki damuwarki kowace iri ce "

Ajiyar zuciya ta sauke tana gyada kanta hakan ya saka shi sakar mata dan murmushin da ya sakata lumshe idannuwanta itama ta mayar masa da martani sannan ta share idannuwanta tana tsaye Kader ya dawo daga bangarensa da jakarsa da wayoyinsa ya wuce wajen motar ya shige ya zauna yana binsa da kallo

Sai da ya nuna mata ciki ta shige sannan ya juyo ya nufi motar yana taku da dan sauri cikin sauka a matatakalar bangaren Mama tamkar wani jarumin indiya ya karaso kusa da motar da ya ga yau kuma hyris ya fitar shi dai ya bude gaba ya shiga ya rufe

Ko idasa zama bai yi ba Kader ya bushe da wata shegiyar daria yana dukan sitiyarin motar wace sai da Hisham ya yi dan tsai dan ihun dariar sai da ya dakar masa kai ya juyo yana kallonsa

Kader ya gumtse dariarsa ya tayar da motar yana kara gyara zamansa ya yi kum kamar ba shine yanzun ya sha daria ba

Sai da ya kaishi balbalin asibitin Hisham ya bude ya fita Kader ya leko kansa ya ce" Gani na yi ashe kaima ka iya iskanci wollah sai wani lumshe ido kake kai ga zakara a gaban kaza ko? "

HISHAM sai da ya yi tsam dan walahi mamaki ne ya kusan halaka shi ya juyo ya ce " Kadri nine zakaran? "

Kader ya tada motar da sauri ya shiga yin ribas yana kallon irin tsayuwar da Hisham ya yi a fili kader ya furta" A yau ka ciri cin uwa kader kana zaman zamanka "

Kai ya girgiza ya nufi ciki ya san zai bada kayansa a kawo masa ne
[7/24, 10:19 AM] BAK'A CE: 🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾
*DUK NISAN JIFA*
_(K'asa zai dawo)_
🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾

_RUBUTAWA_

*SAJIDA*

*SADAUKARWA*

*GA*

*MASOYA NA*


πŸ’«βœ¨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🀝

β˜† *[ T.M.N.A]* β˜† πŸ“–πŸ–ŠοΈ

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_


35


A yau baki daya karatun da aka yi a makaranta sai da ta tsaya aka yi da ita ta samu dukan abinda ta rasa na kwana biyun nan a USB dinta sannan ta rubuta na rubutawa inda Laila ta bata wa'inda ta rubuta mata duka ta hade kayanta waje daya har aka tashi karfe daya da rabi sannan ta haye babur dinta da jakar computerta da dan jan bakin da ta sako a ciki ta samu ta kurta dan jar ta je mata haka bayan shekaran jiya ta mata maganar hakan

Tana nuna takardar nan aka amshi babur dinta aka yi masa waje sannan akai mata jagora

Biye take da dogarin har sai da ya kawota wajen jakadiya sannan ya juya itama jakadiya ta mata jagora har bangaren da NAJEEBA ke hutawa tare da kanwarta daya tana yiwa yarta wasa a cikin lilonta

Tun da ta shiga ta gaisheta Najeeba ta amsa mata da kulawa sannan ta nuna mata wajen zama tana binta da kallo

Zaunawa ta yi a saman kujera Najeeba ta kalli kanwarta ta ce" Ki dauko min kayan nan da na nuna maki a cen saloon "

Mikewa ta yi ta dauki alkyabarta ta dora ta juya ta fice

Wayar Najeeba ce ta dauki kuka hakan ya sakata dagawa a hankali ta ce" Allah ya taimaki babanmu, Allah ya taimaki baban yaya "

Daga cen ya ce" Najeeba, yau mai rabani da ke a gidan mijinki sai Allah, sai na tataka ki yar rainin hankali, yanzu Najeeba a kan me zaki ce mata wai na yi budurwa bayan ke kika ce zaki min budurwa? To budurwar ta gidan uban wa? "

Najeeba ta kalli Bilkisu ta ga tana zaunenta jakarta a kusa da kafarta ta wani nutsu uwa tana gaban malan ta dan yi murmushi ta ce" Umumum yaya Dayabu ka hanna zagi fa "

Dayabu ya yo kwafa ya kashe kiran yana fadin" idan na zo sai na kutuntuma maki wanda zai gigita ki "

Tana kashewa ta kara gyara zamanta tana murmushi ta latsa number mijinta wanta ta tabata yanzun sun fito a masalaci kuma baya shara'ar rana kai tsaka du inda yake yana kishingide ko Nadia na bashi kulawa ko bai nemeta ba

A hankali ya ce" Muradinki nake ki zo yanzu "

Sai da ta kara rage murya sosai ta ce" Yau fa Nadia ce ko ka manta Shaheed? "

Idannuwansa ya lumshe ya ce" To dan yi min umuah mai zafi na ji "

Murmushi ta yi ta ce" Kanwar docter na zaune kuma wayar nan ana jinka fa? "

Bakinsa ya tabe bai ce komai ba hakan ya sakata kara gyara zama ta ce" Wai yaya ne zai zo ya dake ni "

Kishingidarsa ya gyara ya ce" Me kika yi ne Beebah? "

Sai da ta cuno bakinta daidai kanwarta ta kawo kayan tana kallonta ta ce" Ka ga fa, matarsa ce kawai take neman fitino da fitina kala daban daban kuma shi sai yake fadawa Zahra, ita kuwa sai take fada min, ni kuwa sai nace in haka ne na masa mata har nake ce mata yaya gide ya yi budurwa shine fa inaga ko dukansa ta yi oho ka san shi da son mace shine yanzun inaga ya kamo hanya zai zo ya dakar maka mata"

Sultan ya yi dan murmushin zanen nata, ya tabata idan za'a zauna abinda ta aikata ya fi haka, shi yasa ta takaita sosai kuma tana yi tana dan sakar masa yannayin da ta tabata zai tsuma shi bayan yanzun tace ba zata masa kis ba kanwar likita na zaune

A hankali ya ce" to yi mini Ummuah din "

Najeeba ta gyara zamanta ta kara make muryarta ta ja wani dogon kissss mai ratsa zuciya ta sakar masa harda wani dan gurnanin iya shege wanda ya saka Biliisu da sauri ta dago ta zuba mata ido cike da mamaki sai kuma ta yi sauri sada kanta cike da kunyar abinda ta yin

Sai da Najeeba ta gama hankali kwonce ta ce da kanwarta" Ki dauko min dinkin da baki tana sakawa ba na ga kamar zaku yi yannayi da anmatan docter "

Kuma kallonta Bilkisu ta yi ta kara sada kanta

Murmushi NAJEEBA ta yi ta mike ta koma kusa da Bilkisu tana fadin" Mahaifiyarki ta san da maganar koyon kwaliyar ko? "

Bilkisu ta gyada kanta

Najeeba ta shiga waware kayayakin dake ajiye wa'inda Bilkisu ke kallo cike da farin ciki a zuciyarta

Wata doguwar riga ce ta shigo da ita da dan kwalinta mai dan tsayi kadan ta kawo ta ajiye sannan ta kama habarta ta ce" Wai wannan zumbulelen hijab din fa aunty Najeeba ko dai daga makarantar islamiya take? "

Najeeba ta kalli Bilkisu tana murmushi ta ce" Yayanki ne ya dinka maki su ko? "

Bilkisu ta gyada kai da mamakin yaya aka yi ta gane?

Najeeba ta ce" Yayanta ne ya dindinka mata, kuma shi ya hannata kwaliya kin ga wannan jan bakinma yanzu ta shafa shi dan ba madubi aka shafa jan bakin nan kuma idan daga gida ne ya ci ace wani wajen ya dan gogoge"

Bilkisu ta saki baki ta ce" Lah "

Najeeba ta girgiza kanta ta kama hijab din Bilkisu ta cire shi gaba daya, batai aune ba sai ji ta yi ta dungure mata kai tana fadin" Ba dai zaki daina yiwa jiran gawon shanu biyaya ba ko? Walahi ina takaicin abubuwa da dama a rayuwar yayanmu na hausa, watau tun daga cikin gida muke fara nunawa cewar Namiji ubanmu ne, sai ki ga wai dan ana soyaya ko dan kawai ka kawo kayan yarinya har ka dora mata dokoki irin na karta fita koda aiken iyayenta ne sai ta nemi izini a wajenka, kar ta saki ta yi kwaliya bayan ko shafa fatiha ba'a yi ba, kar ta yi kaza kar ta yi kaza, watan abin takaicin ba zai tashi kashe ki ba saima kin buda ido kin ga baya tsinana mata uwar komai sai bakin rai da bakin haki dan ubanta tamkar an ce da ita shi daya ya rage a maza ta zo ta nace ta nuna masa bata san ciwon kanta ba, bata san darajar kanta ba, da shegen biyayar karya biyayar da bata cika yiwa iyayenta ba sai darjejen kato ka gannin ubanta ya zo wanda ya yanka mata ragon sunna shikenan jiki na bari wane ne ya ce kar na yi, wane ne ya ce na yi maza maza na yi, ko ki ga ana iya yi a bakin murhu za'a yiwa saurayi girki, saurayin da bai baki dala ba du ki kwashe yan kayan miya su inna ki hada da su shinkafa komai ki tatara dan tanadinki ki siyo naman da baki ci kika more ba ke ga yar banza wace aka yi asarar haihuwa kawai ki dafa masa ya more ya gyatse ya mike ya kada tsatsaman rigarsa ya bara maki waje kina sakin lebo ya na saniya kina daria ke mai saurayi zamanin nan yana bani takaici kamar na kama yayan mutane na yi ta zanewa!" Tq karashe tana sakin tsakin da ya saka Bilkisu kara wara idannuwanta a kanta cike da mamakinta

Najeeba ta kalli Bilkisu da yanda ta yi sai ta saki murmushi ta ce" Kanwata walahi yau ba da ke nake ba fa, aman dan Allah ina son tambayarki, shin yayanki ya taba furta maki kalmar so? "

Dirshan kanwar Najeeba ta yi wace suke uba daya yar gidan matar da aka sha rigima da maman Najeeba ce ta talabe habarta tana jiran amsar Bilisu

Bilkisu ta sada kai tana ayanna yau na kawo kaina wani wajen kuma na mamaki,

Najeeba ta dora hannunta saman nata ta ce" Fada min?"

Bilkisu ta dan girgiza kanta ta turo bakinta nan da nan yannayinta ya cenza ta ce" Bayan aure ya yi, mamansa ta ce wai mun sha nono daya, kuma sai mama ta ce haka ne, sai aka aura masa bakuwarmu, ni babu komai tsakaninmu yanzun, ya yi aurensa cen ni bana sonsama"

Najeeba ta yi murmushi ta ce" Karya ne "

Bilkisu ta dago yanzun tarr tana kallon Najeeba

Najeeba ta kara yi mata murmushi ta ce" Tashi ki shiga cen ki yi wanka ga tawul nan dan mu dan gyara fuskar ki ko? "

Tashin ta yi, duda bata san a kan me za'a sakata wanka ba aman ita da ta zo koyo sai ta kasance mai yin biyaya domin bata ga an kauce hanyar da zata ki yin biyayar ba

Wanka ta salo ta fito da tawul din a jikinta da kuma wanda take goge ruwa a jikinta tana son daukan hijab dinta

Najeeba ta kamo hannunta ta zaunar da ita tana kallon yannayin tsarin idannuwanta da girarta

Abin goge gira ta dauka ta shiga goge mata sauran jagirar da ta yiwa kanta a jiya wada bata idasa fita ba

Sai da ta goge mata ita tas sannan ta fitar da hodar ruwa

Budewa ta yi a gabanta ta ringa nununa mata har sai da aka samu wace zata hau da kalar fatarta sannan ta jika abin shafawar ta matse shi da kyau ta dan dangwali hodar ta shiga shafa mata ita sama sama ba tare da an kwambala da yawa ba

Sai da ta shafa mata da kyau ta kama ko'ina sannan ta dauki hodar gari ta dora mata ita a sama

Jagira sabuwa ta mika mata ta ce ta saka a idonta

Nan Bilkisu ta so darzawa sai Najeeba ta rike hannunta ta shiga koya mata yanda zata saka ba tare da ta bata hodarta ba

Tana gamawa Najeeba ta ciro gashin idon da ta fitar ta saka masa gam ta dan busar da shi tana kallonta ta ce ta sada dubanta kadan kar ta rufe idannuwanta

Hakan kuwa ta yi Najeeba ta saka mata gashin idon nan sannan ta dauki jagira mai ruwa ruwan nan baka ta dan ja mata a saman idon wajen gashin idon hakan ya saka ya zauna dasss ya kara fitar da idon masha Allah

Cikin nutsuwa ta caje mata girarta da kyau ta daidaita mata ita sannan ta bata dan jan baki mai ruwan lebanta ta ce ta shafa

Shafawa ta yi tana kallon madubi cike da mamakin simple mak'up din yanda ya wani irin fitar da fuskarta ko dan bata cika kwaliya ba?

Sai da ta gama sannan Najeeba ta ce ta saka kayan nan ta maida daurin da ta koya matan nan

Ai kuwa ta warware ta saka rigar da ta kamata dam bale wajen duwawun dan ta fi mai dinkin duwawu

Sannan bata saka bra ba aman kasancewar dinkin mai gidan mama ne sai ya taimaka ya gyara mata su ya kara tsayar da su dama da pant dinta ko da ta yi wanka ta maida abinta a bayi

Gashin kanta ta shiga warwarewa Najeeba dake kallonta ta saka Kanwarta gyara mata shi

Ai kuwa ta caje mata shi gaba dayanta ta yi mata kasa da shi sosai sannan ta saka mata dan karamin ribom ta tufke mata shi ta mata jela daya tak da shi sannan ta bata dan kwalin

Gyara zama ta yi ta kashe daurin nan na zara buhari wanda shine daurin da Najeeba ta koya mata ya hau ya yi das da shi ga gashin idon nan da ya hau fuskar abin ba'a cewa komai

Najeeba dake zaune ta saki murmushi tana kallonta ta ce "kalli"

Bilkisu ta juyo tana kallonta

Najeeba ta koma kadan ta dan gyara zamanta ta shanye idannuwanta sosai sannan ta shiga dago su a hankali har ta idasa dago su ta wani dan juya su kadan sannan ta sauke dubanta a kan Bilkisu ta yada kamar ta ajiye mata abu ne a kanta irin ajiye duban nan tana kallonta ta dan yatsina bakinta ta ce" Maimaita na gani? "

Bilkisu ta sauke ajiyar zuciya, anya zata iya wannan abin kamar ba mutun ke juya akalarsa ba?

A hankali ta ringa kwatantawa, ta yi ta kwatantawa Sunna mata daria har Najeeba ta ce" kallon nan ba wani abu a cikinsa na rashin kunya, idan bakya iya yinsa ki samu wani abu special a gaban madubi wanda kika san idan kin yi yana sakawa a kalle ki sai ki rike abinki, irin idan abu ya baki mamaki, ko ya baki daria maimakun ki bushe da daria aa, sai kin fara dan gabatar da shi sai ki dan saki murmushi kadan, Bilkisu zamani ne ya cenza ta yada ake tafia da kidansa, gyara kuma ba aibu bane in dai zaki rike mutuncin kanki"

Bilkisu ta sauke ajiyar zuciya tana dan yin murmushi

Najeeba ta ce" To matso ki ga mu fara aikinmu, zan ringa yi a fuskarta sai na goge kema ki maimaita min, yanzun dai daga gira zamu fara, zamu yi kamar yi hudu shikenan sai kuma gobe mu dora "

Hakan ta kasance a wannan lokaci, cikin Nutsuwa Najeeba ke koyawa Bilkisu tana kallo, tun tana dari dari har ya zamana ta wani irin sakewa da Najeeba da irin kalamanta, duda har yanzun takan yi mamakinta sai dai kuma wani abin mamaki sai take jin tana da abubuwan dauka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login