Showing 129001 words to 132000 words out of 180809 words

Chapter 44 - DUK NISAN JIFA COMPLETE HAUSA NOVEL

sajida   

02 Feb 2025

12980

Wa ya fada maki? Kin jima da sani ne? Ashe kin san du haka kika zuran ido? Me yasa kika kyale ni ina hauka Aunty? "

Mama ta dan ja hannunta dan ta damke shi da karfi ta ce" Ta yaya kike son na sanar maki bayan number da zan iya samunki ta ita kin yi blosck dina? Bara ki ji, a lokacin da maganar fitarsa waje ta fito abin ya bani mamaki, ba komai ya saka haka ba sai irin makudan kudin da aka ambata cewar gwomnati ta bashi, tun ban saka rai da zai samu ba har na ga abu na tafia ziryen ziryen ba gargada bayan an saba manya na danewa ko su raba tsakiya, kamar da wasa albashinsa ya fi na da yawan masu kudin dake aikatuwa sunna dauka jinna, a hakan ya sa hankalina ya tashi, na kasa zaune na kasa tsaye , shi kansa na titsiye shi kan yaya haka
A nan ne ya ringa nema min hanyar da zata sada ni da shugaban makarantarsu,
A kadan mun dauki wata muna neman kadaituwa da shi kafin muke samu, a ranar na masa bayanin ina son karrin bayani domin ba zan dauki yarona na tura shi kasar waje karatun da ban biya ba ban ga halin biya ba harma a ringa bashi albashi, a lokacin ne ya dubo takardunsa yana dubawa ya bamu labarin wai da HISHAM MUHAMMAD KHARIBULLAH? , ai mahaifinsa MUHAMMAD KHARIBULLAH shi ne a kan komai nasa, a lokacin ya zuba zunzurutun kudade na kula da shi sannan shi ya shige masa gaba a harkar fita hakinsa da kwazon yaron ya saka hankalin manya karkatowa kansa"

Mama ta dan sauke numfashi dan ta ja sheda a lokacin ta ga ashe mahaofiyqr Aisha zaune take tana karkada kafa tana kallonsu, ta dora fa fadin" Na firgita, na tsorata, na ji mamaki a lokacin da aka samu da kyar muka samu ganninsa, mahaifin Hisham naki shine ELHAJ MUHAMMAD KHARIBULLAH , mai kampanin madarar BALARABE, mai gidajen sabulai na ruwa da na omo, mai kampanin magi, shine wannan hamshakin da ganninsa aiki ne ga sauran duniya, wanda bayan dawowarsa ya komawa gwamnatinsa sanadiyar yanzun ya zamana mutuncinka aljihunka hukuncinsa na wara biyu kawai ya yi a gidan yari shima dan su tabatar idan ba aiko shi aka yi ya yi binciken kasa ba, bayan sun yarda da hujojinsa da na mahaifansa suka so bashi kaki, a nan ya kiya domin dama ya shiga aikin soja ne dan ra'ayi, sai dai kash, jinnin dake gudana a jikinsa shi yake gudana a jikin yaron cen, ba yadda bai yi ba dan ya saurare shi aman HISHAM ya kiya, karshema a cen ya baro ni sai kawo ni aka yi wancen gidan,
Ban taba sannin yana da zuciya haka ba sai da ya ce ya ajiye karatun ba zai yi ba, idan na takura zai bar min garin,
A lokacin na yi anfani da damar nan na ringa cusawa Bilkisu kaunar likitanci a zuciyarta, domin shi burinsa idan ya je ya zama soja baban soja ya gaji mahaifinsa sai dai tunda ya ga mahaifin nasa a raye shima ya tafi ya barshi ne sai kawai ya ce shi yanzun bashi da wani burin zama soja, ba zai zama ba,
Wasa wasa na samu ta dauki lamarin, ta nace har zazabi take tana ce masa hammana ina son likita, ina so na zama likita kuma idan na girma zan auri likita,
Ya sha maimaita maganar idan ta girma zata auri likita, ni dai ina gefe ina adu'a ina nasiha
A ranar da suka zo har gidan cen da tsohuwar kakarsa a ranar na ga taurin rai, domin ba yadda bamu yi ba ya dubeta aman ya kiya, karshema a gabansu ya ce shi mahaifinsa ya rasu, hakama danginsa, su barshi ya huta bashi da wani abin so a tatare da su!
Mahaifinsa na kallonsa yake tambayarsa ina mahaifiyarsa ne?, a gaban kakar ya ce "Ta ce na daina damunta da kira, na tafi na nemi na kaina itama ta kanta take, ta bara mana gida mu yi tallah mu ci abinci! Ka ga wannan..........ya nuna ni ya dora da fadin" itace uwata! , ita na sani, ita ke saurarena, ita ta san wahalata, ni dai ita na sani, itace uwata kuma ubana! Idan umarni ne nata zan bi domin ban yarda cewa ba itace uwata ba sai dan abu daya jal da nake da buri a rayuwata!"

Mama ta dago dubanta da idannuwanta da suka cika da hawaye ta ce" Ban taba jin haushinki irin ranar ba, sai naga ribar me kika tafi ci ta duniya? Shin kin manta ana haihuwar sarki da shugaban kasa ne ba shuka su ake ba? Shin kin manta cewa idan har arzikin ne ba sai kin je kin zubar da ahalinki ba in dai kina da rabon yinsa zaki yi? ZAINAB walahi sai na ji bana jin haushin mijinki dan ya yiwa mahaifiyarsa biyaya , a nan na yi anfani da damata a kan yaron nan, na yi masa umarni ina zubar da hawaye , na masa umarnin da baya so, na saka shi amsar abinda ya ce ba zai amsa ba, ya amsa yana hawaye yana cije lebensa jikinsa na rawa, a nan ne na yarda da soyayar da kika haramta bayan Allah ya halata, domin yana kukan nan tana farawa ya ringa share hawayensa yana sakin zancecekun da sam baya cikin hayacinsa, yana fada mata ya daina ba zai kuma ba ta yi shiru zai je ya zama likita ya dawo yana sonta ta daina kuka"


Mama ta share hawayenta tana kallon Tati dake kuka kashirban ta ce" Dangi sunna da daraja, da yawa idan suka bada baya sai dai su dawo su birne nasu, wata tafiar mai daraja ce, watan kuwa asara ce, baban tashin hankalin tafiar da zaka yi ba uwar ba ribar, shi yasa wani sa'in yawon bashi da anfani, ZAINAB lafia tana da anfani a jikin dan adam, duniya kuwa na cike da abubuwan al'ajabi , a jiya na maki magana kan Bilkisu ba ita ba yaron cen ko? Na yi ne dan na dan zaburar da ke, kuma na ga ya yi anfani domin har kin gane yarena! A yanzu maganar da zan fada maki ita ce *AUREN BILKISU DA YARONA RANAR JUMA'A DA SAFE, KODA NA MACE NE A DAURA SHI KAFIN A KAINI MAKWONCINA KODA BILKISU TA MACE NE A DAURA MATA SHI IDAN ANA YI KAFIN A BIRNE TA, IDAN KUWA BAKI YARDA BA KI JA KURTU DA KAMBUNKI NA UWA MAHAIFIYA A KAN YARON CEN NA GANI!*"

tana gama fada ta mike ta bi ta gefen da mahaifiyar Aisha ke zaune ta gama cika ta yi pam tana kallon mama da wani irin kallo har ta bacewa ganninta

Tsaki maman Aisha ta ja ta sauko kusa da Tato dake dan girgiza kai tana hawaye tana sharewa ta zauna tana kallonta ta ce" Zainab, a duniya baki da matsala sai wannan matar da yarta! Wai dama haka take maki wannan abin aman a gaban danki kamar wata zata hadiye ki tana rarashinki tana janki a jiki? Ki duba ki ga gidan nan yanda yake da girma da dakuna da arziki a cikinsa, aman kema wace ta nakudo yaron cen ta haifo shi baki da wani iko da komai , komai sai an baki yadda nake da daki daya haka kema kike da daya a gidan nan, kin ga idan baki yi da gaske ba fa tana iya korar ki a gidan nan domin idan har kika yarda kika bari aka aurawa Hisham Bilkisu kin janyowa kanki matsala, dan malake yaron nan zasu yi sai yadda suka so da shi walahi ki kiyaye!"

Tati na kallonta ido cikin ido da wani irin kallon da sam bata gane meye ma'anarsa ba, sai dai gannin kamar tatin ta tsaida kukan nata ta kuma tsura mata ido tana kallonta ya sakata gyara zamanta ta ce" Ke kike da iko da shi, ba wanda ya kaiki dama a kansa, ba wanda ya isa ya saka shi abinda kika hanna shi yi du duniya kama daga mahaifinsa har ita wannan, ta yaya zaki zauna bayan cin amana da rufe maki maganar mijinki wanda yake daya daga cikin mutun dari biyu na manyan kusoshin duniya baki daya sannan a zo ana maki wani dadin baki da magangannun da basu da kai basu da kafa a kuma maki gargadi kan kar ki yarda ki hanna? Idan kika hanna me zata iya yi maki? Ina ji ba haihuwarki ta yi ba, yau mahaifiyarki kun rabu lafia bale wani ya maki wani abin ya kama ki, dan haka ki tashi ki tsaidawa kowa ruwan miya a gidan nan a bar maki tunkaho ke da gidan danki!"

Ta karashe tana dan daga muryarta dan mama ta jita domin ita yanzu banda haushin maman nan ba abinda take ji, ina dalili mata da shegen iya yi gashi ta isa da yaron domin daga ta fada masa yake hawa ya zauna daram a kan maganar, uwa uba abinda ya fi daga mata hankali jin wai ashe Hisham dan MUHAMMAD KHARIBULLAH daya cilo ne? Bayan nasa arzikin ashe gada ya yi? Ina zata iya bari a yiwa Aisha kishiya? Ai su yanzun likafa ta tashi idanma ana so a sauke mijinta a aiki basu da faduwa domin su suka dace da siriki!
[7/4, 7:43 PM] +234 803 885 6944: 🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾
*DUK NISAN JIFA*
_(K'asa zai dawo)_
🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾

_RUBUTAWA_

*SAJIDA*

*SADAUKARWA*

*GA*

*MASOYA NA*


💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝

☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_



46



Tati kallonta kawai take, sai da ta dasa aya kafin ta mike jiki a sabule ta bi hanyar dakin mama, hakan ya sa mahaifiyar Aisha sakin kayatacen murmushi a kasan zuciyarta cike da farin ciki sannan ta mike ta yi waje dan kiran mijinta ta sanar masa wani sabon labarin, wannan abin ya saka mata tunanin dawowa garin DAMAGARAM da zama domin ita kam inda take gannin maiko maiko cen ta fi wayo

Tati na shiga dakin Mama a hankali ta karasa kusa da ita tana zaune bakin gadonta kanta sade

Gaba daya ta duka kasa itama kanta sade muryarta na rawa ta ce" Dan Allah ki yafe min, ki yafe min, walahi na yarda cewa ni din mai son kaina ce, ni butulu ce kuma ina mai neman yafiyarki domin na rantse maki da Allah na jima cikin duhu ban san cewa a duhu nake ba sai a dazu da na koma tsohon gidan cen na ringa neman hanyar da zan ga MUHAMMAD KHARIBULLAH abu ya gagara, gani ga motocin da yake ciki ina hangen datijon dake ciki aman masu tsaronsa sun mana katanga, ashe haka ake ji? Ashe a banza nake ihu? A lokacin da na ga gawarsa a tv sai nake gannin komaina ya kare na jin dadi neman kudi kawai zai fitar da ni, hakan ya saka na kasa gannin ni'imar dake tare da ni watau yaron da Allah ya bani da kuma ke yar uwata kwalin kwal da gareni, kin ga yau duniya ta koya min hankali, kin ga inada rabo da alamu tunda har Allah ya bani wannan dama, sai dai ban san ta yaya zan gyara laifukan da na aikata ba, ban san ta ina zan bi na gyara ba"

Dago kanta ta yi tana kallon mama ta ce" Yaya mu'amalata da iyayena ta kasance? Yaya aka yi suka yarda suka aura min? Shin tsorona ne ya saka ko kaunata ce ta hanna masu tsawatar min?, na shiga ukuna da ciwo a zuciyoyinsu a kaina suka rasu? "

Da sauri mama ta kamo hannayenta tana dan girgiza mata kai ta ce" Zainab ba zaki fasa kukan ba ko? "

Tati ta fashe da wani irin kuka tana fadin" To ni ai ina sonsa, shine ya wulakantani? Ai sai ya fada min gaskiyar lamari da tun a lokacin na san mahinmancin iyaye da yan uwa kau? "

Mama ta yi murmushi tana kallonta ga kuma hawaye na diga a idannuwanta ta ce" wani lokacin sai na ga kamar wata yar baby idan kika yi wani abin Zainab, ki daina kukan nan haka mana"

Tati ta ringa jan hanci tana kallonta ta dora kanta saman cinyarta a hankali ta ce" Na yi karambani da na shiga hurumin Hisham, walahi bani da kunya, na so kaina, kudi kudi kudi kuma har yanzun na kasa tarawa sai kame kame nake, da kyar nake iya biyan haya da yar kurkurar motata aman na kasa fahimta , Aunty wai har kike cewa idan zan hanna, Aunty Allah ya jarabeni da son Bilkisu so mai tsanani, kin ga ko ke na ga kina mata fada haka nake ji zuciyata na yin sama tana kasa, kwana biyun nan da ta yi tana kuka labewa nake na sha kukana domin a raina nake jin kukan nata, kin ga na yi karyar kuma ta dawo min, to ni koda shi yayan bai yanke aurensu ba ai ni zan je na nemo mai daura masu domin daga yau nima na gane kuma na mike ba mai shiga hurumin iyalina"

Mama har tsigar jikinta ke tashi dan farin ciki, da sauri ta rungumi yar uwarta a jikinta tana mai jin dadin wannan rana, kai ita gwara da aka yi haka, ga dukan alamu zata ga ribar hakuri

A cikin mota shiru suke tafe ba mai yiwa dan uwansa magana, tun da Hisham ya saka Aisha a bayan motar ya koma gidan gaba ya zauna ya fadawa Kader ga inda zasu je Kader kw tukinsa hankalinsa a bakin titi

Kowa da abinda yake sakawa a cen kasan zuciyarsa, Aisha na tunanin rayuwarta da irin juyin da ta zo mata, gata dai yau zaune a bayan mota kusa da mutumen da zuciyarta ke bugawa kamar zata tsinko ta fado idan ta ganshi, bayan ita shaida ce irin kallon da yake bin watanta da shi, uwa uba irin zazafar soyayar da yake mata, aman a haka ta yarda , ta ji ta gani harma suka kasance abu daya da shi, gashi yanzu yau da kwana uku zai dauko sahibarsa, shin yaya uta tata makomar na kutse a cikin masoyan nan biyu zata kasance?
HISHAM kam a hankali yake dan juya agogon azurfar dake yatsarsa ta tsakiya yana dan kallon agogon motar yana dan girgiza kai, to me take nufi da ni ne? Me ya sa ta he ta kwana gidan mutane kuma safia ta yi bata dawo ba? Shin ta san da maganar aurenmu? Yaya ta dauki abin? Shin yaya zamu kwashe da sabuwar rigimamiyar kanwata?......uwa uba idan ya tino da kalmar aure sai ya ji zuciyarsa ta masa wani irin yam yam yam ta yi fadi sai kuma kunya ta kama shi, wai yanzu a nan gaba yana iya mikewa zindir a gabanta? Yar billynsa fa? Yaya zata dauki wannan lamarin? Kar dai ta suma........ dan murmushi ya yi yana girgiza kansa daidai Mai gadi ya wangale masu babar kofar makeken gidan da akaiwa Aisha jere

Sunna tsayawa Aisha ta fara budewa ta fita tana mai bin wannan aljanar duniya da kallo

HISHAM ta madubi yake dan kallon yadda take jujuyawa tana mai yin murmushi domin gidan ya birgeta ainun

Kader ya dan yi gyaran murya ya ce" To wai abinda nake ta tunani shine, zuwa muka yi ka dan zagaya ko me? "

HISHAM ya juyo da sauri yana kallonsa, ya ce" Na zagaya ina? "

Kader ya dan yi murmushi ya ce" To ba aure gareka ba, gashi ka dauko madame kai ga irin mushe, ka hakimce kana murmushi ni dai na san ba'a kawota ba, na san zaka maida masu yarsu sai a hada biyu a kawo maka , ko dai a matse kake ka zo ka dan zagaya kafin a kawo su? "


"KAN UBA" Hisham ya fada a lokacin da bai shirya ba

Da sauri ya yiwa motar lock ya juyo ya shaki kwalar Kader ya ce" Kai yau in ba sai na maka iya shege ba ni ba HISHAM bane! Yau na ga jaraba na zagaya gidan uban wa wai ni Kadiri birin wasanka ne ni ko me? Hawana kake ina sauke ka, so nake na gama da rikicin zuciyata a nutse aman kana min kutse idan na zagaya haramun na yi ne?,"

Bubuga gefen da ake ne ya saka Hisham dan waigawa , ganninta tsaye ya saka shi sasautawa Kader matsar da ta saka shi fifido idannuwa yana makaki

Sakinsa ya yi ya juyo a hankali ya zuge madubin motar wanda baka iya gannin na ciki sai dai shi ya ganka , a yannayin da fuskarsa yake ya kalleta hakan ya saka ta kara nutsuwa a sanyaye ta ce" Mitar na ga tana lilo shine na ce ko lafia? Ko ba a nan zamu sauka bane na sauka?"

Dan shiru Hisham ya yi yana kallonta kafin ya laluba aljihun rigarsa ya ciro kys ya mika mata da kyar ya iya buda bakinsa ya ce" Je ki bude gani nan zuwa, "

Amsa Aisha ta yi ta yi gaba abinta, hakan ya saka suka rakata da kallo

Hisham ya juyo ya ce" Kai kadiri baka jin tsoron rawar kan yarinyar nan kuwa? Ka ga fa na ce mu je ba dan ta tirje irin a rakotan nan, kuma mun zo na bata Ky ba irin ta kiya sai na bude matan nan, bara mu ga ikon Allah hala kokowa zata yi da wannan kwadon mai gardama "

Kader ya yi kuri yana kallon yadda Aisha ta kama kwadon nan kikikiki ta bude shi da karfin balaki a tare suka kalli junna suka maida kallonsu tas ta bude dakin ta yi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login