Showing 3001 words to 6000 words out of 180809 words
ta tsinci kanta da mugun kwadayin son ta shiga cikin wayar ta ga me ta kunsa
Tarin document ne na karatun likitanci, kama daga na baban likitan mata da bangaren kwakwaluwa
Fita ta yi tana dan yatsina bakinta ta ajiye wayar a kasan zuciyarta tana ayanna 'wayoyin yaya ba komai sai karatu'
Sosai suka kara shiga wani aikin na gagawa, farkawar ba ta dadi bace hakan ya sa suka kara bankawa marar lafiar allurar baci wace ke gushe bawa daga hayacinsa baki daya
Sai da suka kuma bude kan suka ga wajen dinkin ne ba'a dinke da kyau ba, dan haka ya ki barawa abokin aikin nasa da kansa ya shiga sake dinkin cikin nutsuwa da maida hankali har sai da ya gama komai aka goge marar lafiar sosai aka mayar da ita dakin da za'a ringa duba dukan motsinta
Fuskarsa hade ya kai dubansa kan abokiyar aikin nasa wato docter Rukaya ya ce" na sauke ki daga kan aiki a kan terrain har sai kin koma kin yi stage na tsayin shekara guda , ki sani da ba dan an ga matsalat nan da wuri ba da jinnin nan zai idasa shiga cikin kanta ne ya hadasa mata dayan biyu, ko haukacewa ko mutuwa, sake na likitoci kan iya janyowa patient matsala, bama mutuwar ake tsoro ba, aa, wahala! Ki cutar da ita, sannan ki cutar da mu, ba da ni za'a yi haka ba! "
Irin yanda yake fada sama sama ya saka du suka nutsu sai da ya gama ya cire safar hannun ya karasa wajen abin zuba datin ya taka da kafarsa ya bude ya zuba su ciki ya rufe ya juya ya bara masu office din ranshi bace
Yana fita suka kaure da maida bayanin laifin na docter ne ta godewa Allah da ba dakatar da ita ya yi ba, ta koma ta kara koyan aiki kafin ta dawo dan kuwa docter HISHAM MUHAMMAD KHARIBULLAH baya tolerat din irin haka, sam baya so ana wasa da lafiar patient, hakan ya sa ya yi fice a aikinsa, ya zama zakara, ya zama tamkar gwal, irin yanda ake burin aiki da shi ko a samu ya gabatar da aiki abin sai hamdallah
Irin yannayin da ya rufe kofar da dan karfi ya sakata zabura daga bacin da ya ringa sandarta sakamakon dogon lokacin da ya dauka a cikin dakin tiyatar
Da sauri ta kai dubanta wajen agogo, gannin har dare ya yi haka ya sakata turo bakinta ta zauna da kyau tana gyara rigar dake jikinta
Bai mata magana ba sai bayi da ya zarce, ya wanke hannunsa sosai ya zubawa fuskarsa ido a hankali ya zuba ruwa yana wanke fuskar nasa har ya ji sanyin ruwan na ratsa shi sosai sannan ya fito domin baya so ko da wasa Bilkissu na ganninsa a yannayin bacin ran da ba ita ta hadasa masa ba
Kys din motar ya dauka ya kai dubansa kanta
Mikewa ta yi dan kuwa ta san ba magana zai yi mata ba, da idannuwan nan nasa tamkar bakon kurma haka yake nuni, haka kuma take gane yarensa
Tuki yake cikin nutsuwa, ita kuma ta kwontar da kanta tana jin sanyin AC din na ratsa gaban jikinta
Wayarsa ce ta shiga ringin
Sarai ya san mamansu ne, dan haka ya ki dagawa ya bari su karasa dan kuwa sun kusa
Sunna karasawa ta sauka sai cika take tana batsewa ta yi bangaren dakinta
A hanya suka hade da mamansu wace ke tsaye tana kai kawo
Da kallo mai kama da harara ta bita hakan ya sa jiki a sanyaye ta shige dakinta ta daura alwallah dan gabatar da shafa'i da wuturi
A hankali ya ringa takawa yana nufa ta wajen da take tsaye ta hade fuskarta
Yana karasawa ya sakar mata lalausan murmushi yana kara kallon kyakyawar fuskarta da ta hade ita a dole fushi take
Hannayensa ya daga cike da gajiya ya kama kunnayensa yana kallonta ya ce" Ki yi hakuri Maman HISHAM "
Baki ta murguda masa ta dago hannunta daya ta ce" Yanzu Hisham shine ka tafi ba tare da kader ba? Wai yaya kake so na yi idan magauta suka cin maka ne?, ni kam aikin nan bana so, sam bana son fitar kowani lokacin nan, tunanina yau idan ka yi aure ka zama magidanci matarka zata iya wannan abin koda yaushe miji ya ficewarsa sai kin ganshi? Ni kam kowani aikin likita ne haka ko me? Yanzu haka baka ci komai a cikinka ba, duba ka ga time dan Allah "
Murmushin dake kan fuskarsa bai gushe ba ya kara sasauta muryarsa da yake jin ta masa nauyi da yawa ya ce" Mama, ke ke cewa aikin lada na yi ta yi har zuwa fitar numfashina, kuma yau kin gaji da fita aikin ladan nawa ?"
Kwal kwal ta ringa yi da manyan idannuwanta wa'inda BILKISSU ta gada a wajenta ta kasa bashi amsa, yaron ya gama sannin lagonta, ya gama karantar wajen da idan ya fada bakinta ke mutuwa murus sai kawai ta bi shi da kallo har ya shige falonsa kafin ta bi bayansa ta yi serving dinsa da kanta sannan ta fito ta nufi dakin BILKISSU
Irin yanda ta tarar da ita ta nutsu da litafin adini a hannunta tana karantawa Ahlari a bayane
Zama Mama ta yi ta mika hannunta ta karbe litafin sannan ta kara hade fuskarta sosai
A hankali ta ce" *BANA SON NA GA KINA BIN YAYANKI A IRIN WANNAN LOKACIN DA IRIN SHIGAR NAN MATSATSIYA MAI GADO, DOMIN KUWA SHI DIN BA MUHARAMINKI BANE* "
BILKISSU ta karashe karshen maganar a saman lebenta dan ta san me maman nata zata fada domin wannan kalamai na mahaifiyarta koda karatu ne ya ci ace ta kawo harda ya zauna mata daram a cikin kwakwaluwarta,
Mamanta ta dora da fadin" A wannan zamani, du uwa ta gari ya dace ta saka idannuwa a kan y'ayanta da suke ciki dayama bale wa'inda basu fito ciki daya ba, ba zan gaji da fada maki cewar ke din mace ce, mutuncinki idan ya zube an gama, ba zan gaji da nuna maki kaunarki da son saka kananun kaya na damuna, ba zan gaji da kara tunatar da ke cewa yayanki ba muharaminki bane BILKISSU"
Kanta ta sada a sanyaye ta ce" Mama, asibiti ne muka je, tunda muka shiga ya yi tafiarsa wajen aiki sai fitowar nan da muka yi , yau komai bai siya min ba yana ta fafara gudu na tabata yana so ya yi ya maido ni ne, mama In Sha Allah zan ci gaba da kiyayewa, zan kare mutuncina da dukan karfina "
Ajiyar zuciya uwar ta yi sannan ta mike ta fita ta nufi dakinta dan zata shiga salolinta na dare ne kafin ta kwonta baci
Ya jima zaune bayan ya gama cin abincinsa ya shiga wayarsa ya shiga duba document dinsa na aiki
Ya jima yana kara dube dubensa, da sababin magungunnan da suka fito wa'inda aka bayar dan a gwada dukansu ya rubuta a baban litafinsa da niyar a gobe gobe zai samo su ya kadaice kansa ya yi nazari a kansu
Karasowar Kader rike da leda ya saka shi sauke ajiyar zuciya ya mike a hankali ya amshi ledar ya fito
Sai da ya je dakin mamansu ya yi ta salama, sai dai jin shirun da ya yi ya saka shi barin wajen dan ya tabata ta yi nisa a bautar Allah
Dakinta ya nufa ya ja ya tsaya yana tunanin yanzun dai may be ta yi bacima
A hankali ya yi knocking
Kamar jira take kasa kasa ta kashe wayar da take ta ce" Waye kuma? "
Tsam ya yi yana tunani, har ta kuma tambayar ko waye hakan ya sa a hankali ya yi gyaran murya yana jin wani abu na tsaya masa a wuyansa
Dirkowa ta yi daga saman bed din ta bude dakin tana wangale baki sannan tana kallon hannunsa ta ce" Lah, yaya ashe kai ne? "
Sai da ya saita muryarsa dan kar ta gane kamar yana cikin damuwa ya mika mata ledar yana kallonta ya ce" Bakwa karatu gobe ne? "
Da dan zumudinta ta leka ledar ta kuma kale shi ta ce" Muna yi yaya ai karatu nake "
Irin yanda ta fadi karatun take ya saka shi kasa yarda, dan kurawa fuskarta ido ya yi na dan lokaci, so yake ya ce da ita 'Bilkissu, ina fatan ba samari kika fara biyawa ba, dan kuwa karatu shine abinda nake so ki yi a rayuwarki koda zaki kula harkar maza sai daga baya' sai dai ya ji nauyin son fada mata hakan, to a kan me zai fada mata hakanma? Ita din kanta ta san ai yanzu bata kai kula samari ba, Bilkissun duka duka shekarunta 19 a dunia fa
Idannuwansa ya kara lumshewa a hankali ya ce" kina shiga ki kashe wayar, ki yi adu'a ki kwonta kin ji? "
Da mamaki ta kale shi, ita kam ta sha tambayar wai shin ana haihuwar mutun shi ba aljanni ba shi ba mutun ba? Yayanta yana fadin abinda take boye masa kuma ya fada daidai
Wata yar daria ta yi tana kallonsa kamar sabuwar halita har ya juya ya bar wajen
Turus ya tsaya gannin Kader tsaye ya harde hannunsa yana binsa da wani kallo
Sasauta yannayin tsukewar fuskar da ya juyo da ita ya yi ya nufe shi
Sai da ya tsaya kusa da shi sosai ya ce" Meye? "
KADER ya yi murmushi yana dan girgiza kansa ya juya ya nufi wajen da ya dora masa shayi mai ciyawa ya ziga shi sosai ya saka masa siga ya zuba masa cikin dan karamin kofi na kwalba ya juyo ya kawo masa
Amsa ya yi ya shiga surba a hankali yana kallonsa sannan yana sauraronsa dan ya tabata da magana a bakinsa
Sai da Kader ya ga ya kusan shanyewa ya ce" Me ya sa kaf cikin mata ita ta fi tsaye maka a zuciya? Me ya sa baka wasa da muradinta ko na second daya ne? Ko dai ita ce wace kake cewa ta fi mata hudu a duniyarka? "
Fuskarsa ya hade sosai yana kallonsa kafin ya mika masa abin shayin ya kara kausasa muryarsa ya ce" Idan kula da kanwata, kareta daga sharin dakarun samarin zamani, kafa kafa da tarbiyarta ya zama abin tuhuma ga mutanen zamani fine "
Yana gama fada ya juya ya nufi bangarensa yana dan girgiza kansa , baci yake so ya yi mai nauyi wanda zai huta ya hutar da du wata gajiya tasa da damuwarsa
.............................................
Agogon hannunta na kampanin Gucci ta kalla, sannan ta bi kawar tata da kallo
Murmushi ta yi mata a karro na ba adadi ta ce" BILKISS, minti talatin da uku kennan kina bani labarin DOCTER, bayan kin san nima ba makauniya bace ina ganni dukan abubuwan da kike zayano min a kansa, BILKISS na san tsadaden gaye ne, namijin abin son kowace mace ne, ke walahi wata ko ba sisi zata iya zama da shi!, abinda nake so ki gane kina cikin matsananciyar soyayar yayanki kin ki amincewa!"
Sakalai ta yi da baki tana kallonta, fuskarta ba kwaliya ko daya, gashin kanta kuwa ta shafa masa jel ta daure shi a tsakiyar kanta, hannunta dauke da agogo fari kar na farin karfe dan siriri mai kyau, sai dan zobenta siriri na azurfa wanda akai mata a Museum ta dan kara murza habarta yar karama ta kikifta idannuwanta ta ce" BAN SANI BA "
"Baki san me ba? " kawar tata ta tambayeta
Bilkissu ta ce" Ban san amsar tambayarki ba, ko nace hasashenki bai tabata a kaina ba ........dan karamin bakinta ta yatsina hakan ya baiwa kusan idannuwanta damar lotsawa kadan sannan ta kalleta da yannayi irin na takaici ta ce" ina mamakin ki Laila, ina mamakin irin yanda kike fasara yawan maganar yayana da nake a wata fasara daban, wai dama dan mutumen da ya tsaya maka a rayuwa ya zama abin wakawarka a dukan motsinka laifi ne? Ke, ke kadai kika san tsakanina da shi, ke dinma dan kin kasance mai yawan zuwa gidanmu ne, Laila dan kawai ina yawan waka maki mutumen da ya dora farin cikina, kulawa da ni da mahaifiyata a matsayin aikin da ya zame masa wajibi , shikenan sai ki yi min fasara daban? Nan idan inai maki maganar yayana ke ba ta Bishira kike min ba? Shikenan sai na baki wata fasara?"
Murmushi Laila ta yi tana dan girgiza kanta ta bar maganar a ranta dan kuwa bata so su yi halin, watau su yi fada daga zaunen nan kowa ya kama gabansa dan ba karamin aikinta bane kan gaskiyar da ta san gaskiya ce take takewa ta yi fushi a kai.
Ba su, su tashi daga wajen nan ba sai da lokacin tashi a makarantar ya yi baki daya sannan suka tashi suka koma kofa Laila ta tayata zaman jiran wanda zai zo daukanta domin yau bata zo da babur dinta ba
A hankali tsadadun yan matan wannan makaranta wato IPES suka ringa watsewa da samarin kowane na kama gabansa
An kusan karasa tashi daleliyar motarsa ta dallo kai, motar da take daya daga cikin motocin da BILKISS ke cewa idan ya shiga kwata kwata sai ya yi daban da yan africa
Daga zaunen da suke a saman kujerun da mai teburin kofar makarantar ya miko masu sunna dan zantawa sai Laila ta ji dif Bilkissu ta daina bata amsa, hakan ya sa a hankali ta kai dubanta wajen da ta tabata shi kadai zai iya garkame bakinta
Ita kanta sai da ta ji gabanta ya fadi domin kuwa shi din ne da kansa ya tuko kansa a wannan mota ya yi wani irin aski irin na samarin zamani wato gashin daga gaba sosai ya fi yawa sannan kamar wanda yake saka masa yambo bakikirin da gashin sai sheki yake, haka kuma irin zaman da ya yi ya dora hannunsa guda a saman sitiyarin motar ya wani lumshe idannuwa ya kafeta da ido abin ba'a cewa komai
Murmushi ta kuma yi gannin Ita Bilkissun ta shiga buda yar jakarta fara kar kirar snas tana dan duba abinda bata ajiye ba cike da basarwa sannan ta dago kanta,
A lokacin ta yi alamun ta ganshi, sannan ta mike suka gaisa da kawarta aminiyarta wace itama ta hau babur dinta tana kokarin tayarwa ita kuwa ta nufi motar
Tun da ta tunkaro yake kare mata kallo, tun daga takalmin kafarta mai tsini wanda ke dauke da fararan kafafuwanta tas tas kamar bata fito daga dakinta bama bale har a yi tunanin ta zo makaranta
Irin dinkin sket dinta da ya bi lafiyar jikinta ya yi mata das, sai farar rigar mai dogon hannu mai botirai wuyanta dauke da Nektie ya sha guga ya kwonta a wajen wuyan da ta bale botira biyu hakan har ya baiwa rigar damar dan budewa ,
Irin tafiar da take har ta karaso inda yake ta dora hannunta ta bude motar ta shiga ta zauna a gefen direba wato gefensa
Muryarta sanyaye, cikin sanyin da shi kadai take yiwa magana da ita ta gaishe shi tana mai bin hannunsa da kallo
Bai amsata ba, haka kuma ya kawar da dubansa daga kanta har sai da ya yi niya dan kansa sannan ya juyo gaba dayansa gefen da take zaune ya zuba mata lumsasun idannuwansa yanai mata kallon kasa kasa wanda da yawan lokuta yanai mata irin kallon nan ne idan ta yi masa wani laifi hakan ya saka ta sada kanta ta nitsu tana sauke ajiyar zuciya a jere a jere
Motar ya tayar sannan ya kama hanya yana jansu, wannan karron a hankali sosai hakan ya kara tabatar mata cewar akoy abinda ta aikata wanda yake son ta gano ta bada hakuri kafin ya gano mata
Dukan tunaninta, dukan caje kwakwaluwarta da ta yi ta gaza ganno amsar tambayarta, ta gaza ganno takamaimain laifin da ta yi, hakan ya saka ta dago da dara daran idannuwanta ta kai dubanta gefen kunnansa mai dauke da bakin sajen dake halaka tunaninta
Haka kawai ta ji idannuwanta na cika da kwallah, sosai ta masu rauraurau dan ta zubar da hawayen ko zata ji dama dama a cikin zuciyarta
Muryarsa a sanyaye ya ce" Idan kika yarda kikai kuka sai kin rama min hawayen nan da zaki zubar ko ta wani hali!"
Makot ta hadiye yawun fake daidai makogwaronta da sauri ta kai hannunta tana son maida hawayen tana sauke ajiyar zuciya har ya ja ya tsaya a kofar gidansu kasan manya manyan shukokin Dabinon dake bada sanyi
Sajen fuskarsa ya shafa a hankali ya juyo, sai da ya hadiye bacin ransa ya ce"
βπ»
πΎπΎπΎπΎπΎπΎπΎπΎπΎπΎ
*DUK NISAN JIFA*
_(K'asa zai dawo)_
πΎπΎπΎπΎπΎπΎπΎπΎπΎπΎ
_RUBATAWA_
*SAJIDA*
*SADAUKARWA*
*GA*
*MASOYA NA*
π«β¨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*π
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_π€
β *[ T.M.N.A]* β πποΈ
https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/
_Bismillahir rahamanir rahim_
3
Sai da ya had'iye b'acin ransa ya ce "Da kin san girman darajarki da baki yarda kin fito daga gida ba har sai kin saka nik'af, safa, da zumbulelen hijab d'in da zai b'oye ko ke wacece a idon duniya, Bilkiss da kin yarda cewar b'alle botiran gaban rigarki da ya zame maki sabo ba mutunci zai kankaro maki ba sai dai masu lek'e su lek'a masu zaginki su zaga ga kuma kin take maganar Allah!"
Irin yanda yake maganar yana dan shafa agogon hannunsa ruwan ash color ta maza da yannayin da fuskarsa ke d'auka a hankali tana kara yin ja irin ransa a mugun bacen nan yake, kuma abin daga cen cikin zuciyarsa yake fitowa yana amayarwa zaka gane abin na ci masa tuwo a kwarya, sannan uwa uba irin yanda ya d'auki doguwar magana har haka 'kok'arinsa, burinsa ya ganar da ita ta laluma ta yada zata fahimci