Showing 93001 words to 96000 words out of 180809 words

Chapter 32 - DUK NISAN JIFA COMPLETE HAUSA NOVEL

sajida   

02 Feb 2025

12989

sosai a cikin kalamanta

Najeeba ta zauna tana gige hannayenta bayan sun gama ta ce" Abu daya nake so da ke Bilkisu wanda na tabata ana fada maki shi a gida, zan kara maimaita maki, Bilkisu na cire maki kadara muguwar kadarar da bana yiwa koda makiyina ita ta fyade, aman bayan wannan Duk rintsi, du abin namiji, du masifarsa kar ki kuskura kar ki yarda ki nuna masa zaki iya bashi kanki dan soyaya ko dan kyansa ko dan arzikinsa, Bilkisu ko wani irin so kike hasashen kina yi masa daga bakin lokacin da ya nuna maki lalata ki kurce shi ki nuna masa daga nan ba ke ba shi!, Bilkisu kar so ya kaiki nunawa namiji alamun kina sonsa komai tsakaninki da shi koda kuwa *YAYANKI NE!* ki rike darajarki, ki rike girmanki, ki rike mutuncinki ta haka zaki wanye lafia da mazan zamani"

Bilkisu ta sauke ajiyar zuciya a hankali ta ce" In sha Allahu Aunty Najeeba zan kiyaye "

Najeeba ta yi mata murmushi tana amsar yar jaririyarta da ta farka ta gyara zara shayar da ita ta ce" Yanzu daga nan umarnin da na baki a matsayina na auntynki tunda kin yarda na zama auntynki shine ki je asibiti direct ki ce da yayanki kin biyo ku gaisa ne zaki je wajen biki "

Sai da gabanta ya yanke ya fadi da sauri ta zarro ido ta ce" Bikin wa? "

Najeeba sai da ta yi daria ta ce" Ba na kowa ba, kawai dai ki dan gaishe shi sai ki yi tafiarki gida ai ba za'a maki fada ba idan kin je wajensa ko? "

Bilkisu ta mike ta yi tsaye gaban madubi a yannayi na tsoro ta ce" Ni Bilkisun Jauro na jewa yayana wajen da ya hanna min yawan shiga dan ya ce waje ne da ya tara mutane kala daban daban maza sosai da mata sai idan da shi ne, ko da shi din sai na saka hijab yau na je masa a haka kusan tsirara? "

Yanzu gaba dayansu suka saka dariar Bilkisu ta yarfe hannayenta ta ce" Marina zai yi, ya yi kwalo da ni koma ya ce zan halaka shi "

Najeeba ta kara sakin murmushi ta ce" Ai halaka shi nake so ki yi !"

Bilkisu ta kara kallonta a sanyaye ta ce" Aunty Najeeba, ina jin tsoronsa walahi, kuma bana son na saka shi a damuwa ko kadan, kin ga baya son hada rigimata da ta kowa, kuma ni ban taba yi masa haka ba "

Najeeba ta ce" Zo ki zauna "

Bilkisu ta koma ta zauna kusa da ita tana kallon kafar yarinyar dake ta wutsil wutsil abinta fara tas kamar farin tsohonta gata katuwa masha Allah

Najeeba ta ce" ki gane, garage ba laifi bane idan har ana yi ana duba bakin gatari, shi wani lako lako ba shi zai kaiki ga ci ba, na san damuwarki dan ni shekaru na shafe a cikin irinta ba tare da na san ita ke damuna ba har sai da na wayi gari na ga ya fito daga dakin watata na yanke jiki na sume dan shirme!, Bilkisu, bana so tafiarmu ta samu tangarda Allah yana ganni ban amshe ki ba sai da na ga take taken yayanki a kanki wanda idan har haka ta ci gaba da faruwa kina da saurin salamawa abu, baki da karfin kokowa da shi, ya kuma san lagonki shi yasa ya dora dokoki irin haka, ba aikin banza zaki yi ba, aman ki san ciwon kanki ta hanyar samawa kanki salama koda a cikin zuciyarki ne, kar ki ji komai, kuma ki jure komai ciki harda hayaniyar duniya , ke dai ki tashi ki je wajen yayanki"

Bilkisu ta sauke ajiyar zuciya muryarta a sanyaye ta ce" A babur na fito aunty "

Najeeba ta kara sakin murmushi ta ce" Hakan shi ya fi komai birgeni bara a kawo maki gilas wanda zai hau kayanki"






................to madallah............


*IN SHA ALLAHU IDAN MUN KAI AURE YAK'IN MATA PAGES 20 ZAMU TSAYAR DA FREE , DOMIN AURE YAKIN MATA NA SIYARWA NE, DU MAI SON TURO DA KATINTA KO TA TRANSFER YA TUMTUBENI TA NUMBERMA KAMAR HAKA 93 81 16 18, sannan zamu dakatar da Duk Nisan jifa har mu gama Aure yak'in mata na gode*
[7/24, 10:19 AM] BAK'A CE: 🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾
*DUK NISAN JIFA*
_(K'asa zai dawo)_
🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾

_RUBUTAWA_

*SAJIDA*

*SADAUKARWA*

*GA*

*MASOYA NA*


πŸ’«βœ¨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🀝

β˜† *[ T.M.N.A]* β˜† πŸ“–πŸ–ŠοΈ

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_


Alhamdulillah, munsan Allah ya azurtamu da masoya masu d'umbin yawa a k'asarmu Niger da d'ayar K'asarmu Nigeria harda ma sauran kasashe na nahiyar Africa.

Ina masoyan *Sajida* da *Samira* littatafansu??? Marubutan nan masu rubuta littafin *Bak'a ce, Mage* da *Badak'ala, Allura ta tono Galma* wanda kuke kauna har cikin ranku. Ku matso kusa don nuna musu d'umbin soyayya da kaunar da kuke musu inda suka zo maku da sabon littafinsu mai taken *AURE YAK'IN MATA* daga jin sunan kunsan cewa littafin kunshe yake da darussan rayuwa wadanda suka shafi rayuwarmu ta aure,kalubalen da mata ke fuskanta a gidan aure da kuma yanayin zamantakewar aure na zamanin yanzu, duk da ba sabon abu bane, amma namu ba irin nasu bane, sai an gwada akan san na kwarai.

Ga mai bukatar wannan littafi *Farashin mai sauki ne* naira dari uku (300) kacal ga yan Nigeria, yan Niger kuma dala dari ne (500)πŸ‘Œ zaka samu wannan littafi mai dubbin darussa a cikinsa.

_Domin tura kudin siyan littafin ga yan Nigeria sai a tura ta wannan account number din *2377403479* Khadija Umar Abubakar. Zenith Bank. Kuma akwai damar tura kati ta wannan lambar *081-686-594-14* IDAN KA YI TRANSFERT SAI KA TURA SHAIDA TA WANNAN NUMBER +227 93 81 16 18._

_'Yan Niger kuma sai ku tura katin MOOV ko Airtel ta dala dari watau 500 francs ta wannan lambar *+277- 94-98-56-52*_

Mun yadda daku, mun aminta da irin kaunar da kuke muna don hakan muna da yakinin cewa zaku siya don nuna mana kalar soyayya da kaunar da kuke mana da littafanmu.πŸ₯°

🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾


36



Kamar da wasa aka kawo mata wani dan siririn gilas fari tas mai kyau ta saka ta dauki jakar laptop dinta bayan ta saka kayan makarantarta cikin jakar ta yi masu salama da katinta ta koma wajen babur dinta

Sosai take jin gabanta na faduwa na zuwa wajen yayanta a irin wannan yannayi, aman maganar nan ta Najeeba ta fi komai tsaye mata a rai wace ta ce ' tun a gidan iyayenku kun nuna masu dama ba maganar ketare maganarsu, sai an je gidan aure zama ya yi zama aka ga halayen kowa a bayane sai ku ce zaku tsiro da bijirewa umarninsu irin na idan suka hanna ku zuwa gaishe da iyayenku, zuwa yan bukukuwan dangi ba na kulun ba, daidai da dan abin ihsanin da zaku kai ya fara gagara, kai bale masu nunawar nan su saurayin kawai suke so bayansa basa son komai din nan, a zo yana samu din aman tuni ya gama sakawa ransa koda bai ciyar da ke ba ke din mamar soyaya ce zaku soye abinku soyayarku ta ishe ku ku rayu, sai ya zo ya fara gannin wata sabuwa wace ke son ya mata dan dinkin sallah, wace ke son ta ringa dan samun abinci mai dan kyau koda ba kulun ba, wace ke son ta ringa zuwa gannin iyayenta mai yiwuwa ba karfi ya kare sunna gajiyar da suke da bukatar taimako aman ba hali baki koya masa ba sai rana tsaka du ki fito da abubuwan nan dole a dawo a fara gannin bakin junna ke da laifinki na sangartar da shi da kasa nuna masa darajarki, ba cewa aka yi ki ringa roke roken maza ba aa, aman kar ki zamanto mai katse masa hanzari idan ya maki kyauta, wannan shishigi ne mai sakawa nadama domin kina tufkawa kanki muguntar da ba zaki iya katsewa bane!, idan kuwa dama bai san badawar ba in kika je ke kika gano!, shi kuwa marar tsoron Allah ya kilace ki ya dauko ki kwaskwaskwas da ke ya hanna maki fita nema ya hanna ki karatun ya kuma rike aljihunsa a haka dan rashin imani har zai so ya nuna kin cenza kin lalace kamar ba ke ba bayan ya manta ba haka ya dauko ki ba, ba suka kike yi tana maki yayafi ba dole sai da gyara!' Sai kawai ta samu kwarin gwuiwa ta babura babur dinta bata zame ko'ina ba sai kofar tangamemen asibitin

Sai a lokacin ta duba agogon wayarta bayan ta tsaya gannin a rufe watau lokacin budewar yama bai yi ba

Lekawa ta ringa yi dan gannin mai tsaron kofar na yau
Ai kau ta ganshi hakan ya sakata sakin murmushi ta karasa wajen kofar a nutse ta gaishe shi

Kallonta yake shima dan har ga Allah ya so shaida mai masa gaisuwar mutuncin nan aman yau din da ya ga ba katon hijab duda ta saba zuwa a babur sai ya so bacewa

Murmushi ta yi ta ce" Kaca nice Bilkisu Hamana ko ya koma gida ne? "

"Kai" ya ce yana ruko ido sai kuma ya ce" Uban wa, wai dama ke ce hajia? Kai lalle masha Allahu, ai ban shaida ki ba walahi bara na bude maki yana ciki likita ai yau tun da ya shigama ban ga fitowarsa ba oga Kader ne ya yi fita ya kai sau uku a raina ina ayana shi kam oga kader kamar mai zaburi leka a kugu "

Ita dai tunda ta samu ya bude mata karamar kofar sai ta bara masa babur din ta rataya jakarta duda tana da nauyi aman ta saba sai wayarta dake hannunta

Dinkin nan ba na fitar tsiraici bane, ko daya ya fan kamata dai ne sannan ba wai dan bata saba fita da kannanun kaya bane aa, irin wajen nan ne bata saba zuwa da shiga irin wannan ba , hakan ya sa take tafe cikin sando tamkar tana gudun a kamata

Kader dake zaune tare da wasu sojojin a kasan shukar mangwaro sunna hira sunna kuma kula da aikinsu suka hangota

Dayan ne ya yi fito ya ce" Akoy mata a damagaram, shagun kuma walahi sun iya kwaliya duba ka ga wannan babyn "

Sauran da basu ganta bane du suka kai dubansu wajen da aka yi maganar

Kader gaba daya ya saki baki da hanci harda daga hannunsa daya ya dora saman kansa a fili ya ce" Balaki, yau akoy balaki a wajen nan "

Mikewa ya yi da sauri ya tarbeta ya tsaya a gabanta bakinsa bude ya ce" Bilkisu hala giya kika sha? "

Bilkisu ta kikifta ido tana dan matse kafa kamar tana jin fitsari ta ce" Walahi yaya Kader nima a tsorace nake dan Allah juyani na koma gida dama sai da na ce mata tsoro nake ba zan iya ba "

Kader ya ce" Wace ?

Ta kara yarfe hannunta ta ce" Gimbiya ce ta ce na fara biyiwa ta nan sai da na ce da ita kwaliya ce na yi baya son haka ka ga da hijabina a cikin nan bara na saka "

Kader ya yi gagawar cewa" Aa aa, ba zaki saka ba, mu je kawai ba abinda za'a yi in sha Allahu "

Gaba ya yi yana bubudewa hankali kwonce tana biye da shi har suka karasa wajen office din

A nan suka ja suka tsaya, a hankali ya ce mata" Buga ki shiga mana "

Ido ta zarro ta make kafadarta ta rage muryarta ta ce" Kai ka buga mu shiga mana "

Kader ya ce" To ai ba ni na zo nemansa ba, a kan me zaki tura ni? "

Bilkisu ta kara turo bakinta gaba ta ce" Ka ga yaya Kader sai an jima walahi bara na tafiata "

Sunna musun nan aka bude office din docter Halima ta fito rike da takardunta bayanta da nurse biyu sai muryarsa cen kasa kasa ya juyo ya ce" Docter ?"

Maganar ce ta tsaya masa a lokacin da ya dora idannuwansa a kansu sunna tsaitsaye sun yi cirko cirko
A hankali ya lumshe idannuwansa sakamakon bugawar da zuciyarsa ta yi ya kuma budewa a kanta

Docter Halima ce ta dawo ta ce" Na'am sire"

HISHAM ya kasa furta koda A daga bakinsa sai da Kader ya dan mika hannunsa daya ya rike kofar ya rike kugunsa da daya da dan daga murya ya ce" HISHAM ana magana"

Da sauri ya juyo ya dora dubansa a kansa, sai kuma ya dora a kan Docyer Halima, kwata kwata manta abinda ya yi niyar fada mata ya yi hakan ya saka shi binta da kallo kafin da yan yatsunsa ya mata nuni da tana iya tafia

Kader ya saki kofar a hankali ya ce" To fah, ni na koma "

Zungui zungui ya bi ta gaban Bilkisu wace take jin fitsari ya kama mata mara taf wanda kwata kwata bata jinsa a dazun yanzu yanzu ne ta fara jinsa kuma har irin kamar zai zubo matan nan.

Kasa motsawa tayi sai hannayenta duka biyu data rik'e hannun jakarta tam tana ta cumimiyeta, a hankali kawai take d'an wulk'ita idonta ta hakan ne zaka fahimci bata suma a wurin ba, wannan jarumtar da gimbiya tayi maganarta take son arowa amma abun ya ci tura.

Da farin kam kallon mamaki ne yake binta da shi, wato har an fara darasin ko? Sai kuma daya fahimci wasu abubuwa a yanzu sai y'a shiga jifanta da kallon "Amma Bilkisu zaki ci gidanku yau." Yasan a bΓ’bur ta tafi, to kenan a kan shi ta dawo ta keto ta cikin garin a haka? Kwalliya fa ce ta rangad'a a fuska sannan ta fito ba hijabi.

A hankali ya shiga gyara fuskarshi daga kallon zai ci mutumcin ta nan zuwa wallahi kuka nake ji, har ga Allah yanda yayi da fuskarshi jira kawai yake ko da k'uda ne ya gifta ta gabanshi ya bashi damar yin kuka, yo ina dalili? Yana zamansa a nutse zata wargaza masa lissafi.

Yanda kalaman gimbiya Najeeba suka shiga kunnuwanta ne a lokacin yasa ta k'arfin halin d'aga k'afarta da k'yar ta shiga takawa zuwa office d'in, saida ta tsaya gaban table d'in idonta dake cike da tsoro na cikin nashi dake d'auke da sirkin ja na tashin hankali, d'an leb'enta da yasha kala yana wani mutsu mutsu kamar kayi kukan kura ka jefashi a bakinka ya kafe da ido sanda ta bud'a ta shiga kakkarwa tana had'a kalaman wajen fad'in "Hamm..mana..barka...dddda."

Shiru tayi ta had'e yawun da take jin su kansu sun mata nauyi tace "Da... Aiki."

Wani iska ta furzo kamar wacce dole aka tilasta mata fad'an maganar, a sannu ya d'an k'yabta idonshi zuciyarshi na tambayar "Dama abin da ta zo fad'a kenan?"

Wani tari ne ya kubce mishi kamar wanda aka sark'e, jujjuayawa ya shiga yi neman ruwa, da sauri ta kai hannunta dake rawa ta d'auki kofin tangaran d'in dake rufe da yar farar takarda kakkaura ta mik'o masa, hannun ya fara kallo mai kama dana jarirai kafin ya kalli fuskarta. Wani k'arfi ne yaji ya zo masa a lokacin hakan yasa shi zabura ya mik'e tare da zagayawa zai nufi inda take.

Har yau dai kalaman gimbiya Najeeba ne suka dawo mata daya sakata tsayawa bata gusa ba, saidai rashin sabon wannan yanayi yasa ta rintse ido gam ta turo leb'enta na k'asa ya fito ciki, saida ya zo daf da ita kuma saiya tsaya cak, da k'arfi k'arfi ya karb'i kofin ya juye a kan shi da yake jin tsakiyar na tafarfasa.

Bud'a idon tayi jin ruwa sun zuba a k'asa har sun waltsa a k'afafunta, kallon fuskarshi tayi a lokacin kai kawai yake girgiza mata, numfashi ya shiga saukewa ba adadi kafin ya damk'o hannunta da k'arfi hakan yasa ta gusawa daga inda take ta matsa daf dashi sosai.

Numfashin da yake fesowa mai had'e da gumi duk a fuskarta ya shiga saukeshi, kamar zaiyi kuka cikin rikitacciyar murya yace "Billy mutuwata kike da buk'ata? Fad'a min dan Allah kin gaji dani ne?"

Tsuru ta masa tana kallonsa dan yanzu kam ya fara bata haushi, dan in ya shiga yanayin nan ranta b'acewa yake da tunanin me yasa baya iya fad'a mata komai to?

Sakin hannunta yayi ya juya gaba d'ayansa da k'arfi yana fad'in "Shiiiit!"

A hassale ya sake juyowa kamar zai mareta cikin d'aga sauti yace "Saida na ce a'a Bilkisu, saida na nuna bana so, amma..."

Nunata yayi yace "Dubeki fa, tsokanata kika zo kiyi? Ni abun wasanki ko?"

Jinjina kai yayi tare da juyawa ya d'auki lotus akan table d'in ya sake matsowa daf da ita, sam ba tare da saninshi ba a rikice ya jawo k'ugunta ya had'a da nashi, fuskarta ya kalla tare da saka lotus d'in nan ya fara kaiwa a kan bakinta dan goge Jan bakin nan dake k'awata mishi bakinta yana neman kauce hanya.

Me Bilkisu zatayi sai kawai ta saki wani marayan kuka cikin sigar shagwab'ar data zama d'abi'arta tare da yarfa hannayenta kamar zata rumgumoshi ta baya, da sauri ya saketa dan bΓ’ kuken ne ya dakeshi ba sai neman taso da fitinar da take, saidai a banza domin kuwa bata daina ba sai ma k'afafu data shiga bubbugawa tana fad'in "Shikenan Hammana ya daina so na yanzu, ni fa wanen biki ne zanje shine na ce bari na kawo maka gaisuwata, ashe nayi ba daidai ba? Shine zaka kamani da fad'a haka."

"Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un." Ya shiga maimaitawa a kan labb'enshi, sunkuyawa yayi ya dire hannayenshi a kan teburin kanshi k'asa ya dafe sosai, ya jima haka kafin ya d'ago a sanyaye ya kalleta, k'wafa yayi yace "Zaki koma gida yanzu, bikin ko na 'yar gidan uban waye ba zaki je ba, ke Bilkisu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login